Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
ya sari guntun kashi Majid in sha Allahu Salma zata yi zaman auren da sai dai mutuwa ta raba su da Malam Mamman. Ko so kake ta share waje ta cigaba da zama a cikin gidan kamar yanda ƴan-uwanka suka yi?". Baba ne ya tsawar mata har ta sanyawa bakinta linzami ta koma harare-harare, kafin Hajiya Babba ta yi gyaran murya da hannu ta yiwa Salma ishara akan ta matso kusa da ita ta kuwa aikata hakan, dafa kafaɗarta tayi tana cewa"Salma ki faɗa min gaskiyan da dashi zamh tsayar da matsaya guda ɗaya, shin kina son malam Mamman har cikin zuciyarki ko kuma wani ko wata ne ya tusa miki soyayyarsa ta ƙarfin tsiya a cikin ranki?". Ɗif kamar an ɗauke wuta ko kuma an yi ruwa an ɗauke haka Salma ta yi shuru yayin da kowa ya zuba mata na jiyamu cike da zaƙuwar jin ta bakinta, sai da Hajiya Babba ta kuma maimata mata a karo na biyu kafin ta durƙar da kanta ƙas ta ce"babu wanda ya yi min dole zaɓin zuciyana ne".
Yanda ta ƙare zancen ƙarshen muryarta na rawa da kuma harɗewan harshe ya sa ni saki tagwayen ajiyan zuciya a jere, domin ni kaɗai nasan wannnan kalaman a iya leɓɓanta suka tsaya basu har zuci ba, wannan furcin natan dashi su Abba suka yanke hukuncin ƙarshe tare da sallamar kowa da kowa.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
________________________________
Page 1⃣0⃣3⃣
Babu yanda na iya izuwa yanzu domin iyayenmu sun gama yanke shawara tare da tsayar da matsaya game da lamarin auren Salma da Malam Mamman baban Zaliha, addu'a kawai na cigaba da yi mata cikin dukkan sallolina guda biyar na farilla da ma na nafilla Allah ya sauya mata hakan ya zamto alkhairi gare ta. Haka aka fara gudanar da shagalin bikin da suka rage tsirarun satikai a ɗaura ana sauran sati guda duk manyan yayunmu mata suka fara zuwa haka nan ma Balkisu, Abasiyya da Hanifa duk sun zo da ƴaƴan su. Maƙil gidan ya cika da ƴan-uwa da abokan arziki mu kaɗai ma gayya ne washe gari Goggo Suwaiba da Anty Zakiyya suka zo su daga nguru, zuwan da kafin bikin daga ni ita har Umma da yaya Majid sai da suka yi dana sanin zuwan ta domin baƙar magana, ba'a da kuma shaguɓen da ake yafa mata akan cewar taƙi aure tare da jingina jinkirin auren da ya faɗo a tsagin tata ƙaddarar ga laifinta. Duk da ba nima ina samu rabo na cikin baƙar maganar amma nawan bai cika damuna kamar na Anty Zakiyya ba da sam bata iya ce musu ko kanzil idan suna yi mata kwankwazo.
Ana gobe ɗaurin auren muna zazzaune a waje saboda tsananin zafi da matsalar wutar lantarkin da muke fama dashi, mun gama cin abincin dare kenan muna hira iska ya dire zancen da ake tattaunawa a faifayi a taron da dangin Umman Balkisu suka yi daga bayan mu.
"Wancan ita ce Na'iman ko?".
Wata muryar da na gaza tantance mamallakiyarta suka sauƙa a ƙofofin kunnuwana, Zainab ce ta amsa musu da cewar"e ita ce Anty Na'ima", sallamarta suka yi kafin wata ta amshe zancen da cewar"wannan uwar matan ita kaɗaj kaya guda, kuma ace bada aure kuma fa wai a hakan ma akwai yayarta da ita ko auren ma bata taɓ yi ba. Ita wannan ɗin boko ta tsaya yi shiya ɗauke mata hankali gabaɗaya har ta mance hanyar nemar lahirarta da kuma aljannarta dake ƙasan dugadigin ƙafarsa" .
Wata murya daban ta yi saurin amshe zancen da faɗin"kuma wallahi in kun lura duk wacce ta kai wani babban mataki a karatun boko bata taɓa samun mijin aure da wuri, don duk jama'ar gari kallon watsatstso suke yi musu da mutuncinsa na ɗiyoyi mata suka daɗe da tanbaɗewa, cewa fa aka yi kamar matansu na sunna haka malaman su na jami'ar suke amfani da su a duk lokacin da suka ga dama".
Kyarma jikina ya fara yi jin zancen matar da ban san ni ba da ya yi mungun sanya hanjin cikina kaɗawa, cak miyau ɗin bakina ya ɗauke na gaza samun ɗigon da zan jiƙa bushashshan maƙoshina da ya kafe kaf kunne na baza da nufin jin ƙarshen zancen nasun.
"Ai kuwa tana wasa da damar ta domin irin wannan damar ga ƴa mace sau ɗaya yake zuwa mata a rayuwarta, da ta sake tayi wasarere dashi kuwa ita za'a bari da cizon ɗan ƴatsa daga ƙarshe".
Duk iskan da bishiyar tsamiyar dake dashe a filin gidan yake badawa hakan bai sanya maiƙo gumin da yake tsatstsafowa daga goshina bushewa ba saɓanin hakan sai ma ƙara tsiyayowa da yake yi, firit na dawo hayyacina daga yanayin da na dulmiya cikin sa sakamakon jin hannun Balkisu saman kafaɗata da kuma muryarta da suka yiwa ƙofofin kunnuwana sauƙan ungulu.
"Ke kuma lafiyarki ana ta hira kin yi wani shuru?".
"Lafiya ƙalau kawai gajiya ce".
Na faɗa ina yarce gumin saman goshina a faƙaice , ban sani ba ko cikin su akwai wacce kunnuwanta suka jiyo mata zancen da na suka jiyo mini. Sai dai bana fatan ma sun ji domin ni zan iya dannewa daren ranar ban iya runtsawa ba sakamakon amsa kuwwan da zantukan suka dunga yi mini a cikin kaina.
Washe gari ta kasance ranar asabar da ƙarfe goman safe aka ɗauren mata uku daga gidanmu, kafin mazan da suka taro a ƙofar gidan sai da aka yj hayaniya tsakanin dangin Umman Ikilima da kuma na Umman Salma wai sun kama su suna gulmar tsufan mijin da Salmar da ta aure, ba kaɗan aka yi hayaniyar kamar za'a ba wa hamata iska sai da Hajiya Babba ta shigo a fusace ta nuna ɓacin ranta ainun kafin aka nutsa.
Tunda na gama ɗaurin kallabin dinkin angon da yaya Majid ya yi mana, nake waya da Nawwara cikin hiran take shaida mata cewar yau ne auren Salma sosai tayi mata fatan alkhairi da addu'o'in zaman lafiya a cikin sabuwar rayuwar da zata fara kafin muka yi sallama, tunda aka je jere gidajen Ikilima da Firdau'si aka dawo da ƙananun zancen wai gidan Firdau'sin ya yi ƙaramin da wasu kayanta ma sai dawo dasu gida aka yi domin rashin wajen inda za'a ajiye su gashi kuma tana da kishiya gida ɗaya kuma zasu zauna hakan ya ƙara rura wutar gutsiri-tsuman aka ta yi, sai bayan sallan magrib sannan aka kai Firdau'si da Salma ita kuwa Ikilima sai wayewar gari aka kai ta.
Tare da su Balkisu da Abasiyya da wasu dangi muka je gidan Salma, tun daga sallaman da muka yi yayin shigowa gidan zugan ƴaƴansa suka zubo mana idano har muka gaisa da matansa biyu da kusan sa'anni da su Umma. Basu ɗaɗe ba dangin suka tafi suka bar mu a kai akai nake sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi don har cikin raina nake ji ɗacin zuwan Salma cikin gidan nan a matsayi mata. Addinina bai haramta hakan ba amma sai dai ƙalubalen dake cikin ire-iren wannan auren nake hangowa ga Salma, ga matan zata yi kishi ko kuma da zunguma zunguman ƴaƴansa samari da ƴan matan da ya haifa ya barsu sakake suna yawo cikin unguwa babu wadataccen tarbiya, balle su ga girman manyan su.
Sai bayan sallan la'asar sannan muka gida, har yanzu gidan a cike da jama'a, salla kawai nayi yaya Majid ya aiko ƙira na hijabin da na iddar da sallan dashi yana kaina na gyara shi na fita yana ƙofar gida tare da wasu maza biyu da suka juya bayansu suna tsaye jikin wata motar da na zubawa idano ina tinano inda na taɓa ganin ta, har na iso gare su bakina ɗauke da sallama ban gano ainihin inda na taɓa ganin motar ba. Yaya Majid ne ya amsa sallamar tawan yayin da su kuma suka zubo mini idano kafin suka amsa sallamar a makare, saurin janye idanona nayi tare da rusunar dasu ƙasa ina jin matsanancin faɗuwar gaba a sanyaye na gaishe muryata tana rawar da ban san dalilina, raina cike fam da mamakin zuwan su garin nan kuma har ƙofar gidan mu ko meya kawo su oho, ban cimma amsar tambayar da na jefawa kaina ba muryar Malam Abdul-aziz ya katse mini hanzari.
"Ƴaƴar amarya ya hikimar biki?".
"Alhamdulillah".
"Masha Allah, Alkah ya basu zaman lafiya yasa sun shiga kenan har abada". Cike da jin daɗin addu'ar dashi na amsa da amin har sau biyu, sai a sannan Mr Saif ya ce dani"ya hutu fa kuna ta hutu ko".
Sai da na ƙara rusunar da kaina na ce"alhamdulillah hutu yana ta tafiya".
"That's good ina sistern ki fa?". Sai da na ɗaga kai alamar tinani kafin na ce"oh Anty Zakiyya tana ciki".
Sai a lokacin yaya Majid ya ce naje na ƙira ta, na koma cikin gida na ƙira ta muka zo tare gaisawa suka yi sosai don ɗaurewa ƙarya gindi har da ƙara tambayarta wai ya jiki don ɗan ruwan da ya fancakala mara kwanakin baya da suka gabata, ta ce dashi daman tun a lokacin ma babu wani ciwon da taji balle ayi mata yaya jiki.
Ina dai ina tsaye ne kawai ba don son raina ba, sai don ba yanda na iya Allah Allah nake yi su tafi na koma ciki na hutu don ji nake yi gabaɗaya gaɓoɓin jikina kamar ana sassara mini gunguwa-gunguwa da adda tsabar gajiyar da na kwaso a jikina, zance suke ta yi da yaya Majid da kuma Anty Zakiyya yayin da Malam Abdul-aziz ya yi gefe kaɗan yana amsa waya ɗago kan da zanyi naga ya saita wayar dai-dai mr Saif da yake tsaye jikin mota Anty Zakiyya na ta ɗan nisa dashi kaɗan, kamar hoto yake ɗauka sai dai bani da tabbacin hakan wannan dalilin ya sanya ni shashantar da zancen.
Yaya Majid ya ce su shiga su gaisa dasu Abba don a lokacin duk suna gidan a sashin su, yayin da mu kuma muka koma namu sashi ni kaɗai ina tafe ina gunaguni da kuma mamakin zuwan su garin nan har ƙofar gidan mu cikin raina.
Sai da ya yi musu iso sannan suka cika suka iske har Hajiya Babba zaune a falon, yaya Majid ya gabatar dasu ga su Abba sannan suka gaisa. Cike da farin ciki Baba yake faɗin"mun gode fa yaro mun gode sosai muna jin labarin ka a wajen Abdul-Majid akan yanda kake kula da yaran nan a can makarantar tare da sanya idanu akan su, mun gode sosai Allah ya biya ka domin bamu da abinda zamu iya biyan ka dashi duk wanda zai taimaka maka wajen gyara tarbiyar amanar da Allah ya damƙa maka ai ya gama maka komai a wannan duniyar".
Tun shigowar su kansa yake ƙasa yana murza yatsun hannunsa a hankali, har cikin ransa yaji daɗin addu'ar duk da domin Allah yake gudanar da hakan da kuma ganin cewar ya sauƙe nauyin alƙawarin da ya ɗaukarwa Majid ɗin game da hakan. A nutse ya furta"ba komai Baba ai shi ɗa na kowa ne baka san wanda zai amfane ba".
"Haka ne kam amma ba kowa ne yake la'akari da hakan ba, a nan kusa kuke ne?".
Furcin Hajiya Babba kenan da ya ƙare cikin sigar tambaya, Abdul-aziz ne ya amsa mata da"A'a Hajiya ba a nan muke ba bauchi zamu je shine muka tsaya a nan muka sanar da shi Majid ɗin gamu a garin su".
Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce"ai kuwa da zaku hutu ku kwana a nan zuwa gobe sai ku je bauchin". Haɗa ido Saif da Abdul-aziz suka yi kafin Abdul-aziz ya musguta haɗi da faɗin"da zamu so hakan ranka ya daɗe sai wajen magani zamu je kuma yau muke da oppoitment da shi malamin da yammaci in Allah ya kaimu".
"Magani?, waye cikin ku ba lafiya?".
"Mahaifiyarmu ce Hajiya take kwance a asibiti tsawon watanni bata san halin da kanta yake ciki ba, shine aka bamu labarin wannan malamin da yake zaune a cikin jahar bauchi zamu jarraba zuwa ko Allah zai sanya a dace".
Shuru falon ya ɗauƙa kafin Abba ya katse shurun ta hanyar faɗin"wani irin rashin lafiya ne?", dalla-dalla Abul-aziz ya yi masa game da jinyar Ummin hakan ya ba wa Abba damar ɗaurawa da"da zaku kwana a nan zuwa gobe in sha Allah, zan haɗa muku wasu rubutu mai ƙunshe da addu'o'in karya sihiri da kuma wasu ayoyin littafin mai tsarƙi ana bata tana sha in sha Allah za'a ga haske".
A raunane Saif ya furta"ranka ya daɗe bata iya ci bata iya shan komai duk tsawon wannan lokacin sai dai likitoti suyi hikima a sanya mata ta hanci".
"Subhanallahi ba komai sai ana shafa mata a jikinta gabaɗaya safe da yamma in sha Allah za'a dace".
Godiya sosai suka gabatarwa Abba tare da bashi tabbacin zasu kwanan zuwa gobe, duk da yaya Majid ya gabatar da sunayen su yayin da ya shigo dasu sai da Hajiya Babba ta ƙara tambaya Abdul-aziz ya faɗa mata, a ɗakin yaya Majid suka sauƙa.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 1⃣0⃣4⃣
Muna can cikin gida bamu san wainar da aka toya a sashin su Abba ba, sai bayan magrib da naje sashin Hajiya Babba take baje mini komai na gigita aihun jin yanda ta bada labarin rashin lafiyar mahaifiyar sun sai na ƙara jin wani sabon tsoron Allah ya ƙara mamaye mini ruhina da ya cika da rauni, naji duniyar gabaɗaya da abinda yake cikinta suka ƙara fice mini daga rai. Ban iya hana hawayen idanuna kwaranya ba domin bani da wannan ikon a wannan lokacin haka na bar su suka cigaba da tsiyaya. Haka nan ma Hajiya Babba duk jikinta a sanyaye yake a lokacin na ƙara jin son rubutu ya ƙara shige mini har ƙuriyar raina na kuma yarda cewa hanya ce babba da zan isar da muhimamman saƙo ga al'ummata a rubuce sai dai ko yaushe tambayar da nake yiwa kaina shine ta ina zan fara?.
Yaya Majid ya shigo ya sanar da cewar akwai baƙi don haka shigo da abinci ishashshe sashinsa, sanda na shigo ɗakin Umma na tarar yaya Majid ya na ba wa Umma da Anty Zakiyya irin labarin da Hajiya Babba ta labarta mini sak duk jikin mu ya mutu har ya ɗauki kololin abinci da babban kofin da Umma ta ciko shi him da kunnun gyaɗan da ta dama ya fice ɗakinsa bamu daina jimami da tu'ajudi ba. Ni kam gabaɗaya sai naji tausayinsa ya maƙale mini a raina ina kwatanwa da in nice a cikin wannan halin da yake ciki ban san yanda zanyi ba ba kaɗan ba jinyar iyaye yake da matuƙar tashin hankali mussamman irin wannan da mutum bai mutu ba kuma gashi a raye kamar wanda yake cikin ƙasa.
Da hantsi aka fara watsewa ya rage sauran tsirarun mutanen da aka haɗa rigima wai an yi sata a ɗakin Umman Ikilima duk kuɗin da ta samo a bikin an neme su sama ko ƙasa an rasa su sunyi ɓatan dabo, gagarumin rikici aka so haɗawa domin ƙiri-ƙiri suka fito fili suka nuna zargin su ga dangin Umman Balkisu akan satar, ranar sai da ran kowa ya ɓaci domin su Abba basu ɗauki matakin wasa ba a take a wajen suka je kowa ya watse kuma idan ba suyi wasa an daina taro kenan a gidan ko meye za'ayi walau biki ko wani taron. Kafin ka ce kwabo gidan sharau kamar anyi shara kowa ya watse sai dai Umman Ikilima na kan bakanta akan cewar dangin Umman Balkisu sai sun fito mata da kuɗaɗenta da suka ɓace. Sau huɗu Salma tana yi mini aike akan naje ina mayar mata da saƙon cewar bana jin daɗi sai zuwa bayan magrib zan shigo tunda bamu da nisa baki da hanci muke da ita.
Abincin rana na musamman Umma tayi ta ɗiba mai yawa da zoɓon da ta haɗa ta ce Majid ya kaiwa baƙi, bayan sallan asr kuwa sai gasu sun shigo bisa jagorancin yaya Majid har cikin sashin mu lokacin ko wacce mata tana zaune ƙofar ɗakinta da ƴaƴanta, cike da tsantsar girmamawan dake nuni da sun ƙoshi sunyi haniƙan da tarbiya da kuma nutsuwa suke durƙusawa gaban kowacce mata suna gaishe ta ba yabo ba fallasa suke amsa gaisuwar suna bin su da wani irin kallo.
Muna zaune da Anty Zakiyya a ƙofar Hajiya, yaya Majid ya ce dani na shiga ɗaki na cewa Umma baƙi zasu shigo na kuwa miƙe na isar da saƙon shi hijabi ta ce na miƙo mata ta sanya a cikinta.
Suka shigo a ƙasa suka zaune kan sabuwar ledar tsakar ɗakin da zuwa na ɗin nan yaya Majid ya sabunta mata ita domin bikin da aka yi suka zaune, suka gaishe da Umma ta amsa musu cikin sakin fuska da kuma fara'a har ta tambayar su yaya mai jiki suka haɗe baki wajen faɗin alhamdulillah da sauƙi. Sun ɗan zauna Umma tana yi musu tini da su riƙe addu'a da kuma sadaka game da jinyar natan domin shi sadaka yana tunkuɗe fushin Allah.
Godiya suka yi mata sosai, sanda suka tashi ficewa Mr Saif ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya ajiyewa Umma fir ƙin amsa tayi sai ma cewa sa tayi"kallon ƴaƴa nake yi kuma don haka babu buƙatar ku ɗaurawa kan ku wani ɗawainiyya Allah ya bata lafiya ku kuma ya tsare muku imanin ku wajen maida duk abinda zai taso game da jinyar da cewar daga Allah ne, kar ku kuskura wani ya juya muku tinani har ku tsirka tauhidinku da wani abun".
Wani ajiyar zuciya ya sauƙe mai ƙarfi yana komawa ya zauna a mazauninsa da ya tashi ajiyar zuciyar kawai ya cigaba da sauƙewa sai can ya ce"in sha Allah mun gode, amma yanda kika ce kina mana kallon ƴaƴa muma kallon uwa muke miki don Allah kar ki hana ni kyautatawa uwata ko don samun yalwa cikin lamurana".
Wannan zancen nashi shi ya sanya Umma amsar kuɗin ba don ta so ba, suka fice daga ɗakin yana fitowa duk idanu suka dawo kansu gaban Umma Ikilima ya tsuguna ya ajiye mata bandir ɗin ƴan ɗari biyar-biyan ɗin da