Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
suna zuwa irin wajajen nan suna ɗaukar hoto suna watsawa a social media. Bazan taɓa mance wata ranar da ta zamto mana baƙar rana ba ta haddasawa Ummanmu bugun zuciyar da tunda ta yanki jiki ta faɗi bata ƙara tashi akan ƙafafunta ba sakamakon cutar ɓarin jikin da ta samu Abba bai yi la'akari da tsawon shekarun da suka ɗeba tare ba da daɗi da babu daɗi bata taɓa gujarsa ba ya yanke alaƙar auren dake tsakanin su akan idonmu. Wani maƙwabcinmu ya tabbatar mana da cewar yaga Anty Mami a manhajar tiktok tana rawa da karkaɗa sassan jikinta cikin shigar banza tamkar ba musulma ba balle har ayi tinanin cewar daga tushen malam bahaushe ta fito, sanda yazo mana da zancen sam bamu amince ba sai da ya nuna mana ita cikin wayarsa nan ma bamu gamsu ba. Fahimtar hakan ya sanya shi bamu shawarar mu kai maka ziyarar bazata a makaranta mu tabbatar ko tana cikin makarantar ko kuma yawon sheƙe ayarta take yi shawarar da ya bamu muka yi kwana biyu a tsakani muka shirya muka nufi makarantar tare da wani ƙanin Umma sai da muka iso muka ƙira ta waya muka sanar da ita zuwan namun akan ta fito ta same mu nan ta soma yi mana kame-kame akan ta fita kasuwa siyayya muka ce mata ba gaugauwa muke yi don ita muka zo don haka zamu jira. Daga haka ta kashe wayarta ma gabaɗaya ko mun ƙira bama samu wata ƙawarta ɗaya tal da muka san su tare tun a makarantar sakandiri muka nema domin ita ma ta sama gurbi a jami'ar. Da farko taso ɓoye mana sai da Umma ta haɗa ta da girman wanda ranta yake hannunsa akan ta sanar damu halin da Anty Mamin take ciki ganin hawayen dake fita daga idaniyar Umma ya sanya faɗa mana komai ta kuma ƙara da cewar yanzu haka ma bata cikin garin sunyi tafiya da sabbin ƙawayen da tayi da kuma samarinsu".
Izuwa sautin kukanta ya daɗu soai fiye da da kamar yanda muma namu sautukan ya zarce misali kuka muke yi bil haƙƙi da dukkan gaskiyar mu cikin mu babu mai ba wa wani haƙuri balle lallashi. Sai ni ne nayi ƙarfin halin tashi na isa ga Nawwara da take kuka tamkar zata shiɗe numfashinta yana wani irin fizga da matuƙar ƙarfin da ya wuce munzali na kwantar da kanta a bisa cinyana ina bubbuga bayanta a hankali cikin sigar lallashi, ganin hakan ya sanya Nazifa ma tasowa ta kwantar da kanta a kan kafaɗuna kukan muka cigaba dashi tamkar waɗanɗa aka aikowa da saƙon mutuwar dukkan iyayensu biyu uwa da uba.
"Ya isa haka ku tashi muyi sallan isha'i gashi ma sai ƙira ake yi".
Da ƙyar nake fizgar numfashina da yake garke mini a ƙirji nake furta maganar cikin sarƙafewar harshe, tare da ɗago su daga jikina sai da na je na saka mana ruwa a buta nayo alwalan sannan suma suka fita suka yo. Muka yi sallan bamu tashi daga kan sallayan ba Nazifa da idonta ya yi ƙulu-ƙulu tsabar kukan da ta yi duk da kuwa bata da hasken fata amma wajen ya yi ɗan ja haka ta ce"sanar da ni yanda kuka iske Anty Mami don wallahi zuciyata bugawa take yi da ƙarfi da ƙarfi kamar zata ɓalle allon ƙirjina taso fata da namana ta bayyano waje tsoro da fargaba sannu a hankali yana ƙara mamaye cikinta".
Wani irin wawan ajiyar zuciya Nawwara ta sauƙe tare da lumshe idanunta ta buɗe su a hankali cikin muryarta da ta fara dishashewa take cewar"daga cikin jami'ar asibiti aka wuce da Umma domin ta yanka jiki ta faɗi, koda ƙaninta ya sanar da Abba rantsuwa ya yi da cewar ƙafarsa ba zata taka cikin asibitin ba koda kuwa ranta ne ya yi bankwana da gangar jikinta tunda tun farko ita ta dage akan dole sai Anty Mamin tayi boko har da sayar da kaddarorinta don haka yanzu ga sakamakon da ta fara girba tun kafin aje ko ina, kwanar Umma ɗaya a asibitin muka koma garinmu saboda rashin kuɗin da zamu biya asibitin muka koma yi mata na gargajiya. Kwanan mu biyar da komawa amma har lokacin wayar Anty Mami baya shiga a wunin na shidan ƙawar nan ta ƙira ta shaida mana da cewar wai sunyi hatsari a hanyar shiga Abuja daga kaduna mun shiga cikin tashin hankali aihun da bana fata koda maƙiyina ne ya faɗa cikin irin wannan halin, haka aka kawo mana Anty Mami tamkar gawa kuɗin da za'a nema mata lafiya ma ya gagare mu yayin da Abba ya ce ba zata shiga cikin gidan ba don shi a ƴaƴansa bai haifi karuwa ba. Sai gidan su Ummanmu aka kaita ƙanin Umman ya sayar da mashin ɗin hawansa aka kaita asibiti aka tabbatar mana da ta sama karaya biyar biyu a hannunta uku a ƙafarta babban tashin hankalin shin tana ɗauke da cutar mai kayar garkuwan jiki watau HIV (Human immune virus). Munyi kuka iya kuka har muka rasa hawayen tsiyaya musha gori da ba'ar mutane da waɗanda suke yiwa Umma zunɗe ga kuma saki ukun da Abba ya danƙara mata a jere reras. Kwanakin Anty Mami goma a gida ta amsa ƙiran mahaliccinta ko sallan jana'izanta Abba bai halallata domin ya ce ya riga da ya cire ta daga cikin jerin ƴaƴan da Allah ya mallaka masa a duniya tun lokacin da ta shiga jami'a daman yasan dole irin wannan ranar zata zo".
Sai da ta zuƙi numfashi ta fesar kana ta cigaba da"Burin Umma akan karatu ya mutum domin ta aza shine akan Anty Mami yayin da ita kuma ta watsa masa ƙasa mai cike da tsakuwa a cikin idanunta, tana kwance tana fama da cutar mutuwar ɓarin jiki yayin da cikin ranta take fama da raɗaɗin sakin da Abba da ya yi magana da kuma maganganun mutanen al'ummata da baza gani su ƙyale. Ba zan iya jurar ganin mahaifiyata cikin wannan halin ba don haka nayi alƙawarin sai na cika mata burinta sai kuma nayi karatun jarida ta yanda zan nunawa duniya cewar ba kowacce ƴa ba ce take lalacewa idan ta yi jami'a da kuma wayar musu da kai akan tasirin ƙawa ga rayuwar ƴaƴansu musamman a jami'o'i. Ƙanin Umma shi ya ɗauki nauyin karatuna duk da shima ba ƙarfi bane dashi aikatau nake yi kafin na sama gurbin karatu na taho. Ba ina yin karatu don kaina bane sai don farfaɗo da mataccen ruhin son karatun da ya daɗe da macewa a cikin zuciyar Umma, ta bani goyan baya ko don mu fahimtar da Abba abinda ya gaza fahimta hakan ya sanya na nema gurbi a jami'ar da Anty Mami ta gurɓace a cikinsa da alƙawarin zaƙulo dukkan wanda yake da hannu da gurɓacewa Anty Mami".
Wani kuka muke yi sosai domin nikam ganin komai nake yana faruwa kamar yanzu duk da kuwa ban san Anty Mamin ba, muka damƙe hannuwanmu waje guda cikinmu babu wanda ya iya furta koda kalma ɗaya sai da muka ɗauki tsawon mintoti a haka kafin nayi jarumtar faɗin"Allah ya jiƙanki Anty Mami ita kuma Umma Allah ya bata ingataccen lafiya".
"Amin".
Nazifa da Nawwara suka haɗa baki wajen faɗi, shuru ya kuma gauraye ɗaki har izuwa lokacin da Nazifa ta katse shi da faɗin"tabbas labarin Anty Mami ba labari bane kawai akwai manyan darasi a cikinsa da zai zama izna ga wasu, in sha Allah zamu ba ki dukkan haɗin kai da gudumawa wajen ganin kin cimma wannan ƙudurin nakin".
Kaina na jinjina wasu sabbin hawayen suna ziraro mini cike da tabbatarwa Nawwara furcin na Nazifa, a wajen baccin wahala ya ɗauke mu muna manne da juna. Sallar asubahi ma a makare muka yi shi haka nan har an shiga lecture sanda muka isa hall ɗin muka yi taking excuse muka shiga, awa ɗaya muka yi muka fito zamu je cafe sanya biro da fulsikaf lokacin wasu sun fito daga lectures mutane him cike a cafe ɗin mun gama sanyan abinda zamu saya mun juya zamu fita naci karo da wani mutum biron dake hannuna ya faɗi na tsuguna zan ɗauka sautin muryarsa suka sanya ni tsaya cak.
"Sorry".
Ya furta da ya sani saurin waigowa don ganin mamallakin muryar, sai dai yawan mutanen wajen ya hana ni tantance wanda ya yi maganar, dafe ƙirjina da yake bugawa da ƙarfi nayi kafin kwakwalwata ta gama tantance mini mai murya nayi saurin furta"YUSUF".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________
Page 6⃣9⃣
Take naji ƙafafuna sun soma rawa tare da barazanar gaza cigaba da juran ɗaukar nauyin gangar jikina, ƙirjina ya yi mini wani iriyar mungun nauyi wani zuffa mai maƙo yana tsatstsafo mini daga goshina.
A zabure na fara waige-waige ina baza idona cikin cincirundon mutanen dake wajen cike fatan idanuna su gane mini abinda mahauniyar zuciyata take nema, tafiya na fara yi ina ratsa cikin mutanen ba tare da damuwar cewar duk maza ne nake ratsawa ba bana jin abinda su Nawwara ke faɗa domin hankali da nutsuwata ya yi ƙaura daga gangar jikina ya tafi can wata duniyar na daban, har na zagaya ta bayan cafe ɗin ban ganshi ba babu ko alamar mai kama dashi balle shi ɗin a zahirance.
Ganin cewar da gaske babu shi a wajen muka ba muryarsa kunnuwana suka jiyo mini ba, ya tilasta mini durƙushewa a wajen a gwiwoyina ina sauƙe ajiyar zuciya a wahale tare da runtse idanuna da ƙarfi sakamakon sarawan da kaina yake yi tamkar zai rabe gida biyu na matse jikina wajen guda duk da zafin ranar dake ratsa ni da hurar da zuciyata take yi bai yi tasiri wajen sanya ni tashi daga wajen ba har sai da Nawwara da Nazifa suka iso wajen.
"Na'ima lafiyarki kuwa?, meye yake damunki?, meye ya faru?".
A jere aka watso mini tambayar da na kasa tantance muryar Nawwara ne ko kuma na Nazifa, ban amsa musu ba har suka ɗago ni daga durƙushewar da nayi muka nufi hostel muna shiga na zube akan katifa kamar jaka ina sakin wani gigitaccen kukan da ya turniƙe mini rai da tun ɗazu ban sama damar sakar shi ba sai yanzun. Sosai nake kukan har na rasa hawayen tsiyayarwa sai na kuma na zuci da yafi raɗaɗi, ciwo, da kuma ƙuna ga mai yinsa.
Cikin sanyin Nazifa ta zauna kusa da ni tare da faɗin"wai menene Na'ima duk kin sanya mu a cikin duhu kuma kin ƙi kiyi mana magana tun ɗazun, dan Allah ki sanar da mu menene ya sanya hawayenki kwarara?".
Muɗik na haɗiye ajiyar zuciyar da nake faman saki a kai a kai, na ma rasa wace ƙaryan zanyi musu a halin yanzu da zai kuɓutar dani daga jerin gwanon tambayoyinsu. Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe kafin na tashi zaune ina fuskantar su tare da yi musu kallon ɗaiɗai na ce"ba komai kar ku damu wani abun kawai na tina".
"Lalle Na'ima dole ki buɗe baki ki ce mana babu komai ai, tunda ba mu kai muji damuwarki ba kuma ba ki ɗauke mu a yanda mu muka ɗauke ki ba. Meye rayuwar ma zaman tare ne fa ya haɗa wataran ma da kuɗi zamu nema ganin juna amma abin ya gagara wannan lokaci shi muke dashi da zamu taimaki junanmu koda da shawara ce ko kuma addu'a, amma idan kina ganin cewar damuwarki ba tamu ba ce fine ba lalle ba dole sai ki cigaba da dakon abin ki cikin ranki ba zai kin faɗa mana ba sai mu taya ki da addu'a Allah ya yaye miki ya kuma kawo miki mafita".
A kufule ta ƙare zancen fuskarta tana bayyanar da tsantsar ɓacin ran da tunda Allah ya haɗa ni da ita ban taɓa ganin sa akan fuskarta ba, kullum cikin fara'a da sakin fuska take amma yau dalilina ga ɓacin rai ɓaro ɓaro shimfiɗe akan fuskarta.
Ganin zata fice daga ɗakin ya sani saurin zabura na diro daga kan katifar tare hanzarin cafko hannayenta na sanya cikin nawa na riƙe gam har yanzu idanuna basu gushe ba suna kwararar da ƙwalla.
Jan hannun natan nayi muka zauna kafin cikin rawar murya na soma faɗin"kuyi haƙuri ba wai inna muku haka bane don ban yarda da ku ko kuma don baku da muhimmanci a gare ni ba, wallahi jin ku nake yi tamkar ƴan-uwan da muka fito ciki ɗaya dasu zan sanar daku zan sanar daku dalilina na gujewa mu'alama da duk wani ɗan namiji amma ba yanzu ba".
"Sai yaushe Na'ima?, nikam sam bangane miki ba sau da dama ko cikin dare na tashi ko muna waya da yaya Amin sai na jiyo sheshsheƙar kukanki dan Allah menene damuwarki?. Koda ba zamu iya yi miki maganinta ba ai sai mu taya ki da addu'a da shawarwari kamar yanda Nawwara ta faɗa".
Ɗaura hannuna nayi akan leɓɓanta na rufe maka baki kirif ina jijjiga mata kaina alamar ba yanda take tinani bane, wasu sabbin siraran hawayen suna ƙara wanke mini fuskana da nake jin idanuna har sunyi mini wani irin nauyi. Na kifa kaina a bisa kafaɗarta ina sakin wani kukan basu ƙara cewa dani komai ba illa jona ni da suka yi muka cigaba da kukan tare.
Mun daɗe a haka kafin Nazifa ta kamo hannuna tare da ɗago ni ta ce"y isa to sanar damu menene in ba yanda muke tinani bane".
Ban san ta inda zan fara buɗe musu wannnan faffaɗan kundin ba mai cike da babi babin ƙunci da aka rubuta shi da ruwan hawaye maimaikon ruwan tawada, mai narkar da zuƙata da yawa har ma a sama bugawar wasu zuciyoyin. Tabbas ba iya fatar bakina kalmar da na furta na cewar na ɗauke su kamar ƴan-uwan da muka fito ciki ɗaya dasu ba yake har cikin ƙasan raina ma hakan zancen take, ban musu adalci ba inda na ɓoye musu abinda yake damuwa domin bana shakka su ɗin masu rufa mini asiri ne mu kashe tare kuma mu birne ba tare da kowa ya ji ba.
Tagwayen ajiyar zuciya mai ƙarfi da bada sauti na saka kafin na ce"Yusuf tabbas shi kunnuwana suka jiyo mini muryarsa sai dai idanuna basu gane mini shi ba".
"Yusuf kuma?, waye shi Yusuf ɗin?".
A tare suka haɗe baki wajen jefo mini tambayar da ta saka ni ƙara sauƙe wani ajiyar zuciyar a karo na barkatai kafin na ce"saurayina na farko kuma tsohon mijina". Tun kafin na ƙare zancen duk suka galalo mini ido cike da neman ƙarin bayani, fahimtar hakan ya sani ɗaga musu kaina cike da tabbatar musu da zancen nawan. "Tabbas kunnuwanku basu jiye muku ba dai-dai ba, ni bazawara ce da ta taɓa yin aure a baya ta fito saboda wasu dalilai masu sarƙarƙiya, na faɗa cikin ƙunci har na fara rasa hankalina ina neman zautuwa ganin hakan ya sanya iyayena yanke shawaran turo ni nan karatu ko zan manta da komai. Wallahi muryar Yusuf naji hakan yana nufin kenan nan ma biyo ni ya yi kamar yanda ya yi alwashi na shiga uku na".
Na kai aya ina rushewa da wani kukan jikina har jijjiga yake yi, Nawwara ta riƙe ni ta ce"ki nutsu tunda dai ba ganinsa kika yi ido da ido ba don muryar kawai ba hakan ne yake nuna cewar shi ɗin bane ki cire komai a ranki dan Allah irin haka sai ki haddasawa kanki wani ciwon kiyi haƙuri kema ki cire shi a ranki". Shuru kawai nayi mata ba wai don zancen natan sun sama wajen zama a cikin kwanyata domin da zan iya cire Yusuf a raina da nayi hakan tun kafin yanzu sai dai bani da ikon akan zuciyata. Salla muka yi muka ci abinci muka yi zaman mu don bamu da wani lecture ɗin a yau bayan wanda muka yi, hankalina da nutsuwa gabaɗaya basa tare da ni duk da kuwa jana da hirar da su Nawwara suke yi a ƙoƙarin ganin na saki jikina na mance da komai. Saurin da ƙirjina yake yi wajen bugu ya tabbatar mini da cewar tabbas akwai wani abunda yake shirin faruwa da rayuwata wataƙil wannan farin-cikin da nake ciki ya juye izuwa baƙin-ciki sai dai babu wanda yasan abinda gobe kan iya haifarwa, na zaɓi na ba wa su Nawwara wani gutsure daga cikin labarina domin sauran sunyi mini wahalar furtawa akan harshe a sannu a hankali sai na faɗa musu komai.
ƙaruwar bugawar zuciyarsa shi ya tabbatar masa da cewar wani abun ne ya taɓa ta mai girman gaske yake shirin afkuwa, dafe dai-dai ƙirjina dake harbawan gudun famfalaƙi ya yi tare da runtse idanunsa yana sauraron saƙon da ƙwakwalwarsa take aikawa ga sauran sassan jikinsa da suka gama yi sanyi ƙalau. Kamar wanda aka tsikarawa matsilli haka ya zabura ya buɗe idanunsa tare da furta"Na'ima".
Ya fara waige-waige a wajen cak ya tsaya jin ya yi karo da mutum tare da ɗan runtse idanunsa dake cike da tsoro da fargaban har ya juyo ya yi tozali da abinda ransa yake wasassafa mishi. Sai da ya haɗiye wani miyau mai ɗacin da ya wanzu cikin bakinsa tare da game ko'ina kafin ya buɗe idanunsa haɗi da sakin wani wahalallen ajiyan zuciya ganin ba abinda yake tinani bane. Kamar an dirsashi yin maganar ya ce"sorry ban lura dake a wajen ba". Bai jira ta cewarta ba ya bar wajen cikin matuƙar sauri kamar zai tashi sama ya kuma hostel domin a cikin jam'ar yake da zama tunda bai san kowa a garin ba sai wani abokinsa da suka yi karatu tare a da.
Kai ya haɗe da gwiwa tare da faɗawa duniyar tinanin da ya fara yin nitso a cikinsa, nemawa kansa mafita da kuma sauƙi shine abinda ya kawo shi garin nan bayan karatun da yake yi sai dai ashe ya yi gudun gara ne ya tadda zago tunda gashi a nan ɗin bai mance da ita ba har gizo take yi mana.
"Rabbi inni lima anzalta alaihir min khayrin faƙir".
Ya furta can ƙasan maƙoshinsa ya daɗe zaune a wajen har sai da aka fara ƙiran sallan zuhr sannan ya tashi ya tafi masallaci, zuciyarsa gabaɗaya babu daɗi shi kansa ba zai iya kama abu ɗaya ya ce shine yake