Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
yana da ƙanne mata in ko babu yana da ƴaƴan ƴan-uwa".
"Mungu na ƙarshe ma kuwa ai faɗi da babban murya". Murmushi kawai Nazifa take yi kanta yana ƙasa mu muke ta faɗar kamar zamu yi aron baki amma ita bata tufa komai ba har muka yi muka gama. Wunin ranar gabaɗaya zancen fashewar result ɗin ake tayi shigo goma sai mutum ya tambaye ka yaya result babu wanda muka sanarwa namu illa muce dashi alhamdulillah.
Sai da dare muka ƙara duba na Nazifa gabaɗaya ma exams ɗinta ba'a ɗaura ba haka wajen yake empty, test kawai aka sanya mata 12 shikenan mamaki muka yi aihun domin exams ɗin shi muka yi ƙarshe kuma ga sauƙi kamar banza.
Sai da muka sati guda cikin wannan jimamin da rashin sanin abin yi, ranar wata labara muna zaune a hall muna jiran lecturern ya iso kaman an ce ɗaga kanki idanuna suka sauƙa akan Mr Suleiman yana shigowa cikin hall ɗin, shuru ya karaɗe gabaɗaya hall ɗin idanunsa suna ɓoye cikin baƙin gilashi ya tako har izuwa kan stage din dake hall ɗin yana bin kowa da kallon ɗaɗɗaya.
Kafin ya yi gyaran kafin ya soma"i'm the one that going to take over from where Mr Daniel stop for good two week". Tsif ya koma ɗaukar hall muka fara fito da abubuwan rubutun har ya gama lecture din ban fahimci komai ba, ya bamu assigment ya ce individual kuma kowa shi zai fi submitting da kansa ba a class rep za'a haɗawa ba bai ko kalle inda muke ba ya fice muma muka fice. Sai da muka biya ta wajen Mama Marry muka gaisa muka amshi babynta ta zuba mana masa da yawa sannan muka wuce hostel.
Zaune yake gaban Ummi ya naɗe ƙafafunsa wajen guda kansa yana ƙasa yana murza zoben dake ƴatsarsa ta tsayi a hannun hagu, sosai ya ba ta dukkan nutsuwa da hankalinsa yana sauraron ta.
"Saifuddeen ka miƙa dukkan lamuranka ga Allah in sha Allah ba zaka taɓa kunya ta ba".
Sai da ya saki tagwayen ajiyan zuci kana ya sama sarari furta"in sha Allah Ummi".
"Zan baka saƙar gold ɗina ka sayar sai ka riƙe kuɗin a wajenka, kayi hidimar biki". Sai a lokacin ya ɗago idanunsa ya sauƙe su a kanta"Ummi akwai kuɗi a wajena zasu ishe ni kar ki damu da wannan".
"Saifuddeen kar kayi ƙoƙarin ɓoye gaskiya da fuskarka ya riga ya bayyana ta, na san babu wasu kuɗi a wajenka hasalima cikin kwanakin nan kana cin matsalar kuɗi ga yanda iftila'in da ya faɗa a gidan gonanka. Ka sayar da saƙar kayi amfani da kuɗin daga baya sai muga abinda Allah zai yi".
Rasa abunda zai ce guda ɗaya ya yi illa juya kansa da kawai yake yi, har ta ƙare zancen natan yana mamakin yanda ta fahimci halin da yake ciki na matsalar kuɗi a kwanakin nan, da salary kawai ya dogara ga yanda rayuwa ya yi tsada sai kuma kuɗaɗen da yake saving a accout ɗinsa. A hankali ya furta"Allah ya saka da mafificin alkhairinsa gare ki Ummi".
Cike da jin daɗi ta amsa da"Amin amin, munyi magana da Antynku ta ce za'a haɗa lefe a kano daga nan kawai sai a cewa dashu yobe".
Kansa ya jinjina da izuwa yanzu hakan ya zame masa ɗabi'a ya ce"hakan ma zan ƙira ta nima". Da haka suka cigaba da tattaunawa game da zancen bikin da yake gabatowa, sai da aka yi sallan isha'i ya shiga ɗaki sannan ya ƙira Anty Fauza game da zancen haɗa lefen sosau suka tattauna tare da tambayarta nawa ya kamata ya turo.
"Nima tawa gudumawar kenan Saifuddeen kar ka takura kanta duk abinda yake gare ka ta tura sai a ƙara a kai".
Jinjina girman gurbin da tayi occuying a cikin birnin zuciyarsa yake yi, tabbas bayan Umminsa Anty Fauza ita ce mace ta biyu da bashi da waɗanda suka kai su balle su kai su a kaf cikin rayuwarsa, wani nauyinta ya ji sosai don shi kam bai san abinda ya kamata ya tura ba bisa wannan zaɓin da ta bashi. Sallama suka yi bayan ya gama jeranta mata godiya, 500K ya tura mata nan take. Cikin guda ta kammala komai ta sanar dashi videon kayan ta aiko masa ya nunawa Ummi abun sai son barka.
Yaya Majid ya ƙira ya sanar dashi za'a kawo lefe sannan ya ƙira Anty Zakiyya ma yake sanar da ita.
"To Allah ya kaimu goben da rai da lafiya, su kuma Allah ya kawo su lafiya ya mayar dasu lafiya".
"Amin ya Allah amma ina mai ba ki haƙuri". Da sauri ta furta"haƙuri kuma na meye?". Sai da ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe su kafin ya ce"za ki auri marar dangin ne bani da kowa daga Ummina da ƙanina Umar sai kuma Antyna da zasu kawo lefe gidanku gobe, wataƙil bai fi daga ita sai kuma wasu mutane biyu ba zasu kawo kayan saɓanin yanda ake kawowa wasu".
Sosai jikinta ya gama mutuwa murus, tallafe kuncinta tayi haɗi da cewa"wannan ba matsala kuma bana tinanin hakan ma zai zamo matsala a gidan mu, koda kuwa mutum ɗaya ne ya kawo. Batun dangi kuwa ai kai kake da dangi masu yawan gaske ma kuwa".
"Ni kuwa?".
Kanta ta ɗaga masa tamkar tana gaban sa kana ta ɗaura da"ƙwarai kuwa kai da Allah ya yi wa gata ka rayu har tsawon wannan lokacin da mahaifiyarka, ga kuma ɗan-uwa ba ko wani ba wa Allah yake yi wa irin wannan gatan ba sai ɗan baiwa. Waɗannan sun isa dangi kuma garkuwa a gare ka" .
Cije leɓɓansa ya yi yana shafa gefen fuskansa sosai yake jin zantukan natan suna samun matsugunin zaman dirshan, a cikin zuciyarsa sai da ya ɗauƙi sakannai kafin ya a sakalance ya furta"haka ne kam to yanzu dai za'a kawo kayan amaryan bata nan kenan?" Sai da ta murmusa kana ta ce"ai ko tana nan ma ba lalle ta gani ba". Zaro idanunsa waje ya yi"meyasa?".
"Kai ai sai a bani lambar yabon rashin kunya". Bai san sanda wani dariya mai ƙarfi ya kuɓuce masa ba sosai yake sakin sa babu ƙauƙautawa da rabon sa da ya yi makamanciyar sa har ya mance.
Sai da ya tsagaita don kansa ya ce"to meye abin rashin kunya sai yaushe kenan za ki gani?".
"Ai sai an kai ki gidanki sai ki ga kayan".
"To shikenan tunda haka n...". Bai ƙarisa ba saboda sallamar da Farouk ya fara yi a ƙofar ɗakin yana knocking a hankali tashi ya yi ya buɗe masa sannan ya dawo mazauninsa ya zauna yana cigaba da wayan.
Ɗago idanunsa ya yi ya sauƙe akan Farouk ɗin da ya tsaya yana kallonsa, idonsa ɗaya ya ɗaga masa alamar lafiya ya sakar masa da murmushi kamar mai raɗa ya ce"please Yaya Saif haɗa mu ni gaisa dan Allah".
Bai ce dashi komai ya ɗauke idanunsa daga kan sa yana cewa"Umar ne wai za ku gaisa".
"Ni ai har nayi fushi ko sau ɗaya bai taɓa cewa zamu gaisa ba".
Miƙa masa wayar ya yi ya tashi ya shiga bathroom ya saƙarwa kansa shower, sannan ya fito ɗaure da towel a waist ɗinsa ware idanunsa ya yi akan Farouk ɗin da ya zage yana ta zuba suturai babu alamar zai tsagaita nan kusa, kansa kawai ya jinjina ya wuce ya ɗauko kayansa daga wardore ya sanya dai-dai sanda suka yi sallama ya na ajiye masa wayar. Hannu ya miƙa masa ya riƙe suka wuce ɗakin Ummi.
Yaya Majid na ƙira nake sanar dashi result ɗin mu da aka sake ya yi mana murna da fatan alkhairi sosai ban ɓoye masa komai ba har na Nazifa na sanar dashi ta yi ta jimamin zancen. Shi ya ce damu idan ta rubuta lambar booklet ɗin ta ba exams ɗinsa zai mu iya zuba wajen exams officer muyi reporting za'a nemo booklet ɗin. A bakinsa nake jin kawo kayan lefen Zakiyyan, muna gama wayan kuwa na ƙira Goggo na dunga zazzaga mata rikicin Anty Zakiyya bata sanar dani za'a kawo kayan ba ita dai lallaɓa ni kawai take yi kafin ta miƙawa Anty Zakiyyan wayan na ɗaura daga inda na tsaya da rikicin. Ita lallaɓa ni tayi nan nake tambayarta yaushe zata koma potiskum ɗin ta ce dani su Abba sun ce sai an shiga satin bikin sannan zasu zo tare da Goggo.
Washe gari tun asubahi Farouk ya tafi kano domin shi zai yiwa su Anty Fauza jagoranci izuwa cikin garin potiskum, da ita da wasu aminanta biyu suka taho karɓan girma da mutuntawa aka yi musu sosai a potiskum. Cirko-cirko matan gidan suka yi tsaye suna leƙo kayan akwatin da ake shigowa dashi ana wucewa sashin Hajiya Babba dashi, kallon-kallo suka shiga aikawa junan su kafin Umman Salma ta ce"to waɗannan kayan fa na waye?".
Ɗage kafaɗa Umman Ikilima tayi"ke kuwa kya tambayi kaza hanyar zuwa rafi, ina zan san na waye ne".
"Zainab amshi wayata ki ƙira Adamu ko iyayensa ne suka kawo kayan". Juya idanu Zainab dake tsaye ta gefe tayi ta karɓi wayar tana nemo lambar Adamu ta danna masa ƙira tana komawa gefe guda, idon kowa ya dawo kanta har ta gama wayar ta dawo cikin shaƙewa murya ta ce"Umma ya ce wai ba shi bane".
"To tirkashi to in ba shi bane waye kenan?, na ga dai yanzu a kaf gidan nan ku ne za'a auren nan kusa" .
"To Umma ya dai ce bashi bane". Zainab ta faɗa tana danƙwafa mata wayarta a gaban ta ta shige ɗakin su. Ɗaya bayan ɗaya duk suka watse ana sakin ƙananun maganganu.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 1⃣1⃣4⃣
A sashin Hajiya Babba aka bar kayan, rashin samun fuska shiya sanya matan da zugan ƴaƴansu yiwa bakunan su linzami.
Tunda aka sanya lokacin bikin kullum cikin lissafi nake yi izuwa yanzu na sanar dasu Nawwara cewar bikin Anty Zakiyya ya matso amma ban yi gigin sanar dasu wanene mijin ba duk aminta da yardan dake tsakanin mu, kullum muka yi waya da Umma sai na yi ta roƙon ta akan ta tambaya mini su Abba su lamince mini na dawo ta kan ce dani"ki ƙara haƙuri ko ita Zakiyyan ma sai an shiga satin bikin suka ce zata zo, kin ga kema wataƙil sai lokacin".
Babu yanda na iya haka nake haƙura idan muka yi waya na haɗa su su gaisa da su Nawwara. Da kanta take ƙara jaddada musu zuwa bikin natan wajibi ne a gare su, sai ranan talatan bikin da safiya yaya Majid ya ƙira ni a waya yake sanar dani cewar na taso gobe. Ranar tsabar murna bacci na ma ragagge ne Nawwara ta ƙira kawunta ta sanar dashi da farko bai bar ta ba sai da muka ta yi masa magiya kana ya amince bayan ya ce mu turo masa lambar yaya Majid su yi magana, haka nan ma Nazifa ta ƙira yaya Amin ta sanar dashi da kan shi ya yi mata alƙawarin zuwa ya kawo mu har cikin garin potiskum.
Washe gari kuwa tun gabani ƙarfe goma mun gama shiri muka yi sallama da kowa, bai ɓata lokaci ba yaya Amin yazo ya kwashe mu har cikin potiskum har ƙofar gida ya kaimu bisa ga kwatancen da nayi masa. Muka ɓalle marfin ƙofar muka fito dai-dai na yaya Majid yake fitowa daga cikin gidan muka bar su suna gaisawa da yaya Amin mu kuwa muka shige ciki.
Babu yawan jama'a a gidan daga iya yamu ƴaƴan dangin sai kuma wasu daga cikin matan unguwan, tun kafin mu ƙariso suka zubo mana na jiyamun su suna bin ɗagawa da sauƙewa ƙafafun mu da muke yi a tare da kallo.
"Lalle marhaban da zuwan manyan ɓaki kune tafe cikin wannan ranan?".
Furcin Hajiya kenan da suka yiwa kunnuwana diran ba zata, na waigo da sauri ina jan hannun Nazifa muka isa gare ta bisa tabarman da take zaune tana gyaran tumatur muka zauna. Annurin dake kan fuskana har cikin zuciyana na gaisa ta ta amsa mini cikin kulawa da hakan ya bani ƙarfin gwiwan ɗaurawa da"Hajiya waɗannan ƙawayena ne Nawwara da Nazifa".
Gaishe ta suka ƙara yi ta amsa tana bin su da kallo haɗi da faɗin"kun sha hanya kam sannunku".
"Yauwa mun samu ku lafiya ya shirye-shirye?".
"Alhamdulillah".
Ɗan waigawa nayi na ce"ina Umma ba ban ga ta tunda muka shiga?".
"Yanzu ta tashi daga nan wataƙila ta shiga bayi ko kuma tana ɗakinta".
Kaina na jinjina ina miƙewa haɗi da faɗin"bari mu shi ciki". Da kalman to ta raka mu dashi muka tashi sai da kuma gaishe da kaf matan dake gurin cikin jimla guda kana muka nufi ɗakin Umma.
Bata ciki illa wasu mata huɗu da muka iske da ban shaida su ba muka gaishe su muka fice izuwa ɗakin mu da su Zainab suke amfani dashi. Sharewa nayi na kunna mana turaren wuta na tsinke kafin na fito domin kai musu ruwan wanka bayi ina fitowa muka yj kiciɓus da Daada faɗaɗa fara'ata nayi na gaishe ta, fuskarta da murmushi ta ce"ba zan amsa ba tun ɗazun ba ki nema inda nake ba, sai yanzun".
Kafin na bata amsa na jiyo muryan Umman Balkisu tayi caraf ta amshe zancen da faɗin"ina kuwa zata neme ki har ta gaishe ki Halimatu, mu ma nan gaisuwar kamar ba'a so aka jefo mana ita daman meye kike tsammani daga gare ta da ya wuce hakan?". Ta ƙare zancen tana kwaɓe fuska tare da sakin wani dogon tsaki mai dogon zango.
"A'a Zinaru ki ce dani ita ce ƴar bokon gidan na kun mana, oh ni Lauratu jikar mutum huɗu idan baka mutuwa a wannan duniyar zaka ga abu iri-iri ke kuma salon da bokon ya koyar dake kenan?".
Ƙuri nayi ina bin su da ido cike da maɗaukakiyar mamakin furcin nasun, don cikin su gabaɗaya babu wacce bamu gaishar ba kafin mu shiga ɗaki. Ban dawo daga iyon da nake yi a cikin koramar ruwan mamakin da na dulmiya ba naji hannun Daada bisa kafaɗuna na maido da dubana izuwa gare ta, har yanzu da wannan fara'an a kan fuskar ta ce"wani abun kika fito nema ne?".
Kaina na jijjiga mata a sanyaye na ce"A'a mun zo tare da ƙawayena ne zan kai musu ruwan wanka".
"To ki koma wajen su zan sa a kai musu, in an kai zan sanar dake".
Ban iya amsa mata da baka ba sai kaina da na ƙara jinjina mata na koma ɗaki ina satar kallon matar, ban bari su Nawwara sun fahimci komai daga yanayina ba na saki fuskana mu ka fara hiran mu.
Har abinci Daada ta aiko musu muka ci suka yi wanka muka yi salla sannan muka fito zan kai su su gaisa da Hajiya Babba, a daidai mashigar shiga sashinta muka haɗu da Umma da Goggo Jummai su na ƙoƙarin fitowa rungume Umma nayi cikin ƙololuwar farin-cikin ganin ta ina gaishe ta ta amsa mini. Sake ta nayi ina gabatar mata da Nazifa da Nawwara ɗaya bayan ɗaya suka haɗe baki suka gaishe ta amsa musu cike da kulawa kafin ta shiga jera ta mini tambayoyin na basu abinci sun ci na ce da ita e. Fita suka yi mu kuma muka shige rasa inda zata sanya mu Hajiya Babba tayi don murna bakinta sam ya gaza rufuwa, nan muka zauna Hajiya Babba tana ta cika su da suturu har sai da aka yi asr muka yi aka yi magrib sannan muka koma sashin mu Nurain ya maƙalƙale mini duk inda zan jefa ƙafata yana bi ye dani tamkar jela. Ina ƙoƙarin zame rigar jikina Nazifa ta ce"ni kuwa ina sistern naki Salma da aka yi bikinta kwanaki?".
"Salma tana nan kusa ma muke may be sai gobe zata zo, har su Abasiyya da sauran yayunmu".
"Ni kam tun zuwan mu ban ga Anty Zakiyyan ba?".
"Tana nguru a can gidan Goggon mu gobe zasu iso". Na faɗa ina jame rigar daga jikina tare da ɗaura zani.
"Gidanku da yawan ku abin ku ku kaɗai ma kun isa taron biki masha Allah, ina sha'awar irin haka". Ban kai ga bata amsa ba sallamar da Zainab tayi muryarta a cunkushe ya ƙare mini hanzari.
"Anty Na'ima su Abba ba ƙira". Tana dasa aya ta saki labulen da ta ɗago ta koma, wata rigar na ɗauko na sanya a jikina ba ɗauka hibaj a kai na juyo na kallon su na furta"ina zuwa". Kafin na fice izuwa sashin su Abba da sallama ɗauke a bakina na shiga falon da ya sama halaltan kusa dukkan jama'ar gidan ina zama Hauwa'u da Amina suka shigo a ƙarshe muka cika cif-cif.
Tsawon mintoti babu wanda ya yi magana sai fitar numfashin juna da muke sauraro, sai can Baba ya soma faɗin"mun tara ku ne game da wani lamarin da yake gudana a cikin gidan nan, tun daga zuwan kawo waɗannan kayan". Ya ƙare zancen yana nuni da akwatunan da sai yanzu ba lura dasu guda bakwai reras wani na kan wani bi-da-bi masu launin ruwan zuma, zancen da ya ɗaura dashi ya dawo dani hayyacina tare da ɗauke idona daga bin akwatin da kallo da nake yi na maida gare shi.
"Auren ɗaya daga cikin ƴaƴanku za'a jibi juma'a idan Allah ya kai mu". Zaro idanu kowa ya yi ba tare da samun ƙarfin yin magana ba, a hakimce Umman Zainab ta furta"In ce iyayen Adamu ko yaron dake zuwa wajen Zainab?".
Wani murmushi taƙaitacce Baba ya saka kana ya ce"ba iyayen Adamu bane domin tunda muka ce ya turo ba mu sake jin ɗuriyarsa ba daga shi har iyayen na sa..".
"To in ba shi bane waye kenan ko ɓatan hanya aka yi aka kawo kayan nan bisa kuskure?".
Sai a lokacin Hajiya Babba ta magantu"kayan lefen ɗiyarku ne Zakiyya da za'a ɗaura jibi in sha Allahu". Ɗif numfashin da yawa mazauna falon ya ɗauke na wucen gadi, razani bayyane ɓaro-ɓaro a bisa fuskokin su, murya a dishashe Umman Balkisu ta furta"wacce Zakiyyan tukunna?".
"Zakiyya dai guda ɗaya da muke da ita a cikin gidan nan". Goggo Jummai ta bata amsa a dake.
"Tirkashi! tashin hankali wai na zaune ya faɗi".
"Ko akwai wata matsala ne?". Hajiya Babba ta jefa mata tambayar tana saida idonta a kanta, sai da ta yarce zuffan da ya yi mata lijib a saman goshinta kana ta sama damar faɗin"a'a babu wata matsala Allah