MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  True Hausa Novels

Chapter   13 / 58

36K to 39K   out of 171.2K words

fice. Kusa inda nake zaune yaya Majid ya zauna yana fuskantar Anty Zakiyya sosai tare da jifan ta da kallon da yafi kama da na tuhuma ya ce"yaya jikin na kin kike jinsa yanzu?"


Sai da ta haɗiye kuoan da yake shirin fin ƙarfinta ya fito waje kafin ta sama damar cewa dashi"da sauƙi".


"Allah ya ƙara sauƙi".


Da amin na amsa dashi ban da Anty Zakiyya da izuwa yanzu hawayen da take danne fitowar su suka fara gudu a tudun fuskarta cikin kukan take faɗin"yaya Majid dan Allah ka sanar dani shin zantukan da kunnuwana suka jiyo min daga bakin Umman Salma akan ina ɗauke da ciki gaskiya ne?, ko kuwa zafin ciwo ne ya haifar min da jiye jiyen abubuwan da basu afku ba". A tare muka sauƙe numfashi da yaya Majid kafin shuru ya karaɗe ɗakin sai can yaya Majid ya katse shurun ta hanyar faɗin"ki kwantar da hankalinki Zakiyya anyi miki gwaji kuma babu inda ya nuna cewar kina ɗauke da juna biyu, daman nasan ƙarafi ne kawai suke ƙoƙarin yi miki zuciyata ba zata taɓa yarda da cewar wai ke ɗin za ki aikata haka ba amma lokaci ya yi da zan nuna musu kuskuren da suka daɗe suna yi".




Cikin mu babu wanda ya amsa masa da hakan ya bashi damar miƙewa tsaye tare da zura dukkan hannunwansa cikin aljihun dogon wando kalar ruwan ƙasan dake jikinsa yana ɗaura da faɗin"ku fito mu tafi bari na biya sauran kuɗin gado dana magani".


Yana dasa aya ta fice ba tare da ya jira amsar da zamu bashi, kallon Anty Zakiyya nayi da ta kwantar da kanta jikin matashin dake bayan ta ta lumshe idanunta da suka yi wani irin mungun rama a sanyaye nake faɗin"Anty Zakiyya ki kwantar da hankali bakya ɗauke da komai, ki cire damuwar komai daga ranki ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah domin shi ne kaɗai zai iya miki abinda koda duniya da abunda yake cikinta sun haɗu ba zasu iya yi miki ba. Ta yaya ma za'a ce kina ɗauke da ciki abinda ba ruwa ake shan sa ba balle ace kin sha cikin ruwan randa". Bata ce dani komai ba illa sauƙe numfashi da take yi wani nabin wani ban gusa ba na cigaba da kwantar mata da hankali da tausasan kalaman da nake da yaƙinin zasu yi tasiri a cikin zuciyarta.


Dawowar yaya Majid shi ya sanya mu tashi muka fito ina riƙe da hannun Anty Zakiyya muka hau abin hawa muka nufi gida, muna isa muka sauƙa muka shiga muka bar yaya Majid yana biyan kuɗin mai adaidaitan, tun daga zaure muke jiyo hayaniyar da ƙaragin da yake dukan ƙofofin kunnuwan mu babu ƙauƙautawa har muka ƙarisa sashin namun da muke jiyo hayaniyar daga cikin sa.


"Sharri aka yi mata?, ni dai wallahi ban yi lalacewar da zan zauna nayi wa sa'ar ƴar cikina sharri ba da girma na. Kowa ya ga irin rashin lafiyar da Zakiyya take yi a cikin gidan nan yasan da cewar ciki take ɗauke dashi domin duk laulayin masu ciki babu wanda bai bayyana a gare ta ba, daman ai ni nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya wacce ta kasa auruwa ai dole ta sama karuwar cikin gida".


Furcin Umman Salma kenan da suka fara yiwa ƙofofin kunnuwan mu sallama, tunin ƙafafuna suka yi sanyi suna rawa da ƙoƙarin yasar dani a ƙasa, da hanzari na ƙara ƙarfin riƙon da nayi wa hannayen Anty Zakiyya dake cikin nawan kafin nabi jama'ar dake wajen da kallo da na lura da har yanzu basu farga da shigowar mu cikin gidan ba.


Dukka matan gidan mu ne tsaitsaye a wajen illa Umman mu da Hajiya da ban gansu tsaye a wajen ba, sai kuma ƴaƴan su da suke tsaye cirko-cirko har da Abasiyya da gobe zata koma gidan mijinta. Kyakykyawan ajiyar zuciya na sauƙe tare da haɗiye wani miyau da ya wuce mini ta maƙoshi da ƙyar na buɗe baki da nufin cewa wani abun yaya Majid ya shigo idanunmu suka sarƙafe cikin na juna ƙirjina ya buga da ƙarfin ina addu'ar Allah ya sanya bai ji furcin na Umman Salma ba domin yanda naga idanunsa sun ƙara canja launi.


Sai a sannan suka lura da mu Salma ta nufo mu da ɗan hanzarinta tare da cewar"kun dawo?".


Cikin mu babu wanda ya tanka mata, illa yaya Majid da ya tako ya cire hannun Anty Zakiyya daga cikin nawa ya riƙe tare da ɗaukar hanyar ɗakin Umma ina biye dasu duk suka zubo mana na jiyamun su suna raka mu dashi.


"Zinaru ai kuwa dai gaskiyar ki ciki ke cikin Zakiyya tunda ga jini yana bin ƙafafunta, ba mamaki zuwa suka yi aka cire ciki sun faɗa layin masu tsoron kunyar duniya sama da ta lahira".


Cak muka tsaye yaya Majid yana ƙara matse hannuwan Anty Zakiyya dake cikin nasa da matuƙar ƙarfi kafin ya laune leɓɓansa da matuƙar ƙarfin gaske yana runtse idanunsa, tare da fitar da wani hucin daga bakinsa da ya tsorita ni matuƙa gaya. Da ƙyar na cira kaina na bi Anty Zakiyya da kallo matuƙar razana ya bayyana a fuskana domin tabbas jini ne ke bin ƙafafun Anty Zakiyya ga zaninta ta baya da ya ɓaci kasancewar hijabinta ya ɗan ɗage. Fisgan da yaya Majid ya yi mata ya ƙara jefa ni cikin firgici bai tsaya ko'ina ba sai gaban Umman Salma da Umman su Anty Kubra da tayi furcin.


Ganin baya cikin hayyacinsa ya ma kasa magana illa jijjiga kansa kawai da yake yi har yanzun yana cire da leɓɓansa, nayi saurin isa gare shi ina faɗin"dan Allah kayi haƙuri yaya Majid ka kyale su kazo muje, meye zai ɗaga maka hankali bayan mun san cewar bata ɗauke da juna biyu a tare da ita dan Allah ka bari kazo muje kawai".


Na ƙare zancen ina sakin hawayen da suka wadaci kurmin idaniyata tare da jan hannunsa, kafin ya ce dani wani abu Umma ta fito ta fito daga ɗakin ban yi zaton tana cikin gidan ba kasancewar ban ganta a wajen ba isowa gare mu tayi haɗi da faɗin"Majid wuce ɗaki ka jira ni".


Bai ce komai ba ya wuce ɗakin dake da kansa da jijiyoyin kansa suka shimfiɗa raɗau-raɗau a saman goshin, riƙo hannun Zakiyya tayi kafin ta kallo ta ce"wu muje".


Ta wuce gaba muna biye da ita har cikin ɗakin ina iya jiyo shewar da suka saka yayin da muke shigewa ɗakin dashi, zaunar da Anty Zakiyya tayi tare da riƙo dukkan hannayenta ta sanya cikin nata kafin ta cilla idanunta cikin nata tana cewar"yaya jikin nakin?".


Maimakon ta bata amsa sai ma fashewa tayi da wani irin azababben kukan da sautin sa ya karaɗe dukkan ɗakin kafin ta furta" Umma wallahi ban aikata ba Umma ban zubar da mutuncina ba ban wofantar da tarbiyar da kika bani ba ban kuma kauce daga gwadaben da kika ɗaura mu ba ki yarda dani Umma wannan jinin kuma wallahi al'adata ce tazo tun a asibiti naji alamunta ban yi tinanin ya ɓata min jiki har haka ba".


Ta ƙare tana ƙara fashewa da wani matsanancin kukan tana kifa kanta akan cinyar Umma, a hankali take bubbuga bayanta cikin sigar lallashi kafin ta ce"kiyi shuru Zakiyya har cikin zuciyata ban yarda da wannan zancen nasun ba domin ni nasan irin tarbiyar da na ba wa ƴaƴana, duk da ba'a shaidar ɗan yau amma ina da yaƙinin cewar ba zasu taɓa kaucewa hanyar da na ɗaura ku ba don haka ki kwantar da hankalinki".


A hankali sautin kukan natan yake raguwa illa ajiyar numfashin da take sauƙewa kamar zata sheƙe, ɗakin ya ɗauki shuru kafin yaya Majid ya katse shi da faɗin"Umma Zakiyya bata ɗauke da komai domin munje asibiti anyi mata gwaji gama takardan nan a hannuna likita ya tabbatar mana da maleria da taifot ne ke damun ta".


"Na sani Majid na sani daman shashi faɗi ne kawai irin nasu, duk ku kwantar da hankalin ku musamman kai Majid da kayi matuƙar fusata akan lamarin".


Sai da ta ɗan tsagaita kafin ta ɗaura da"Iyayenku maza sunyi ta neman wayarka domin jin asibitin da kuke je amma baka ɗauka ganin ka ya sanya su fita neman ku, ki tashi Na'ima ki saka mata ruwan wanka tayi tsaftace jikinta". Jikina a sanyaye na miƙe na fice kamar kazan da kwai ya fashewa a ciki.


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________




Page 5⃣4⃣




Koda na fito fillin tsakar gidan toshe kunnuwana nayi tare da shafe idanuna a ƙoƙarin gujewa kaina gani ko jin wani abun da zai kuma baƙanta mini rai da ruhi, wuta na fara ƙoƙarin haɗawa Hajiya ta katse ni da tambayar meye zanyi na sanar da ita cewar ruwan zafi zan ɗaura ta ce akwai a ɗakinta a flask ta shiga ta ɗauko mini, tare da ita muka dawo ɗakin Ummata muna zama yaya Majid yana ficewa Hajiya ta raka shi da ido haɗi da faɗin"babban mutum kenan tsoho mai ran ƙarfe ya fusata sosai".


Sauƙe numfashi Ummata tayi kafin ta furta"yanzu ma faɗan da nake yi masa kenan, a matsayinsa na babban bai saurin fusata da fushi bai kamace shi ba".


"A'a Aminatu kyale shi ya yi abinda ai da can da ba'a taɓo shi ba bai yi ba, ko yanzun ma da dalili. Ni wallahi da nice nake da wannan santalelen saurayin babu wanda ya isa ya taka ni cikin gidan nan ya kwan lafiya yanzu dai yaya jikin Zakiyyan?".


"Alhamdulillah da sauƙi wanka ma zata yi yanzu don ta sama ƙarfin jikinta sosai".


Sosai take yiwa Anty Zakiyya sannu a kai a kai har ta fice izuwa banɗaki bata daina ba, idanunta ta komar kaina tare da cewar"ke kuma kukan ya isa mana uwar masu gida".


Sai a sa'ilin na farga da cewar hawaye ne suke kwance mini fuskana, nayi saurin kawar dasu ina rusunar da kaina ƙasa da hakan ya ba wa Hajiya damar ɗaurawa da"ki daina wannan kukan domin bashi bane mafita in za ki tashi tsaye ma tun wuri ki tashi ki san inda yake miki ciwo ki kwaci ƴancinki a hannunki, duk wanda ya ce miki kule ki kalli cikin idonsa kice masa cas a wani dalili za'a dunga ci muku kashi kuna kyale wa".


Murmushin da yafi kama da na yaƙe kawai nayi mata ina wasa da yatsun hannuna maganar da Umma ta soma yi ya sa ni ɗago kaina kaɗan ina kallon fuskarta.


"Falmata kenan ai haƙurin dai shi yafi domin duk wanda ya rungume su to haƙiƙa ya rungumi nasara ya kuma ɗauki hanyar ɗaukaka".
Taɓe baki Hajiya tayi haɗi da cewar"ai wani haƙurin ma cuta ne wallahi musamman irin naki Amina ai yiwa ƴarki ƙazarin cikin shege amma kice wai haƙuri, in ce dai sanin haƙurin zaku yi akan komai shiyasa suke yi muku komai zuƙatan su suka raya musu kun zamto tamkar jujinsu da suke watso muku shara. Allah ma ya sani wallahi nikam Falmata ɗiyar Babagana da Yalwa jinin kanurai ba zan ɗauki wannan cin kashin ba duk wacce ta nuna mini ɗan yatsa sai na sauƙe shi kamar yanda duk shegiyar da tayi min kan ice to ni sai nayi mata na rodi ina dalili".


Yanda ta ƙare zancen a fusace kaɗai ya isa ya tabbatarwa mai sauraron ta ta kai ƙololuwar gejin ɓacin rai, ban yi mamaki ba domin sanin kowa ne a cikin gidan mu babba da yaro Hajiya bata ɗaukar wargi sannan wandon roba ce dai-dai ƙugun kowa shiyasa zai yi wuya kaga sauran matan da ƴaƴan su suna shiga shirginta rayuwarta take yi na ƴancin kai da mutunta kanta ta hanyar janye jikinta daga lamarin da bai shafe ta ba, kasuwancinta take yi babu ka hannun yaro tana sayar da turarukan wuta kasancewar ta jinin kanurai da suka san sirrin ƙamshi wannan halayyarta tan da suka yi kamanceceniya da ta Umma ya sanya suka fi kowa shiri a tsakanin raguwar matan gidan mu, kuma ni shaida ce soyayyar Hajiya gare mu babu sirki domin sam babu algus a cikinsa balle ya gauraye da wani abun.


Murmushi kawai Umma ta sarka mata, nikam tashi nayi domin na basu waje na wuce ɗakinmu tare da zare hijabina kafin na fito nayi alwala na haɗe sallan zuhr da asr nayi su na daɗe ina lazimi akan sallayan kar izuwa sa'ilin da Salma ta shigo tana sanar dani su Abba suna nema kowa a sashin su.


Dam dam ƙirjina ya bada domin bana buƙatar neman ƙarin bayanin ko ba'a faɗa mini ba nasan wannan zaman ma akan mu ne, tunin naji hawayen da ban dalilin su sun ciko mini kurmin idaniya na miƙe da ƙyar na saboda ciwon da jikina yake yi mini na rufawa Salma baya.


Maƙil falon yake cike da jama'ar gidan mu da Allah ya albarkace mu ta wannan fanni alhamdulillah, zama nayi ina gaishe dasu Abba suka amsa mini a gajarce ganin kowa ya hallara har da su manyan ƴaƴanmu da suke gidan aure da kuma Goggo Suwaiba ya bani tabbacin ni ce ƙarshen zuwa falon.


"Mun tara ku a nan ne domin wata magana mai matuƙar muhimmancin da muke buƙatar ayi ta a gaban kowa da kowa, domin ba zamu ɗauki wani abun ba kuma da ya ƙetarewa hukucin da zamu zartar yanzu balle muyi amfani da wannan kalmar ta haƙuri ko afuwa duk ba zasu yi tasiri ba, don haka kowa ya kasa kunne ya ji ni da kunnuwan basira".


Furcin Baba kenan da ya ƙara nutsar da falon shuru ya karaɗe ko ina tamkar babu wasu halittu masu motsi da suke zaune a cikin sa, sai da ya numfasa na tsawon daƙiƙun da ba zasu gaza biyar ba kana ya ɗaura da cewar"game da abinda ya faru ɗazu akan jinyar Zakiyya da har wasu daga cikin ku masu rangwamen tinani da ƙarancin hankali gami da hangen nisa da rashin sanin darajan kai balle tinanin kun girma suke yi mata ƙazafin cewar ciki ne a jikinta don haka yanzu muke son su faɗi shaidar su na faɗin hakan ko kuma hujjar da zasu kare kansu dashi, domin bincikan likita ya tabbatar da babu ciki a jikin Zakiyya hasalima malaria da taifot suke damun ta".


Ya ƙare zancen karkaɗa farar takardan dake ɗauke da sakamakon gwajin da aka yiwa Anty Zakiyya a asibiti, tsif falon ya kuma yin wani shurun da hakan ya ba wa Baba ƙarami damar faɗin"ke Zinaru ke muke saurara domin ke kika yi wannan zancen na cewar jiki ne a jikin Zakiyya, har kina faɗin duk alamomin masu laulauyi sun bayyana a gare ta".


Tsuru Umman Salma tayi da ido tamkar shege a rabon gado, kafin ta furta" ni kuma inji uban waye?, wallahi malam sharri ake son maƙala min".


"Zinaru kin san dai wallahi na wuce inyi miki ƙarya da girmana da komai, akan idona kika furta wannan kalaman cike da tabbaci kuma yanda kika faɗi haka nan nazo na juyewa su Yaya babu ragi balle kuma ƙari amma yanzi kice sharri za'a yi miki".


Goggo Jummai ta faɗa idanunta kar akan Umman Salma da take zuffa Baba ya ce"ba ɓata lokaci bane ya tara mu a nan masalaha muke son samarwa wannan iyalin, shin Zinaru anyi hakan ko kuwa?".


"E haka ne na faɗa amma wallahi sharrin sheɗan ne da kuma kuskuren harshe dan Allah malam kayi min aikin gafara har dalilin hakan ka turbuɗe igiyoyin auren mu da suka rage saura ɗaya da shima yake reto ".


"Ke ce babbar sheɗaniyar kuma sheɗaniyar kanta da kanta". Hajiya ta furta rai a matuƙar ɓace, sai a sannan Abba ya furta"to alhamdulillah tunda kin amsa laifinki ki kwantar da hankalinki babu abinda zai taɓa igiyoyin aurenki sai dai hukuncin da za ki fuskanta".


Rushewa Umma Salma tayi da kuka tare roƙon Baba ƙarami da ya rufa mata asiri kar ya ce zai sake ta bisa wannan dalilin. Hajiya Babba da tun ɗazun bata ce komai ba sai yanzu da ta furta"Zinaru ai ba kuka bane ya kamace ki idan kina da rabon hankali to izuwa yanzu dai ya dace ace kinyi shi ga ƴaƴa a gabanki har da jikoki amma har yanzu ba ki san annabi ya faƙu ba. Wai ku sai yaushe ne zaku yi hankali kunsan cewar kun girma yanzu ba ƙananan yara bane ku?, Zakiyya ai kamar ƴa take a wajen ki yanzu inda Salma ce ko kuma Dijama za ki so kiji wani yana jefar su da wannan mummunan zargin koda kuwa bare ne balle makusancin su?, abinda ba zaka so ayi wa naka ba ya dace ka guji yiwa wani kuma shi ɗa da dukiya ai ba'a yi musu mungunta domin baka san wanda zasu amfana ba. Duk abinda yake wakana a cikin gidan nan ina sane dasu ba wai bana ji bane haka nan ba wai bana gani da idona bane illa iyaka dai ina kawar da idanuna ne duk gori da baƙaƙen maganganun da suke ƙunsawa yarinyar akan ƙaddarar rashin mijin da ya faɗo a tsaginta duk ina sane dasu kuma in sha Allah matuƙar Allah ya bamu tsawon rai zaku sha mamakin mijin da Allah zai azurta Zakiyya dashi, kowacce ta mayar da hankalinta idan kuwa tayi kunnun uwar shegu to ta san sauran ban zan ƙara tausar mazajenku ko kuma dana su duk hukuncin da suka yi niyyar ɗauka akan su tunda ai shi tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan duka".


Sosai kowa ya kuma shiga tairayinsa da kuma nutsuwa Hajiya Babba ta cigaba da faɗa tamkar zata ari baki Goggo Suwaiba na bata haƙuri sannan ta ɗan lafa. Kafin furcin Baba ƙarami ya ƙara hargitsa falon na cewar da ya yi Umman Salma ta tafi gidan su sai tayi hankali sannan ta koma kuka take yi wiwi har da majina su Salma na taya ta tare da ba wa Baba ƙarami haƙuri, bai kula su har sai da Umma ta sanya baki tana bashi haƙuri da cewar indai ita ce kam ta yafe mata ita bata ƙullace ta a ranta ba kuma a take a wajen ta sanya Zakiyya ita ma ta ce ta yafe mata ƙazafin da tayi mata da kalaman ɓatanci


"Wannan shine gargaɗina na ƙarshe gare ki Zinaru wallahi duk ranar da kika ƙara aikata makamancin hakan to sai kin koma gidanku babu abinda

13 / 58