Author : Azizat Hamza Category : Top Hausa Novels 2025
yanzu mata su dinga damunka da waya"
Mayar ma sa da wayar ta yi tana murmushi " My Darling ka san ina kishin ka dayawa"
Bai ce ma ta komai ba ya cigaba da duba saƙonnin masoyan na sa.
"Ka ci abinci?" ta tambaya lokacin da ta kwanta gefen sa.
"Na leƙa ɗakin Junior ya riga yayi bacci, i guess tare ku ka ci dinner kenan"
Still bai amsa ma ta ba.
Ta sani idan SSK yana harkan rubuce-rubucen sa baya taɓa ba da hankali a wani abun daban, shiyasa ta haƙura da maganan ta manna ma sa kiss a kumatu tareda faɗin goodnight ta ja bargo ta kwanta. Gobe babban rana ce a gareta shiyasa dole daren yau ta samu isasshen bacci.
A wajen SSK ba komai ya hanashi kula matar ta sa ba sai ganin cewa ɓata lokaci ne a gareshi ya faɗa ma ta kuskurenta. Shi ba ma'abocin yawar magana ba ne hakan ya sa tun farkon auren su ya ke ɗagawa Bilkisu ƙafa, sai dai maimakon abubuwan su ragu sai ya zama ƙaruwa kawai su ke yi.
Irin rayuwar da yai buri idan yai aure ba ita ce rayuwar da ya ke yi yanzu ba.
A wassu lokutan yakan yi tunanin idan da Misturah ya aurah abubuwa ba za su zo ma sa haka ba. Kafin ya faɗa soyayyar Misturah ta kasance abokiya a gareshi wacce ya ke iya gayawa damuwar sa, wacce ya ke iya neman shawara a gurinta kuma ya samu shawara mai kyau.
Duk da sun taso gida ɗaya babu wannan kusancin tsakanin sa da Bilkisu. Har yau da su ka kusan cika shekaru shabakwai da aure ba zai ce ya gama sanin halin Bilkisu ba haka nan itama yanada yaƙinin ba ta san wanene Saifuddeen ba. Suna rayuwa ne tareda shamaki kamar labule a tsakanin su. Tun kafin ya zama Mataimakin Gwamna baya samun kulawar daya dace a wajen Bilkisu sannan daga shiga gwamnati abubuwa suka sake taɓarɓarewa.
A lokutan dayake cikin ƙunci ya ke buƙatar nitsuwa daga matar sa. A lokutan da kansa ya ɗau zafi daga harkokin gwamnati ya ke buƙatar samun mafaka a wajen matar sa. A lokutan ne za ka ga Bilkisu ta shagalta da harkokin siyasa ko kasuwanci.
Tunda ta sako maganar taron matan Gwamnoni da za ayi baya tunanin ta sake saka shi a lissafinta. Idan har ta tuntuɓeshi to tana neman shawara ne bisa jadawalin da ta tsara na abubuwan da za a gabatar ranan.
SSK ya juya ya kalli Bilkisu da ta ke gwarti alamun baccinta yayi nisa kenan.
Kafin ka yi aure duk irin waɗannan ƙananan abubuwa ba ka saninsu sai kun zauna tare na wani lokaci.
Akwai lokutan da idan zai kwanta sai ya saka auduga ko earbud a kunnensa saboda yadda Gwartin Bilkisu ke hana shi bacci, a hankali har jikinsa ya saba da hakan.
Aure sai da haƙuri, abunda ake gayawa sabbin ma'aurata kenan. Alokacin ba sa gane me ake nufi da haƙuri har sai sun kwana biyu da aure.
A farkon auren su yayi haƙuri da lokutan da zai shiga banɗaki yaga Bilkisu ta jefa pant mai haɗe da pad cike da jini a loundary basket ɗin su. Ko kuma a lokutan da ta ke fama da mura ka ga tissue papers da ta face majina da shi a kan gadon su. Ba zai taɓa mantawa da ranan da ya shiga banɗaki tsantsin majina da aka fyace a ƙasan tile ya ɗebeshi ya faɗi ƙasa ba. Yayi haƙuri da kasancewarta ba ta girki saboda a gidan su bata yi, duk da kuwa girki na cikin abubuwan da ke taɓa ma sa zuciya. Girkin Misturah na ɗaya daga cikin abubuwan da suka saka shi faɗawa soyayyarta tun bai shirya hakan ba.
"Saif wannan pepper soup ɗin yana narka zuciyar namiji yana saka mishi nitsuwa. Inada yaƙinin koma mi yake damunka idan ka ci wannan peppersoup ɗin za ka samu sanyi" abinda ta faɗa kenan lokacin da ta miƙa ma sa ɗan ƙaramin food basket da ta riƙo ma sa.
Misturah ta yi gaskiya domin ranan da ya sha wannan peppersoup ɗin ya samu nitsuwa.
SSk ya kai hannunsa ya shafa gashin wig da ya ɗan bulloƙo ta gefen hular baccin Bilkisu.
Yayi haƙuri da kasancewarta mai saka gashin wig duk da kuwa warin gashin na tada ma sa hankali.
Namiji na son mace da za ta fahimceshi, ta saurari maganar sa. Sai dai Bilkisu ba ta ɗaya daga cikin irin matan nan.
Sau dubu Bilkisu za ta yi iƙirarin tana tsananin son shi tana kuma kishin sa, hakanan kuma sau dubu ba za tayi abubuwan da zai cire shamakin da ke tsakanin su ba, har ta samu damar mallake zuciyarsa.
A lokutan kaɗaici he find solitude in poetry, shiyasa ya ke ɓoye kansa da sunan KaSaSa wanda acronym ne na sunansa.
SSK yai murmushi ganin Bilkisu ta maki kanta tareda sosa tsakiyar kan.
Duk wani mulki daya ke da shi ya tsaya a bakin ƙofar gidan sa ne, a cikin gida shi mijin Bilkisu ne, Abban Nana, Mahira da kuma Junior.
SSK ya muskuta ya jawo Bilkisu jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, rabon daya samu nitsuwar miji da mata daga gareta kusan sati biyu kenan.
"Darling na gaji" ta faɗa cikin magagin bacci
"Kar ki damu ba abinda zan yi" ya furta a hankali wani abu na sukan ƙirjinsa...
***
"Kina jina? zan turo miki kuɗin idan na dawo daga office. Ya jikin Muttaƙa?
Tana saƙale da waya a kunnenta yayinda ta ke ƙokarin ɗaura agogo a hannunta.
"Sumayya ki tabbatar Ale bai san da kuɗin nan ba. Kuɗin maganin Muttaƙa kuma ki tabbatar an siyi duka magungunan shi"
Ajiye wayar ta yi ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta wuce inda Umma ke ƙoƙarin raba abun kari. Kunun gyaɗa ta yi da ƙosai da kuma soyayyen dankalin Hausa.
"Umma zan wuce" ta faɗa da yaren kurame
Umman ta amsa ma ta da cewa ta tsaya ta ci abinci.
"Zan makara Umma, amma ki haɗa min kunun da dankalin in tafi da shi office"
Murmushi Umman ta yi sannan ta fara neman inda za ta zubawa Asiya kunun.
Minti shida kacal ta ƙara aciki ta fito ɗauke da jakarta da kuma ledan da Umma ta ba ta. Motar Ubayd na jiranta a ƙofar gida dan haka tana shiga ya ja motar da gudu. Gaisawa su ka yi a tsanake ta cigaba da duba wayarta tana bitar report ɗin da ta haɗa jiya.
Tafiyar minti shabiyu ya kaisu ma'aikatar su ta yiwa Ubayd sallama ta shige ciki yayinda shima Ubayd ya wuce Asibiti.
Tana shiga office ɗin su ta printing report ta wuce da shi office ɗin Editor I.
"Weldone Shahida" ya faɗa lokacin da su ka gama duba report ɗin tare wanda kusan gyaran da ke ciki kaɗan ne.
Tana komawa office ta samu sauran colleages ɗinta suna hiran taron da za ayi yau a jihar ta su. Da SSK da matar sa Bilkisu duk babu wanda ke burge Asiya a cikinsu.
"Shahida kin san wa za'a tura yau?"
Shahida ta girgiza kai tana cigaba da latsa laptop ɗinta.
Mike ya sake cewa " ina tunanin Abigail za a tura, gashi har yanzu ba ta iso ba"
"Mike kar ka dameni dan Allah. Idan ba ta zo ba MD zai iya bawa wani ai, ko kai ko Usman"
Ta sani magana ya ke son gaya mata akan kada ma tasa ran MD zai bari ta je ta covering report ɗin wajen taron da za ayi na matan Gwamnoni. Ba ta san mi ta tsarewa Mike ba a wannan office ɗin. Tun tana bautar ƙasa kafin a ɗauketa aiki yake sa mata ido cikin lamurranta.
Ta cigaba da aiki tana yi tana shan kununta.
CY ya shigo office ɗinsu da sauri. "Aseey ki je office ɗin MD yanzu-yanzu"
"Miya faru?" Ya ɗaga mata kafaɗa ya fita da sauri.
Ta yi saurin kurɓan sauran kunun daya rage sannan ta goge bakinta da tissue ta fice daga office ɗin da sauri tana lura da yadda Mike ke binta da mugun kallo.
Ba ta da ikon yiwa MD musu lokacin daya sanar da ita cewa itace za ta kawo rahoton wajen taron da za ayi yau.
Lokacin da za ta tafi ya ce "Asiya bana son shirme"
"Ok Sir"
Ta sani Abigail yai niyyar tura wa saboda Abigail ta fita gogewa a wajen aiki. Tunda aka buɗe gidan talabijin ɗin ta ke aiki da su kusan shekaru shahuɗu da suka wuce kenan. Rashin Abigail Manji ne ya sa MD ya waiwayeta. A wajen CY ta ke jin labarin wai Abigail tayi tafiya, jiya da daddare mahaifinta ya mutu a chan ƙauyen su.
Ba su kaɗai ba ne 'yan jarida da su ka zo ɗaukan rahoto kusan kowanne gidan jarida sun aiko da wakilan su. CY ya fito da kayan aiki ya shiga saita camera ɗin.
***
Chief of staff (COS) ne ya shigo ofishin mataimakin Gwamna da sauri hannunsa riƙe da ipad.
"Your Excellency za ka so ganin wannan"
SSK ya karɓi pad ɗin daga hannun COS ya danna kan video dake screen ɗin.
Yar jarida ce a gaban hall ɗin da ake taron matan gwamnoni tana bada rahoto.
"Kaman yadda al'umma su ka shaida irin almabazzarancin da akayi a wajen wannan taro wanda ake iƙirarin anyi shine saboda talakawa. Ko ta ina talaka zai anfana da mawaƙan nan Wizkid da Patoranking da aka ɗauko daga Lagos domin matan Gwamnoni su shaƙata da waƙoƙin su?. Yayinda matar mataimakin Gwamna wato Hajiya Bilkisu S Kachallah take magana akan yadda za a gina gidan marayu, talakawa na nan suna alhinin rashin albashi, rashin ruwa ga uwa uba malaman makarantar firamare da ke yajin aiki tun sati uku da suka wuce har yanzu Gwamnati ba ta waiwayesu ba.
Na zanta da wasu matasa inda su ka bayyana mini cewa taron da Hajiya Bilkisu ta yi wani farfaganda ce kawai da ke son ɗauke hankalin talakawa daga matsalolin da su ka sha mu su kai..."
Tsaida video ɗin yai ya miƙawa COS ipad ɗin
"Your excellency kana buƙatar mu tuntuɓi gidan talabijin na Hill TV ne?"
"A'a"
COS na fita daga office ɗin SSK ya ɗau waya ya kira commisioner of finance...
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
03
"Aseey we are dead" CY ya faɗa lokacin da suka shiga mota za su koma office.
"Ni fa ka ganni nan ba na tsoron ta ɓaci wallahi. Gaskiya ce zan faɗa ko da ba za ta yiwa wasu daɗi ba. Idan ban faɗi gaskiya ba miye amfanin aikin jaridan da na ke yi"
"Dama kin fi kusa da MD ai"
"Kai ka san wannan"
Lokacin da su ka isa office Asiya ta ɗauka MD zai ma ta faɗa amma bai ce komai ba. Ta yi mamaki kam dan indai MD da ta sani ne to da tuni ya fara diri akan ta sako maganar albashi a rahoton da ta kawo.
Awa ɗaya bayan SSK ya kalli rahoton Asiya, ya saka hannu aka sakewa ma'aikata albashin su, zuwa yammaci kusan fiye da rabin ma'aikata kowa ya ji alert ɗin albashinsa.
Mintuna kaɗan bayan SSK ya sake albashi kiran Gwamna Saminu Bacchi ya shigo wayarsa.
Duk da Gwamna Saminu ya girme shi da shekarun da ba za su wuce biyar zuwa shida ba, SSK bai chanchanci irin tsawan da Gwamnan ya masa ba akan ya sake albashi kafin ya dawo.
Bayan ya ajiye wayar ne ya fara tunanin anya kuwa zai iya cigaba da irin wannan tozarcin..
***
Daf an kusa tashi aka kawowa Asiya Shahida letter daga office ɗin MD. Tana gama karantawa ta wuce office ɗin sa da sauri.
"Sir yanzu aka kawo min wannan letter, ban gane ba. Two weeks suspension sannan ka maida ni copy editor"
"Kafin ki tafi ki je ki reporting a wajen News Director"
"Sir???"
"Ba za ki sake airing komai ba har sai kin iya banbanta professional da personal affairs"
Sai yanzu ta gane ashe shirunsa ɗazu ba yana nufin cewa ransa bai ɓaci da abinda ta yi ba ne.
"Idan kuma ba ki gyara ba, Hill TV za ta iya ɗaukan mataki mai tsauri akan ki"
Haƙuri ya ke so ta bashi ta sani kuma ba zata bayarba.
"Shikenan Sir, nagode" daga haka ta fice daga office ɗin tana dunƙunƙune takardar da ke hannunta.
Ko jira lokacin tashi ba ta yi ba ta ɗau jakarta ta bar station ɗin...
Asiya na zaune akan stool a ƙofar ɗakinsu tana yiwa Ummanta kitso Ubayd ya shigo gidan da sallama. Da sauri Umma ta jawo hijabinta da ke gefe ta saka ta bar Shahidah da buɗe baki. Umma ba dai kunya ba. Ta faɗa a zuciyarta. Wai dan ma ba ayi aurenta da Ubayd ba kenan.
Ubayd ya tsugunna ya gaishe da Umma. Ya iya gaisuwa kam amma har yanzu bai fahimtar yaren kurame sosai kodan bai taso a gidan ba ne?
Ya ajiyewa Umma wata ƙatuwar leda tareda kuɗi acikin envelop.
Umma ta shiga yi ma sa godiya, ta zunguri ƙafar Asiya alamar ta tayata yiwa Ubayd godiya.
"Ya Ubayd yaushe aka yi albashi?"
"Ai inaga ke ce dalilin wannan albashin, da safe da ki ka yi maganan albashin nan zuwa ƙarfe ɗayan rana mutane sun fara ganin alert. Ni nawa ya shigo ƙarfe uku da rabi ne lokacin ina Alwala a masallaci"
"Mugu ba. Yana tsoron kar ubangidan sa ya dawo ya samu bai biya albashi ba ya haushi da faɗa"
"Ikon Allah, yanzu ya biya albashin ma bai miki ba"
"Dama ya so yin kasuwanci da albashin mutane ne, Allah ya kamashi"
Ubayd ya girgiza kai kawai ya wuce ɗakin Inna Yaha dan ya kai mata nata kayan.
***
Yau Gwamna ya dawo daga tafiyar da yai, kusan ya ƙara kwanaki biyu bisa ranan daya ɗiba zai dawo. A ranan ne kuma abubuwa da dama suka faru.
A chan gidan Yallaɓai Alhaji Kachallah ne zaune a falon gidan yana jiran fitowar Yallaɓai. Kusan minti ishirin da biyar yai yana zaman jiran sa kafin ya fito yana dogara sandar ƙarfe wacce ta ke ta ado ba wai dan yanada matsalar ƙafa ba.
Minti biyar ya ɗauka yana yiwa Yallaɓai bayanin abinda ke tafe da shi.
Ya ƙara da cewa " ina fata idan lokaci yayi ba za a juya min baya ba"
Yallaɓai yai murmushi ya ce "Alhaji Kachallah ka sani sarai bana magana biyu. Abu ɗaya ne zai sa na chanja maganata, idan har shi ya karya dokar wannan tafiya"
"Ina tsoron kada Mr Paul ya idda mugun nufinsa. Idan har kujerar mataimakin Gwamna ta kuɓuce mani, Yallaɓai za a samu matsala a wannan tafiya"
"Ka kwantar da hankalinka ba abinda Mr Paul zai iya yi"
Alhaji Kachallah ya miƙe ya ce "ni zan wuce"
Bayan tafiyar Alhaji Kachallah Yallaɓai ya dubi kujerar da Alhaji Kachallan ya tashi akai, itace dai kujeran da Mr Paul ya zauna akai jiya yana kawo ƙorafinsa akan a dakatar da tafiyar Alhaji Kachallah saboda akwai giɓi sosai a tafiyar ta sa.
"Ba shi da experience ko kaɗan a wannan harka Yallaɓai. Yanada sanyin zuciya idan aka ɗaura shi akan kujera zamu samu matsala da shi. Ya kamata a datse..."
Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu. Mr Paul yai tsit yana zazzare idanu.
Yallaɓai yai murmushin gefen baki, yana son irin wannan wasan...
***
Cikin shiga ta alfarma shiga ta ƙasaitattun mata Hajiya Bilkisu ta fito daga ɗakinta. Wani tsadadden leshi fari ta saka ɗinkin buba da zani, ta saka takalmi mai tsini kalar ja wanda yai dai-dai da kalar clutch bag ɗinta, ɗan kunne da awarwaro da kuma sarƙa,
Tana takunta ɗaiɗai har ta sauko ƙasa.
"Hajjaju Makkatun, Hajjan Gwamna, Hajjan mu" ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya tana ɗan tafa hannu.
"Hansa'u kenan"
"Hajja idan na girma ina son zama kaman ki"
Wani lokaci takan ɗan tausayawa Hansa'u. Wacce ta kawota ta gaya mata cewa auren wuri aka mata tana shekara goma shauku, ta wahala sosai a wajen Kishiyarta. Tana shekaru shabiyar mijin ya rasu. Ba a jima ba ta haihu ɗan bai zo da rai ba wannan psychological trauma ɗin shine ya taɓa ma ta ƙwaƙwalwa. Anyita magani ana tunanin Aljanu ne ko sammu amma shiru. Bayan shekaru ana jinya shine wata Gwoggonta ta kawota Birni dan ta koyi sana'a tunda ta ƙi auruwa. Hansa'u akwai aiki kam amma akwai shirme da shiririta dan har yanzu hankalin ta kaman na budurwar ƙauye ce 'yar shekaru shabiyar. Kusan ko da Hajiya Bilkisu ta girmeta to abinda za ta bata ba zai wuce shekaru biyu ba.
"Hansa'u Malamin Junior ya zo ko?"
"Eh Juno yana karatu da malamin sa a waje"
"Good, idan ya gama lesson ki tabbatar yayi wanka kafin ya ci abinci. Ni zan fita"
"Hajjan mu a kawo mana tsaraba"
Hajiya Bilkisu ta ɗan yi dariya sannan ta fita daga gidan ta nufi motarta inda driver ke jiranta.
Kai tsaye gidan Gwamnati aka wuce da ita. Ba wannan ne farkon zuwanta gidan ba amma abin mamaki ba a bari ta ƙarisa falon First lady ba kamar yadda ta saba yi idan ta zo. Mai aikin gidan ta ce ma ta First lady na da manyan baƙi dan haka ta jira a falon baƙi kafin su tafi.
Da farko abin ya yiwa Hajiya Bilkisu banbaraƙwai saboda irin haka bai taɓa faruwa ba amma daga baya sai ta yi tunanin ko dai first lady na tare da surkuwanta ce. Ba abu ne ɓoyayye ba a wajenta irin takun saƙa da ke tsakanin First lady da Maman Gwamna. Rabuwa su ka yi da matarsa ta farko wacce sun yi kusan shekaru ashirin da biyu tare kafin su ka rabun, hakan kuma ba ƙaramin ƙona ran mahaifiyar Saminu Bacchi yai ba, Murjanatu itace uwar 'ya'yan sa guda shida amma haka ya rufe ido ya shure ya saketa ya auro Hajiya Sha'awanatu. Kusan shekaran su bakwai da aure amma har yanzun tsakaninta da Mahaifiyar Saminu Bacchi ba sa ga maciji.
Zaman jiran da ta ke gani ba zai wuce minti ishirin zuwa talatin ba shine ya zamana har ya wuce awa biyu.
Sau biyu tana turawa a duba ma ta first lady amma sai a ce tana tareda baƙi.
Tun Bilkisu na ɗaukan abun ba komai ba har ya zo ya fara ba ta haushi.
Awa uku da zamanta a falon ta miƙe tsaye dan ta wuce gida zuciyarta cike da ƙuna. Barka da dawowa ta zo yiwa First lady ba wai zaman walaƙanci ba. Ko bakin ƙofa ba ta kai ba ta jiyo shewar first lady da wasu mata. Ta juya