Author : Azizat Hamza Category : Top Hausa Novels 2025
kasa zuwa gaida Abba tayi tana zaune a ɗaki ta kasa leƙa ko ƙofar ɗaki tunda tayi Alwalar Asuba.
Ɗumamen da ke gabanta ma turashi gefe tayi dan ba iya ci zatayi ba.
Shigowar Abba ɗakin da sallama yasa ta miƙewa a firgice, tun jiya take jimamin shirun Abba.
Shiga ta musamman yai, yasa babbar riga kamar mai zuwa ɗaurin aure.
"Ina kwana Abba" ta faɗi tana rusunawa
"Lafiya Asiya Shahidah"
"Abba kayi haƙuri, wallahi ban san ya akayi na watsa masa ruwan ba"
"Ba tarbiyyan gidan nan bane. Ba kuma tarbiyyan Gwani bane Allah ya jiƙan rai. Girmama na gaba koda ba Shugaba bane tarbiyyan musulunci kenan, tarbiyyan da nake da yaƙinin mun miki kenan Asiya. To amma..."
"Abba ka yafe min"
Shi kansa Abba tun jiya ya kasa yarda Asiya ce tayi haka sai yanzu da ta jaddada masa. Jiya ya ji gudun Asiya zuwa banɗaki bai kai minti ɗaya ba kuma ya ji ƙaran tashin mota hakan ya sashi zuwa falon nasa da sauri.
Jug ya fara gani a ƙasa, wajen da Gwamna ya zauna kuma akwai alaman ruwa a wajen. Ya duba ƙasan wajen nan ma akwai ruwa a malale. Wajen baiyi kamada kwaɓewar ruwa bisa tsautsayi ba yafi kama da cewa watsashi akayi.
Kasa gaskata cewa Asiya ce ta aikata hakan yayi. Ya so kiran Gwamna amma rasa abinda zai faɗa masa ya sa ya fasa kiran. Ya kwana da tunanin mi zai yi, daga baya ya yanke shawaran zuwa wajen Gwamna ya bashi haƙuri. Lokacin daya tura saƙo wa Gwamna da bai ga reply ba tsoro ya shige shi. Bayan kamar minti arba'in Gwamna ya masa reply akan ya zo ƙarfe goma da minti shabiyar.
"Zan je na bawa Gwamna haƙuri dan gidana ba gidan da ake walaƙanta baƙo bane balle baƙo kuma shugaba. Kamar yadda na faɗa kiyi duk abinda kika ga dama"
Yana juyawa yai kiciɓis da Umma. Allah Sarki ta jima a wajen amma dake bata ji bata san mi suke tattaunawa ba. Ta shiga tambayar Abba miya ke faruwa amma yace mata kar ta damu idan ya dawo zai mata bayani.
Bayan fitar sa Umma ta tsare Asiya da tambayoyi. Daga ƙarshe dai sai da Asiyar ta faɗa mata abinda tayi. Umma ta kama baki tana zaro ido...
Abba na fita waje Ubayd na ƙoƙarin tsaida motarsa. Bai gaya masa abinda Asiya tayiwa Gwamna ba ya dai ce ya zo ya raka shi wajen Gwamna.
Haka suka wuce gidan Gwamnati kowa da abinda ke ransa.
Daga waje Ubayd ya nuna ID card ɗinsa amma duk da haka sai da masu gadi suka kira suka tabbatar da ana tsammanin zuwan su kafin aka barsu suka shiga ciki.
Wani security ya musu jagora har ofishin Sakataren Gwamna bayan ya sanar da Gwamna zuwansu sannan yace su shiga ciki.
Kwarjini Gwamna ya ƙara yiwa Abba. Kunyarsa ta gama cika shi lokacin da Gwamna da kansa ya miƙa masa hannu sukayi musabaha sannan ya jagorance su zuwa wajen kujeru inda yake zama ya tattauna da baƙinsa.
"Ranka shi daɗe, ba zan iya bayyana maka yadda raina ya ɓaci jiya ba. Ina roƙon ka dan Allah kayi haƙuri ka yafe mata. Asiya..."
"Ba komai Malam Nuhu, ya wuce a wajena. Infact na yaba da ƙarfin gwiwarta. Sai dai ina tausayin mijin da zata aura kar watarana yai laifi ya sha ruwan zafi" yai maganar yana dariya
Abba ya dara yayinda Ubayd ya sunkuyar da kai yana kallon fiskar wayarsa wanda hoton Asiya ne a wayar, bai ɗago ba sai da yaji Abba yace " ka ji abinda Gwamna yace ko Ubaydullahi, sai ka zage damtse"
Gwamna ya kalli Ubayd sannan ya kalli Abba hakan yasa Abba yai saurin cewa "ɗana kenan Ubaydullahi wanda zai aureta nan da watanni kaɗan masu zuwa"
"Allah ya musu jagora"
Abba ya amsa da Amin. Ko sakan talatin ba ayi ba Sakatare ya shigo ya ce da Gwamna lokacin tafiya yayi. Gwamna ya miƙe yai wa su Abba sallama dan fita zasuyi da tawagarsa zuwa wani ƙauye da akace za a buɗe firamare school na farko a wajen...
Gwamna yana ƙauye Alhaji Sani Kachallah ya kira shi akan yana son ganinsa idan ya dawo.
A ofishin Gwamna suka tattauna sabon batun daya ɓullo wai Matar tsohon Gwamna tana son shigar da Gwamna Saifuddeen ƙara.
"Umaru Kwom ne da wannan aiki. Shegiya ko idda bata gamaba tana maganar shiga kotu" Alhaji Sani ya faɗa da ƙarfi.
"Ko sun shiga kotu Baba ba abinda zasu samu sai baƙin ciki. Saminu Bacchi died a natural dead. Ni da likitan mun tattauna kuma ya gaya min jininsa ne ya hau sosai, stress ya sa shi faɗuwa har..."
"Na san wannan Saifu. Abinda nake gujewa shine wannnan maganar zata ɓata maka lokaci. Zaka ɓata ƙarfinka wajen biyewa shirmensu sannan alokacin Kamfen zasu dinga ɓata maka suna da zancen. Mutumin da ke karkara idan aka ce masa Saifuddeen Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna ba zai nemi gaskiyar magana ba. Abinda zai yi shine shi da iyalensa ba zasu zaɓi Saifuddeen Kachallah ba. And kasan ƙarfin ƙuri'un 'yan ƙauye kuwa ?"
"Baba inaga gara su shiga kotun a gama maganar kawai sab..." sai yai shiru tunowa da yai yadda Abba ke ƙoƙarin risinawa lokacin da yake bashi haƙuri. Idan aka shigar da maganar nan kotu Asiya za ta shigo ciki kuma za ta iya zuwa kurkuku ko ta biya tara mai yawa idan bata iya kare iƙirarinta da shaidu ba.
"Kar ka damu zan yi maganin matsalar. komai zai warware"
***
Musababbin zuwanta China ba dan saro kaya bane sai dan ta ga Malamin taurari wato Tsu Zhang. Shekaru ishirin da suka wuce a garin New Haven, Connecticut ta ƙasar America lokacin tana karatu a Jami'ar Yale wata Ƙawarta mai suna Paula ta gayyaceta wani taro da za ayi na mabiya addinin Buddha, inda aka gayyaci Malamin addini wato Monk Tsu Zhang ya zo ya yi mu su Lakca. Bayan an gama lakcan Paula da saurayinta Simon wanda basu jima da shiga addinin Buddhancin ba suka nemi ganawa da Malami Tsu Zhang, ya ba su lokaci da adreshin wajen da zasu sameshi.
Bilkisu ba ta bisu ba lokacin da suka je ganinsa amma ga mamakinta da suka dawo Paula tace mata Tsu Zhang ya faɗi saƙo a bata.
"Yace kinada ƙaddarar matar babban mutum yace tauraronki zai haska tareda ta mijinki"
"Haka yace? Taya ya sani?"
Tambayoyinta kenan lokacin da Paula ta sanar da ita saƙon Tsu Zhang. Bata tuna da wannan batu ba sai ranar da aka rantsar da Mijinta a matsayin Gwamna. Godiya take son yiwa Tsu Zhang shiyasa ta nemi ƙawarta Paula wacce take aure a ƙasar Brazil. Paula ita ta bata addreshing Tsu Zhang a China.
Bata sha wahalar samun inda Tsu Zhang yake ba sai dai kuma sai da ta booking lokaci saboda yanzu Tsu Zhang ya tsufa baya karɓan baƙi sosai.
A wani tafkeken temple (wurin bautan gumaka) Bilkisu ta samu Tsu Zhang. Lokacin da aka kaita wajensa ta jima zaune tana jiransa saboda meditation da yake yi. Lokacin daya buɗe ido bai juyo gareta ba, daga inda yake zaune yana fuskantar ƙaton gunkin Buddha dake ɗakin yace " akwai wani tauraro daya fito a gefen tauraron mijinki. Yadda tauraronki ke haskawa tareda ta mijinki haka wannan tauraro zai dinga haskawa tareda shi har sai tauraron mijinki ya haskaka fiye da tunaninki. Idan kikayi ƙoƙarin disashe wannan tauraro babu makawa da taki tauraron data mijinki haskensu zai dinga disashewa. Ki sani taurari uku a waje ɗaya suna bada haske na ban mamaki "
"Ban gane ba..."
Hannu ya ɗaga mata hakan ya sa tayi shiru. An riga an gaya mata cewa Tsu Zhang idan yai magana baya ƙarawa sannan baya maimitawa.
Har ta bar temple ɗin hankalinta bai kwanta ba. Wani irin tauraro ne ya shiga tsakaninta da ta Saifuddeen?...
***
Abba daya dawo bai gayawa Asiya komai ba, ya dai yiwa Umma bayanin komai, tareda faɗa mata yadda Gwamna ya tarbesu da mutunci suka rabu ana raha. Ubayd kam ko gidan bai shigo ba dan har yanzu fishi yake da ita.
Umma ta bata shawaran ta je ta bawa Gwamna haƙuri amma har yanzu bata yanke shawaran zuwa ba. Gani take idan ta je kamar ta ƙasƙanta kanta a wajen Gwamna ne.
Haka dai ta dinga saƙa da warwara har dare. Ƙarfe takwas da minti Arba'in Ubayd ya kirata yace ta sameshi a waje. Da murna ta fita dan a ganinta ya sauƙo kenan.
"Kin ji cewa Sha'awanatu Bacchi zata shigar da ƙara akan kashe mijinta da aka yi?" Ya faɗa yana tsareta da ido.
"Na gani a newsline"
"Kin shirya shiga kotu dan kare kanki kenan?"
"Ya Ubayd..."
"Tambaya na miki"
" ban so haka ta faru ba"
"Abinda kike so kenan Asiya. Ina so ki sani cewa shari'arku ta tsaya a wajen gidan nan. Nothing should happen to my family Asiya, kada abinda ya samu Abba ko wani acikin gidan nan. Rigimarku ta siyasa ta tsaya chan nesa da mu"...
Washegari ƙarfe shaɗaya ta shirya ta wuce gidan Gwamnati. Indai baiwa Gwamna haƙuri shi zai sa Umma da Abba da Ubayd suyi farin ciki da ita to za tayi. Wunin jiya ko kallon kirki Abba bai mata ba. A duniyar nan babu Uban da take da shi daya wuce Abba. Ale Faruƙ haihuwarta kawai yai amma Abba shine Ubanta.
Tunda ta fito daga keke Napep zuwa shiganta Gate sai ɗaukan hotonta ake ta yi. Ta turawa Sakatare text jiya da dare bayan ta bar wajen Ubayd akan tana son ganin Gwamna kuma shi yace ta zo ƙarfe shaɗaya na safe.
Tana isa wajensa yace ta shige ofishin, Gwamna yana jiranta. Gwamna ne zaune tareda Alhaji Sani Kachallah lokacin data shiga ofishin.
" 'yar jarida mai ƙwazo" Alhaji Sani ya faɗa yana murmushi.
Asiya tayi saƙeƙe tana kallonsa.
"Bismillah, zo ki zauna ai wannan zama naki ne"
Ɗan ɗosanuwa tayi a bakin kujera ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya yayinda ta sha jinin jikinta saboda kwarjini da suka mata.
Alhaji Sani ya ɗauki kofin shayin da ke gabansa ya kurɓi kaɗan kafin ya kalli Asiya yace " akwai saƙon da za ki gani gobe. Tukwici ne daga gareni. Ina fata idan kin ga saƙon zai faranta miki rai sosai"
Haƙuri ta zo bawa Gwamna amma kuma ta kasa furta komai. Bata gane inda maganar Alhaji Sani ya dosa ba.
Da ƙyar ta iya haɗa kalmomi biyu tace "ban gane..."
"Idan kinje gida ki gaishe da mahaifinki"
Ba sai ya ƙara magana ba ta sani managarsa na nufin ta tashi ta tafi.
Gwamna baishe da ita uffan ba sai ma kauda kansa da yai gefe...
Daga gidan Gwamnati shagonsu ta wuce wanda tunda sukayi hatsari rabonta da wajen. Tana wajen Umaru Kwom ya turo mata saƙo akan ya kamata su haɗu
su tattauna. Ta tura masa saƙo akan yai haƙuri ba zata iya taimaka masa ba.
Saƙon Alhaji Sani Kachallah ya isowa Asiya ƙarfe takwas na safe lokacin tana shirin fita shago tunda yanzu ta bar aiki a Hill TV. Aliyu ne ya shigo ɗakinsu da gudu sanye da uniform ɗin makaranta.
"Miya sa baka tafi makaranta ba Ali?"
"Anty Shahidah wai kije yanzu-yanzu inji Abba" ya faɗa sannan ya ruga da gudu.
Hijab ɗin Umma dake kan gado ta saka sannan ta wuce falon Abba da sauri.
Tana zuwa ta ganshi ya ƙurawa TV idanu.
Baice komai ba dan haka itama ta maida hankalinta kan talabijin ɗin. Bayan minti uku sannan aka fara karanta labarin daya sakata riƙe kai. Hotonta aka nuna tana magana da wani security a bakin gate ɗin gidan Gwamnati sannan ga tanan tana ƙoƙarin shiga office ɗin Gwamna daga nan kuma sai aka nuna hoton wasiƙa zuwa ga Gwamna wanda sunanta da sa hannunta ke ƙasa. Mai karanta labaran yana karanta wasiƙar hawaye na zubowa a idon Asiya yayinda ilahirin jikinta ya ɗau rawa.
Cin mutuncin da za a mata kenan a ɓata mata suna.
Abba ya rage volume ɗin TVn sannan ya juyo ya kalli Asiya.
"Abba wallahi ban rubuta wata wasiƙa ba"
"Wanda bai ji bari ba ai zai ji hoho ko Asiya. Kin dai ji yadda 'yan siyasa suka juya labarinki"
"Na shiga uku"
"Kiyi addu'a Allah ya sa ya tsaya a iya haka. Idan kuma taurin kai da kika saba za ki yi to Bismillah"
Kafin ƙarfe goma na safe ko ina ya ɗauka 'yar jarida Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta yiwa Gwamna tayin soyayyarta ne shiyasa ta yaɓa masa baƙin fenti da bai amince da ita ba. Hatta cikin rahoton data kawo tana aibanta SSK lokacin daya ke mataimakin Gwamna sai da aka nemo aka dinga yaɗawa.
Kowa a jahar sai tofa albarkacin bakinsa yake yi akan zancen. Wasu suce Asiya irin matan nan ne masu bibiyar 'yan siyasa amma shi Gwamna SSK babu ruwansa da harkan mata. Wasu kuma suce neman suna take yi saboda ta fitar da labarin da zai yi fice da ita a duniya amma dake Allah ba azzalumin bawa bane shiyasa asirinta ya tonu. Wasu kuma cewa suke akwai lauje a cikin naɗi ƙila an yiwa Asiya barazana ne shiyasa ta rubuta wasiƙar nan. Wasu kuma suna ganin 'yan adawa ne suka biyata dan ta ɓatawa Gwamna suna. Maganganu dai kala-kala.
Maganar shigar da ƙara da ake ta raɗe-raɗin Matar tsohon Gwamna za ta yi kuwa sai ya zo ya bi ruwa.
Lokacin da Likitan tsohon Gwamna yai bayani a gidan talabijin tareda fitar da report na gwaje-gwajen da akayiwa Gwamna Saminu Bacchi bayan rasuwarsa hatta Umaru Kwom sai da ya ji jikinsa yayi sanyi domin babu yadda za ayi ya samu nasara kan tuggun daya shiryawa SSK duk da kuwa ya yarda koda SSK bai sa an kashe Saminu Bacchi ba to Alhaji Sani Kachallah zai iya aiwatar da hakan.
A ranan wani Malamin addini ya fito yai bayani akan yarda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau. Yai maganar cewa yana cikin rashin yarda da ƙaddara mutum ya fara bibiyar dalilin mutuwar wani. Gwamna Saminu Bacchi lokacinsa ne yayi shiyasa Allah ya ɗauki ransa abinda al'umma za su yi shine a cigaba da yi masa addu'a da shi da duk wanda suka riga mutuwa. Ita kuma Asiya Allah ya shiryeta.
A rana ɗaya tal sunan Asiya ya chanja zuwa maƙaryaciya. Washe gari da safe wani mawaƙi ya shiga studio ya sake waƙa yana yabon Gwamna yana aibata sunan Asiya.
Sai da Asiya ta gama shirya kayanta tsaf kafin ta wuce falon Abba, baya nan dan haka ta tura masa saƙo akan cewa zata koma gidan Baffa Malam.
Idonta yayi jaa duk sun kumbura saboda kuka. Umma ta goyi bayan shawaran data yanke data ce zata je ta zauna a gidan Baffanta har sai saura sati biyu bikinta kafin ta dawo...
***
"Your excellency inada magana"
"Bismillah Malam Baffayo"
"Yarinyar nan Asiya rayuwarta na cikin haɗari"
Gwamna ya zaro ido cike da mamaki.
" na samu labari daga majiya mai ƙarfi cewa mutanen Umaru Kwom suna son kasheta saboda a tada sabuwar fitina tunda wancan ta mutu"
"How could they, ina kaji wannan magana?"
Sakatare yace " Excellency a bar kaza a cikin gashin ta"
Lokacin daya bar office kai tsaye Kachallah house ya wuce wajen Alhaji Sani.
Bayan ya yiwa Alhaji Sani bayanin da Sakatarensa ya masa sai kawai ya ga ya ɓigire da dariya har da kakkautawa.
Ya sake baki yana kallon Baffan nasa.
"Wani lokaci Saifu kaman baka san mi ake nufi da siyasa ba. Ba abin mamaki bane idan sun yi niyyar kasheta saboda wata manufarsu, sai dai duk ta inda suka ɓullo ina nan ina jiransu. Har yaushe ma Umaru ya girma da zai ce zai ja dani"
Wani abu ya daki zuciyar Saifuddeen. Ana maganar kashe ran yarinyar da bata ji ba bata gani ba amma yana dariya. Ba zai taɓa bari a hallaka rai a rikicin Gwamnatinsa ba.
"Baba ba zan bari su taɓa lafiyarta ba balle ma har su kasheta matuƙar ina raye"
Alhaji Sani ya kalli SSK da alamar tambaya a bakinsa amma bai furta ba sai yace " kenan zaka aureta?"
"Baba ban gane ba" Gwamna ya faɗa cikin rashin fahimtar manufar Alhaji Sani Kachallah.
"Hanya ɗaya da zaka iya kareta kenan Saifu" Alhaji Sani faɗa yana cigaba da dariya.
WAIWAYE...
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
09
*WAIWAYE*
Abu ne da muka sani cewa Allah zai iya jarrabtar mu ta kowani fanni na rayuwarmu. Zai iya jarrabtarmu ta wajen dukiya, lafiya, 'ya'ya, mata, 'yanuwa, iyaye da sauransu.
Asalin iyayen Lukman Fulanin Baroroji ne wanda basa zama waje guda su jima.
Lukman yaro ne da aka haifeshi da ƙusumbi (hunchback). Yana shekara uku mahaifiyar sa ta rasu wajen haihuwa. Matar uban sa da ake kira da Gaji ta ce ba za ta iya riƙe shi ba, shiyasa Uban sa ya damƙa shi wajen Yayar mahaifiyarsa mai suna Habbi. Yana cika shekara biyar a wajenta ta ɗauke shi ta kaishi wajen Malam AbdulWahab Falke Almajiranci wanda ya kasance Kawu a wajen mijin ta.
Tunda aka damƙa Lukman wajen Malam kuwa Mahaifin sa bai taɓa waiwayan sa ba har Allah ya ɗau ran sa, shekaru biyar bayan rasuwan Asiya mahaifiyar Lukman ɗin. Itama Inna Habbin sau ɗaya ta je ta duba Lukman daga nan ba ta sake zuwa ba har rai yai halin sa.
Malam Falke ya zamewa Lukman Uwa da Uba sannan Malami. Duk cikin Almajiran Malam, Lukman ya fi ƙoƙari da hazaƙa. Ya maida hankali sosai wajen karatu. Ɗan sarari da su ke samu da sauran ke watayawa cikin gari shi yana amfani da wannan lokaci ne yai ta ƙoƙarin rubutu a Allon sa.
Malam Falke Allah bai bashi 'ya'ya dayawa ba. Yaran sa biyar ne kacal sai kuma 'ya'yan da ya ke riƙewa. Huɗu daga ciki mata ɗaya kuma namiji. Kafin a kawo masa Lukman ɗansa namiji ya jima da rasuwa, dan shekaransa shida ya rasu bayan wata ƙaramar jinya.
Dayawa mutane sukan ɗauki Lukman a matsayin ɗan Malam ne saboda irin kulawar da Malam ke bashi.
A hankali da ya dinga lura da baiwar karatu da Allah ya bawa Lukman sai ya zamana ya fara ba shi karatu na musamman. Duk wani ilimi da ya ke da shi to yana ƙoƙarin ya ga cewa Lukman ya samu, yana ma sa tanadin zama magajin sa. Koyaushe baya rabuwa da yiwa Lukman Du'a'ul Fahmi.
Lukman yana shekara tara yai saukan ƙur'ani (tartil) yana shekaru shahuɗu yai haddar ƙur'ani kuma cikin watanni bakwai ya rubuta ƙur'ani da ka.
A hankali ya dinga haddace manya-manyan litattafai na addini. Yana shekara shabakwai