Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
tausayinsa suka soki dai-dai ƙalbina da dafinta ya barbazo a ko'ina a cikinta tunin ƙwalla suka baƙunci kurmin idaniya da suka fara tsiyaya a hankali suna shawagi a saman dakalin fuskana.
Hajiya Babba ta ɗaura da nata"takwara ina yi miki fatan alkhairi da addu'ar Allah ya sanya kin fata a sa'a kin kuma shiga da ƙafar dama ya kaɗe dukkan sharri ya sada ki da nasarorin dake ciki".
Kalmar amin ita ce take fitowa daga bakunan mutanen wajen, kafin Baba ƙarami ya amshe zance da faɗin"babu abinda zance dake domin duk abinda zan faɗa Hajiya da yaya sun faɗa miki shi illa iyaka na ƙara maimata miki wani abun domin su kasance kamar tini a gare ki, ki riƙe mutuncinki a duk inda kika kasance kuma ki riƙe addininki koda wasa kar kiyi wasa dashi kuma ban da biyewa shashanci maza da mungayen ƙawaye".
Haka suka yi tayi mini nasihohi masu ratsa jiki da katse wa mutum jiki ta hanyar tsirkar masa da dashen imani a cikin ƙirjinsa, har su Goggo Suwaiba da Goggo Jummai sai da suka yi mini nasiha sosai. Kuka kawai nake yi bil haƙƙi na ma kasa samun bakin da zan furta musu kalmar godiya. Duk suka sanya mini albarka Hajiya Babba tana jana da tsokala a ƙoƙarin ganin na warware daga suƙurewar da nayi da baya rasa nasaba da kewar su da zanyi da kuma fargaban yi rayuwa ba tare dasu a kusa na ba in ba aure ba da ya zama dole mutum ya dusa daga gaban iyayensa ko tafiyar cikakken sati ban taɓa yi ba balle irin wannan da zaka yi nisa da gida sai jifa jifa ka sanya wani naka cikin idonka.
Idona ƙulu-ƙulu na fito daga sashin na nufi namu sashin kamar wacce aka zarewa laka a jikinta ina tafe ina jan ƙafa ina shigowa sashin aka ɗauke wuta duhu ya mamaye yalwataccen filin tsakar gidan namun. Muryar Umman su Ikilima shi ya fara yiwa ƙofofin kunnuwana dirar mikiyar da ya sanya ni tsayawa cak tamkar sassaƙaƙƙen ice ina jin wani jiri mai ƙarfi yana ƙoƙari kifa ni da ƙasa.
"Ai ni ido kawai na zuba musu daga su Malam, Hajiya Babbar har ita Aminatun da Na'ima da suke wani rawar jiki da komawar ta makarantar ko yaushe ana hanyar kasuwa zuwa yi mata sayayya, nan gashi auren su Firdausi ne ke matsowa amma da nayi masa maganar zamu fara taro tun yanzu kaɗa baki ya yi ya ce min bashi da kuɗi. Amma da yake lamarin na ƴar gold ne ya sako bakin aljihu kamar bai san wahalar nema ba. In ba'a yi sharan masallaci ba ai ala dole ayi ta kasuwa wanda babu godiya balle madalla ta yaya za'a tura zankaɗeɗiyar baligar yarinya mai cikakken lafiya kamar Na'ima wai jami'a alhalin tana bazawaran da ta san daɗin ɗan namiji me kike tinanin zai faru? bacin ta ɓuge da bin maza".
"Hmm kedai bari nima nan ido kawai na tsura musu domin ganin dogon ruwansu, yanda suke murnar wannan tafiyar ta tan ni nan na faɗa miki wannan zancen nan gaba kaɗan zata jirkiɗe ta koma baƙin-ciki lokacin da ta kwaso musu abun kunyar da zasu rasa inda zasu sanya kansu, wataƙil ma su haɗiye zuciyoyinsu su mutu".
Wani irin zafi naji cikin ƙirjina ya riƙe mini haƙarƙari gabaɗaya, cak yawun bakina ya kafe tamkar rijiyar da aka yi yasa na gaza samun wanda zan jiƙa bushashshen maƙoshina dashi. Babu shiri jikina ya ɗauki rawa dai-dai sannan aka dawo da wutar nefa haske kwayayen wutan suka garauye filin tsakar gidan, ban sani ba ko lura dani tsaye a wajen ne ya sanya su yiwa bakunan su linzami oho, koda da ban ɗago ba ina jin idanunsu a jikina alamar ni suke kallo. Naso bin shawarar zuciyata da take cewa dani kar ma na nuna musu cewar naji abinda suke faɗi sai dai yanayina ya riga da ya fallasa hakan don haka bani da wani zaɓi.
Kamar wacce ake janta hakan na isa gabansu tare da cilla ƙwayayen idona cikin nasu, tun kafin nayi maganar hawaye suka fara kwaranyowa daga idona. Cikin shaƙewar murya nake faɗin"In sha Allah zan riƙe kaina a duk inda na kasance kuma ba zan taɓa watsawa waɗanda suka ɗauki yarda suka ɗaura mini ƙasa a idanunsu ba, zanso ku ɗauke ni ƴa kamar yanda ni nake muku kallon uwaye a gare ni domin a wannan lokacin ina buƙatar addu'ar kowa ciki kuwa hadda ire-irenku".
Ina dasa aya a nan naja sanƙararrun ƙafafuna nayi wucewata ɗakin Umma ba tare da na yarda mun haɗa ido da Hajiya da fitowarta kenan ba daga ɗakinta tana tsaye ta ɗago labuyen ɗakin. Zaune na iske Umma na faɗa jikinta tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taɓa zuciyar duk wanda yake saura, ba kaɗan ba ta rigice sai jero min tambayar lafiya take yi babu ƙau-ƙautawa ganin halin da ta shiga ya sanya ni cewa da ita kawai kewarsu da zanyi ne yake saka ni kukan.
Sai naga ita ma hawayen sun mata ido ta riƙo haɓata tana kallon cikin idona take faɗin"ba kuka za kiyi ba Na'ima addu'a za ki yi Allah yasa kin fara a sa'a kuma ya haɗe miki hau da bala'i da sharrin dake cikinsa, ki kama kanki ki riƙe mutuncinki ki kuma kare martaban gidan da kika fito daga cikinsa. Kinga salla ki riƙe salla kar kiyi wasa da addininki duk shagogin da za ki shiga ki tabbatar kinyi ta akan lokaci kar kije garin neman duniya ki ɓata lahirarki, ba ruwanki da ƙawaye balle kuma shiga shirgin maza abinda ya kai ki kaɗai shi za kiyi".
Kwantar da kaina nayi a kafaɗarta tare da lumshe idona ina jin nasihar tatan tana ratsa ni sosai, har Anty Zakiyya da yaya Majid suka shigo suma suka ɗaura daga idan ta tsaya kafin muka kafa dandalin hira har ƙarfe goma sha biyun dare kafin kowa yaje ga makocinsa.
Washe gari ƙarfe goma na gama shirina tsaf yaran gidanmu sai shigwa suke yi muna sallama Balkisu, Abasiyya duk sun zo munyi sallama da ɗaiɗaiko wanda suke gidan aurensu suma sun zo duk da kuwa mafi yawansu ba zuwan Allah da annabi bane.
Su Abba suka ƙara yi mini nasiha sosai tare da ɗaukar wani kuɗin suka bani suka ce na riƙe a hannuna hakan nan ma Hajiya Babba da Ummata duk sun bani Yaya Majid da Goggo Jummai tare dasu zamu je.
Da guntun hawayena na fito daga ɗakin Umma bayan mun gama yin sallama zan tafi, Firdausi ta fito daga bayi da sauri ta nufi tana faɗin"tafiya Anty Na'ima?".
Na ɗaga mata kaina haɗi da faɗin"e Firdausi amma in sha Allah zan na zuwa ganin ku ai".
Kamar jira take Ummansu ta amshe zancen da faɗin"ai ita ma in sha Allahu ba za ki dawo ki iske ta a cikin gidan ba lokacin tana ɗakin mijinta tana bautar Allah don mu ba duniyar bace a gabanmu".
Bance da ita komai ba illa murmushi mai ciwo da na sakar mata na shige ɗakin Hajiya ita ma tayi mata sallama ta rako ni da addu'ar fatan alkhairi muka ɗauki hanya dasu yaya Majid.
Ba'a cikin jaharta ta yobe jami'ar take ba don akwai tafiya tsakanin mu sosai sai da bayan sallan zuhr muka isa cikin gari muka hau adaidaita ya kaimu makaranta.
Idanuna suka sauƙa akan sunan jami'ar da aka rubuta da manyan harrufa a mashigar shiga(ba sai na kama sunar jami'ar ba domin zan yi tonon sililin da ba kowa zai so ji ba).
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
______________________________________
Page 6⃣2⃣
Bansan dalilin da ya sanya mini faɗuwar gaba da matsanacin bugun da ƙirjina yake yi ba, muka kusa cikin makaranta tun daga kallon farko da nayi mata na yaba da kyawunta da kuma tsaruwarta korayen shuke-shuke shar-shar dasu abin gwanin ɗaukar ido da sha'awa ga dogayen gini hawa hawa. Shimfiɗaɗɗen kwaltar da aka zuba muka bi izuwa cikin makaranta mutane ne kowa yana abinda yake gabansa babu ruwan wani da wani balle shiga shirgin juna, idan ka iya allonta sai ka wanke kasha idan kuwa baka iya to shima ruwanka.
Kasancewar yaya Majid ya taɓa zuwa makaranta lokacin da yazo yi mini rejista ya sanya mu kai tsaye ya wuce damu department ɗinmu.
Dake ƙarƙashin faculty of social sciences nan ma nasha kallo don komai a tsare yake ga wasu kujerun da aka yi su da ciminti a jera su reras suna kallon juna, mun daɗe muna tsaya cikin department ɗin har wasu suka fito daga lecture, idanuna na tsura musu don ba kaɗan ba suka burge ni cikin dress code ɗin su na suit kamar yanda tsarin yake maza dogayen wanduna ne a jikinsu mata kuwa siket chiristan su saka wando da hula ko gyale a maimakon hijab.
Ganin muna ɓata lokacin ya sanya mu fitowa muka ɗan ƙara zagaya makaranta yaya Majid sai nuna mini wasu wajajen yake yi kamar su school library, cafe ɗakunan karatu da dai sauransu daga nan muka zarce wajen masu gadin da muka barwa ajiyar kayan akwai labourers da suke shigarwa mutane kayan ciki ana biyan su, muma su suka ɗauka mana bisa jagorancin suka kai mana har bakin female hostel ya dire mana da taimakonsa na sama room ɗinmu da nake riƙe da lambar ɗakin ya kwatanta mini. Nida Goggo Jummai muka shiga yaya Majid ya tsaya daga waje domin labourer ɗin ya shaida mana cewar maza basha shiga kayayyakin kuwa ya kawo mana su har bakin ƙofa muka ƙarisa shiga dasu.
Nan ɗin ma kowa harkan gabansa yake wasu suna taran ruwa, wasu suna zaune suna kitso wasu kuwa suna hira gefe guda kuwa masu duba takardunsu nayi gefe can masu waya nayi suma. Daga ni har Goggo Jummai bin su muke yi da kallo baki a hangame kafin ɗaga daga cikin waɗanda suke ɗebar ruwan ta ka katse mana hanzari da faɗin"bayin Allah sannunku sabuwar zuwa ce ko?".
Kaina na ɗaga mata Goggo Jummai ta ce"e ƴar nan ɗakin nan muke nema". Ta ƙare zancen tana miƙa mata lambar ɗakin da ta bar ɗeban ruwan ta taso ta mashi takardan ta duba da murmushinta fal akan fuskarta kamar gonar auguta ta ɗago kanta tare da sauƙe manyan idanunta a kaina tana faɗin"ai wannan ɗakinmu ne shikenan mun cika mu uku abin mu muje na kai ku".
Godiya Goggo Jummai tayi mata sannan muka nufa ɗakin tana gaba muna biye da ita a baya har cikin ɗakin, dake ɗauke da dungu uku ɗauke gadaje uku biyu daga farko sai ɗaya daga can ciki sai kuma wani ɗan lungu da suka shimfiɗa sallaya da nake kyautata zaton cewar wajen salla suka tanada. Da taimakon baiwar Allahn nan muka jere kayan na shimfiɗa shimfiɗa akan katifar dake kan gadon da sauran kayana cikin lokan dake manne cikin ginin ɗakin.
Sai da aka yi ƙiran sallan asr sannan muka kammala duk muka yi alwala muka yi salla, ta kawo mana shinfaka da wake.
Washe baki Goggo Jummai tayi tana bin ta da kallon birgewa kafin ta furta"sannu baiwar Allah kina ta wahala damu ko sunanki ba ki faɗa mana ba".
Sai da ta saki dariya ƙasa-ƙasa kana ta amsa da faɗin"sunana Nawwara".
"Masha Allah Nawwaratu to Allah ya yo albarka ku maida hankali ga karatunku don Allah, ga Na'ima nan mu kula da junan ku".
Haɗe baki muka yi da Nawwara wajen furta kalmar amin idanunmu cikin na juna ina ƙara yin soyayyarta na mamaye dukkan kusurwan ƙalbina a ɗan zaman awannin da muka yi da ita nikam na fahimci bata da matsalar rayuwa uwa uba ga sakin fuska fara'a kuwa tamkar gonar auduga kyauta take raba dariyarta ga kowa sanannane a gare ta ko kuma baƙo, sai da muka ci abincin sannan Goggo Jummai ta miƙe zata tafi muka fito raka ta har da Nawwara muka iske yaya Majid yana fitowa daga masallacin dake cikin makarantar suka gaisha da Nawwara bayan Goggo Jummai ta shaida masa cewar ƴar ɗakinmu suka gaisha har gate muka raka su.
Sanda naga cewar da gasken tafiya zasu yi na saki kuka tare da rungume Goggo a jikina tsam kamar wani zai kwace mini ita. Itama ta fara hawaye yaya Majid ne ke rarrashinmu haka ina ji ina gani suka hau adaidata suka tafi suka barni sai da adaidaitan da suka hau ta ɓacewa ganina sannan muka koma hostel muna tafe Nawwara tana jana da hiran da bana fahimtar komai don tun yanzu hankalina ya yi gida.
Muna isa na ƙira Umma na sanar da ita mun isa har su yaya Majid sun jiyo ta ce mini ai sunyi waya da Majid ɗin ma ya sanar mata komai nasihar dai ta ƙara yi mini da umarta ta da na zauna da duk wanda Allah ya haɗa dasu lami ya lafiya ƙalau ba tare da wata fitina ya taso daga wajena ba. Mun daɗe muna wayar har sai da naji matar nan ta kamfanin layin Mtn ta fara yi mini gargaɗi akan saura na naira uku a cikin katin ɗari biyun da yaya Majid ya sanya mini da zamu taho kana na haƙura na kashe wayar.
Na tambayi Nawwara ina ne banɗaki domin babu abinda nafi so yanzu kamar na watsawa gajiyayyan jikina ruwan, ta nuna mini da kanta ta ɗeba mini ruwa ta kai mini kana ta haɗo ni da omo da tsintsiya ta ce na warke banɗakin dake da ƙarancin tsafta kafin nayi wanka.
Sosai naji daɗin jikina da nayi wanka na fito na wuce ɗakin mu, su biyu na iske su ɗayar tana ninke hijabinta da ta cire shi na shigowa musayar murmushi muka yiwa junanmu. Kafin tayi mini sannu na amsa mata ta kallo Nawwara da take zaune tann aikin danna wayarta ta ce"ko ita ce kike faɗa min?".
"E ita sunanta Na'ima ɗazu suka zo, Na'ima da Nazifa ƴar ɗakin nan ce ita ma".
"Sannunki".
Na kuma faɗa ina tsayar da idona akan farar fuskarta, ta amsa mini dai-dai sanda take ajiye hijabinta da ta kammala ninkewa tana faɗin"ba kiyi girki bane Nawwara?".
Harararta tayi"ko nayi ma to babu rabonki a ciki domin don Na'ima nayi ehe malama in za ki zage ki nemawa cikinki abinda za ki ci ma ya fi miki".
Kwaɓe fuska tayi ta ce"haba dai besty wallahi ba ki san gajiyar da na kwaso bane nayi matuƙar gajiya kinsan Antyn nan tawa fa da shegen son jiki da ka ce zata sake maka komai tayi kwanciyarta".
Dariya sosai Nawwara ta saka har da riƙe ciki da hakan ya ƙara ƙular da Nazifa ta banka maka harara, dariya ce ta kubce mini ba tare da na shirya ba da hakan ya sanya Nazifa kallo ni kana ta ce"har da kema ko?".
"A'a wallahi ni ba ke nake yiwa dariya ba, akwai abin nakun ne kamar drama shi ya sanya ni dariya. Amma kiyi haƙuri bari nayi salla sai mu ɗaura abincin". Tun kafin na gama ta daka tsalle ta rungume ni tana murna, Nawwara ta saki tsaki ta ce"haka dai kika iya sai shegen cin tsiya amma bakya son aiki sam baƙya son motsa jikinki, a hakan wai kike cewa Anty son jikine da ita har kura ce zata cewa kare maye".
Duka Nazifa ta kai mata tayi saurin kauce, doguwar rigar material mai sauƙin nauyi na saka sannan nayi sallan magrib ban tashi daga wajen ba sai da aka yi isha'i nayi ina raka'ar ƙarshe wayata da na jona a caji ta fara ruri kafin na sallame ƙiran ya tsince ban bi ta kanta ba har sai da na shafa addu'ata kafin na ciro ta dai-dai sanda ƙiran Abba yake kuma shigowa cikin wayar wani annashuwa suka wanzu a fuskana da sauri na ɗauka ina gaishe shi ya amsa mini ina ta tambayarsa yaya mutanen gidan ya saki dariya da faɗin sai ka ce ba yau kika tafi to su na nan yanda kika barsu. Nima dariya nayi sannan na ce ya ba wa Hajiya Babba wayar ya bata muka gaisa haka nan ma su Baba da Baba ƙarami mun daɗe muna wayar har Nazifa ta fito daga wankar da ta shiga Nawwara ma ta shigo, na sanya wayar a handsfree na cewa Hajiya Babba ga ƴan ɗakinmu zasu gaisa sunji daɗi sosai suka gaisa kamar sun san juna a zahiri. Sai da na katse ƙiran muka huta gawayi muka tafasa taliyar da na taho dashi don Nawwara ta ce mini raba girki suke yi kwana bibiyu a tsakaninsu.
Muna ci muna hira don suma duk ƴan department ɗin mu ne hakan ya ƙara ƙarfafa hirar tamu da muke yi akan lectures ɗin da zamu fara yi jibi.
AYI haƙuri da wannan
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 6⃣3⃣
Washe gari na tashi cikin matuƙar nishaɗin da ni kaina ban san dalilinsa ba, tunda kafin na tashi daga baccin gajiyar da nake yi wayata take ta faman ruri da ƙyar na iya cira kaina na ɗauko ta ganin sunan yaya Majid ya bayyana cikin screen ɗin ya sanya baccin idona wartsakewa tas murmushi mai kyawu ya lulluɓe fuskana. Na ɗaga wayar cike da zumuɗin son jin muryarsa kwana ɗaya da nayi ba tare da na sanya su a cikin idona ba wani kewarsu ya riƙe mini ƙirjina ji nake yi tamkar nayi wata guda ban gansu ba, ina ɗauka na fashe masa da kukan da ya sanya su Nawwara tashi suka zubo mini ido fahimtar da wanda nake waya kuma ba wani abin tashin hankali bane ya sanya su komawa suka kwanta bayan sun gama yi mini dariya.
Nikam kukan nake yi da dukkan gaskiyata shima yaya Majid ɗin yana sakar mini dariya, ya ba wa Umma muka gaisa haka nan ma goggo Jummai da Hajiya Babban ita kam mun daɗe muna hira da ita kafin muka yi sallama. Rumgume wayar nayi a ƙirjina tare da lumshe idanuna wani siririn hawaye suna biyo kuncina yayin da tsantsar ƙaunar ahalina da ban taɓa haɗa shi da komai ba suna ƙara wanzuwa a cikin ƙalbina tabbas suna da matsayi na musamman a gare ni da babu wanda zai iya isowa idan suke ba balle har ya yi cuɗanya dasu a wannan fannin.
A hankali na ware idona da suke a lumshe ina bin ɗakin namun da kallo, wai yau ni Na'ima