Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
ya zaro daga aljihunsa ya ce a sayawa amare tsintsiya sannan suka fice daga sashin.
Ina daga zaune cikin ɗakin Umman ina hango duk abinda yake gudana a filin tsakar gidan saboda labulen ƙofar ɗakin da aka yaye shi saboda zafi, caraf Umma Ikilima ta ɗauke kuɗin daga inda ya ajiye ta sanya cikin rigar mamanta tana huci take faɗin"babu uwar amaryan da zan ba wa ko ƙarfanfana a cikin kuɗin domin riƙe su zanyi maimakon kuɗina da aka sace".
Nan kuwa Umma Firdau'si tayi tsaye ta dire akan ba ta isa ba sai an kasafta kuɗi a cirewa kowacce uwar amarya a cikin su nata kason, wani hayaniyar suka so haɗawa da ya sanya ni sakin wani sakakken ajiyar zuciya ina jinjina lamarin irin na gidan mu.
Suna fita daga sashin suka koma ɗakin yaya Majid domin suyi wanka su shirya, Abdul-aziz ne ya fara shiga banɗakin yayin da shi kuwa ya zauna akan katifa ya jingina bayansa jikin bangon ɗakin tare da lumshe idanunsa wani farin-ciki da daɗi game da sha'awa yake ji a duk lokacin da ya ga iyali suna zaune waje guda irin haka ba kaɗan ba abin yake faranta masa ruhi yanda ya gansu da yawan su rigis dasu abin gwanin ban sha'awa sai hakan ya burge shi tare da kwaɗayin ina shine yake zaune cikin nashi ƴan-uwan cikin gida ɗaya kuma ƙarƙashin inuwa ɗaya irin haka, sai dai hakan bai samu ba a gare shi jin an taɓo kafaɗarsa ya sanya shi buɗe idanunsa akan fuskar Majid ya sauƙe da ya ɗage masa gira ɗaya alamar lafiya, sai da ya gyara zamansa kafin ya furta"garin ku da kuma gidan ku ya burge na daɗe ban ga iyalin da suka burge ni kamar wannan ba nice family Allah ya ƙara haɗa kawunan ku waje guda".
Cije leɓɓansa yaya Majid ya yi kafin ya ce"Amin". Cikin ransa yana ƙara gastawa cewar haƙiƙa bai san irin tarin matsaloli da ƙalubalen dake cikin iyalin bane da wataƙil ko da ganganci bakinsa ba zai furta wannan kalmar ba, sai da suka shirya tsaf sannan suka sashin su Abba kallon tsaf Baba ƙarami ya yi musu kafin ya ce"har kun fito?".
"E ranka ya daɗe".
Ruwan dake kusa dashi cikin ƙaramin jarka Abba ya ɗauko ya maido dashi gabansa haɗi da cewar"to alhamdulillah ga ruwan rubutun da zaran sun isa a fara yi mata amfani dashi har na tsawon kwana bakwai sannan akwai wasu addu'o'in da zan baku da za'a dunga yi mata tofin su a kowani dare".
Sosai yake jin bakinsa ya yi masa nauyin da ya gaza furta koda kalma ɗaya daga cikin tarin kalaman godiyan da suke ransa, ƙasa kawai ya yi da kansa yana jin wasu hawaye na taso masa sai dai ƙarfin hali gami da jarumta irin nashi ya sanya hawayen maƙalewa a kurmin idaniyarsa. Abdul-aziz ne kawai ke ta zubo musu godiya da addu'o'i suna amsawa shi kam jan jikinsa ya yi ya matso gaban Abban tare da haɗe dukkan hannayensa biyu bakin na rawa sai dai baya jin abinda yake furtawa. Fahimtar hakan ya sanya Abba miƙar dassi tsaye yana cewa"ba komai ba sai kayi min godiya ba domin Annabi ya yi sanar damu cewar mu sanar da ƙanƙanin ilmin da Allah ya bamu sani a kanshi domin alfanan wasu, don haka babu godiya tsakanin mu Allah ya bata lafiya shine fatan da zamu yi yanzu".
A zuciyarsa ya amsa da amin har suka fito waje bai ce komai ba sashin Hajiya Babba suka shiga suka yi mata sallama, sannan suka yo sashin mu ina banɗaki lokacin naji shigowa da ficewar su duk gabaɗaya bai fi minti biyar ba, har cikin mota yaya Majid ya yi musu rakiya Abdul-aziz sai faman godiya yake yi masa babu ƙauƙaurawa. Babu shiri yaya Majid yaji Saif ɗin ya rungume shi tsam a jikinsa yana saki wasu tagwayen ajiyar zuciyoyi a lokaci guda.
Da ƙyar ya zare jikinsa suka yi sallama akan cewar zasu waya sannan suka shige motar suka tafi, sai da suka ɓacewa ganinsa sannan yaya Majid ya koma cikin gida sashin mu ya shigo yake labartawa Umma cewar har sun tafi lokacin ina ƙoƙarin tayar da sallan asr. Tunda suka fara tafiya har suka isa Saif ɗin bai ce komai kai tsaye asibitin suka fara nufa suka tsaya a masallaci suka gabatar da sallan magrib a masallacin suka haɗo da Farouk suka shiga ciki tare ɗakin Ummin suka nufa yanda suka barta haka nan suka same ta nauyayyen ajiyan zuciya ya sauƙe yana zama kusa da ita idanu ya zuba mata tamkar yau ce ranar farko da ya fara ganin ta.
Abdul-aziz ne yake ba wa Farouk labarin jahar yobe da kuma karamcin da suka nuna musu, ranar sai wajen ƙarfe goma sha ɗaya suka koma gida sai da suka fara biyawa gidan Abdul-aziz sannan suka wuce.
Washe garin ranar ya sanar da Anty Fauziyya komai kuma aka fara amfani da magani ga Ummin, da kansa yake yi shafe mata jikinta dashi sannan ya yi mata addu'o'in dare kafin su bar cikin asibitin. Kwanaki biyar a jere ana shafa mata maganin a yammacin na shida yana zaune a kusa da ita yayin da Farouk yake gefe yana danna wayarsa, jarice a hannunsa sai dai gabaɗaya hankalinsa ba da ita yake ba illa da tunanin da ya yi nisan kiwo a cikinsa, sai da Farouk ya taɓo shi kafin ya dawo ya hayyacinsa wayarsa da take ta ringing ya miƙa masa yana faɗin"yaya Saif tun ɗazu wayanka yake ringing a kusa da kai amma baka ɗauka ba". Sai da ya saki ajiyar zuciya sannan ya amshi wayar tare da picking ɗin call ɗin Abdul-aziz ɗin ya sanya a kunne shi sallama kawai ya yi ya yi shuru. Daga ɗaya bangaren Abdul-aziz ya ce"ka duba what'sapp ɗinka i drop you a message". Katse ƙiran ya yi ya kunna data ya hau what'sapp ɗin hoton da ya turo masa ya buɗe turus ya yi ganin hoton da aka ɗauka ba tare da sanin ba tabbas shine da yarinyar da ya watsa mata ruwa.
Ihun da Farouk ya tsala shi ya sanya shi kai dubabsa gare sa, nuni ya yi masa da Ummin da take motsa dukkan hannayenta da kuma idanunta da take ƙoƙarin buɗewa, zumbur ya miƙe ya saki wayar ƙasa ya fice ƙiran likita.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 1⃣0⃣5⃣
Tare da likitoti biyu suka dawo cikin ɗakin suka ce su jira su waje, tunda suka fito suke faman safa da marwa a bakin ƙofar ɗakin rayukansu cike da zulumi da kuma fargaba. Kujerun da suke jere da juna a wajen ya zauna yana dafe kansa da yake barazanar tarwatsewa into piece saboda azabar sara masa da yake yi kusa dashi Farouk ya zauna tare da kwantar da kansa saman kafaɗarsa yana sauƙe numfashi. Gabaɗayan su rarrashi suke tsananin buƙata cikin wannan halin da suke ciki sai dai babu mai iya rarrashin wanj a cikinsu saboda raunin da ya yi kaka gida a cikin zuƙatansu.
Sunfi mintin talatin zaune a wajen kafin likitotin suka fito ganin su ya sanya su saurin miƙewa suka isa gare su har suna rige-rigen furta"yaya jikin natan?". Kallon juna likitotin suka yi tare da sakarwa junan su murmushi kana ɗaya daga ciki ya miƙawa Saif hannu suka yi musabaha yana faɗin"ku kwantar da hankalin ku my friend she's getting better, impact ma zan iya cewa ta sama lafiya sai dai ƙananan abubuwan da ba za'a rasa ba you can go in and see her".
Sanƙarewa ya yi cak a wajen har likitan ya zare hannunsa daga cikin nasa bai motsa ba balle ya ce dashi wani abun, cikin wani matuƙar hanzari da sauri suka ƙarisa cikin ɗakin tare da Farouk a ƙofa suka tsaya suna tantance aihinin abinda idanusun yake gano musu, Ummi ce zaune akan gadon ta jingina bayanta cikin matashin da aka sanya mata ta baya fuskarta tayi wani fayau da ita idanunta ƙar akan su. A tare suka zube akan gwiwoyinsu tare da yin sujudul-shukr ga ubangijin da bashi da abokin tarayya wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Sun daɗe kafin suka ɗago suka ƙarisa gare ta cikin rawar murya da na jiki Saif ya furta"Ummi ke ce ina ji na?". Kanta ta ɗaga masa wasu hawaye suka wadatar kurmin idaniyarta da take matse fitowar su a ƙoƙarin ganin ta ƙarfafawa ƴaƴan natan gwiwa, kusa da ita Farouk ya zauna tare da riƙe hannunta dukka ya sanya cikin nasa murya a karaye yake cewa"Alhamdulillah Allah mun gode maka da ka dawo mana da farin-cikin mu a rayuwa".
"Ina ne yake miki ciwo yanzu?".
Sai da ta sakar masa murmushi kana ta ce cikin muryarta da bata fita sosai sai da ya matso kusa da ita sosai sannan ya ji abinda take faɗi"babu inda yake min ciwo Saifuddeen". Da sauri ya ƙara cewa"to me za ki ci na kawo miki?". Kanta ta jijjiga masa da hakan ya sanya shi ƙara komawa kalan tausayi matuƙar raunin dake cikin ƙalbinsa ya ƙara bayyana ƙarara a bisa fuskarsa.
A sanyaye ya furta"bari na fita na samo miki wani abun ko marar nauyi ne sai ki samo ki ci, Umar ka zauna a nan kar ka matsa ko'ina". Kansa Farouk ɗin ya ɗaga masa shi kuma ya fice tafe yake cikin wani irin saurin da jefa ƙafarsa kawai yake yi ba tare da ya san inda yake sauƙewa ba, kusa da asibitin ya sama wani restaurant ya sayo mata abu marar nauyi ya haɗo mata da madara ya dawo. Inda ya barta nan ya iske ta zaune da wayarsa a hannunta Farouk na nuna mata wani abu bai mayar da hankalinsa ba illa kofin da ya ɗauko ya dama mata madaran a ciki ya miƙa ya zauna ya fara bata sai ta sha sosai sannan ya bar ta, ya tashi da nufi zuba mata abincin da ya sayo ya riƙe hannunsa komawa ya yi ya zauna tare da zuba mata ido.
Wayarsa da yake gefenta ta ɗauko ta miƙa masa karɓa ya yi yana kallon abinda take yi masa nuni dashi a cikin wayan, ras gabansa ya yi wani mummunan faɗuwa don ganin hoton da Abdul-aziz ya turo masa ne da ya jefar da wayar ba tare da ya fita daga kan hoton ba shi take nuna masa. Murmushi dole ya ƙaƙalo a ƙoƙarin ɓoye firgicin da ya shiga sannan ya ce"wani abu kike buƙata Ummina?".
Murmushin ita ma ta mayar tana ta soma faɗi a hankali"kunyi kyau". Sadda kansa ƙasa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ranar wuni suka yi gabaɗaya babu inda suka motsa ko salla nan cikin ɗakin suke yin sa, farin-ciki da kuma murnan ganin Ummin nasun ta sama lafiya shi ya mantar dasu ƙiran Abdul-aziz da Anty Fauziyya su sanar dasu wannan dandaɗan labarin.
Sai da yamma Abdul-aziz yazo asibitin ya tarar da labarin sosai ya nuna zallar farin-cikinsa tare da jeranta godiya ga Allah mai komai mai kowa da ya nufe su da ganin wannan daren da ba zai taɓa shuɗewa ba cikin tarihin rayuwar su, sai dare ya bar cikin asibitin duk da dokar asibitin ne ba'a kwana wajen mai jinya amma ranar da kansa babban likitan asibitin ya bar su suka kwana kusa da Ummin su don babu wanda bai san rashin lafiyan da ta shafe watanni tana yi ba cikin asibitin. Washe gari ya ƙira Anty Fauziyya ya sanar da ita muryarta kaɗai ya isa bayyanar da sirrin farin cikin da ya gama mamaye mata birnin zuciyarta, video call ta ƙira ya hasko mata Ummin ta ganta duk da har yanzu muryata bata fita sosai sai ka kasa kunne sannan ya iya jin abinda take furtawa. Wayar Majid yake ta ƙiran don ya sanar dashi amma ake shaida masa da cewar tana kashe dole ya haƙura ya tura masa saƙo kawai, sosai suka cigaba da yi mata amfani da ruwan rubutun da kuma addu'o'in a yinin rana na uku da buɗe idonsa duk suna zaune a cikin ɗakin har da Abdul-aziz da bai jima da zuwa ba, Ummin tayi wa Saif ishara da hannu akan ya matso cikin saurin ya dawo kusa da ita ya zauna ta yanda zai iya jin abinda take faɗa da kyau.
"Wacece wannan yarinyar?".
Da sauri ya ɗago kansa yana kallon fuskarta da ta kafe shi da ido dole ya rusunar da nashi ƙasa, yana tinanin wacce yarinya ce sai can ya tino wacce take magana a kai a ɓoye ya sauƙe ajiyan numfashi da mamakin yanda ta kasa mancewa da ita da kuma zancenta. Numfashi ya cigaba da sauƙewa kafin ya kai ga furta wani abun ya ji ta kuma cewa"tun yaushe kuke tare da ita?".
Tsam ta gama ɗaure sa da jijiyoyin jikinsa gabaɗaya ya rasa abinda zai ce da ita, bai saba yi mata ƙarya ba kuma sanin da ya yi mata duk wani abun da ta dage akan sa to tabbas ya zama gurbi ne a cikin zuciyarta bata cika riƙe abubuwa irin haka ba a lokaci da dama sai dai bai san me take nufi ba game da wannan zancen.
"Mun ɗauki lokaci tare da juna".
Amsar da yaji bakinsa ya furta kenan ba tare da ya yi shawara da zuciyarsa ba, da hakan ya sanya Abdul-aziz da Farouk gabaɗayan su zubo masa idanunsu cike da mamakin furcin nasan. Sakakken ajiyar zuciya Ummin ta saka kafin ta ce"alhamdulillah Saifuddeen bani da wani burin da ya wuce yanzu na ganka ka zama cikakken mutum ƙarƙashin sunnan ma'aiki, ko bayan raina zan kwanta cikin salama cikin kabarina idan na tina cewar kana da aure akwai wacce zata kula da kai da kuma ɗan-uwanka Farouk".
Tsit ɗakin ya ɗauki shuru hakan ya bata damar ɗaura da"ku ne rayuwata ku ne dangi kuma ahali a gare ni, kune jigo kuma madogara a gare ni, ku ne komai nawa cikin wannan duniyar. Ina ji a jikina cewar ba zan yi rayuwa mai tsayi daku ba a gaba shiyasa yanzu bani da wani burin da ya yi min saura a duniya fiye da naga ƴaƴanku, kunyi min komai da duk wasu ƴa'ƴa na gari zasu yiwa iyayen su wannan burin kawai ya rage min a rayuwa".
Sosai jikinsa ya yi wani irin mungun sanyi don bai zata zata ja zaren zancen da nisa har haka ba, da bai furta kalman da ya yi a baya ba sai bakin alƙalamin ya bushe babu damar maida hannun agogo baya balle ya sama damar goge kuskuren da ya aikata. Ƙara motsowa ya yi kusa da ita yana fuskantan ta sosai yake faɗin"in sha Allah Ummi wannan burin ma zamu cika miki shi, za ki ga aurena za ki matata za ki ga ƴaƴana Ummi. Amma mu bari ki ƙara samun lafiya tukunna koma menene zai biyo bayan hakan". Hannunta ta ɗaura saman nashi tana faɗin"Saifuddeen gobe ta Allah ce mai rabo da nian kwana ne kawai yake iya iskan ta, don haka ina son ayi komai yanzu a ina take da zama?".
Wani zuffa ne ya keto masa mai maiƙo da ƙyar ya haɗiye wani tulin miyau ɗin da ya wuce masa ta maƙshi tamkar ƙarangiya, kafin ya ce da ita wani abun Farouk ya yi saurin faɗin"Ummi likita fa ya ce ki daina yawan magana saboda yanayin jikin nak...".
Bai ƙarisa ba sakamakon muryar Saif ɗin da ya sauƙa a kunnuwansa cikin faɗin"a jahar yobe take". Wani kallon mamaki Abdul-aziz ya jefa masa, kwantar da murya ya yi ya cigaba da faɗin"amma Ummi mu bar maganan yanzu mu yi wani lokacin yanzu dai samun lafiyarki shine abinda muka fi mayar da hankali a kai".
Murmushi kawai take sakar masa da har sai da haƙwaranta suka bayyana masu ɗauke da kyawawan wushirya a tsakankanin su, zallar farin-ciki yake hangowa a cikin ƙwayoyin idanunta duk da bakinta bai furta komai ba a nutse ya miƙe ya fice daga ɗakin yana jin wani azababben ciwon kai Abdul-aziz ya rufa masa baya.
Sai da ya kua ficewa daga ward ɗin Abdul-aziz ya cim masa riƙo shi ya yi saboda jirin da ya ga yana ɗiban sa ya zaunar da shi, kafin ya ce"meyasa meyasa meyasa Saif zaka ɓoye mata wannan gaskiyar?, meyasa zaka sanar da ita abinda kai kanka ka san bashi bane meyasa?".
Bai ce dashi komai illa dafe goshinsa da ya yi da dukkan hannayensa biyu tare da lumshe idanunsa ya ce"tana so tana so Abdul-aziz farin-cikinta shine samun lafiyata shin baka ga yanda fuskarta ya ƙawatu da annashuwa da annuri ba?, i will explain everything to her daga baya".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 1⃣0⃣6⃣
Rurin da wayar Abdul-aziz ya soma yi shi ya dakatar dashi daga yunƙurin son furzo zancen da ke cikinsa, zaro wayar ya yi daga aljihun ganin Farouk ne mai ƙiran ya sanya shi saurin ɗauko cike da son tsoron ko wani matsalan ne ya taso.
"Yaya Abdul likita ne yazo ya ce yana buƙatan ganin yaya Saif a ofishinsa, shi kuma ya bar wayarsa a nan na san kuna tare don Allah ka sanar dashi don ya ce da gaggawa yake son ganin sa".
Sakakken ajiyan zuciya ya sauƙe yana amsawa cikin faɗin"ok in sha Allah zan sanar dashi yanzu". Yana gama faɗin haka ya datse ƙiran yana maida duban sa ga Saif ɗin da har yanzu yake dafe da goshinsa idanunsa a lumshe, kusa dashi ya tsaya ya dafa kafaɗarsa a nutse ya soma faɗin"likitan Ummi ne yake buƙatar ganin ka yanzu a ofishin sa ka tashi kaje". Idanunsa da suka soma sauya launi ya ɗago ya zube su a fuskar Abdul-aziz ɗin ba tare da ya ce dashi ko kanzil ba, sosai Abdul-aziz ɗin ya tsorita ganin yanayin da ya shiga hakan ya sanya shi taimaka masa ya miƙe tsaye har cikin ofishin ya kai sa tare da zaunar dashi zai juya ya yi masa alama da hannu akan ya zauna.
"Ina jinka doctor".
Ya furta cikin jawo numfashin sa da yake garkewa a ƙirji, numfasawa likitan ya yi tare da gyara zaman farin gilashin dake saman karan