THE GOVERNOR'S-MATAR GWAMNA --Document Complete .txt

Author :  Azizat Hamza Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   11 / 21

30K to 33K   out of 62.2K words

Malam ya tura shi Borno wajen wani Babban Malami. Bai dawo ba sai da yai shekaru huɗu a chan. A sanda ya dawo ne kuwa ya tarar da Malam ya aura masa wata 'yarsa.











Rumaysa'u wacce aka fi kira da Tabawa ita ce auta cikin 'ya'yan Malam. Ita ce kuma Allah ya jarrabce shi da ita.


Saɓanin sauran yayyanta da su ka yi karatu sosai har su ka yi sauka tun ma kafin ya aurar da su ita fir ta ƙi karatun.


Bayan nan, ƙiriniya da yawace-yawace da ta tsirfata da tara samari ya sa ya ce zai haɗata aure da wani Almajirin sa. Tabawa ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba za ta auri Almajiri ba. Yayi yayi da ita ta ce ba za ta aure shi ba. Ƙarshe ma ta kai ƙarar sa wajen Maigari.







Malam ya haƙura ya aura ma ta wanda ta kawo ta ce tana so. Da ke babu albarkan iyaye auren dudu wata biyar su ka yi ya rabu ta dawo gida ta fara zawarci. Kafin kace me sunan Tabawan Malam ya sake zama tamkar waƙa a wajen samari da bazawarai.


Lokacin da Malam ya ce ta fito da miji sai ta nuna Chukudi a matsayin wanda ta ke so. Kasuwanci ya kawo Chukudi garin, ɗan kuɗin da ya ke kashewa Tabawa shine ya tsole ma ta ido har ta zaɓeshi a matsayin wanda za ta aura, duk da addinin su ba ɗaya ba, al'adar su ba ɗaya ba, uwa uba ba asan minene asalin sa ba.






Wannan karan da Malam ya hanata auren sai wayan gari aka yi aka ga ta gudu daga gidan. Ita da Chukudi aka neme su a gari aka rasa. Wannan cin mutuncin har kwantar da Malam yai, kamar ma ba zai tashi ba sai kuma bayan ya sha jinyar watanni sai gashi ya samu sauƙi amma baƙin cikin da Tabawa ta ƙunsa ma sa yana nan yana cinsa, kullum addu'ar sa gareta Allah ya shiryar da ita. Ya sha tsayuwar dare akan lamarinta sai dai ita ɗin wata jarrabawa ce da Allah ya ma sa.







Shekara ɗaya da rabi kafin Tabawa ta dawo gida. Ranan da ta dawo mutanen gidan da ƙyar su ka ganeta saboda lalacewa da ta yi. Bayan ta bi Chukudi zuwa ƙauyen su ashe niyyansa shine ya tsafeta yai kuɗi da ita. Da ƙyar Allah ya kuɓutar da ita daga kaidinsa, sai dai tunda ta bar ƙauyen ta rasa gane kanta. Ta jima tana garari kafin ta samu ta warke ta dawo wajen Babanta dan ta san nan ne kawai gatan ta.


Malam ya karɓeta ne da sharaɗi guda, za ta zauna tsakani da Allah da duk wanda ya aura ma ta. Kaman da gaske ta ce ta amince.


A take ya ɗaura ma ta aure da Lukman ya kuma tura wasiƙa akan Lukman ya dawo gida idan Malaminsa ya sallameshi. Bai samu dawowa ba sai bayan wata uku.







Kafin ya dawo Malam ya gyara ma sa ɗakuna biyu cikin gidansa inda anan za su zauna da Tabawa.






Lokacin da Malam ya sanar da Lukman maganar auren da yai masa ya sha mamaki sosai. Ya san halin Tabawa sarai kuma duk abinda ke faruwa babu wanda ba shi da masaniya akai. Ba wai ba zai karɓi zaɓin Malam ba ne amma yana tunanin anya kuwa Tabawa za ta zauna da shi?






Tsoronsa kuwa ya tabbata domin lokacin da Malam ya haɗa su zai mu su nasiha Tabawa ta ƙeƙasa ƙasa akan ba za ta auri Mai ƙusumbi ba. Ita duk zaman nan ta ɗauka ɗaya daga cikin manyan Almajiran Malam aka aura mata, bata san Lukman Maiƙusumbi ba ne.







"Baba ba zan zauna da Maiƙusumbi, Miskini, marar asali ba. Duk cikin Almajiranka ba wanda ba sa zuwa wajen 'yan uwan su lokaci zuwa lokaci amma wannan bai taɓa zuwa wajen na shi ba. Ƙila ma ɗan shege ne"






"Rumaysa'u!"







"Baba zan auri kowa amma banda shi Wallahi"






"Na fi ƙarfin Miskini" ta ƙara jadda masa kafin ta fice daga ɗakin Malam ɗin.







Duk ƙoƙarin da Lukman ya ke akan kada yai hawaye agaban Malam sai da hawaye su ka zubo ma sa.



Dai-dai yana gogewa da gefen hannun rigansa Malam ya ce "Lukman ka tashi ka je za a kawo maka ita yanzu"














"Malam ka yi haƙuri Dan Allah, tunda ba ta so a bari na sawwwaƙa ma ta"






Ran Malam cike da ƙuna ya ce " ka san Allah idan har Rumaysa'u ba ta karɓi auren ka ba sai na tsine mata"






Lukman ya zaro ido waje.






"Kai ne aka cuta da na haɗaka aure da mace kamar Rumaysa'u, na yi haka ne dan ko Allah zai shiryar min da ita ta hanyar ka"










A chan cikin gida kuwa Tabawa ta dinga faɗa wai a rasa wanda za a aura ma ta sai Maiƙusumbi. Wata Gwoggon ta da ke gidan ta fito ta dinga surfa mata masifa.


Yadda ta dinga kiranta da butulu shiyasa jikinta yai sanyi.


Duk da tarin laifuffukanta itakam ta ƙwammace ta zauna ba aure da ta auri Lukman Maiƙusumbi. Kusan shekaru biyu kawai Lukman ya ba ta. Tun suna yara ta tsaneshi. Yadda Malam ya ja shi a jiki ya maida shi ɗansa na dole ba ƙaramin ɓata ma ta rai ya ke yi ba.










Bayan Gwoggo ta ƙare mata faɗan ita da Kulu yayar Tabawan suka tarkaɗata zuwa sashen da aka gyarawa Lukman. Tabawa ta sa a ranta zata zauna ne zuwa abubuwa su lafa, nan da lokaci kaɗan za ta rabu da shi ko da ta ƙarfi ne.






Har ta fara bacci Lukman ya shigo ɗakin jikin sa a sanyaye. Umurnin Malam na ƙarshe kafin ya taho ne ya dagula ma sa lissafi.






"Wallahi idan har ba ka tare da matarka daren yau ba. Ban yafe karatun da na koya maka ba"






A gigice ya bar wajen saboda bai ga alaman wasa a wajen Malam ɗin ba.






Da lallami ya nemi Tabawa amma ta ƙi bashi haɗin kai wannan ya sa shi binta da ƙarfi ya karɓi haƙƙin sa. Ya sha tsinuwa a wajen Tabawa kam kafin ya gama saboda da farko ta rena ma sa kan cewa za ta iya ƙwatan kanta a wajen sa. Ƙaramin ruwa gareshi shiyasa ta ke ma sa kallon ƙashi da rai ba ta san yadda ya ke a bushe haka ya ke da ƙarfi ba.






Tun daga ranan kuwa ba abinda ya sake shiga tsakanin su. Iya kyautatawa yana yi ma ta amma itakam kullum cikin zagi da tsinuwar sa ta ke, tareda cewa ya saketa indai shi ɗan halak ne.






Awata na biyu da auren ta gane ciki gareta. Ta yi kukan baƙin ciki sosai dan haɗa iri da Lukman mugun abu ne a wajenta.






Wasu ƙulle-ƙullen magani ta nema ta sha wai dan cikin ya fita. Ba ta jima da shan maganin ba ta cika gidan da ihu. Iyaji Mahaifiyarta ta zo ta sameta cikin jini.


Kwanan ta uku a Asibiti kafin aka sallameta. Sai da su ka dawo gidan ne ma Iyaji ta tabbatar ma ta da cewa cikin jikinta na nan.






Ta sake shiga damuwa dan da ƙarfi ba ta son abin cikin ta.


Ƙarshe Sheɗan ya kaɗa mata kai ta aiwatar da abinda ya zo ya rabata da Mahaifinta har abada.






Guba ta zubawa Lukman a abinci akan idan ya ci ya mutu sai ta yi takabar sa ta huta da auren baƙin ciki.






Lukman ya zo ya fara cin abincin kenan ko loma biyar bai yi ba wani jikan gidan ya leƙo akan ya je Malam na kiran sa. Ya wanke hannu ya fita.






Yana wajen Malam suna magana cikin sa ya fara murɗawa tun yana daurewa har ya riƙe cikin yana murƙususu a ƙasa. Malam ya ɗauke shi aka yi Asibiti da shi bayan ya bashi zumar daya tofa ayoyin shifa a ciki. A chan ne aka ce mu su maganin ɓera ya ci.






Ko tantama Malam bai yi ba ya sawa ransa Tabawa ce da wannan aikin. Sawa yai a kira ma sa ita. Lokacin da ta zo yana tare da Lukman da ke zaune gefen sa yayi wani fayau da shi saboda a yau ɗin ne aka sallameshi daga Asibiti.






Ko gaisuwarta Malam bai amsa ba ya umurci Lukman ya saketa. Takardar da Malam ya miƙo ma sa ya karɓa hannunsa na rawa.






"Ka rubuta ma ta saki na ce" ya sake maimaita ma sa da ɗan karfi.






Alƙalamin da ke gefen Malam ya ɗauka ya rubuta wa Rumaysa'u saki ɗaya da rubutun Ajami.






Yana rubutun Tabawa na murmushi.


Malam ya dubeta ya ce "Bayan Lukman bana tunanin za ki samu wani namijin ƙware da zai sake neman auren ki Rumaysa'u".






Magana ce ya mata amma kasancewarsa Uba gareta sai abin ya zame mata baki.






Abin mamaki ko Wata ba'ayi ba da rabuwar su Malam ya aurawa Lukman 'yar uwarta wadda su ke 'ya'yan Baffanu (cousins).






Indo budurwace mai ƙarancin shekaru amma ta yi biyayya ga zaɓin Malam ta zauna da Lukman tsakani da Allah.






Cikin Tabawa na wata takwas Malam ya rasu mutuwar da ya girgiza su sosai.


Sati uku da rasuwan ta haifi ɗa namiji. Sunan Baba ta so sakawa amma saboda jinin Lukman ne sai ta ƙyamaci hakan. Da kanta ta samu Lukman akan sunan ɗanta Faruƙu. Ranan suna kuwa bai chanja ɗin ba aka sawa yaro Faruƙ.










Tunaninta ta rabu da auren Lukman za ta buɗe da wani auren mai kyau sai kuma duniya ta juya mata baya.






Halayyar ta na baya su suka bayyana wa kowa da ke son zuwa aurenta.


Tabawa ce dai da ta gudu da wani Arne na kusan shekaru uku. Tabawa ce dai da ta kai ƙaran mahaifinta wajen Maigari, Tabawa ce dai... Tabawa ce dai...










Tun tana zaune ba ta komai, da abubuwa su ka fara kwaɓe ma ta ɗan sauran kuɗin da ta samu na gadon Malam ta fara sana'ar tuyar ƙosai. Wasa-wasa sai da Faruƙ ya shekara shida kafin ta samu miji ta yi aure. Aure ta yi amma ɗan ƙaran wahala take sha a cikinsa ko da wasa Ƙaura Mafarauci bai ɗauketa da daraja ba. Tana zaune da matan sa biyu amma duk ciki ta fi su wahala. Bayan duka da ya ke mata da har ya zame mata jiki 'yan kuɗaɗen sana'arta duk shi ya ke karɓa ya sha giya da su. Ƙarshe jari ya ƙare. Ta yi zagin ta yi faɗan duk dan ya saketa amma ya ƙi.


Ga shi shekaru bakwai tare amma ko ɓari ba ta taɓa yi ba, shiyasa ma ta kasa miƙawa Gwani Lukman ɗansa Faruƙ lokacin da ya buƙaci hakan. Duk yadda ba ta son Ubansa haka ta ɗaurawa Faruƙ tsananin so. A shekara ta tara da auren Ƙaura ya rasu. Ta yi farin ciki da mutuwar sa sosai. Tana ƙarisa takaba ta dawo gida lokacin ba wanda zai ganta ya ce zai waiwayeta saboda yadda ta tsofe ta lalace.






Bata yi niyyar sake Aure ba amma ganin Indo da Gwani Lukman suna zaune lafiya ya sa ta kasa zaman gidan nasu. Lukman shi ya gaji Malam, tun bayan rasuwan sa Makarantar Malam ba ta watse ba. Wani fili da ke gefen gidan Malam wanda tun Malam na raye ya ba shi kyauta ya samu ya fara ginawa, cikin shekaru biyu kuwa ya kammala shi da Indo su ka tare a gidan da yaransu guda biyu maza AbdulWahab da su ke kira da Malam sai Zakariyya da su ke cewa Zakari.






Cikin shekarun nan Allah ya ɗaukaka sunan Gwani Lukman Baba fiyeda ta Malam Falke. Babu wanda ke duba ƙusumbinsa sai tarin Ilimin da Allah ya bashi. Daga garuruwa daban daban ana zuwa ɗaukan karatu wajen sa. Tuni sunan sa ya koma Gwani Baba.






'Ya'yan sa Malam da Zakari kuwa sun zama abun kwatance cikin gari. Ga tarbiyya ga karatu.






Kukan Lukman kullum akan Faruƙ ne wanda Tabawa ta janye shi daga jikinsa. Tun yana yaro idan ya sa shi ya zo wajen sa karatu yake guduwa. Da ya fara masa duka sai ya dena zuwa kwata-kwata, Tabawa ta ɗaure ma sa gindi har da samun Lukman akan ya bar ma ta ɗa ba lallai ne sai ɗanta ya zama Malami kamar sa ba.






"Ba a chanjawa tuwo suna Ruma. Duk lokacin da ki ka kalli Faruƙ na san fiskata kike gani a tasa. Ki bani ɗana Allah ya taimakeni na ɗaura shi akan tarbiyya mai kyau"






Ruma ta ce ba ta san zance ba.


Lokacin da ta koma gida haka ta titsiye Faruƙ a gaba tana kallo wani abu na sukanta a zuciya.


Kallo ɗaya za ka yiwa Faruƙ ka san jinin Gwani Lukman ne. Idan ka cire ƙusumbi da bashi da shi komai na Gwani ya ɗauko, hatta da murmushi idan yai sai ka ɗauka Gwani ke yi.


Ta sani Lukman kyakyawane sosai, Ƙusumbin da ke bayansa da kuma ƙaramin jiki da Allah ya bashi shine kawai naƙasu da Allah ya mishi.






Bayan ta gama takaba da shekara ɗaya ta auri Saleh. Ganin Saleh babban mutum ne dan ya ɗara shekaru hamsin alokacin kuma shine sarkin noman Doka wani garin da ke maƙotaka da su ta yi tunanin samun lamuni a auren.


Da Faruƙ ta tare duk da kuwa alokacin yana kusan shekaru shashida a duniya ya ƙi karatun Arabi ya ki ta Boko. Ko Primary bai gama ba ya dena zuwa.






Ta ɗan samu zaman lafiya na ɗan wasu watanni kafin asalin halin Sarkin noma ya bayyana ma ta. A gidan Sarkin noma ne ta ƙwammaci tun asali da ba ta rabu da Lukman ba. Bayan munanan halinsa kuma ga uƙubar kishiyoyi. Lokacin da ta fara Sana'a tana ɗan samu abun rufawa kanta asiri ɗaya daga cikin kishoyinta ta je aka mata surkulle kasuwan ƙosai da ɗanwake da ta keyi ya lalace ga uwa uba ciwo da aka sa ma ta. Ko shekara Faruƙ bai yi da ita ba ya tafi Birni neman aiki, bai sake waiwayanta ba. Haka ta zauna cikin ƙunci ita kaɗai.






Dama tunda ta rabu da Lukman zumuncinta da 'yan uwanta ya yi rauni. Lokacin da ta koma Doka da zama da abubuwa ke mata daɗi ba wanda ta waiwaya a cikin su.










A shekara na uku da rashin Faruƙ wata rana da Adda Karime ta kawo ma ta ziyara. Ashe Allah yayiwa mahaifiyar su Iyaji rasuwa kusan wata biyar da su ka wuce ba ta sani ba. An aikawa Saleh lokacin mutuwar amma bai gaya ma ta ba.


Tabawa ta yi kuka sosai.


Lokacin da Adda Karime za ta tafi ta roƙeta da Allah akan ta faɗawa Gwani ya nemo ma ta Faruƙ tunda Karimen ta faɗa ma ta suma rabon su da Faruƙ ɗin tun bayan tarewar ta.










Addu'a sosai Gwani ya sa gaba akan Allah ya dawo ma sa da Faruƙ gida tunda Tabawan da ya ke tunanin yana wajenta ma tace ba ta san inda ya shiga ba.






Allah maji roƙon bawa a cikin wata na huɗu sai ga Faruƙ ya shigo gari. Idan ka ganshi ba za ka ce ɗan Malam kuma jikan Malami bane. Ya tara uban gashi yana sanye da wando na yayi wanda ta matse daga sama daga ƙasa kuma ta buɗe.






Cikin ikon Allah da Gwani yai ma sa maganar aure sai ya amince. Ɗan kuɗi da ya zo da shi da kuma abinda Malam ya haɗa mi shi da shi yai jari ya fara kasuwanci.






A hankali kuma Allah ya sa ma sa albarka a ciki, cikin lokaci kaɗan ya samu rumfar kan sa a kasuwa.






















***










A wani madaidaicin gida kuwa wata budurwa ce ke aikin wanke-wanke. Kwanukan yawa garesu, kuma yawancin su robobi ne madaidaita hakan zai sa ka kira su da kwanukan saida abinci.






Daga yadda budurwar ta duƙa tana wanke-wanken wani yaro wanda ba zai wuce shekaru goma ba ya ɗira ma ta dundu a baya. Budurwar ta juyo a zabure tana zare ido.






"Kurma ki je inji Mama" ya faɗa yana nuna mata dai dai barandar da ɗakuna uku su ke jere reras.






Maimakon ta ɓata rai da abinda ya mata sai ta masa murmushi. Ta goge hannunta ajikin zaninta ta wuce ɗakin Mama Asabe.






Tana ɗaga labulen ɗakin sai da ƙirjin Mama Asabe ya buga saboda ta ɗauka mijinta Malam ne. Ganin Kurma ce ya sa ta ɗan sauke ajiyar zuciya.


Cinikin da su ka yi da safe da kuma na rana ta ke irgawa.






"Yawwa Kurma zo ki je ki auno min shinkafar gobe wanda ya rage ba zai kai ba"


Ta ƙarisa maganar tana miƙa mata wani dunƙulen kuɗi da ta ajiye a gefe.


Bayan da Kurma ta karɓi kuɗin a hannunta ta cigaba da yi ma ta bayani da hannu ta yadda za ta gane. Tun tana shekara huɗu aka kawo mata ita kuma cikin shekaru goma ba abinda ba ta iya ba a yaren kurame.






Yadda ta jaddada ma ta cewa a rumfar Ale Faruƙ ta ke so ta siyo ma ta shinkafar hakan ya sa ta yi saurin zuwa ta ƙarisa wanke wanken da ta ke yi dan daga gidan su zuwa rumfar Ale Faruƙ aƙalla sai ta yi tafiyar minti shabiyar zuwa ishirin.










Lokacin da za ta fita daga gidan ne ta ci karo da Malam a zaure. Ta ɗan risina ta gaida shi kafin ta wuce.






Malam Sabo Yayan Mahaifinta ne. Bayan rasuwan mahaifiyarta lokacin tana watanni bakwai da haihuwa Mahaifinta Malam Inusa bai ƙara aure ba har Allah ya ɗauki ran sa shekaru uku bayan rasuwan matar sa. A wajen Inna Talatu Zainab kurma take tun rasuwan mahaifiyarta amma bayan rasuwan Malam Inusa, Yayansa Sabo ya karɓota ya kawota wa matar sa Asabe. Da niyyar zai ɗauki nauyin marainiyya ya karɓeta amma ba wannan ne gaban sa ba irin gadon gona da gida da ƙanin sa ya bari. Ba ayi shekaru biyar ba ya cinye komai, ya siyar da gida ya siyar da gonan duka sun bi ruwa babu ko ɗaya yanzu.






'Ya'yan Mama Asabe Maza huɗu ne shiyasa ta ke moran Zainab Kurma son ranta tun tana ƙarancin shekaru.










Yau rumfar Ale Faruƙ a cike ta ke da mutane magidanta da zawarai. Benchi uku aka jera kuma duk sun cika da mutane. Yankan farce akewa Ale Faruƙ lokacin da ya ɗaga ido yaga Kurma na tahowa rumfarsa kanta a ƙasa saboda kunya.






Yana ganin yaron shagonsa Iro ya miƙe yai saurin miƙewa ya ƙariso wajen.


Da hannu ta ke nunawa Iro daron shinkafar da ke kan

11 / 21