MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  True Hausa Novels

Chapter   9 / 58

24K to 27K   out of 171.2K words

matsanancin son da ya amsa sunan so kuma yake alfaharin faɗi gaban kowaye musamman yanzu da take ɗauke da cikin ƴarsa ko ɗansa a maƙale ƙasan mararta, duk wayewar gari sonta ƙara rubanya yake yi a cikin ransa sai yasan tayi masa nisa tayi masa tazaran da ba zai iya cimma ta cikin sauƙi da kwanciyar hankali ba, nisan da ba zasu ƙara haɗuwa ƙarƙashin inuwar igiyoyin aure ba sai dai abu ɗaya da ya sani shine bashi da wata mata a duniya sama da Na'ima ko a aljanna ma zai so su kasance tare.


Jirin da suka fara shammatan ƙafafunsa, ya sanya hawa mashin ɗin tare da tada ta da matuƙar gudu ya fice daga cikin makarantar. Ji yake yi tamkar ba zai iya riƙe kansa ba balle mashin ɗin da yake sarrafa ta, a hankali idanunsa suka fara rufewa duk yanda yaso buɗe su da ƙoƙarin gangarar da mashin ɗin gefe guda ya tsaya gagaran sa hakan ya yi sai ji da ya yi tamkar ana ƙara ingiza ƙarfin gudun da mashin ɗin yake yi bisa titin da zata sada shi da gida.


"Hasbunallahu wa ni'imal wakil".


Ya furta can ƙasan maƙoshinsa da hakan ya sanya idanunsa buɗewa kaɗan, suka yi masa tozali da ƙatuwar motar tilelen da tayo kasan gadan gadan idanu kawai ya ƙura mata sam ya kasa yunƙurin kauce mata haka nan ita ma bata dakata daga tunkaransa ba.


Zafin buguwan da yaji ya ratsa ƙoƙon kansa sakamakon wancakalar dashi da mashin ɗin tayi gefen guda, yana raba raɗaɗin ga dukkan sauran gaɓɓan jikinsa ya sanya numfashinsa fara fizga, ihu da salatin jama'ar da akan idonsu lamarin ya wakana da suka saka a tare shi ya zamto ababen ƙarshe da kunnuwansa suka jiyo masa, kafin ji da ganinsa suka ɗauke.


Haka kawai na tsinci kaina cikin matuƙar faɗuwar gaba, raina sai tsinkewa yake da ban san dalili ba runtse idona nayi a hankali ina maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihir raji'un cikin raina, maganar da Salma ta fara yi mini shi ya dawo dani cikin hayyacina.


"Na'ima lafiya kuwa kin zauna kinyi shuru?".


Sai da na ƙirƙiro murmushin dole na dasawa fuskana kafin na amsa mata cikin faɗin"lafiya ƙalau har yanzu Abasiyya bata dawo daga sashin hajiya Babban ba?".


Sai ta taji jima kafin ta ce dani"e bata dawo ba na sinci zancen dai a tsakar gida wai Sagir ne yazo suna can suna tattauna dasu Abba". Jin hakan ya sanya ni yiwa bakina linzami ban kuma cewa komai kamar yanda gabana bai bar faɗuwa ba haka na ƙarar da wunin ranar tamkar marar lafiya sam na gaza gane meke damuna da har yanayi na ya fallasa hakan.


Ina zaune ɗakin Umma bayan na iddar da sallan magrib Umma ta shigo da damuwa sosai a fuskarta don duk yanda taso ɓoye hakan sai da sirrin zuciyarta ta bayyana bisa kamalalliyar fuskarta, a tare muka jefa mata tambayar lafiya nida Anty Zakiyya da take ninke kayan wankin da muka yi, sallamar yaya Majid ta katse ta daga zancen da take son furtawa.


Wayata ya ajiye mini a gabana kafin ya zauna a kusa dani yana tambayar lafiya?, Umma ta numfasa kana ta ce"lafiya ƙalau ku taya ni da roƙon Abbanku ya dawo da Halimatu ɗakinta kan ƴaƴanta, domin na tabbata duk inda take yanzu hankalinta ba a kwance yake ba babu macen da take jin daɗin zawarci koda Kuwa ita ta nema sakin da kanta daga ƙarshe sai ta cizo ɗan yatsa, sai dai duk naso gyara lamarin yaƙi saurara ta balle ya fahimce ni".


Ɓoyayyan ajiyan zuciya na saka ina jinjina ƙarfin zuciya irin na Umma, ina ƙara gasgata sahihancin wannan zancen da ake cewar zuciya mace kan iya ɗaukar komai kuma su nuna tamkar babu komai, wani sadaukar sai mace wani ƙarfin halin sai mace wani juriyar sai mace wani haƙuri wallahi zuciyar macece kawai ke iya danne shi, saɓanin ɗa namiji. Ina alfahari da Umma a ko yaushe kasancewarta uwa a gare ni da kyawawan halayyarta suka zamto mini ababen koyi ta kuma zamto madubin dubawa a gare ni, muryar Anty Zakiyya suka dawo dani daga tinanin da na zurma.




"Umma kenan kiyi haƙuri kawai ki taya ta da addu'a, komai kike ba gani ita zata yi ba balle har tayi miki godiya".


Murmushi kawai Umma ta saka tana faɗin na saka mata ruwa a buta tayi alawa, miƙewa nayi na zuba ruwan sannan na dawo na sanar da ita ta fita domin yin alawan. Na ɗauki wayata na kuma gefen tinawa da nayi akwai bashi a layin tun sanda naci na ƙira Balkisu lokacin da suka je mini ɗin ya sani kwaɓe fuska ina kallon yaya Majid kafin na ce"yaya wata waya nake son nayi kuma wallahi na duba balance ɗina na tarar da akwai bashin da suke bina, babu damar ƙara cin wani".


"Waye za ki ƙira?".


"Maman Hanan".


Sai sannan ya sauƙe ajiyar zuciya bai kuma cewa dani komai ba illa zaro wayarsa da ya yi daga aljihunsa ya yi danna-dannensa sannan ya mayar da ita aljihunsa. Ƙarar shigowar saƙo wayata ya sani buɗewa a gagauce yaya Majid ne ya turo mini katin ɗari biyu tunin suka janye naira ɗarinsu da suke bina suka bar mini ragowar. Godiya nayi masa sai dai bai amsa mini ba illa murmushin da ya sakar mini yana ficewa daga ɗakin gabaɗaya. Nima ɗakinmu na koma domin yin wayan na kuwa iske ba kowa lambar maman Hanan na shiga dannawa ƙira sai dai har ta katse ba'a ɗaga ba, a jere sai da na ƙira sau huɗu amma duk ba amsa ba. Ajiyar wayar kawai nayi na tashi nayi sallan isha'i ina kai sujjadan ƙarshen naji rurin wayata sai da nayi sallama na shafa addu'ata sannan na jawo wayar nabi bayan ƙiran da maman Hanan tayi mini.


A hankali nayi sallama sai dai maimakon ta amsa mini sai ce dani tayi"Na'ima kece?".


"E".


Rushewa tayi da kuka sosai, hakan ya tsorita ni har na fara tinanin ko wani ne ya rasu"Anty lafiya kuwa menene yake faru naji kina kuka?".


"Na'ima ba lafiya, Yusuf ne ya yi hatsari gamu nan a asibiti bai san inda kansa yake ba balle tantance waye a tsaye a kansa".




MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________________




Page 4⃣7⃣


Ɗim naji kunnuwana sun daina jiyo mini ragowar zancen da ta cigaba da furtawa, illa iska kawai da nake ji a masarrafan jina kafin daga bisani shima ya tsaya cak. Rawar da jikina ya ɗauka ya sanya wayar sulalewa ƙasa ba tare da nayi wani yunƙurin taro ta ba balle a kai na bata amsa lamau na kwanta akan sallayan ina fitar da numfashi a cunkushe ƙirjina yana mini wani iriyar zafi da raɗaɗin tamkar ana watsawa mai ƙona garwashin wuta a fatar jikinsa kwatankwacin irin tsananin azabar da nake ji a dukkan sassan jikina. Zancen na maman Hanan suna yi mini yawo cikin kaina tare da yi mini amsa kuwa a kunnuwana.




Cike da azaba na yarfa hannu sakamakon wani iriyar ciwon da naji a marata yana zarge ni har gadon bayana da naji ko motsawa bana iya yi balle tashin zaunen da nayi ƙoƙarin yi, a hankali hawaye suka bin gefen fuskana jikina ya yi mini nauyin da ko hannuna bani da damar motsawa shi balle sauran gaɓoɓin jikina. Murtsukuku na fara yi a wajen domin na saka taimakawa kaina, a ƙirjina numfashin da yake fita a wahale yake tsayewa duk yanda naso buɗe bakina domin ƙwalla ƙiran kawo mini agaji ko taimako hakan ya zamto mawuyacin abu a gare ni, juyin na cigaba da yi kawai cike rashin mafita.


A hankali na fara jin sauƙar wani abu mai ɗab ɗumin yana bin cinyoyina yana sauƙa har ƙasan dugadugaina, dai-dai nan tsananin azabar ciwon ya yawaita jikina ya ɗau zafin yawun bakina ya kafe tamkar tafkin da ƙasa ya tsotse ruwan cikinsa hawaye da gumin ciwon suka cigaba da gudana akan dandamalin tudun fuskana suna sauƙa izuwa saman haɓata.


"Innalillahi wa inna alaihir raji'un wayyo Allahna".


Abinda nayi nasarar furtawa kenan a raunane bayan nasha gumurzun raba tsakanin haƙwarana da suke karafɗiya da juna, na cigaba da juyi cikin jinin da yake zuba daga jikina ina yarfa hannu so nake ko yaya ne na samarwa kaina miyau ɗin da zan jiƙa bushashshen maƙoshina da nake jin tamkar ana kekketawa da kaifin almakashi amma na gaza yin hakan.


Ƙara sakin jikina nayi har yanzun numfashi yana fita a wahale kuma ɗaɗɗaya, a raina nake maimata kalmar shahada ina jiran na ga ta inda mala'ika aza'ilu zai fito domin ɗaukar raina. Idanuna suka rufewa da hakan ya hana ni damar hange abunda ke gabana.


"Innalillahi Na'ima jini fa ke fita daga jikinki, lafiyarki kuwa?, bari nake na ƙira Umma".


Furcin da kunnuwana da jinsu ya ɗauke na wucen gadi kenan da suka jiyo mini maganar a rarrabe da na kasa tantance muryar bai maganar. Idanuna sun rufe bana ganin komai haka nan kunnuwana basa tantance mini ababen da suke faɗa illar sautin kukan da ya cika ɗakin da suke naɗo mini shima ƙasa ƙasa nake jinsa, sai dai saƙon yana isa har can ƙasar ƙalbina kafin kuma numfashin da yake barazana da rabuwa da gangar jikina ya tsaya cak.




Ban kuma sanin inda kaina yake ba balle sanin waye tsaye a kaina haka nan ban san iya adadin daƙiƙu, mintuna, awanni da kwanakin da na ɗauka cikin wannan halin da bani da wani marafa da gawar dake kushewa illa bugawan da ƙirjina yake yi a raunane. Wani sanyi naji yana ratsawa har cikin ƙashina da hakan ya tilasta mini ƙara matsa marafan idanuna da na kasa buɗe su tinanin inda nake ya faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu hannuna na jawo gangar jikin ta ƙi bani haɗin kai wajen aiwatar da hakan tilas na haƙura ina motsa leɓɓana da ni kaɗai nake iya jiyo abinda nake faɗi.


"Yusuf Yusuf Yusuf kana ina?, kazo na ganta".


Hakan na cigaba da faɗa ba tare da sama damar buɗe idanuna ba, har zuwa wani lokaci da naji baƙuwar murya sun dirarwa ƙofofin kunnuwana.


"Sannu kina jina?".


Kaina kawai nayi jarumtar ɗaga don ba ganin sa nake yi ba, balle nayi ƙoƙarin bashi amsa da kalmomin baki.


"Buɗe idonki na gani".


Shuru nayi don nasan ko nayi yunƙuri aikata hakan ba zan iya ba, sai da ya ƙara maimata maganar a karo na biyu kafin na fara buɗe idona a hankali wani farin haske na gani da hakan ya sani saurin mayar da idona na rufe babu shiri.


"Ki ƙara gwadawa a hankali".


Ban yi musu ba duk da raɗaɗin da nake jin idanun suna yi mini a duk sanda nayi yunƙurin buɗewa, ji nake tamkar an sanya gum mai danƙo an manne mini su tare da fatar idon. A hankali na kuma buɗewa yanzu dai hasken da nake gani ya ragu sai dai dishi dishi nake gani komai, maganar da ya yi wanda banji da kyau ba ya sani saurin kai duba gare shi tabbas namiji ne kamar yanda muryarsa da daɗe da bayyana mini jinsin nasan, sai dai bana iya ganin fuskarsa ƙara maimaita maganar da ya yi ya katse mini hanzari na ɗauke idona daga kansa.


"Tashi ki zauna".


Yunƙurin hakan nayi amma na gaza yi, hawaye suka gangaro mini ta gefe da gefen kuncina. Da ƙyar na tashi na zauna bayan gwadawa da nayi a karo na barkatai na kasa. Numfashi na jawo mai ƙarfi na fesar ta bakina.




Sai a sannan idanuna suka buɗe sosai har na bi ɗan madaidaicin ɗakin asibitin da aka shafe shi da farin fanti da kallo, kafin na sauƙe idona akan fuskar likitan da shima ɗin ni yake kallo.
"Ina ne yake miki ciwo?".


Ta ina ma zan fara domin duk jikina gabaɗaya ciwon yake yi mini, ko motsi nayi sai naji zafin hakan har cikin raina, cike kulawa ya ƙara maimata mini tambayar kamar yanda yake yi tun ɗazu bana amsawa sai ya maimaita. A wannan karon maimakon na amsa masa sai ma tsananta hawayen da nake yi nayi cikin dushashewar muryar dake bayyanar da halin da zuciyata take a ciki nake faɗin"ina Umma ina sauran ƴan gidanmu?, ka ƙira mini Ummata".


Na ƙara maganar ina sanya fuskana cikin tafukan hannuna, ban damu ba da ƙarin ruwan da aka yi mini da na fizge dalilin hakan ya haddasa mini zubar jini daga hannu, ina jin shigowar wasu nurses biyu da ya yi ƙira su, su suka kwantar dani tare da mayar mini da ƙarin ruwan bayan sun yi mini wata allura a ciki da babu jimawa bacci ya ɗauke ni.


"Umma! Umma kizo kusa dani ina Yusuf yake wani hali yake ciki?, ance ya yi hatsari".


Suna zantukan farko da suka fitowa daga bakina, a lokacin da duk ƴan gidanmu suka ɗebe tsammanin da samun rayuwata, kallon ɗaɗɗaya nake binsu dashi da duk suke zagaye dani wasu na sharar ƙwalla. Muryar Abba ita ta fara dawo dani cikin hayyanacina.


"Mamana ki kwantar da hankalinki Yusuf yana lafiya yanzu ma daga wajen sa muke. Koma ki kwanta ki sanar dani ina ne yake miki ciwo".


Ƙwallar da suka ciko mini kurmin idaniya suka fara tsiyaya sannu a hankali suna wanke mini fuska, na riƙo hannun Umma da ta tazo ta dawo kusa dani gam cikin nawa magana nake yi mata amma na kasa sai binta da nake kawai da kumburarrun idanuna, ita ma nata idanun cike taf da ƙwalla ta shafo goshina haɗi da faɗin"ki daina kuka kinji Na'ima ko wani bawa da irin nashi ƙaddara, ki zama mai juriya da ɗaukar ƙaddara a duk yanda tazo miki sai Allah ya yi miki tagumashin da ba ki taɓa tsammani ba".


Kaina kawai na ɗaga mata don ni dai ban fahimci inda maganganun natan suka dosa ba, ta cigaba da shafa goshina har izuwa gefen fuskana. Baba da Baba ƙarami sai jera mini sannu suke yi tamkar zasu mayar da ciwon jikkunan su, haka nan ma yaya Majid da Anty Zakiyya. Sannan raguwar mutane da duk matan gidanmu sai kuma Salma suma suka hau layin yi mini yaya jikin, kaina kawai nake ɗaga musu sai murmushin ƙarfin halin da nake sakar musu don wani tsanancin ciwon ciki nake ji.


"Sannu Na'imatu yaya jikin nakin?".


Na tsinkayi muryar Umman su Anty Kubra, ita kaɗai nayi ƙarfin halin furta mata kalmar"Alhamdulillah". Ta taɓe baki tana bina da wani irin kallon da na kasa fassara ma'anonin da suke ƙunshe a cikinsa sai dai kawai na ɗauke kaina ina kallon rufin ɗakin da ya zamto shamaki tsakani na da sararin samaniya.


"Mu nan duk hankulanmu ya tashi tsawon kwanaki huɗu duk bana cikin ainihin nutsuwar mu, yanda muke ganin rana haka muka ganin dare ashe ke duk akan namiji ne ma ciwon nakin. Mijin da kowa yasan cewar babu aure a tsakanin ku tunda saki uku ya gifta mijin da tunda ya sako ki bai ƙara waiwayarki ba balle duba halin da kike ciki duk da kuwa yasan da cewar kina ɗauke da cikin ƴarsa ko ɗansa a tare ke. Shine daga jin halin da yake ciki ke uwar masu tausayi da kinibibi kika ɗaurawa kanki wannan ciwon gashi ai yanzu kiyi sanadiyar zubewan cikin dake jikin nakin sai naga ta faɗi Allah wadaran naka ya lalac...".


Tsawar da Baba ƙarami ya daka mata a gigice shi ya hana ta ƙarishe zancen, cikin zallar ɓacin ran da babu sirki da suka bayyana akan fuskarsa ya nuna ta ƴar manuniyar yatsarsa yana faɗin"Zainabu meye haka?, kinyi hauka ne ko ko wani abun kika sha da ya sanya ki fita hayyacinki har kike wannan kalaman. Ba ki ga halin da wannan yarinyar take bane? ba ki ga yanayin da take a ciki bane shin yanzu ne lokacin da ya dace kiyi mata wannan maganar?".


Shuru tayi don duk ta gama daburcewa da hakan ya ƙara harzuƙa Baba ƙarami ya kuma faɗin"ince dai ba da Zainabu nake magana ba ko?".


Cikin in in nan da ban santa dashi a duk tsawon rayuwar da muka yi tare cikin gida ɗaya ta soma cewar"kayi haƙuri malam kawai nayi takaicin cewar akan mijin da tasan ba zasu sake zaman aure ba ta sanya kanta cikin wannan halin. Amma idan kaji zafin furcina Allah ya hucu zuciyarka".


Wani kallo ya watsa mata kafin ya shiga yi mata nuni da ƙofar ficewa ya ce"tashi maza ki koma gida bana son ganin ki a nan".


Sumi sumi ta tashi ta fice, ɗakin ya ɗauki shuru kafin Abba ya fara ba wa Baba ƙarami haƙuri da cewar ya dunga kai zuciyarsa nisa lamarin mata sai da haƙuri da kau da kai matuƙar kana ƙaunar a zauna lafiya.


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


___________________________________________




Page 4⃣8⃣


Rawa bakina ya fara yi tamkar sabuwar haihuwar kazar da aka sheƙawa ruwan sanyin a jiki ko kuma wacce ke mashashshara, na kafe Ummata da idanuna da ƙwalla ya ciko kurmin su. So nake naji gaskiyar abinda naji daga bakin Umman su Anty Kubra daga bakinta zanfi yarda kuma zuciyata zata fi ɗauka.


Kamar wacce tasan abinda nake saƙawa cikin raina ta ƙara ƙarfin riƙon da tayi wa hannayena da har yanzu suke a cikin nata kafin ta furta mini"kiyi haƙuri Na'ima ki rungumi wanna n ƙaddaran da ta faɗo a tsagin rayuwarki, komai kika ga ya faru da bawa to haka Allah ya tsara ya faru dashi kuma babu mai ikon hana hakan faruwa". Shuru nayi hawayen da nake danne zubar su suka fara shawagi a saman fuskana duk yanda naso tsayar dasu na gaza samun wannan ikon sai gudana suke yi tamkar burɗaɗɗen famfo.


"Mamana kiyi haƙuri ki daina wannan ki sanya wa ranki dangana, da kuma yarda da cewar komai kika samu ko kika rasa daga Allah ne babu wani mahalukin da zai samar miki abinda zai yi miki ba, ko kuma ya ƙwace miki abinda ya sanya shu cikin rabonki. Don Allah ki cire damuwar komai daga cikin ranki in sh Allah rayuwarki zata inganta kuma sai kinyi dariya komai zai wuce har ya zama labari daga labari ya koma tarihi ba abinda yake dawwamamme a cikin duniyar nan face ikon Allah".


Haɗiye ragowar kukan da yake taso mini nayi sakamakon wannan furcin na Abba da suka ɗan sanyaya mini sashin ruhina har ina jin sauƙin nauyin

9 / 58