Author : Azizat Hamza Category : Top Hausa Novels 2025
zaɓi Alhaji Bala Yamai ne a matsayin mataimakin Gwamna saboda an riga an wanke sunansa daga laifin rashawa da ake tuhumarsa da shi shekarun baya, ya haɗa da cewa Alhaji Yamai yanada experience a harkar siyasa fiye da shi shiyasa ya zaɓe shi. Lokacin da ya gama bayanin lokacin da aka ɗibarwa shirin ya ƙare dan haka Asiya bata sake wata tambayar ba ta ƙarƙare shirin.
CY na cewa Cut Gwamna ya miƙe ya tafi yayinda muƙarrabensa suka bi bayansa cikin sauri.
"Aseey kin fuck up Wallahi" CY ya faɗa yana girgiza kai yayinda Sunusi yake jimamin yanzu ɗan alkhairin da za a basu ya wuce tunda gashi ran Gwamna a ɓace ya bar wajen su.
Lokacin da aka katse shirin aka saka talle COS ya zame jiki ya wuce office ɗinsa. Abu ɗayane ya zo masa wato Asiya taji abinda ya faɗa idan ba haka ba babu yadda za ayi ta kawo maganar mutuwar tsohon Gwamna. Tunda aka bashi matsayin Chief of staff lokacin Gwamna Saminu Bacci ya saka CCTV a office ɗinsa saboda shiga masa office da akayi ba da izininsa ba aka bincika masa wasu takardu. Ya kori sakatariyarsa a lokacin amma ya sani ba da saninta aka yi hakan ba, bai jima ba kuwa ya gano wanda yai hakan. Babu wanda ya san yanada ɓoyayyiyar camera a office ɗin nasa. Kasantuwar Sakatariyarsa Jennifer bata desk ɗinta sanda ya shigo ya ƙara tabbatar masa da cewa Asiya ta ji wayar da yai tun ma kafin ya duba CCTV footage ɗin. Bai sha mamaki ba da yaga Asiya laɓe a bakin ƙofarsa da 'yar ƙaramar na'ura da yake da tabbacin recorder ce lokacin daya kalli footage ɗin.
Asiya tana waya da Ubayd wani security ya iso ya ce ta biyo shi. CY da Sunusi suka zaro ido tareda tambayar lafiya. Bai ce musu komai ba yai wa Asiya jagora suka bar wajen. Asiya ta tsorata amma ta dake bata nuna ba saboda kar ta bada kanta, yau duk yadda za ayi sai dai ayi amma bazata taɓa fito da recorder ɗin nan ba.
Office ɗin Chief of Staff ya kaita kamar yadda tayi hasashe. Tayi mamaki da taga Sakatariya a office ɗin farko wanda ɗazo da ta zo babu ita. Lokacin da ta shiga office ɗinsa Mr Lamara Damana yana tsaye ya haɗe gira.
Jakarta security ɗin ya ce ta miƙo tana miƙa masa ya zazzage kayan ciki a walaƙance. Powder, lipstick, hankerchief, jotter, biro da earpiece ne a ciki. Wayar hannunta security ɗin yace ta kawo ta miƙa masa ba musu tana kallon COS da shima ya zuba mata ido yana mata kallon tsana.
Wata na'ura da ke detecting devices security ɗin ya bi ya zagaye jikin Asiya da shi amma bai detecting komai ba.
COS yace ya miƙa masa wayar Asiya sannan ya basu waje. Bayan fitan security ɗin COS ya kalli Asiya ya ce "na san ba a waya kika ɗauki maganarba dan haka ki fito da recorder ɗin"
"Ikon Allah, ina tunanin ka manta cewa ni 'yar jarida ce, wannan cin zarafi da kake min zai ja maka matsala" Asiya ta faɗa a kausashe.
Wani murmushin gefen baki COS yai wanda idan ba lura kayi ba baza ka gane murmushin yai ba saboda yadda gefen bakin ya tattare kamar mai shirin kuka.
"Asiya Shahidah Faruƙ Baba. Na san kina sane da haɗarin da ke tattare da wuce gona da iri a cikin aikin ku"
"Are you threatening me?"
"You know better"...
Lokacin da ta isa wajen su CY ko magana ba ta musu ba ta wuce gaba suka bi bayanta suna tambayar miya faru. Sai da suka shiga mota Asiya ta karɓi jakar camera da ke hannun CY ta buɗe wani ƙaramin zip ta ɗauko recorder a ciki ta damƙe shi a hannunta, yadda ta damƙe shi har sai da hannun ya fara rawa. CY kallonta yake yi cike da tambayoyi a harshensa amma ya yi gum da bakinsa tunda tace musu kar wanda ya mata magana.
Maimakon office gida tace Sunusi ya sauketa. Tana shiga ɗaki ta samu Umma na wanki a tsakar gida, ganin Ummanta duƙe tana wanki ya tuna mata da washing machine da ta ce zata siya tun watan daya gabata. Rashin lokaci ya sa take bada kaya a wanke mata sai ta haɗa dana Umman amma tunda Umman ta ce ba ta son a fita mata da kayan wanki waje ya sa duk weekend indai tana gida take wanke kayan mahaifiyarta.
A tsanake ta gaisheta tace mata ta zo ɗaukan abune dan kar ta firgitata. Tana shiga ɗaki kai tsaye laptop ɗinta ta buɗe ta fara ƙoƙarin tura abinda ta naɗa zuwa Laptop ɗin. Maganganun COS sun ɗan razanata amma idan ta tuna itama tanada abinda zai iya wargaza mulkinsu sai ta tausashi ranta.
Kafin ta gama abinda take wayarta ta shiga ruri. MD ne ta sani kuma ba zata kulashi ba sai ta gama abinda takeyi. A ƙalla ta kai awa ɗaya da rabi a gida kafin ta shirya ta koma office.
Ta ɗauka MD zai mata faɗa kaman yadda ya yi a waya amma sai ta ji ya tausasa kalmominsa gareta "Asiya ban san mi kika naɗa a gidan Gwamnati ba amma ina so ki sani cewa zaki iya taka Gwamna ki kwana lafiya amma Lamara Damana ba zai barki haka ba"
"MD kana so kace..."
"Asiya na san kinada ƙoƙari sosai wajen dukkan ayyukanki amma ki sani ana iya barin halak saboda kunya"
Za tayi magana ya ɗaga mata hannu sannan ya cigaba " already mutane sun fara reacting wa interview da kikayi amma nan da kwanaki kaɗan komai zai lafa, saidai idan kika sake bijiro da wani abun Asiya ba ke kaɗai fitinar za ta shafa ba idan ba ki ji ta ma'aikatarmu ba to ta iyayenki fa?"
Jikinta yai sanyi ta kasa cewa komai.
"Asiya you are a field reporter not investigative reporter, kada kiyi aikin da ba naki ba. Faɗa da 'yan siyasa ba abu ne da ake ƙareshi ta daɗi ba"
"Sir, kana nufin na watsar da gaskiya na rungumi ƙarya kenan?"
"Ban san mi kika sani ba Asiya amma koma minene ki yiwa Allah ki haƙura dashi saboda mutuncin ki. Lamara Damana ba mutumin da za ki iya ja da shi bane"
"Shikenan na ji"
Bayan Asiya ta bar office ɗin. MD ya sauke ajiyar zuciya. Kashedi Chief of staff ya masa ɗazu daya bugo akan in har aka fitar da wata magana da ta shafeshi Hill TV za ta rasa matsugunni a Jahar Congo. Ba wannan ne matsalar ba. Jin ya ambaci sunan Asiya ya sa shi fahimtar dalilin dayasa Asiya ta yiwa Gwamna tambayoyin da tayi, duk da bai san takamaimai mi Asiyar ta jiyo ba amma yanada yaƙinin abune da ya shafi mutuwar tsohon Gwamna. Duk wanda ya ke bibiyar siyasar jahar ya san cewa Lamara Damana shine shugaban munafukan gidan Gwamnati masu hana ruwa gudu. Mr Damana ya fara aiki daga Sakatare ne a hankali ya dinga shiga cikin manya ya zamana anyita ƙara masa matsayi har ta kai lokacin Gwamna Saminu Bacchi aka bashi muƙamin Chief of Staff. Tunda aka koma mulkin farar hula babu Gwamnan da Mr Damana bai yi aiki da shi ba.
"Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta naɗi abinda yafi ƙarfinta, idan ya fito waje bana tunanin za ta sake yin rahoto da bakinta" kashedin COS na ƙarshe kenan.
Yana son Asiya tun farkon zuwanta ma'aikatar lokacin da tazo yin bautar ƙasa. Ya nemi soyayyarta ta ƙi shi, wanda yanzu ya riga ya haƙura tunda yaji ance an kawo kuɗin aurenta.
Duk da COS bai buɗa ba ya fahimci mi yake nufi sarai dan ba yau ya fara aikin jarida ba. Ba zai taɓa mantawa da wani ogan sa edita Mr Simon da suka fara aiki tare lokacin yana Lagos ba, shima kamar Asiya taurin kai ne da shi, indai a wajen bayyana gaskiya ne to baya jin tsoro. Ranan da gidan jaridarsu ta wallafa shafi akan wani asiri da Mr Simon ɗin ya jiyo na wani fitaccen ɗan siyasa ranan bai kwana duniya ba domin yana hanyar dawowa daga office motarsa tayi bindiga ta kama da wuta.
Ba zai manta da wani abokinsa Ja'afar ba. Ja'afar Bello investigative reporter ne daya binciko yadda wata Matar Minister ke safarar 'yan mata karuwanci zuwa ƙasashen waje. Yanada isassun evidence a kanta har an fara shari'a haka kawai aka nemi Ja'afar Bello aka rasa, ko sama ko ƙasa. Yanzu shekaru shatara kenan babu labarinsa.
Yana tsoron kada taurin kan Asiya ya jawo mata fitina.
Asiya koda ta koma office tunanin maganganun COS da ta MD ta dinga yi, a wani ɓangare kuma tana tunanin bazata taɓa bari Gwamna Saifuddeen yaci bulus ba. Ta sani cewa abinda ta naɗa bai kai evidence da za a iya kama Gwamna ba amma idan har maganan ta fito zai jawo cecekuce har a fara bincike, koda ya sha yanzu lokacin zaɓe abokan adawa za su yi kamfen da maganar su hana mutane zaɓanshi, ko kuma idan har akabi komai da gaskiya to dole ne ayi impeaching ɗinsa. Babu abinda take ganin yanzu zai faranta mata rai a rayuwa sama da taga an tsige Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah ...
***
A office Asiya ta dinga jayayya da zuciyarta akan ko ta bi shawaran MD tayi shiru da abinda ta ji ko kuma dai ta fitar da shi ta tada fitinar da zai jawa Gwamna matsala. Shawara ta yanke akan idan Ubayd ya zo hira za ta nemi shawaransa ta ji mi zai ce. Daga baya ta kasa haƙuri har zuwa lokacin ta kira numbarsa tace ya hau whatsapp akwai abinda za ta gaya masa. Sai bayan minti shabiyu ya hau saboda yana duba wani patient ne a lokacin da sukayi waya.
A tsanake ta masa bayanin komai da kuma abinda MD ya faɗa mata. Bai tsaida ita ba har sai da ta gama bayani ta ce miye shawaransa gareta.
" Asiya Shahidah na roƙe ki da girman Allah ki haƙura da abinda kike shirin yi domin ba zai haifar da ɗa mai ido ba. For God sake! we are getting married soon. Kina so rikicin siyasa ya jawo miki wata fitinar ne? Idan har abinda kika ji gaskiya ne then you are not safe Aseeya ba ke kaɗai ba hatta 'yan uwanki ba su tsira ba. Asiya ina za ki iya rikici da Lamara Damana?, Please ki mayar ma sa da recorder ɗinnan ki nuna masa ba za ki taɓa fitar da maganan da kika ji ba"
Tana gama karanta rubutun ta sauka tareda jan dogon tsaki. Wai sunata maganan Lamara Damana, Lamara Damana, shi waye da za ta ji tsoronsa. Idan har ba za a fitar da labarin a ma'aikatarsu ba ai akwai social media. Ringing ɗin wayarta ya dawo da ita daga tunanin da takeyi. Koda ta ɗauki wayar Ubayd cigaba da roƙonta yayi yana cewa ta masa alƙawarin ba abinda za tayi, da ta ga ya dameta tace mishi ta ji za ta yi shiru sai dai chan ƙasan ranta ta san ba haka bane.
Lokacin da suka tashi CY ne ya nemi ya kaita gida saboda yana son jin labarin miye dalilin sauya tambayoyi da tayi, sannan miye dalilin da yasa COS ya nemi ganinta.
"Na san gulma ne ya kawoka Clement kuma ba za ka ji komai ba"
"Ahn-Ahn, Aseey Darling ya zaki fassarani haka, jiya ma fa ni na kai ki gida"
"Ahaf, ka gama kame-kamen naka dai ka dawo hanya, magulmaci"
CY yai dariya ya wuce gaba.
Suna fita daga ma'aikatar Obinze Maigadi ya ɗaga waya jiki na rawa ya kira wata number ya ce yanzu Asiya ta fita daga ma'aikatar tasu ya haɗa da cewa tare take da abokin aikinta akan machine kafin aka katse kiran.
CY na tuƙi yana yiwa Asiya taɗin budurwarshi mai suna Evelyn da ta ce masa dole sai ya koma ɗariƙar Katolika (catholic) kafin ta iya auren shi, Asiya tana masa dariya. Ba suyi aune ba dai-dai za suyi kwana wata babbar mota da basusan daga ina ta fito ba ta zo ta mangajesu hakan yasa Asiya tsalle sama ta faɗi gefe yayinda motar tabi ta kan machine da ta danne CY ta wuce da bala'in gudu...
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
07
"Darling" Bilkisu Kachallah ta kira da fake American accent ɗinta wanda kunnen Saifuddeen ya kasa banbance "Dolin" tace ko kuma "Durling". Ya dai ɗago ido ya kalleta ba tareda ya furta komai ba. Ya sani ya kamata ya ce mata tayi kyau ko kuma yace jan lingerie (rigar bacci) data saka ya amshi jikinta sosai amma bai ce komai ba.
A mafiya lokuta idan ta yi shiga irin wannan tana buƙatarsa ne, ba kawai buƙata ba domin daga ƙarshe idan ta kwanta gefensa tana shafa gashin ƙirjinshi a hankali za ta bijiro masa da wata buƙatar ne, mafiya yawanci abubuwanda take tunanin ba zai mata su ba idan ta tambayeshi kafin ta shigo turakarsa su take tambaya.
Rabonsa da ita tun ranan farko da suka tare a gidan Gwamnati. Ba wai baya buƙatarta bane amma rashin nuna damuwarta gareshi yasa yake haƙuri da ita, ƙila saboda a koyaushe baya son takura mata ne. She's not yet 40 amma kuma lamarin sex life ɗinsu ya lalace tun lokacin da ta haifi Junior.
Takardu yake dubawa ta tura takardun gefe ta shiga kissing ɗinsa, farko daga goshinsa, kunnensa kafin ta kai bakinsa. Ba a jima ba ya tureta yace " ki bani minti goma na ƙarisa aikin dana ke"
"Haba Darling, ka san yaushe rabonka da ni kuwa? Aiki can wait please" ta faɗa tana zunɓura baki.
So yake ya ce mata laifinta ne idan bai nemeta ba tsawon kwanakin nan, saboda duk lokacin daya samu free time yake buƙatar kulawarta baya samu, amma bai faɗi hakan ba sai yayi mata murmushinsa mai shiga rai yace " kar ki damu, ba zan jima ba"
Bilkisu ta kwanta gefen gado tana kallon ceiling yayinda ya cigaba da duba takardun da idan bai duba yanzun ba bashida lokacin duba su gobe. Kusan minti talatin da uku kafin ya gama komai lokacin har Bilkisu ta fara gwarti. Ya je ya ajiye takardun acikin wani file ya saka a briefcase.
Bai tashi Bilkisu ba saboda ya san a gajiye take yau tace masa ta fita duba gidan marayu bai san details ɗinba kuma bai tambayeta ba.
"Shine baka tasheni ba" ta faɗa lokacin da ta tashi da Asuba.
"You're tired"
"Still" ta faɗa tana haɗe rai.
"To barin dawo daga masallaci"
Lokacin daya dawo daga sallar Asuba ta riga tayi wanka ta chanja kaya, ba rigar bacci ta sa ba amma shima kamar na jiya guntu ne mai hannun spaghetti, rigan ya kamata sosai, ya bayyana ƙaton tumbinta da yake a taƙune.
Kamar yadda yai hasashe yana shirin miƙewa ya je yai wanka ta faɗa masa buƙatarta na son buɗe Bilkisu Kachallah Foundation dan tallafawa marayu. Ajiyar zuciya yai sannan yace "Allah ya sanya alkhairi" ya wuce banɗaki tda sauri...
Meeting biyu ya shiga daga zuwansa office, yanzun ma wani meeting ɗin zai shiga nan da minti talatin. Yana duba report ɗin da aka kawo masa. Sakatare ya shigo da wasu takardu a hannunsa.
"Your excellency na samu COS ya reschedulling ziyarar da za ka kai ƙaramar hukumar Antu zuwa jibi laraba"
"Ok" Gwamna ya faɗa yana cigaba da duba takardun da ke gabansa.
"Excellency kafin na manta. 'Yan jaridar da suka zo jiya sun yi hatsari"
"Asya!" Gwamna ya ɗago kai da mamaki
"Ita da abokin aikinta suna komawa gida wata babbar mota ta afka musu..."
"Is she alive?" Ya faɗa da tsananin damuwa a tattare da shi
"Na ji labarin dukansu suna raye. Ita Asiya ance nata da sauƙi amma shi ɗayan kam rai a hannun Allah"
"Hasbunallah! Keep me posted akan labarinta" ya faɗi labarinta kamar ita ɗaya akace tayi hatsarin.
Bayan fitan Sakatare daga office ɗinsa ya ɗaura haɓarsa akan hannunsa yana tuna siririn ushiryar dake tsakanin haƙoranta wanda yake ƙara mata kyau idan tana murmushi.
***
Umma ne a gefen gadon da aka kwantar da Asiya lokacin da Ubayd da Abba suka shigo. Abba ya tambayeta ko Asiyan ta tashi tace masa bata tashi ba. Lokacin daya zauna ta tambayeshi jikin abokin aikin Asiya Abba yace ance musu har yanzu bai farfaɗo ba. Ubayd ya ƙurawa Asiya da ke kwance ido bai san lokacin da hawaye ya fara zubo masa ba. Ba dan kariyar Allah ba da ita ne ke halin da CY yake ciki ko kuma ace da yanzu an jima da bisineta. Yai saurin goge hawayensa dan kar Umma ta gani. Alhamdulillah ya furta a ransa kafin ya yiwa su Umma sallama ya fita.
Ba a jima ba Asiya ta farka a karo na biyu tun safiyar yau. Da farko data farka kuka ta dinga yi tana faɗin a kaita wajen CY. Yadda ta birkice musu sai da aka mata alluran bacci.
Wannan karan ma data farka sunan CY ta kira. "Abba CY ya mutu ko?, sun kashe shi ko?"
"Kwantar da hankalinki Shahidah. Yana nan da ransa"
Da bata faɗa gefen titi ba, da ba wannan zancen akeyi akanta ba. Gefen goshinta, kunnenta da kafaɗarta sai kuma gwiwarta da ya kurje su kaɗai ne ciwon jikinta, sai dai saboda irin faɗuwar data yi duk jikinta ciwo yake mata.
Asiya ta sauke ajiyar zuciya hawaye na zubo mata.
"Abba idan CY ya mutu bazan taɓa yafe musu ba. Kuma sai na..."
"Asiya!" Ya kira sunanta da ƙarfi har sai da ta tsorata.
"Ba abinda zakiyi, kina jina? Nace ba abinda zakiyi. Zan mummunan saɓa miki idan kika sake maganan mutanen nan"
"Abba..."
"Zamuyi magana idan munje gida"
Ta kalli Abba da mamaki, ba yadda za ayi yai wannan maganar sai dai idan har yasan wani abu. Kenan Lamara Damana ya tuntuɓeshi.
Da yamma da Ubayd ya dawo ta tambayeshi ina CY yace mata CY na CUTH (Congo University Teaching Hospital ) an ɗaura shi a na'ura saboda ya shiga coma.
"Mutuwa zai yi ko?" Ta tambaya murya na rawa
"Mine mutuwa a hannun Allah take. Ki masa addu'a amma he's in a very bad shape infact an yanke masa hannu ɗaya"
"Ya Allah!" Ta riƙe baƙi.
'Yan wajen aikinsu sun zo sun gaisheta. MD shi kaɗai yazo da yamma lis kuma bai jima ba saboda lokacin ɗakin nata akwai