THE GOVERNOR'S-MATAR GWAMNA --Document Complete .txt

Author :  Azizat Hamza Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   15 / 21

42K to 45K   out of 62.2K words

kuka saboda Ale Faruƙ ya gaya mata cewa ya karɓi kuɗin aurenta a hannun Alhaji Talba. Tana shekaru shabiyar alokacin, Alhaji Talba kuma zai iya kaiwa shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar. Da kuka wiwi ta iso zauren Gwani inda yake koyarda wasu manyan Almajirai dama wasu ɗalibai magidanta dake ɗaukan karatu a wajensa.






Bayan sun keɓe ta fara bayani






"Shi Baba komai kuɗi komai kuɗi. Ni gaskiya ba zan yarda ya sayar dani ba, ai bance masa aure nake so ba. Ni gaskiya karatu zan yi" tayi maganar cikin kuka.






"Ishiru Uwata, faɗa mini mi aka miki?"






Asiya ta goge hawaye ta zayyane masa duk abinda ya faru kan cewa Ale ne da safe ya gayawa Iyani da Fulani cewa su shirya karɓan baƙi gobe za a kawo kayan gaisuwar Asiya.






Ta haɗa da cewa " shi Baba rayuwarsa ta ƙare a kuɗi da mata. Abin kunya kwanakin baya daya saki Delu ina Bibalo ya auro. Bibalo fa, yarinyar da tun tana ƙarama take fama da taɓin hankali. Tsofai tsofai da shi ya ɓata mata rayuwa gashi Aljanunta sun hanata zama a gidansa"






Jin irin maganganun nan na fitowa daga bakin jikarsa zuciyarsa ta shiga ƙunci. Yai saurin karanto Isti'aza a zuciyarsa sannan ya riƙo hannun Asiya yace


*"Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?"*


Tayi shiru tana kallonsa. Ya cigaba da yi mata nasiha tareda cewa ba abinda zata iya yiwa Ale sai dai ta rinƙa masa addu'ar Allah ya shirya shi, domin shi ɗin Uba ne gareta hakan kuma ba zai chanja ba har abada.






Bayan wannan abinda ya faru Gwani ya kira Ale Faruƙ ya masa faɗa yace bai hanashi aurar da 'yarsa ba idan ya ga hakane mafi alkhairi amma matuƙar yana raye ba zai taɓa bari ya mata auren dole ba kuma ko yayi bai yafe masa ba.


Saboda fasa auren da akayi Alhaji Talba ba ƙaramin rigima sukayi da Ale ba dan sai da suka yi kaca-kaca da shi.






Wannan dalilin ne kuma yasa Asiya ta dawo gidan Gwani da zama permanently har lokacin data samu admission a Congo University ta koma gidan Ummanta da zama.










Ale Faruƙ na kasuwa aka zo aka sameshi da zancen daya saka shi shiga mota ba takalmi dan har sai daya fita daga motar ya tunkari motocin Alhaji Sani Kachallah daya taka wani ƙaramin kara mai tsini ya lura cewa ashe babu takalmi a ƙafarsa. Wannan bai karya masa gwiwa ba yai saurin cire karan a ƙafarsa sannan ya ƙarisa motar daya ke tsakiya wacce yake tunanin a nan babban baƙonsa yake.






Samun buɗi ya sa Ale Faruƙ ya gyara ƙofar gidansa dama sashensa, wanda yanzu falo biyu gareshi ta farko ta karɓan baƙi ta biyu kuma wanda yake kallo ya ci abinci sannan anan yake zama da 'yan uwansa da abokansa na kusa lokaci zuwa lokaci.






Lokacin da Alhaji Sani ya fito daga mota har ƙasa Ale ya durƙusa yana kwasan gaisuwa fiskarsa washe kaman an masa albishir da Aljannah. Jiki na rawa ya masa jagora da tawagarsa ta mutum uku zuwa falonsa. Sai da suka zazzauna ya sake risinawa ya gaida su. Alhaji Sani da wani tsoho da yake tunanin zai kai shekaru casa'in sun girmeshi sosai amma sauran biyun ɗaga cikinsu zai kai sa'an Bellonsa sai ɗayan kuma dai zaiyi sa'an ƙaninsa Zakari.






Ƙokarin fita ya nemo musu ruwa yai amma Alhaji Sani ya dakatar da shi yace idan akwai wanda zai kira ya kira domin sun zo neman auren 'yarsa ce.






Ale Faruƙ ya ɗau waya ya fara kiran Baffa Malam yace ya zo maza-maza akwai manyan baƙi na jiransa. Bai san wacce cikin 'ya'yansa ake so ba amma cikin 'ya'yan dake gabansa mata da suka kai aure ba suyi aure ba, su biyar ne. Asiya data haura ishirin, Nafisatu da Ɗayyiba da suke shatakwas sai Sumayya data ke shabakwai sannan Baraka dake shashida. Koma waccece a cikinsu Alhaji Sani na nunawa to ya bashi ita ne kawai, babu mahalukin daya isa ya hana. Gwani ne ya isa ya dakatar da shi akan lamurran 'ya'yansa kuma Allah ya jiƙan rai ya jima acikin ƙasa.






Malam Audu maƙocin Ale ne ya fara isowa kafin Baffa Malam da Baffa Zakari wanda dama jiran baƙin suke dan tun jiya da dare Abba ya kira Baffa Malam ya sanar dashi abinda Gwamna yace da kuma matakin da shi ya ɗauka na janye neman da ɗansa ke yiwa Asiya. Baffa Malam da Baffa Zakari sun tattauna tsakaninsu kuma sun zuba ido ne tun jiyan suga yadda komai zai wakana tunda magana irin wannan Ale ne zai yanke hukunci ba su ba.


Minti bakwai da zuwan Malam Audu suma suka iso, dake kujerun sunyi kaɗan A ƙasa suka zauna tunda uban gayyarma a ƙasa suka sameshi. Duk da Alhaji Mustafah Kachallah Baffa a wajen Alhaji Sani ya nemi su Baffa Malam su zauna a kujera, Baffa Malam da Malam Audu ne kawai suka zauna a kujera.






"Na bayar" Ale Faruƙ ya faɗa tun kan Alhaji Mustafah ya ƙarisa bayaninsa.






"Idan hakane zamu ajiye sadakin yarinyar da kuɗin mun gani muna so idan yaso a hankali sai a kawo sauran abubuwan. Sannan kuma idan babu matsala muna so nan da sati biyu ko uku a ɗaura auren"






"Wallahi ko yanzun nan kuka ce a ɗaura mun shirya"






Baffa Malam ya bi Ale da ido. Kuɗi ai ba hauka bane. Tunda ya shigo falon ya lura da yadda Yayan nasa ke yi kaman wani wawa a gaban waɗannan mutane. Ya yarda suna da kuɗi sunada matsayi, suna da daraja a idon al'umma. Amma ba wannan bane zai sa kuma su basu wuƙa da nama a lamarin auren 'yar su. Sunada 'yanci ai. Ya dai yi shiru ne kawai saboda sanin halin Yayansa da yai, abune mai sauƙi a wajensa idan yai magana ya fara masa gori cewa ai shine Uban Asiya.






Miliyan ɗaya cash aka ajiye musu. Sadaki dubu ɗari biyar sauran dubu ɗari biyar kuma kuɗin na gani ina so kamar yadda suka faɗa.


Su Baffa Malam ne suka raka baƙin waje yayinda Ale ya shige ƙuryar ɗakinsa yana neman wajen yiwa kuɗin mafaka.






Sanda ya fito zai bisu ya ci karo da kayan da aka jibge a ƙofar falon, tarkacen kayan gaisuwane su buhun gishiri, buhun suga, kwalin sabulai, kwalin minti da cingam, damin goro kusan kashi goma da kuma ƙwaryan Zuma guda uku.


Ya haɗiyi yawu ya yi waje da sauri lokacin har motocin baƙin sun riga sun juya...










***










"Ba zaku maidani mahaukaciya ba Baffa. Ta ina za'a karɓi kuɗin aurena bayan akwai maganar aurena da Ya Ubayd. Baffa kaima ka koma son abin duniya ne kaman Baba?"






"Zauna Asiya"






"Noo Baffa. Ka gayamin gaskiya, kuɗi da mulki sun fara tsole muku ido kuma?"






"Ki zauna aka ce miki ko" Baffa Zakari ya daka mata tsawa.






"Wannan abin yafi ƙarfinmu. Amma duk abinda kika gani ya faru da bawa to rubutacce ne daga Allah. Ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara. Insha Allah zamu cigaba da yi miki addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi a rayuwarki"






"Shikenan dan kunga Gwani baya raye sai ku yanke hukunci bisa son zuciya. Baffa wannan son zuciya ne, da ku da Baba duk dukiya ce ta tsole muku ido. Ba zan auri kowa ba sai Ya Ubayd"






Daga haka ta bar musu ɗakin da gudu.


Ranan ƙarfe bakwai na yamma a gidan Abba ya mata. Tayi ta kiran nambobin Ubayd amma duka a kashe su ke. Hankalinta ba zai iya ɗaukan wannan abin ba. Ta yarda da ƙaddarar data faɗa mata na abubuwan da suka faru da ita cikin kwanakin nan. Yanzu ma maganarta ya ja baya a duniyar yanar gizo an koma gulmar wani ɗan film da aka ce yana luwaɗi.






Umma ma kamar kowacce Uwa ta damu da halin da 'yarta ta shiga musamman data ganta a fige kamar kazar sadaka.


Ta yi iya baƙin ƙoƙarinta wajen nuna mata cewa hukuncin da aka yanke mata ana mata zaton alkhairi ne ba sharri ba.






" Addu'a shine abinda ya rage miki yanzu Asiya ba kuka ba"






Maganar Mama kenan lokacin da ta riƙe mata ƙafa tana kuka akan ta tayata roƙon Baba da Baffaninta.






Itama Umman sunan addu'a take kira mata. Addu'a, Addu'a, Addu'a. Ta fa gaji da jin wannan suna.






Lokacin da tace zata fita, Umma cewa tayi sai dai dole su tafi da Gwani ko Aliyu. Dake Aliyun ne ke kusa shine ya rakata gidan su Umma Hussaina.


Rabonta da gidan ma zai iya kaiwa shekara.


Ta tsammanci samun Ubayd a gidan amma aka ce mata yayi tafiya.


Ta jima tana zaune a ɗakin Umma Hussainan kafin daga baya ta haƙura ta miƙe ta tafi ko sallama bata yiwa Umma Hussaina ba.






Damuwa kan chanja tunanin mutum matuƙa. Wasu lokutan Asiya sai ta shirya zata gudu sai ta fasa, wani lokaci kuma tayi tunanin ta kashe kanta ma kawai ta huta. A wasu lokutan kuma tayi tunanin samun bindiga ta je ofishin Gwamna ta bindige shege kowa ma ya huta. Wani lokacin kuma tayi tunanin ta haukace kawai saboda a dakatar da komai. Wasu lokutan ma zuciyarta na riya mata cewa ƙila ba Ale Faruƙ bane ubanta. Abin da ya fi riƙe mata rai ma bai fi yadda Ubayd ya ɓace mata ba, ga numbarsa da har yanzu bata shiga.


Ta fara tunanin ƙila Gwamna ne ya sa aka ɗauke shi, an ƙi faɗa mata ne kawai.






Sati ɗaya tayi a gidan bata san inda kanta yake ba. Abba da Umma kullum suna nuna mata ta saki ranta komai zai zo ya wuce amma zuciyarta bai shirya ma yarda da zancensu ba balle har ya amince da shi. Ubaydullah shine masoyinta na farko kuma na ƙarshe, ita tunda ta taso ma bata taɓa son wani ba, ko crush na primary ko secondary school bata taɓa ba. Ubayd ta fara so tun lokacin da ya ɗauka mata tsumman abunta, tun lokacin bata san so ba.


Saboda Ubayd bata taɓa bawa wani damar shiga rayuwarta ba. Ko lokacin da take Jami'a da tayi tashe, samari ke mata chaa babu wanda ta taɓa buɗewa ƙofa. It has always being Ubayd and will always be.






Yayinda Asiya ke fama da damuwa, a chan gida kuwa Ale Faruƙ ya kasa ya tsare wajen ganin wannan biki ya tafi yadda ya kamata. Sati ukun nan gani yake kaman ba za su iso ba. Tun yanzu ya fara kiran kansa sirikin Gwamna har tambayar siriki yai da turanci aka ce masa Inlaw amma idan shi ya faɗa sai kaji kamar 'yanlo yace.


Yi masa kirari da sirikin Gwamna kaga ya ɗau kyautan dubu ya baka mutumin da ɗarinsa idan ba a mace ba baya iya bayarwa.






Tuni yasa aka yiwa gidansa sabon fenti. Matansa da sauran yaransa duk ya musu ɗinkin biki kala biyar biyar hatta yayyen Asiya da ke gidajen mazajensu ya aika musu da nasu kayan. Wannan kashe kuɗi ko a sallah albarka. Shi dai yanada abu ɗaya gidansa ana cima mai kyau amma wani siyan kayan sawa ko na ado to ko a sallah sai anyi da gaske, yawanci ma iyayen 'ya'yan ke musu. Haka batun makarantar boko idan ka wuce sakandare sai fa ka tallafawa kanka. Mace ɗaya ce tayi karatu a 'ya'yansa mata bayan Asiya, itama kuma a gidan mijinta tayi. Adda Hadiza kenan da ta karanci ɓangaren midwifery.










***






"It was for political reasons Bilkisu"






"Shine sai dai naji a bakin Babana"






"Sanda kika dawo bana gari kuma wannan magana bata waya bace"






"Saifuddeen ka rasa wacce zaka aura sai 'yar Kurma jikar maiƙusumbi" ta tintsire da dariya. "I'm sure ba wai zaka nemi haihuwa da ita bane ko? dan ba zan juri ganin 'ya'yan guragu, kutare da makafi a gidan nan ba"






Gwamna yai seƙeƙe yana kallonta. Ita ce dai da take zuwa gidan marayu tana ɗaukan hotuna da naƙasassun yara.






"Na ɗauka baka ƙyamar nakasassu Bilkisu"






"Oh please Saifuddeen. Ka sani sarai campaign nake yi"






Ido ya zuba mata ya rasa ma mi zai ce. She never seizes to amaze him.





"And Darling, ka sani zan haƙura ne kawai saboda lokacin campaign ya kusa, bana son abinda zai ɓata maka ƙuri'u. Abu na ƙarshe kuma shine ka nema mata wani gidan dan a nan" ta juya yatsarta manuniya "ni kaɗaice Matar Gwamna"...



2g Novels







Home / THE GOVERNOR'S WIFE / THE GOVERNOR'S WIFE 13
THE GOVERNOR'S WIFE 13
2g novels THE GOVERNOR'S WIFE










*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....













*©Azizat Hamza*





wattpad Azi_zat










Bismillahir Rahmanir Rahim

















Book one

















*Assalamu Alaikum*






*Barkanmu da warhaka. Babu kalmar da zan iya baku haƙuri da shi daya wuce na haɗa ku da Allah. Dan Allah kuyi haƙuri.*


*Ban so na kai waɗannan ranaku babu update babu bayani ba. Amma akwai dalilin daya sa na yi haka.*





*Kwanan baya nayi rubutu ina son na yi copy and paste sai nayi deleting nashi. I was blocked, for days na kasa sake typing. Daga baya nace ni da update sai na kammala typing part 1. Na dena hawa online ne saboda bana son distraction.*


*Wanda suka min magana ta whatsapp ko wattpad ban amsa ba, ina baku haƙuri. Wanda suka kirani numba na a kashe suma ina basu haƙuri. Ya kamata ace nayi muku bayani amma banyi ba. Ina neman afuwa akan haka.*


*Insha Allah part 2 zai fara zuwa daga ranan Asabat idan Allah ya kaimu.*






*Nagode da haƙuri da ni...*
























13














Matar Gwamna. Ayyiriri Amarya"







"Queen Bee bana so, ki bari. Tukunna ma ya akayi kika sani? "






Queen Bee ta ɗaga mata waya tana faɗin Umma.






"Haba Asiya! So kike a kaiki gidan Gwamna kamar wata ƙwarangal. Look at you"






"Idan wannan ya kawoki, tashi ki tafi"






"Baki isa ba, Wallahi baki isa ki ja mana kunya ba. Dole sai anyi miki gyaran nan"







"Zaki yi ki barni dan ba abinda zanyi"






Duk yadda Queen Bee ta so su fara gyara Asiya bata ba da haɗin kai ba. Duk da Umma ta sa baki hakan baisa ta chanja ra'ayinta ba.







Ana saura kwana bakwai a ɗaura aure, da safe irin ƙarfe goma shaɗaya aka kawo lefen Asiya. Lokacin bata gida, ta raka Sumayya makaranta, za ta fara registration dan ta samu admission a Jami'ar Congo.






Lokacin da Asiya da Sumayya suka shigo gidan, a cike suka samu da mutane, yawanci maƙota ne sai kuma 'yan tsirarun 'yanuwansu dake zaune a Congo.






Faty 'yar Inna Yaha ce ta jata suka shige falon Abba saboda ɗakin Umma a cike yake da baƙi.







"Ban gane mi yake faruwa ba, wani taro ake yi a gidan?"






" 'yaruwa kinga lefenki kuwa?"







Ƙoƙarin buɗe ɗakin Abba ta shiga yi Asiya ta katseta. Bata buƙatar ganin koma minene aka kawo. Ashe shiyasa jiya da yamma Umma da Fatyn suka wuni suyan kaji a kitchen.






"Ki barshi Faty, ba sai na gani ba" Faty bata bari ta ƙarisa ba ta jata suka shige ɗakin.


Akwatuna ne akan gado gefen gado da duk wajen da akwai sarari. Wasu baƙaƙe, wasu ja, wasu blue, wasu brown, wasu lemon green da kalan silver.







"Ashirin da huɗu cif" Faty ta faɗa tana wage haƙora.






"Yanzu Anty Faty an buɗe dukkansu?" Sumayya ta tambaya cike da farin ciki.






"Guda shabiyu aka buɗe, Hajiya Adda tace a barsu haka, wai da ana maida kayan an rasa zannuwa uku a ciki"







Asiya juyawa tayi ta bar musu ɗakin dan ba zata juri ganin kayan takaicin nan ba. Ubayd ya kammala haɗa kayanta kawowa ne kawai ba ayi ba. Akwatuna biyar ne kuma ta riga ta san minene a ciki saboda fiye da rabin kayan kuɗi ya bata ta siya, wasu kuma sukan je siya tare. Lefen da Ubayd ya haɗa shi take so, ba wannan kayan ƙaryar ba.






Fita tayi daga gidan gaba ɗay ta wuce shagonsu. Tana cikin keke text ɗin Umma ya shigo, ta maida mata amsa da cewa shago zata je.












Saura kwana huɗu ɗaurin aure sai ga text ɗin Ubayd a wayarta, yace ta zo ta sameshi a office ɗinsa da ƙarfe biyar na yamma. Ƙarfe uku text ɗin ya shigo, dan haka tana sallar La'asar ta ce da Umma zata fita, Umma tace ba inda za ta je. Hakan ya sa ta mata ƙarya akan gidansu Queen Bee za su je karɓan saƙo ita da Sumayya. Umma tace su je amma lallai su dawo kafin ƙarfe shida na yamma.










***






"Daddy da gaske aure zaka ƙara?" Nana tayi magana tana tsare mahaifinta da idanu.






Gwamna yai shiru bai ce komai ba.






"Ka bata amsa mana Mijin 'yar Kurma"






Gwamna ya maida dubansa ga Hansa'u da ke bawa Junior abinci a baki yace "Kada ki sake bashi abinci a baki. Kada wanda ya sake bashi abinci a baki"






"Tuba nake ranka ya daɗe" Hansa'u ta faɗa tana ajiye cokalin da ke hannunta






"Kar ka saukar da fushinka akan ɗana. Kai ka sawa kanka auren jikar maiƙusumbi" Nana da Zunnairah suka fara dariya ƙasa-ƙasa.






Ko kallon Bilkisu bai yi ba ya miƙe ya bar dining room ɗin. A irin wannan ranaku da yake samun daman zama da iyalinsa ba abinda yake so sama da soyayyarsu. Sai dai yanzu kam Bilkisu ta gaza bashi wannan soyayyar. Dolene ya takawa Bilkisu birki. Juniour ba yaro bane da sai an bashi abinci a baki. Nana ta yi girman da bai kamata ta masa magana karangatsau haka ba, sai dai koma minene shi ya jawo wa kansa.






A ƙaramin falo Bilkisu ta zauna ita da babbar ƙawarta Madam Bintu suna tattaunawa kan kasuwancinsu. Bayan Hansa'u ta kawo musu abin taɓawa sai kawai suka ga ta zauna a tsakiyar falon ta ƙurawa TV ido.






"Hansa'u lafiya? Baki da aikin yi ne?"






"Shirin su Aarti da Yash zan kalla"






"A duk faɗin gidan nan sai a nan zaki yi kallo. Tashi maza ki bani waje" Bilkisu ta daka mata tsawa.






"Kema dai Bilkisu miyasa zaki kawota nan. A chan gidanku ma tana shirme balle a nan"






"Akwai ƙauyanci a tattare da ita amma ta iya aiki ne Bintu. Kuma gaskiya ban sake da ma'aikatan gidan nan ba duba da cewa sun yiwa Sha'awanatu aiki a baya. In fact, chief cook ɗin ma sai dana sa aka chanja shi"






"Wai baza ki tashin bane?"


Hansa'u ta miƙe tana susa kai ta bar wajen.






***






Da sauri-sauri take tafiya zuciyarta na tsalle a cikin ƙirjinta. Ita kaɗai ta san ya take ji a ranta.


Tana son shi, tana fushi da shi, tana kuma tausayinshi.






Sai da ta ja dogon numfashi kafin ta buɗe ƙofar office

15 / 21