Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
Abba ya miƙe ya fice yaya Majid ya yi saurin rufa masa baya, Baba da Baba ƙarami ma tsawarta suka yi sosai musamman ga matayensu tare da basu misali da abinda ya faru da Daada duk wacce bata maida hankalinta ba ko kuma ta kuma tayar da wani rikicin irin hukuncin da zai hau kanta kenan, kar ma suyi tinanin wai ƴaƴan dake tsakanin su zai dakatar su ko kuma tsofan da suka yi, babu ruwan su zasu tura mace gidan iyayenta inta taɓa zawarcin ta gyara halinta ala bashi sai ta komo. Haka duk muka watse kowa cikin sanyin jiki, sauƙe ajiyan zuciya naje yi a kai a kai tamkar wacce tayi gudun ceton rai, ina daga ɗakin Ummata nake jiyo koke su Abasiyya Anty Hasina tana faɗin babu inda zata je zata ƙira mijinta sai ta koma zama tare dasu in ya yarda kafin an abinda Allah zai yi.
Wani kuka ne ya kubce mini mai ɗan karen ƙarfi, ina jin wani iri a zuciya ina kwatantan raɗaɗin rabuwa da uwa da zuƙatan su Abasiyya suke a ciki duk ta dalilina. Babu shiri na miƙe ko ta kan Umma da Anty Zakiyya da suke ƙiran sunana ban bi fa na fice ɗakin Daada, na durƙusa a gabanta cikin kuka ina mai neman gafararta cikin su gabaɗaya babu wanda ya tanka mini balle na sa rai ga cimma abinda nake biɗa daga gare su, na daɗe durƙushe a wajen kan ƙafafuna suka yi tamkar basu gannin ba sai haɗawa Daada kayanta suke yi, sai da Anty Zakiyya ta shigo ta janye ni muka fita.
Daren ranar da zazzaɓi na kwana sosai a jikina, sallan asubahi ma a zaune nayi shi na daɗe ina addu'ar kar Allah ya ƙara sanya na zamto ɓacin ran wani balle har ya ƙulla ce a ransa. Washe gari da yaya Majid ya shigo gaida Umma, kasancewar a ɗakinta na kwana ba sashin Hajiya Babba ba, ya ce naje na ƙira masa Abasiyya tazo yana son magana da ita.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 4⃣5⃣
Tunda na tunkari ɗakin kunnuwana suke jiyo mini tashin kukan da Abasiyya take yi a hankali yana dukan dodon kunnuwana, a sanyaye na shiga ɗaki tana can kan gadon ƙarfen Daada mai rumfa ta naɗe cikin bargo gefenta kuwa Ammar ne shima idanunsa shar da hawaye yana kwance yana baccin da a kallo ɗaya da nayi masa na gane baccin na dole ne.
Sai da na zuƙa numfashi na fesar kana na furta"Abasiyya".
Bata ɗago ta kalle ni ba balle nasa rai ga cewar samun amsa daga gare ta, sai dai ta sausauta ƙarfin kukan natan. Fahimtar ba zata ce dani komai ba ya sani ƙara cewar"dan Allah Abasiyya kiyi haƙuri ki daina wannan kukan, sai ki sama kanki wani damuwar ai jego fa kike yi dan Allah kiyi haƙuri ki taso muje yaya Majid yana son magana dake".
Ɗago kanta tayi tamkar zata ce dani wani abun sai kuma tayi shuru kawai ta ɗauke kanta daga gare ni, ban daddara ba naja ƙafafuna na zauna bakin gadon cikin sanyin murya nake faɗin"dan Allah kiyi haƙuri kinji ƴar uwata tashi muj...". Saurin ɗaga mini hannu tayi tare da runtse idanunta da suke zubda ƙwalla har yanzu kafin ta ce dani"ya isa haka Na'ima ki tashi ki fita dan Allah na gama ki da girman Allah ki fita ki barni, bana son ganin kowa bana son magana da kowa bana son ganin kuwa kusa dani ki barni dan Allah ki fita kawai".
Ta faɗa tana haɗe dukkan hannayenta waje guda alamar roƙo, kukan da ta kuma fashewa dashi ya sanya Ammar farkawa a razane kafin shima ya tsala wata iriyar ƙara, tagwayen ajian zuciya na sauƙe ina duk raina a jagule ban kuma cewa komai ba illa sa hannu da nayi na ɗauki Ammar da naga alamar bata da niyyar kula shi balle lallashinsa na fice dashi.
Ɗakin Umma na wuce dashi ina jijjigashi cikin sigar lallashi, yaya Majid da Anty Zakiyya suka zubo mini idanu cike da son ƙarin bayani ajiyan zuciya na kuma sauƙewa a karo na barkatai kafin na zaune ina aza Ammar bisa cinyar ina shafa bayansa a hankali da yanzu ya tsagaita da kukan illa ajiyar numfashi da yake sauƙewa a kai a kai.
"Ina Abasiyyan?".
Furcin yaya Majid suka katse mini hanzari a raunane na furta"bata jin daɗi ina ga kamar ba zata iya fitowa bane na same ta ma a kwance".
Kansa kawai ya jinjina tare da miƙewa ya amshi Ammar daga hannuna suka fice da kallo na raka su ina jin ƙwalla sun ciko mini kurmin idaniya wanda ban san dalilin taruwar su ba.
"Allah ya kyauta".
Anty Zakiyya ta furta tana ficewa daga ɗakin riƙe da kayan wankin da ta haɗa zata yi, tagumi na zabga hannu bibiyu cike da tausayin kaina, a hankali na kai hannuna ƙasan marata ina shafawa a hankali don yau banji motsin abinda ke cikina ba tun asubahi ƙarƙarfan numfashi na fesar daga baki mai ɗan ɗumi, haka nan kawai naji buƙatar na kunna wayata domin ina son sanin halin da maman Hanan take ciki. Allah ne shaida ban taɓa ɗaukar maman Hanan matsayin facala ba hasalima kallon ƴar uwa nake mata da zuciya baya bambamta matsayin da take dashi a gare da Anty Zakiyya da muke jini ɗaya da ita, ta nuna mini tsantsar so ta kuma jani a jikinta tare ɗaukar duk damuwata tamkar nata bata taɓa munafurtata ba balle na kama ta da cin amanata shiyasa nima na damu tunda naji halin da take ciki kuma nake son sanin yaya take yanzu, cike da fargaba da faɗuwar gaba na tashi na buɗe sif ɗin Umma na ɗauko wayata da tun zuwa gidan ban bi ta kanta ba batirinta na haɗa na jona ta kawo sai dai ta yi mini kukan rashin caji.
Fita nayi da nufin miƙa ta ga yaya Majid ya jona mini a ɗakinsa tunda tashin hankali bai bar ni na ɗauko cajata ba, kiciɓus muka yi dashi zai shigo ɗakin na ja da baya ina bashi waje. Ammar dake saɓe a kafaɗarsa da ya yi bacci ya miƙo mini shi tare da faɗin"je ki kwantar dashi".
Amsar sa nayi da ledar da yaya Majid ya miƙo mini na kayan ƙwalan da lashan da ya saya masa, na wuce ɗakin Daada domin kwantar dashi ɗin, yanda na barta haka na same ta sai dai yanzu babu kukan sai sakin ajiyar numfashi da take yi tamkar wacce tayi fafata a gasar tseren gudu. Kwantar dashi na fito na ba wa yaya Majid waya da na iske shi suna magana da Anty Zakiyya da take wanki a tsakar gidan, sai da suka gama ya fita dai dai fitowar Umman Anty Kubra daga ɗaki ta bishi da harara ko gaisuwar da muka haɗe da Anty Zakiyya wajen yi mata bata amsa ba, ta fara haɗa wanke-wankenta. Ɗauraya na fara yiwa Anty Zakiyya har muka gama wanki dai-dai muna haɗa bokatin Umma ta shigo sashin sannu da aiki tayi mana ta wuce ɗaki muka rufa mata baya.
"Ina Abasiyya kuwa banji motsinta ba tun safe a cikin gidan, ko Ammar ban gani ba anya kuwa tayi wanka ma?".
Naɗe kafaɗarta Anty Zakiyya tayi alamar bata sani ba, sai ni nayi ƙarfin halin faɗin"tana ɗaki a kwance wankan gaskiya bana tinanin tayi".
Ina faɗin haka Umma ta fita wuta ta hura ta ɗaura mata ruwan zafin wanka, sai da ya tafasa ta ce na kawo mata bokati ta juye shi da tiririnsa ta kai bayi, ta kuma cewa na ƙira mata Abasiyya tazo tayi wanka har ruwan ya huce. Na wuce ɗakin Daada domin ƙiran Abasiyya sanda na shiga na iske ta zaune da waya maƙale a kunnenta alamar waya take yi ɗan ja da baya nayi don kar ga Allah bana son jin abinda take faɗi a wayar balle har zuciyarta ta raya mata zargin ko leɓe nake yi ba, sai na ɗan ɗauki mintona kafin na kuma saka kai ɗakin lokacin wayar tana ajiye gabanta.
"Umma ce daman ta ce kizo kiyi wanka ga can ruwa a bayi an kai miki".
A karon farko kenan da ta ɗago idanunta da suka sauya launi izuwa kalan ja ta zuba mini, kafin ta furta"dan Allah ki fita bana son ganin ki, ki fita tun kafin na aikata miki abinda zuciyata take kimtsa min".
Ta faɗa a zuciye tana miƙewa tsaye tare da yi mini da ƙofar ɗakin tabbacin bata son gani na balle saurara maganganun da suke fita daga bakina. A tare Salma da yaya Majid suka shigo ɗakin wanda hakan ne ya dakatar dani daga furcin da nake son furzowa.
"Kuma ki zauna Abasiyya ina son magana dake".
Muryar yaya Majid suka ratsa kunnuwanmu gabaɗaya,Ba don taso ba Abasiyya ta koma ta zauna sai don kwarjini da cika idon da yaya Majid yake yiwa duk yaran gidan, hatta su Anty Maimuna da Anty Hajara da suka girme masa a shekaru. Muma zaunawa muka yi gabaɗayan mu, kafin yaya Majid ya yi gyaran muryar da ta ƙara fallasar da tsantsar kamanceceniyar halayya da ɗabi'unsa da Abbanmu bayan kamar dake kwance saman fuskokinsu kafin ya soma faɗi cikin kwantar da muryarsa"duk abinda ya faru bamu ikon hana sa faruwa matuƙar Allah ya ƙaddara hakan a gare mu, sanin hakan ya kamata mu watsawa zuciyoyinmu ruwan sanyi tare da nusar da ita abinda ta mance cewar dukkan bawa yana tafe da ƙaddararsa ce dake rubuce cikin littafinsa tun kafin samuwar ruhinsa a bayan ƙasa, bai kamata mu ɗauki gaba ko riƙe juna a ranmu ba akan abinda bamu da ikon hana sa faruwa ko ikon tariyo abinda ya wuce balle har mu gyara kuskurenmu".
Daga haka ya tsagaita tana haɗe hannayensa waje guda, har sai yatsun hannunsa suka ɗan bada sautin ɗas kafin ya ɗaura da faɗin"ina shiga ɗimuwa kwarai da jin cewar kin haihu ba rai wanda ni ne sanadiyar hakan ko kuma ince sila. Don haka naso mu zauna dasu Abba dashi Sagir ɗin domin kawo maslaha amma su Abba sunce sai kin gama warware tukunna ran kowa ya huce daga zafin da ya ɗauka a yanzu. Ina mai ba ki haƙuri Abasiyya Allah ya sani ban yi miki haka ba da wani nufin kamar yanda kowa yake kallon abin a haka, yanda na ɗauki Na'ima da Zakiyya da muke uwa ɗaya dasu haka kema na ɗauke ki kema da duk sauran yaran cikin gidan nan, rashin ɗanki da kika yi Allah yasa mai ceto ne a gare ki ya ƙarawa zuciyarki dangana kuma ina mai ba ki haƙuri ko ba a faɗa a idanunki na hangi raɗaɗin da kike ji a ranki a dalilin hakan kuma ga abinda ya kuma faruwa da Daada".
Fashewa sosai Abasiyya tayi da wani kuka mai ƙarfi har da dafe goshinta, tana jijjiga kanta cikin mu babu wanda ya ce komai balle yunƙurin lallashinta. Nikam ta ƙasa idona naje yarce ƙwallar dake sulalo mini, shuru ya ɗauki ɗakin sai can Abasiyya ta katse shurun ta hanyar faɗin"yaya Majid wallahi ban riƙe ka a raina game da hakan ba haka nan ma Na'ima, shima kuma Sagir rashin fahimta ne ya sa shi faɗin abinda ya faɗa da kuma fushin da yake ciki akan maganganun da Anty Hasina ta shirya masa ya hau ya zauna, abinda yafi damu yanzu kawai rashin Daada a kusa dani ne. Yaya Majid nima fa ina da hankali kuma bazan taɓa yarda mijin da muka haɗu dashi da haƙwarana talatin cur ba ya wulaƙanta min dangi har da ikirarin kai su kotu".
Musgutawa yaya Majid ya yu tana ƙara fuskantar ta kafin ya furta"ai Abasiyya tana hujjar da zai hau dokin fushin da yake kai a yanzu, kuma hakan da ya yi ya nuna cewar yana kishinki kuma zai iya tsayawa tsayin daka wajen karɓa miki ƴancinki a wajen kowa, in sha Allah zamu zauna dashi yanzu dai ki tashi kije kiyi wankan Daadar ma zata dawo da yardan Allah".
"Yaya Majid daga jiya zuwa wayewar garin yau da babu Daada a cikin gidan nan na fahimci abubuwa da yawa wallahi, nayi tinanin Umman su Anty Kubra ita zata fi kowa kawo min ɗauki da shiga damuwa game da halin da nake ciki, duba da yanda kafin Daada da Anty Hasina su bar gidan nan yanda ta bata amanar kuɗa dani har nayi arba'in na koma gidana. Kuma duk abinda ya faru ita take zuga Daada da ƙara yi mata fanfo amma tun bayar tafiyar Daada ko ɗakin nan bata leƙo ba balle tinanin halin da nake ciki".
Ta faɗa tana ƙara tsananta ƙarfin kukan da take yi, dafa ni har Salma kusa da ita muka koma muna bata haƙuri da lallashin zuciyarta, fita yaya Majid ya yi bayan shi ya gama yi mata nasiha da kwantar mata da hankali. Da ƙyar ta fito saboda jirin da ta ambata yana damunta Umma da kanta tayi mata wankan sannan ta dama mata kunu tasha ta wanka.
*Allah yasa kun fahimci saƙo dake cikin wannan page ɗin, ƴar uwa ki nutsu ki kuma hankalta. Ba kowa bane za ki saki baki wajen faɗa masa matsalar da kike fuskanta a gidan aureki wani sai ya gama saurara ya barki ba tare da samar miki da mafita ba sai dai ma yafi kowa yaɗa sirrinki. Wani kuma maƙiyin farin ciki da kwanciyar hankalinki ne zai zo miki a suffar masoyi ya zuga ya kuma tura ki damin da za ki yi tsalle dubu ba tare da kin fito ba, kamar yanda Umman su Anty Kubra ta aikatawa Daada ta kuma ɗauke kai daga kula da ƴaƴanta bayan ita ce silar komai, wallahi MATAN AREWA mu hankalta.*
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________________
Page 4⃣6⃣
Zaune yake a ofishinsa ya kwantar da kansa cikim kujerarsa da take juyawa dashi a hankali lokaci zuwa lokaci. Kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatarwa kanka cewar a hargitse yake haka nan babu alamar nutsuwa da hankalinsa basa a tare dashi, a karo na barkatai ya furzar da zazzafan iska daga gare shi yana zame hannunsa da ya tallafi kuncinsa dasu dukkan su biyu. Sumar kansa ya shiga barbazawa yana lumshe idanunsa da suka yi ciki ciki suka kuma rine sosai kafin ya dafe goshinsa da jijiyoyin kansa suka shimfiɗa raɗau raɗau bisa namar goshin nasan.
Da ƙarfi ya ture tulin littattafan dake gaban suka zube ƙasa, da damƙo sumar kansa sosai tamkar zai tsige gashin kan nasan. Ciro leɓɓansa ya yi kamar zai huda su kafin ya koma sakin ajiyar zuciya a wahale.
Ya daɗe a haka cikin zafin zuciya da raɗaɗin da yake ji a dukkan sassan jikinsa, ya kai wani wawan bugu a teburin dake gabansa yana huci cike da ƙasa iya riƙe kansa balle dakatar da abinda ke kai kawo masa a ransa.
Da saurin mai gadi ya shigo ofishin ganin sa a wannan yanayin ya sanya shi yin turus yana tsura masa idanu a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya tausayinsa yana mamaye ruhinsa da halin da ya tsinci kansa da har yanzu babu wanda yasan dalilin canjuwar tasan sai dai hatta masu sharan makarantar sun fahimci sauyawan da ya yi duk da bashi da sakin fuska da magana sosai yana girmama duk wanda yake gaba dashi a makarantar koda kuwa a ƙasan sa yake hakan bai hana shi bashi girman sa na babba. Har ya iso gaban teburin bai ɗago kansa ba balle ya buɗe idanunsa da ya runtse su suna tsiyayar da siraran hawayen da suke gudana ta gefe da gefen kuncinsa, cikin taushin murya Baba mai gadin ya furta"yallaɓai lafiya kuwa?, lokacin tashi ya yi har kowa ya watse amma kai kana nan gashi har yamma ta kusa kawo kai, nima alwalan sallan asr na zagayo yi nayi motsinka na ce bari nazo na dub...".
Saurin ja da baya ya yi ba tare da ya ƙare furzar da zancen dake bakinsa, sakamakon jinannun idanunsa da Yusuf ɗin ya watso masa yana kafe sa dasu jajawur launin farin idon nasan ya jirkice ɓakin ya saje da launin jan ga hawayen da har yanzu suke gudana a dandamalin tudun fuskartasan.
"Auzubillahi! yallaɓai lafiyarka kuwa?, lafiya kake?".
Ya faɗa a rikice, kallon sa kawai malam Yusuf ɗin ya cigaba dayi yana motsa leɓɓansa a hankal sai dai sautin maganar da yake yi ciki ciki bata fia yanda koda na kusa dashi ne zai ji balle na nisa, so yake ya amsa masa koda ɗaya ne ki zai yi sausauci wutar da take cin zuciyarsa.
Cikin ƙarfin hali ya ɗaga masa kansa duk yanda yaso sakar masa murmushi domin share kokonton da ta bayyana a dattijuwar fuskar Baba mai gadin gagaransa hakan ya yi. Mai da kansa kawai ya yi ya kwantar yana sauƙe numfashi a wahale sunayen mahaliccinsa tsarkaka ɗari ba ɗaya yake jiƙa harshensa dashi ko zai yi ɗan ji sauƙi, bai gusa ba yana yi ya fara ji tamkar ana rage masa nauyin da ƙirjinsa ya yi masa. Ganin har yanzu Baba mai gadin yana tsaye cike da damuwa yana mai cigaba da jeranta masa tambayoyin da shi kansa bashi da amsar su ya sanya sa cira kansa tare da jarumtar jawo numfashinsa ya kalle shi gami da faɗin"lafiya ƙalau Baba".
"Kamar yaya lafiya yallaɓai ai kowa yaga yanayinka yasan ba lafiya ba".
Murmushin dole ya kuma sakar masa da yake jin ciwonta har cikin ransa, kafin ya miƙe tsaye makullin mashin ɗinsa kawai ya ɗauka ya fice daga ofishin ɗin. Ba tare da ya kuma kallonsa ba balle amsa masa tambayoyin da ya cigab da jifansa dasu haka nan ya bar ofishin a buɗe don bai da nutsuwar tsayawa ya rufe ta.
Yana tafiya yana haɗa hanya tamkar bugagge haka ya isa inda ya ajiye mashin ɗinsa, ya daɗe a tsaye a waje dafe da goshinsa da yake jin kansa yana sarawa tamkar zai rabe izuwa gida biyu duk abubuwan da suke gabansa ganin su yake yi bibiyu. Sanyayyan ajiyan zuciya ya sauƙe yana jin wani miyau mai ɗaci yana taruwa masa a baki.
Haka nan yake jin yau idan bai ga Na'ima ba babu abinda zai hana numfashinsa barin gangar jikinsa, Allah ya sani yana yi mata