Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
ɓaci".
"Ki kwantar da hankalinki Na'ima in sha Allah babu abinda zai faru, inma ya faru ko ki sanya a ranki cewar zan wanke ki tas".
Ta faɗa ba tare da ta juyo mun haɗa ido ba, fita tayi ta barni da sakin wani wawan ajiyan zuciya fargaba da zulumin da na kwana dashi a raina suna ƙara tsananta.
Wani ƙaton taƙaici ya rufe ni sai yanzu ma nake jin haushin kaina to in yazo ma meye zance dashi?, meye zai mini?. Ƙwalla suka baƙunci kurmin idona ina tuna yanda ya wurgo mini farar takardan dake ɗauke da saki uku reras a fuskana. Nayi nisa cikin tinanin ban yi aune ba naji an turo ƙofar ɗakin an shigo, nayi saurin kai duba wajen gabana ya yi wani irin mummunan faɗuwa tamkar wacce tayi tozali da mutawarta. Duk yanda naso janye idona daga cikin nasa hakan ya gagare ni kamar yanda shima ya kasa kawar da nashi idon daga kaina. Lumshe idanuna nayi na buɗe su a hankali ina bin sa da kallon tamkar yau ce ranar farko da na saba sanya shi a idona.
Ya yi wani irin mummunan ramar nan marar daɗin gani a ido balle furtawa cikin kalmomin baki, farin nan nasan duk ya rikiɗe ixuwa launi mai duhu idanunsa sunyi ciki-ciki ga bangejin da yake kewaye da kansa da kuma hannunsa da kamar ɗaurin karaya ce sai ƙafarsa da yake ɗingisata.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 5⃣0⃣
Kalmar auzubillahi na shiga nanatawa cikin raina domin samun nutsuwar da na rasa. Kafin nayi ƙarfin halin janye idona daga cikin da nasa da suka sarƙafe cikin na juna tun ɗazu.
Runtse idona nayi da ƙarfin ina yaƙar zuciyata akan abinda naji yana daso min a zuciyata, ina mai cigaba da nanata kalman nan da nufin samarwa kaina nutsuwa. Ina jin takunsa ya iso har gaban gadon da nake kwance lamau haske ya gauraye ɗakin saboda wutar lantarkin da aka kawo.
"Na-Na-Na-Na'ima".
Ya furta a rarrabe tamkar yaro mai koyan magana, ban buɗe idanuna ba domin jin muryar tasan tayi ta kai mini har cikin kwanyata tana yawo a jikina hakan nan banda niyyar cewa dashi wani abun illa wasu hawaye masu zafin da suka tsiyaya daga idona suna fareti a saman kuncina.
"Na'ima dan Allah ki buɗe idonki ki kalle ni ki kalle ni koda kuwa hakan shine alfarma na ƙarshe da za ki yi min cikin wannan rayuwar. Ki dubi yanda rashin ki ya mayar dani ya zuzurata ni har yana ƙoƙarin raba ni da hankalina dan Allah Na'ima ki duɓe idonki ki kalle ni".
Yanda ya yi maganar ta ƙarshen muryarsa har wani shaƙewa take yi alamar yana dab da sakin kukan, sai da na sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfin da ta gigiza ni ruhi kafin na sama sararin faɗin"babu wata alaƙa da ta rage tsakanin mu Yusuf babu domin da hannunta ka datse hakan. Mun haramta ga junan mu don haka babu amfanin wannan maganar ma da yanzu meke yi da kuma kallon ƙuri da muke yiwa junan sai dai ma mu kwasawa kanmu zunufi".
"Ina sonki Na'ima kin sani kema wallahi ina sonki, son da ban taɓa yiwa wata ƴa mace a gabaɗaya tahirin rayuwata. Ban taso cikin gatan rayuwa da iyayena dukka biyu hakan ya sanya ban san wani abu wai shi soyayya ba Anty Binta ce ta raine mu tun muna da ƙarancin shekaru soyayyarta kaɗai muka sani kuma shine a cikin zuƙatan mu.
Ke ce mace ta farko da na fara sanya ta cikin raina haka zalika ke ce farkon ɗiya mace da na faro da sunan soyayya mai ƙarfi. Yawan rantsuwa ba halayyata bace amma na rantse miki da sarkin da yafi cancanta ban san yaya aka yi har na rubuta miki saki ba. Ban san yanda komai ya faru ba hasalima gani nake yi kamar mafarki nake da zarar na tashi zan farka na ganki kusa dani ina cikin wani halin da ni kaɗai nasan yanda nake ji a raina babu wani maganin da zai yi tasiri a jikina face ke kece maganin cutar da take wahalar da rayuwata Na'ima".
Sai a sa'ilin na buɗe idona sai dai ban kai duba na izuwa fuskarsa ba, tsayar da idona nayi akan rufin ɗakin cikin zubda ƙwalla na soma cewar"baka san yanda aka yi ba fa ka ce Yusuf?, shin kayi tunanin halin walagigin da zaka tsoma rayuwata a ciki balle makomata?".
Ina iya jiyo yanda ya sauƙe wata shirgegiyar ajiyar zuciya kana ya furta"bana cikin hayyacina Na'ima a lokaci don Allah ki yarda dani ki tausayawa halin da nake ciki".
A zafafe na tashi na zauna haɗi da cewar"na taimake ka Yusuf?,wani irin taimako zan yi maka bayan a lokacin da nake buƙatar naka taimakon ka buya mini baya a lokacin da nake yaƙinin zaka tsaya tare da ni tayi tafiyarka babu wani taimakon da zamu iya yiwa junan mu. Na roƙe ka ka tashi ka fita kar ma wani daga gidan mu ya shigo ya same ka ko kuma a lura baka ɗakinka a biyo sahunka".
Bai ce dani komai har na ƙare maganar ina haɗe hannayena waje guda alamar roƙon hawaye suna cigaba da fita daga idona, koda da ban ɗago ba a jikina nake jin cewar idanunsa sun kaina.
Bai ce komai ya miƙe tsaye da ƙyar daga ɗan tsugunan da ya yi gaban gadon, na sata kallonsa naga ya kawar da kansa gafe yana share idonsa da suke zubda ruwar ƙwalla da hannunsa ɗaya mai lafiyar, caraf idanun mu suka sarƙe cikin na juna nayi azaman janye nawa daga cikin nasa ina rusunar dasu ƙasa da hakan ya ba wa hawayen da suka cika kurmin idon damar tsiyaya.
"Ina sonki ina sonki ba zan taɓa daina sonki ba matuƙar ina numfashi a bayan ƙasa, kuma ba zan taɓa barin ki ba".
Tsoro maganarsa ta ƙarshe ta jefa mini cikin ƙalbina har ban san lokacin da na ɗago nayi masa kallo ido cikin ido ba tare da cewar"baza barni ba fa ka ce?, mu ba yara bane yanzu ya kamata mu faɗawa kanmu gaskiya mu kuma mu sanya zuciyar mu dangana akan abinda ya faru mu haƙura da juna Yusuf".
Katse mana hanzari Hajiya tayi da take tsaye a ƙofar ɗakin, da hakan ya dakatar da yaya Yusuf da maganar da ya yunƙuro zai furta. Kunya ta kuma rufe ni domin har ga Allah nikam na mance da kasantuwarta a cikin ɗaki tayi ta sakin baki ina faɗim maganar dake cikina ashe duk suna sauƙa a kunnuwanta.
"Kaje kawai Yusuf kar ɗan uwanka ya dawo daga masallaci bai tarar da kai ba kuma a ɗakin ba kaje ka kawai".
Ƙasa ya yi da kansa yana goge hawayen da suka ɓata masa fuska kafin ya kallo ni kallo mai cike da ma'anoni ya ce a gajarce"na gode Anty".
"Yauwa Allah ya ƙara lafiya".
Banji ya amsa mata ba illa ficewar da ya yi yana ɗingisa kafarsa, na raka shi da kallo hawaye suna gudana akan dandamalin fuskana. Ina mamakin yanda ya zubda hawaye haka sosai abinda a tsawon zamana dashi ban taɓa cin karo dashi ya yi ba kenan. Cikakken namiji ne yaya Yusuf mai ƙoƙarin danne komai a ransa saboda ƙarfin hali da taurin rai irin nasa, sau da yawa ko iyayensu ya tina dasu sai dai kawai idanunsa su kaɗa suyi jajir amma baya zubda hawaye amma yau shine da kuka shaɓe shaɓe tamkar ƙaramin yaro.
Ƙarƙarfan ajiyan zuciya na sauƙe kafin muryar Hajiya su yiwa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya da suka sani wartsakewa.
"Sai haƙuri Na'ima shi rabu akwai shi da zafi da kuma ciwo sai an kai zuciya nisa".
Kaina kawai na jinjina mata ina son yi mata godiya amma na kasa da kanta ta haɗa mini ruwan wanka na shiga nayi. Tun kafin na fito nake jin hayaniyar mutane a ɗakin ƙasa-ƙasa alamar mutanen sun fara zuwa.
Ko da na fito Anty Zakiyya, Goggo Jummai da Hajiya Babba sai kuma yaya Majid da yake dubbuba magungunan da nake sha da likitotin suna ɗaura ni a kai, na tarar a ɗakin na gaishe gabaɗaya suka amsa mini cikin sakin fuska tare da tambayata yaya jiki na amsa da kalmar alhamdulilah sannan na ƙarisa shirya da yake daman na shiga da kayana banɗakin mai kawai na shafa Anty Zakiyya ta tsiyaya mini kunnun tsamiyar da yasha tsamiya a kofi na karɓa ba don jin cewar zan iya sha ba tare da tambayar ta ina Umma ta amsa mini da faɗin wai sai anjima zata zo da rana. Kaina kawai na jinjina na fara kurɓan kunnun a hankalin kaɗan nasha na ajiya da faɗin na ƙoshi dai-dai nan likita ya shigo ya duba jikina tare da yi mini wasu tambayoyi ya ce in sha Allah zuwa yamma ma za'a iya sallama ta sai dai na kula da shan magunguna da kuma ƙaurace dukkan abinda zai ɗaga mini hankali balle a kai ga ya jefa ni cikin damuwa.
Tare dasu Hajiya Babba muka wuni yaya Majid ne kawai ya tafi wajen aikinsa, har yamma raina cike da damuwar halin da naga yaya Yusuf a ciki ko yanzu yaya yake oho. Kifiyar tausayinsa suka sauƙa dai-dai ƙirjina tare da yin nasarar tartsawa mini raunanniyar ƙalbina.
Hajiya Babba ta ce goggo Jummai ta ƙira Umma ta ce ta zauna kawai ba sai tazo ba tunda sallama ma za'a bamu, da yammaci kuwa kusan ƙarfe biyar aka sallame ni tare da shawarwarin likitotin kuma haɗa kayan mu zamu gida.
A farfajiyar asibitin suka yi kiciɓus da Anty Binta da maman Hanan suna shigowa ɗauke da kololin abincin. Ko gaisuwa bata shiga tsakanin Anty Binta da Hajiya Babba ba maman Hanan ce kawai ta gaishe ta a masa mata a daƙile tayi gaba abin ta.
"Yaya jikin nakin?".
Maman Hanan ta furta tana tsayar da idonta a kaina, murmushin ƙarfin hali na sakar mata kafin na ce"alhamdulillahi da sauƙi mum gode".
Taku uku ta ƙara ta matso kusa dani haɗi da cewar"kiyi haƙuri Na'ima lokacin ina cikin tashin hankali har na kasa sarrafa kaina na sanar dake mummunan maganar da tayi silan zuwan ki asibitin nan".
Da murmushin na kuma cewa"kar ki damu ba komai". Har ta buɗe baki da zummar cewa wani abu ƙiran da Anty Binta da tunin tayi gaba ta ƙwala mata ya sanya ta haɗiye zancen.
"Me kika tsaya kina yi a nan?, uwar miye kuke faɗawa juna?".
"Babu komai Anty tambayar ta nake yi yaya jikin natan".
A ɗan daburce tayi maganar kafin ta furta kamar yin raɗa"zamu yi waya". Ta bi bayan Anty Binta da ɗan saurinta, nima bayan su Hajiya Babba nayi da har sun kusa kai wa gate ɗin ficewa daga asibitin muka tari abun hawa muka nufi gida. Har muka isa ban daina saƙa da warwaran da nake yi cikin raina ba, muka iske Umma zaune a filin gidan tana ƙoƙarin haɗa wuta ganin mu ya sanya tasowa tana bi mana barka da zuwa kafin sauran yaran ma suka yi mana bamu zauna ba muka wuce sashin Hajiya Babba nayi kwanciya ta bayan ta bani gwaɗon zolaye na ɗan caccakala. Bayan sallan magrib Salma da Abasiyya suka shigo duba ni suna ta jinjina rama da duhun da nayi cikin kwanakin. Murmushi kawai ni dai nake yi musu don ban da abin faɗa, har sun miƙe zasu fice Salma ta ajiye mini wayata akan cinyata tana cewar"ga wayarki tun da aka kai ki asibiti take wajena naso kai miki ita asibiti sai kuma wannan abin ya faru da ya sani ban ƙara komawa ba". Kaina na jinjina mata tare da sakar mata da murmushin yaƙe suka fice bayan munyi juna a kwana lafiya. Na shiga banɗaki domin sauya augudar matan dake jikina naga jini ya tsaya mini na sama tsarki, nayo wanka na fitk nayi sallan isha'i. Shuru na zauna a ɗakin ni ɗaya na zabga tagumi tamkar wacce aka aikowa da saƙon rasuwar uwa da ubanta na gaza taɓuka komai har aka yi ƙiran isha'i ban gusa daga inda nake zaune ba babu shiri wasu hawaye suka shiga zubo mini so da ƙaunar ɗana ko ƴata da na rasa suka ƙara mamaye zuciyata da fama mini raunin da har yanzu nake jinyarsa.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________________
Page 5⃣1⃣
Juyi kawai nake yi akan gadon Hajiya Babban amma bacci dai kam sunyi ƙaura daga idanuna da suke soye ƙas tamkar na kifaye, a karo na barkatai na sauƙe wata shirgagiyar ajiyar zuciya ina runtse idona sakamakon sarawan da kaina ya yi mini kamar zai rabe izuwa gida biyu. Ina fesar da numfashi mai zafi daga bakina da na gaza samun yawun da zan jiƙa bushashshen maƙoshina da nake jinsa kamar rijiyar da ruwan cikinta ya daɗe da ƙafewa.
"Ina sonki ina sonki ba zan taɓa daina sonki ba matuƙar ina numfashi a bayan ƙasa, kuma ba zan taɓa barin ki ba".
Kalman yaya Yusuf kenan da suka shiga yi mini amsa kuwa a ƙofofin kunnuwana suna yi mini yawo cikin kwanyata tamkar yanzu yake furta su. Babu shiri na tashi zaune kamar wacce aka tsikarawa matsilli ina rarraba idanu cikin ɗakin saboda gizon da fuskarsa yaya Yusuf mai ɗauke da rauninka da ya yi yayin hatsari da suke gilmawa ta cikin idanuna da suke runtse su. Wani kuka mai ci zuciya da baya fitar da sauti suka tsarƙe ni cikin raina ina kamo duk wata addu'ar da tayi nasarar zuwa mini a wannan lokacin a ƙoƙarin samarwa ruhina sauƙi azabar da nake ji a cikinsa. Ganin da gaske bacci ba zai ziyarce ni ba ya tilasta mini tashi na fita waje nayo alwala sannan na dawo ɗakin na tada salla na daɗe ina sallan har sai da naji ƙafafuna sunyi sanyi laƙwas sannan na sallame a bayyana nake addu'ar nemawa kaina sauƙi a wurin mafi cancanta sarkin da bashi da abokin tarayya bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba.
"Ya Allah kaine masanin abinda yake ɓoye dama na zahiri kai ne masanin sanin abinda yake cikin zuciyoyi kuma kai ne mafi sanin gaibu watau abinda gobe zata haifar. Kai ne mai juya tsananin zafi izuwa sanyi kai ne mai juya dare izuwa rana ya Allah kamar yanda cikin ikonka da ƙudirarka kake sanya hasken farin wata kore duhun dare yayin da alfijir yake keto ka yaye mini damuwar dake cikin zuciyata, na yarda da ƙaddara kuma na karɓa wanda ya faɗo a tsagina sanin da nayi komai ya faru da bawa na daɗi ko akasin hakan daga gare ka ne. Ka kawo mini sauƙi daga tsananin da nake ciki kayi mini zaɓi mafi zamtowa alkhairi ga rayuwata ya arahman rahim".
Cikin sanyin jiki na ƙare addu'ar kana na shafa jikin luƙus, na faɗa wani duniyar daban da nafi samun nutsuwa a cikinta watau duniyar tinani ban san da bacci ɓarawo ya ɗauke ni ba, sai jin Hajiya Babba nayi tana ƙiran sunana da faɗin na tashi asubahi tayi da ƙyar na tashi saboda baccin dake idona nayi sallan tare da yi azkar ɗin nan Hajiya Babba ma tana zaune gefe tana jan carbi sai dai idonta suna kai ta tayi mini ƙuri.
"Daren jiya kuwa kin samun bacci?".
Tambayar da ta jefo mini da ban shirya mata ba, ita ta dawo dani cikin hayyacina cikin yaƙe na amsa mata da faɗin"e Hajiya".
"Ai shi wanda ya sama bacci ma daban yake da wanda bai runtsa ba Na'ima". Shuru nayi mata don yanzu kam na rasa abinda zan faɗa mata na ƙwaci kaina, ta sausauta amon muryata ta ɗaura da cewar"Takwarata ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai zai wuce wataran sai labari idan tafiya tayi nisa wataran ma mai labarin ba zaka ganshi ba". Kaina kawai na ɗaga mata don kalamar godiyar nake son furta mata ma ta maƙale mini a maƙoshi. Sosai tayi ta yi mini nasiha har garin ya ƙara haske tar jikina ya yi sanyi sosai har wani ɓarin zuciya tana cewa dani babu dalilin da zai sanya na saka damuwa a raina akan abinda bani da ikon hana sa faruwa ko kuma ikon tariyo abinda ya riga da ya wuce.
Sai wajajen ƙarfe bakwai na shiga sashin mu domim gaida Umma da ragowar matan gidan da mamakina na iske filin tsakae gidan sharau ba kowa face yara masu tafiya makaranta da suke ta shiri sai kuma Umman Ikilima da take iza wuta gaishe ta nayi ta amsa mini fuskarta ba yabo ba falla kafin na kutsa kai ɗakin Ummata. Tana zaune bisa sallaya tana karatun littafi mai tsarki kan gadonta kuwa Anty Zakiyya ce kwance. Sai da nayi wa kaina mazauni ina jiran Umma ta kai ƙarshen ayar da ta ɗauko na suratul Muhammad kafin na ladabtar da murya na gaida ta amsa mini.
"Anty Zakiyya bata tashi bane yau?".
Na faɗa ina bin ta da kallon mamakin rashin farkawan natan domin sam ba ma halayyarta bane komawa bacci bayan asuhabi, zancen da Umma ta fara yi suka katse mini hanzari tare da sanya ni janye idona daga kan Anty Zakiyya.
"Bata jin daɗin jikinta shiyasa ta kwanta kinsan ta kuma da ƙin shan magani kamar meye".
Murmushi na saka taƙaitacce domin sanin halin Anty Zakiyya akan magani har gobe indai tana ciwo bata ƙaunar shan maganin sai yaya Majid ya tsaya a kanta tare da zare mata ido kafin ta haɗiya. Fatan samun lafiya nayi mata Umma ta shiga tambaya ta yaya jikin nawan na ce da ita alhamdulillah domin babu inda yake yi mimi ciwo a halin yanzu. Haka muka ta zantawa a tsakanin mu a nan nayi kari kafin Hanifa ta shigo wai Hajiya Babba na ƙira na. Na miƙe naji tana zaune a falonta na iske ta na zauna tare da faɗin"Hajiya gani".
"Yauwa daman wayarki ne ake ta ƙira ta cika min kunnuwana da ruri shine na sanya Hanifa ƙiran ki kizo ki duba".
Ɗakin na shige inda na ajiye wayata tun daren jiya da Salma ta bani ita ban bi ta kanta ba balle damuwa da sanin halin da take ciki. Ina shigowa ƙiran yana katsewa na isa da ɗan saurina na ɗauke ta, kusan tuntsirewa nayi zan faɗi duk da kuwa a zaune nake saboda tozali da nayi da sunan dake yawo cikin