Author : Azizat Hamza Category : Top Hausa Novels 2025
suka tafi chan kudu leburanci shikenan ya lalace da shaye-shaye. Baya bin mata, dan akoda yaushe addu'ar Gwani Allah ya raba shi da sata da kuma zina.
A shekarar da Gwani ya rasu a shekaran ya dawo gida. Bai dawo da komai ba saboda komai ya tafi a shan abubuwan maye.
Ale ya masa aure ya buɗe masa shago ko zai nitsu amma inaa. Kafin wata shida komai ya ƙare a shagon, ita kuwa Amarya shekara ɗaya tayi da 'yan kwanaki iyayenta suka sa ya saketa saboda tunda aka kawota ko hannunta bai taɓa riƙewa ba.
Ale ya kaishi wajen wani abokinsa mai maganin gargajiya a duba shi ko bashida lafiya ne, amma akace lafiyarsa lau.
Ƙannensa maza biyu sun yi aure harda 'ya'ya, sannan suma kasuwancinsu ya fara bunƙasa tun lokacin da Ale ya yaye su daga kasuwancinsa, amma Yaya Bello kam sai zaman daba...
***
Asiya na aiki a laptop ɗinta Sumayya ta shigo ɗakin da sallama.
"Kai Anty na gaji" ta ajiye jaka ta faɗa kan gado
"Tun yanzu? Shekara huɗu zaki yi, idan kuma aka shiga yajin aiki ƙila kiyi biyar ko shida"
"Kai! Allah ya sawwaƙa"
"Welcome to the game sister, haka muma muka yita cika bakin nan, daga ƙarshe sai da muka ƙara wata biyar akan shekaru huɗun daya kamata muyi"
"Anty kin san me, wata a ajinmu tace tana son ƙawance dani, ta nuna min hoton da mukayi a wajen dinner ashe nima na zama celebrity"
"Ban yadda ba"
"Iye?"
"Ban yadda da ƙawancen nan ba. Duk wacce za ta shiga jikinki saboda ke ƙanwar Matar Gwamna ce ba ƙawa ce da zata ɗore ba. Sannan ina so ki sani cewa matsayina na Matar Gwamna na lokaci kaɗan ne"
Sumayya tayi saurin miƙewa zaune.
"Anty dan Allah kada kice min za ki bar gidan nan. Kwana biyu dana yi a gidan nan ban taɓa gani kin shiga sashen Gwamna ba, idan ya dawo ko..."
"Bana son gulma. Kada ki bari wani matsayi ya ruɗe ki dan ba mai ɗorewa bane"
Sumayya ta riƙe baƙi tana kallon Asiya da hankalinta ke kan abinda take ta rubutawa a laptop ɗinta.
Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, Sumayya ta je ta buɗe.
Da ta dawo ta miƙawa Asiya wani envelop tace Uwani ce ta kawo.
Asiya ta karɓi envelop ɗin ta yaga ta fito da wasiƙar ciki.
"Shegiyar mata wai office of the first lady, ko uban wa ya bata office oho"
"Anty minene?"
"Bilkisu Kachallah ke gayyatata taron gajiyayyu da naƙasassu da za ayi gobe Asabat a foundation ɗinta"
"Anty zaki je?"
"Idan ban je ba ai ta ci nasara a kaina"...
Tunda aka kawota bata taɓa fita ba, a ranan da ta yiwa Yaya Bello maganan zama Direbanta washegari ya niƙo garinsa ya taho.
Kiran Yaya Bello tayi a waya tace masa gobe za su fita za ta aiko Sumayya da key ɗin mota ya duba lafiyar motar.
Washegari kuwa ƙarfe shaɗaya Asiya da Sumayya suka wuce wajen taro.
Lokacin da suka je an tanada mata waje na musamman kusa da Bilkisu Kachallah. Tana zama Bilkisu tace "ƙarfe goma aka fara taro, nan gaba ki duba agogonki da kyau"
"Ohh sorry! Kin san yau Excellency zai bar gidana, dole na kimtsa shi kafin na fito. Kin san ai yana jimawa a banɗaki idan zai yi wanka, da muka shiga tare kuwa na yi ƙoƙarin na dirzashi da kyau amma dana taɓa shi sai jikinsa ya ɗau mazari..."
"Shut up!" Bilkisu ta faɗa a fusace, bata san ma maganar ta fito da ƙarfi ba sai da ta ga wanda suke kusa da su na kallonta. Sai ta bige da kama hannun Asiya tana dariya kamar irin wasan nan take. Asiya ta yi murmushin nasara, yau duk ta inda Bilkisu Kachallah za ta fito tana nan dai dai da ita.
Kiran Bilkisu Kachallah da aka yi ta zo tayi bayani nan take naƙasassun wajen suka fara tafi suna kiran sunanta.
Ko da za su shigo hall ɗin abin daya fara ba wa Asiya haushi shine UWAR MARAYU da aka rubuta a saman hoton Bilkisu Kachallah. Bilkisu ba ta yi kama da macen da za ta so talaka ba balle maraya amma da sannu za ta karya mata fiffiken da take furkawa da shi.
Maganan minti shabiyar tayi sannan ta ce zata kira 'yaruwa, ƙanwa, kuma abokiyar zamanta ta zo ta faɗi abu ɗaya ko biyu a wajen duba da cewa ita ɗin ma ta fito daga tsatson naƙasassu.
Asiya ta cizi leɓenta lokacin da Bilkisu Kachallah ta kirata da 'yar Kurma jikar maiƙusumbi.
" Hajiya Asiya Kachallah" MC ɗin wata mata wacce bleaching ya gama koɗar mata da fiska ta sake kiran Asiya a karo na biyu bayan Bilkisu ta koma ta zauna.
Dai dai zata tashi taji Bilkisu tace "maza aje a gaya musu yadda ake kula da naƙasassu"
Sallama Asiya tayi lokacin data karɓi mic a hannun MC. Jin an amsa ƙasa-ƙasa ya sa ta ƙara maimaita sallamar da muryarta mai kaifi, wannan karan suka amsa da ƙarfinsu.
"Barin baku wasu labarai masu daaaaɗiiiii" ta ja ƙarshen maganar tana juya hannunta. Nan da nan aka saka dariya
"Akwai wani yaro da aka haifeshi da ƙusumbi shekaru tamanin da biyar da suka wuce. Aka damƙa shi wajen wani malami dan yai karatu tun yana shekara shida haka. Wannan yaro yai karatu sosai a wajen Malaminsa dama wasu Malaman daban. Yai aure Allah ya azurta shi da 'ya'ya uku Maza. Wannan yaro mai ƙusumbi ɗinkin hula yake yana ciyar da iyalinsa da gumin hannunsa har Allah ya ɗau ransa. Sai dai kun san me? Kafin ya rasu yayi karatun ƙur'ani, ya ji haddan Ƙur'ani har mutane su ka rinƙa kiransa da Gwani. Wasu daga cikin ɗalibansa sun ce kafin Gwani ya rasu ya rubuta ƙur'ani daga farko har ƙarshe da ka sau ashirin da ɗaya wasu ma su kance sau talatin ne. Lokacin da Gwani ke ciwon ajali kafin a bashi abinci ya ci sai ya yi ƙoƙari ya rubuta ayoyin ƙur'ani a Allonsa kafin ya ɗanɗani abincin. Har ya koma ga Allah bai taɓa roƙo ba, bai taɓa zuwa maula wajen Attajirai ba.
"Akwai wata mace dana sani da aka haifa da lalurar kurmanta, aka mata aure, suka rabu da mijinta da 'ya ɗaya tsakaninsu. Wannan mata ta sake aure mijinta ya taimaka mata ta fara karatun yaƙi da jahilci. Ta koyi sana'ar ɗinki da saƙa, yanzu haka matar nan Allah ya rufa mata asiri tana ɗinki tana kuma saida kayan sanyi irinsu, Zoɓo, kunun Aya da sauransu.
"Akwai wani gurgu a ƙasan layinmu kullum idan zan wuce Islamiyya yana zaune a ƙofar gidansa yana gyaran takalmi , da Allah ya yassara masa har takalma ya saro na maza da mata yana saidawa, duka a ƙofar gidansa.
"Lokacin da nake bautar ƙasa a wani gidan talabijin akwai wata mata makauniya wacce ke gabatar da shiri na musamman dan wayae da kan al'umma akan mahimmancin ilimi wa naƙasassu. Inaga za ku tuna da Dr Hajiya Laraba Bakatsine wacce ta rasu farkon shekaran nan, ga wanda basu sani ba degree uku ta yi kuma duka da lalurar makanta.
"Abu na ƙarshe da zan faɗa shine, naƙasa ba lasisi bane na yin barace-barace ko maula. Ina so ku sani Naƙasassu na da damar yin kasuwanci ko sana'a, sannan su nemi ilimi kamar kowa. Ina fata Gwamnati za ta bawa naƙasassu damar yin kasuwanci d neman ilimi kamar kowa. Mu tashi lafiya"
Kafin ta kai kujerarta wani gurgu ya turo kekensa ya sha gabanta, idonsa fal da hawaye ya haɗe hannunsa biyu ya fara mata godiya, kan kace me, naƙasassu sun yanyameta suna mata godiya. Maganganunta sun taɓa naƙasassu da dama a wajen, wanda zuciyarsu ta kafe kuwa, sun sawa ransu cewa bara sana'a ce kuma ko me za a musu sai sun je Kudu sun yi sana'ar su.
Yadda ka san sassaƙa Bilkisu akayi haka ta daskare akan kujera ta kasa motsawa. Ba ta hango wannan ba, ba haka ta shirya ba. Da ƙyar ta iya tashi lokacin da aka kirata ta zo ta rufe taro da addu'a. Asiya ta yi murmushi lokacin da taji Bilkisu tace ayi salati wa Annabi amma ba ta buɗe baki anji salatin ba, sai ta rufe ido tana muimui da baki kaman Akuya na cin ciyawa...
***
A wani ƙaramin ɗaki kuma wata mace ce sanye da riga da zani da ɗankwali dukkansu daban-daban. Kallo ɗaya zaka mata ka kirata 'yar ƙauye, sai dai yanzu da take gaban wata na'ura tana magana da harshen faransanci dole ka kirata gogaggiyar 'yar boko, yadda take magana da harshen ka ce a birnin Paris aka haife ta.
Cikin bayaninta take bayyana cewa har yanzu bata samu ƙwaƙwƙwaran hujjar da take nema ba, amma kuma tanada yaƙinin za ta samu nan bada jimawa ba. Babu tantama matar da take bincike akanta tana kasuwancin miyagun ƙwayoyi, amma saboda matsayinta ba za a kamata ba sai da hujja mai ƙarfi. Hujjar take nema sama da shekara ɗaya da take aiki da ita.
"Ba matsalata Bilkisu Kachallah ba, matsalata Madam Bintu ce ka sani. Dan haka ba ruwana da matar da Gwamna ya aura, that's his business"
Mutumin da take magana da shi yace "akwai jami'ar DEA da zata zo daga America kan batun safarar miyagun ƙwayoyi, idan ta iso zan haɗaki da ita. Agent Dahlia tanada interest sosai akan case ɗin nan, kuma na san za ta taimaka sosai"
"Yes Sir" daga haka ta rufe na'urar ta ɓoye shi a ma'ajiyarsa...
"Hansa'u...Hansa'u...Hansa'u"
Masu aiki uku ne a gaban Bilkisu Kachallah amma ba su take nema ba. Hansa'u ta iso da gudu tana faɗin "Hajjaju nah ki gafarceni, sallah nake"
Bilkisu ta ce " Sallan Uwarki, matso nan" Hansa'u ta matsa kusa da ita kafin ta gama matsawa ma Bilkisu ta ɗauketa da mari tana faɗin " dan Ubanki kashe min ɗa zaki yi? "
"Hajiya wane Ubana" Hansa'u tayi maganar tana sosa kumatu
"Uban me ya hana ki sawa junior inhaler a aljihunsa?"
Ta sani lokacin data shirya Junior ta saka masa inhaler a aljihun wandonsa sai dai in cirewa yai, amma a yadda Bilkisu Kachallah ke tiriri ba zata saurari bayaninta ba sai dai kawai ta bada haƙuri.
"Tuba nake Hajjaju, mantawa nayi"
Bilkisu ta sake kai mata duka tana faɗin "idan haka ya sake faruwa sai na yanka ki a gidan nan"
Abu biyu ne ya haɗuwa Bilkisu, na farko ta ƙumso baƙin ciƙin Asiya, na biyu kuma ta shigo falo ta samu ɗanta na kokawa da numfashi babu kowa kusa da shi. Saboda mijinta da ɗanta na da lalurar Asthma ba a rasa inhaler a jakarta. Hakan ya sa ta ciro ta jakarta ta matsa masa a baki.
Hansa'un dai aka saka ta goyi Junior ta wuce da shi ɗaki.
Da dare da Gwamna ya dawo gidan Gwamnati saboda kwanan Bilkisu ne. Bilkisu ta same shi ta fara sauke masa fushinta.
"Saifuddeen sati ɗaya da zuwanta amma har ka fara nuna banbanci. Ta ya zaka siya mata sabon mota bayan akwai mota a gidan da za ta yi amfani da shi.
I thought you said you married her for political reason, miyasa kake wanka tare da ita? Have you slept with her?"
Gwamna ya fara rage kayan jikinsa ya manta da ita a ɗakin. A gajiye yake baya son abinda zai ɗaga masa hankali.
"Saifuddeen ka gaya min gaskiya, ka..."
"Wanda suka kawo miki gulmar za ki tambaya bani ba"
"Ita da bakinta ta faɗa min yau kun yi wanka tare"
Har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa yai murmushi ya wuce banɗaki. Kafin ya kulle ƙofa Bilkisu ta faɗo ciki tana faɗin da ita zai yi wanka.
Lokacin da Sakatare ya nuna masa video na abinda ya faru a wajen taron da Bilkisu ta shirya ya jinjinawa Asiya saboda tarko Bilkisu ta ɗana mata lokacin da ta kirata da 'yar Kurma jikar maiƙusumbi. Ya sani ta so Asiya ta harzuƙa ne ta faɗi baƙaƙen maganganu a wajen ko ma ta zagi Bilkisun da wani abu, sai kuma Asiya ta nuna mata cewa ita ɗin 'yar jarida ce.
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
16
Asiya da Sumayya na cin abincin dare Sha'awanatu Bacchi ta kirata. Jinjina ta mata kan abinda ya faru a wajen taro, ta bata shawaran kada ta taɓa bari Bilkisu Kachallah ta taka ta sannan idan tana son samun matsayi sama da Bilkisu dole ne ta koma gidan Gwamnati. Asiya ta mata godiya ta ajiye wayar tana murmushi.
"Anty Ale ya kira wayarki ɗazu da kika shiga banɗaki"
"Kin ɗauka?"
"A'a"
"Good"
"Anty, har yanzu fishi kike da shi?"
Asiya ta ajiye cokalin hannunta tace "taya ba zan yi fushi ba Sumy. Bayan kuɗin da Mutumin nan yake da shi, bayan kuɗin daya karɓa a wajen 'yanuwan Gwamna, kwanana huɗu da aure ya kirani yana cewa na nema masa kwangila a wajen Gwamna. Wani uban ƙwarai zai yiwa 'yarsa haka. Dan ba a chanja Uba ne da tuni na chanja shi"
Sumayya ta sa dariya.
Basu gama cin abincin ba Nana ta kira Asiya. Ko a ina ta samu numbarta oho.
"Antyna ina gayyatarki birthday na da za'ayi ranan Friday. Dan Allah ki zo"
"Wai ni yarinyar nan mi kika ɗaukeni ne?"
"Please Sweet Anty"
Asiya ta yi shiru na 'yan sakanni kafin ta ce "zan zo"
Tana ajiye wayar tace "inaga Gwamna mahaukata ya ajiye a gidansa"
Sumayya ta kwashe da dariya ta ce "Anty ai harda ke"
"Zan saɓa miki Sumy. Ni sa'ar ki ce"
"Anty ke fa kika faɗa da bakinki"
"Da matarsa da 'yarsa duk basu da kai, ranan da ta zo nan kinga yadda take girgiza kai kaman notinan kanta sun kunce, ni cewa ma nayi kan roba gareta"
"Kai! Anty"
Asiya ta sa dariya.
***
"Babu birthday wannan karan. In fact har na bar kujeran nan babu birthday, babu anniversary, babu wani celebration da za ayi sai dai biki ko suna"
"Wasa kake Saifuddeen. Mun yiwa Junior nashi farkon shekara ita kuna Nana sai kace ba za a mata ba. Ina ruwana da abinda mutane za su faɗa. Mu fa ba matsiyata bane, babu abinda muka rasa kafin ka hau kujeran nan dan haka dole ne mu kashe kuɗi wajen taya first born ɗinmu murnan cika shekara shabiyar a duniya"
" lokacin da Mahira tace ba ta son birthday ta gudu wajen Dadda, wani abu ya sameta da ranan ya zo ya wuce ba tareda anyi komai ba"
"Darling Mahira daban Nana daban"
"Dukkansu 'ya'yana ne Bilkisu. Kuma yadda ba ayi na Mahira wannan shekaran ba, ba za ayi na Nana ba"
Bilkisu ta matso kusa da shi, ta riƙe hannunsa tana murzawa a hankali, ta sassauta murya tace " na san baka son abinda zai jawo maka magana a gari, nima bana son haka. Ka yi haƙuri muyi mata small get together birthday party, acikin gidan nan, daga ƙawayenta sai 'yanuwa. I promise babu, 'yan jarida da za su zo. Na yarda Mahira ba ai mata birthday ba wannan shekaran, amma kasan itace tace bata so, Nana kuma tana so. Ba kuɗin Gwamnati zamu yi amfani da shi ba ka sani. Na maka alkawarin ni zan ɗau nauyin komai daga aljihuna"
"Still dai..."
Shhhh ta faɗa tana rufe masa baki da yatsunta biyu. Ta sani an gama kenan, Saifuddeen mijinta bai iya dogon jayayya ba...
Ranan Alhamis Gwamna Saifuddeen Kachallah ya wuce Birnin tarayya wani taro da za su yi na Gwamnonin Arewa.
Ranan Jummu'a kuwa Bilkisu Kachallah ta shiryawa 'yarta bikin birthday.
Babu taro sosai saboda taron strictly na wanda aka gayyata ne.
Ana tsakiyar taro Asiya ta zo, Nana na ganinta lokacin za ta yanka cake ta je da gudu ta rungumeta. Bilkisu Kachallah ta hangame baki tana mamakin 'yarta.
Asiya ta karɓi ɗan ƙaramin akwatin gift da ke hannun Sumayya ta miƙawa Nana ta ce "Happy birthday"
Nana ta sake rungumeta tana faɗin "thank you, thank you"
An ci, an sha, an bada kuma an karɓi kyaututtuka. Ana daf da za a rufe taro Asiya ta tafi.
Da Asiya ta dawo gida, dare ta bi tana tsara labari a laptop ɗinta, da ta gama ta turawa Mr Bassey tareda hotunan data ɗauka.
Washegari jaridar Climax ta fito da labarin birthday ɗin 'yar Gwamna. Hoton Nana sanye da wata matsatstsiyar doguwar riga kanta babu ɗankwali shine a shafin farko na jaridar, an rubuta *Gwamna Saifuddeen Kachallah ya zubar da miliyoyi wajen yiwa 'yarsa birthday*
A ƙasan labarin kuwa irin ɓarnar kuɗi da akayi aka lissafo, tun daga decoration, abinci, cake, souvenirs dama kayan da Nana da Bilkisu Kachallah suka dinga chanjawa a wajen, duk an bayyana. Daga ƙarshe aka ƙiyasta jimillar kuɗin da aka kashe zasu kai miliyan arba'in.
Lokacin da Bilkisu Kachallah ta ga jaridar Climax cilli tayi da wig ɗin kanta tana faɗin koma waye yai rubutun nan sai ta sa an ɗaure shi. Ta kira wani numba tana faɗin a nemo mata wanene ke da jaridar Climax, sannan tana son sannanin ɗan jaridar daya yai rubutun nan.
Duk wanda suka zo bikin sai da aka karɓi wayoyinsu saboda ba a son ɗaukan hoto. Mai hoto ɗaya ne ta yadda ya ɗau hotuna a wajen, cousin ɗin Nana ne ɗan Anty Rufaidah, babu yadda za ayi ya siyar da hotunan Nana wa 'yan jarida. Koma waye ya fitar da hotunan nan sai ta sa an hukunta shi.
Gwamna Saifuddeen na ɗakin hotel da suka sauka Chief of Staff ya nuna masa jaridar Climax a wayarsa.
Gwamna ya haɗiyi yawu da ƙyar. Ba abinda aka rubuta ne ya dameshi ba sai ganin duk cikin hotunan Nana da aka ɗaura babu wanda tayi shiga na mutunci aciki. Ya cizi leɓensa na ƙasa yana inama Nana a wajen Dadda ta taso kamar yadda Mahira ta taso a wajenta, ƙila da duk wannan ba zai faru ba. Da farko Bilkisu ya ɗaurawa laifi daga baya kuma ya gane cewa shine silar komai, ya barwa Bilkisu ragaman tarbiyyan 'ya'yansa bayan ya san irin tarbiyar da itama ta taso a kai.
"Wa ye keda jaridar Climax?"
Ya tambayi COS bayan wasu mintoci daya ɗauka bai yi magana ba.
"Da dai wani ne Mr Emmanuel Bassey amma na ji ance wani ɗan siyasa ya siyi jaridar watanni biyu da suka wuce"
"Ka bincika min waya siya"
"An gama excellency"
***
Asiya kuwa tsaf ta shirya dan fara aiki da investigative reporter mai suna Fou'ad Salisu. Shekaransa uku da fara aiki amma ya fitar da manya-manyan report guda biyu da ya ɗaukaka shi a ƙasar da ma duniya baki ɗaya.
Fou'ad