Author : Azizat Hamza Category : Top Hausa Novels 2025
iya controlling kanta ba ta ma sa rashin mutunci ba.
"Zan dawo gobe, zan jira ko ƙarfe nawane sai na ga Gwamna da kaina na bashi wasiƙar. Zan haƙura ne kawai idan shi da bakinsa ya ce ba zai yi hira da ni ba"
Daga haka ta fice daga office ɗin ta bar Sakatare baki buɗe.
Bayan tafiyar Asiya da Sakatare ya shiga wajen Gwamna kai ma sa wasu takardu sai ya haɗa da wasiƙar Asiya.
"Wannan fa?" Gwamna ya tambaya yana ɗaga envelope ɗin da wasiƙar ke ciki.
"Your excellency gidan talibijin na Hill TV ke son hira da kai"
"Malam Baffayo hira da 'yan jarida sai gaba, we have better things to do with our time now"
"Yes excellency"
Daga haka ya fita bai sake ɗago maganar ba.
Washegari kuwa kamar yadda Asiya tayi alƙawari sai gata a ofishin Gwamnati sai dai wannan karan ko ƙarasawa ofishin Sakataren Gwamna ba ta yi ba aka dakatar da ita.
"Ban gane in tafi ba. Ina son ganin Gwamna ko akwai dokar da ta hana hakan?" Asiya ta faɗa wa security guard ɗin daya tsareta cikin tsawa.
"Gwamna baya office ki je ki dawo wani lokaci"
"Ba inda zan je. Gwamna yana nan. I need to have audience with him"
" idan ba ki fita ta lallami ba, za a fita da ke ta ƙarfi. So please leave"
"Ba inda zan je fa" Asiya ta faɗa tana gyara tsayuwarta.
A ofishin Sakatare kuwa Gwamna ne ya zo wucewa zuwa wani exco meeting ya jiyo hayaniyar da ake yi hakan ya sa shi ya ɗan tsaya.
COS da ke bayan sa ya kalli Sakatare cikin tsawa yace "wai wacece a wajen nan ne?"
"Wata 'yar jarida ce ta dage sai ta ga Gwamna".
"Kul ka taɓa ni, wallahi yatsata ka taɓa sai ka san wacece Asiya-Shahida a garin nan. Na san 'yanci na dan haka kar ka kuskura ka min barazana"
Wannan karan tana maganar ta zauna a kan kujera da ke Lobby ɗin tareda ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana huci.
"Malam Baffayo ka ce ta dawo ranan Monday"
Ba da ƙarfi yai maganar ba amma duk sun ji shi. Bai jira mai Sakataren zai ce ba ya wuce abinsa.
Asiya ta zauna na kusan minti shabiyar kafin Sakatare ya fito.
"Malama Asiya ya da haɗe rai haka"
"Ba fa inda zan je" ta faɗa tana girgiza kai
Sakatare ya miƙa ma ta wani envelop. Tana gama karanta takardar da ke cikin envelope ɗin ta saka ihu. Sai kuma ta yi saurin rufe bakinta da hannunta.
Sakatare yai dariya ya ce " gaskiya kin taki sa'a. Gwamna ya amince ya ganki ranan Monday, best of luck"
Fiska a washe Asiya ta ma sa godiya ta tafi. Shi kan sa Sakatare yayi mamaki da amincewar Gwamna cikin sauƙi haka.
***
A chan ɗakin da ake taro kuwa dukkan wanda ya ke da alaƙa da wannan taro ya riga ya hallara dama Gwamnan kawai ake jira.
COS ne ya ja masa kujera ya zauna yana kallon mutanen da ke wajen ɗaya bayan ɗaya. Kusan minti guda ya ɗauka sannan ya ja dogon numfashi sannan ya ce "gentlemen ina buƙatar report na wannan wata"
"Kwamishina Isiaka" Gwamna ya kira yana duban wani ƙaton baƙin mutum sanye da babbar riga kalar light blue. Kwamishinan ilimi yai gyaran murya sannan ya fara bada bayani wanda ya ɗaukeshi tsawon minti huɗu da rabi.
"Not impressive Kwamishina Isiaka. Ban ji ka yi maganar Albashin Malaman firamare da za a ƙara ba"
"Your excellency mun submitting budget farkon watan nan amma abunda ya iso mana daga hannun Kwamishina of Finance shi mu ka yi amfani da shi"
Gwamna SSK ya juya ya zubawa Mr Paul idanunsa ma su kaifi hakan ya sa shi fara wiki-wiki da ido.
"Mr Paul!" Gwamna ya faɗa da ɗan ƙarfi.
"Excellency saboda akwai basusuka dayawa da tsohon Gwamna ya bari muna so a fara rage wannan kafin a fara maganan ƙara albashi"
"Abinda aka fara tunkarana da shi lokacin dana ƙarfi wannan kujera shine maganan ƙarancin albashin Malaman Firamare. If i can remember clearly. Sai da na ce Kwamishina Isiaka ya drafting budget ya nuna maka, kana tunanin da wasa na yi maganar?"
"No your excellency" Mr Paul ya faɗa yana sunne kai ƙasa.
"Ina Kwamishinan raya karkara"
"Your excellency" wani mutum fari dogo ƙyamusashshe ya faɗa yana ɗaga hannu.
"Banga report dana buƙata ba tun farkon watan nan"
Cikin turancin sa da take nuna asalin harshen bahaushe ya fara bayani.
"Na tura memo wa Kwamishina Paul ya kai sau huɗu amma babu wanda ya reply aciki"
Wannan karan ma Gwamna ƙurawa Mr Paul ido yai.
"Your excellency budget da aka yi da tsohon Gwamna babu buƙatun Kwamishina Ɗanladi a ciki shiyasa babu yadda za ayi yanzu a ƙirƙiro kuɗi a bashi sai yai haƙuri sai wata shekarar"
"Oh hakane ko?. Ina buƙatar budget da aka drafting na wannan shekarar da kuma abubuwan da akayi da su haɗe da receipts na komai. Kwamishina Paul zan saurari report ɗinka gobe da safe a office ɗina"
Mr Paul ya taƙune fiska kamar wanda ya tauna flagyl yayinda sauran excos da ke wajen kowa ya sha jinin jikinsa.
Lokacin da SSK ya ke mataimakin Gwamna bai taɓa ɗaga murya ba, infact idan za ayi meeting sau dubu to zaka iya irga iya maganan da yai a meeting ɗin amma wai yanzu roughly wata biyu daga rantsar da shi ya rikiɗe musu ya koma wani Zaki.
Magana ta ƙarshe da aka yi shine maganar naɗa sabon mataimakin Gwamna wanda Gwamna ya tabbatar mu su da cewa ranan talatin ga wata za'a rantsar da mataimakin Gwamna wanda har yanzu basusan ko wanene ba.
"Babu mamaki idan kuka cigaba da irin wannan sakacin a office ɗin ku zan sake sabon cabinet"
Gwamna na gama faɗin haka ya miƙe tsaye yana ɗaukan wayoyinsa guda biyu da ipad yayinda sauran excos ɗin ma suka miƙe tsaye suna faɗin "Excellency"...
A ɓangaren Asiya kuwa tana fita daga gidan Gwamnati ta wuce ma'aikatar su. Tun a hanya ta kira CY ta ma sa albishir.
Tana isa kuwa Office ɗin MD ta fara wucewa. Tana shiga ta ajiye ma sa takardar hannunta wanda tunda ta cirota daga cikin envelope ba ta iya maidashi ciki ba.
"Yaushe zan koma bakin aikina?" Ta faɗa tana kallon MD daya wangame baki saboda ganin seal ɗin Gwamna akan takardar.
"That's fantabulous Asiya. Ya kika yi? Kai i'm happy. This means gidan talabijin ɗin mu ne za ta fara hira da Gwamna Saifuddeen. Whoaw!"
Asiya ta sa dariya. Farin cikinta ko kaɗan ba shi da alaƙa da kasancewarta 'yar jarida ta farko za ta yi hira da Gwamna SSK tun da ya hau kujerar Gwamna. Farin cikin ta ya zo daga abu biyu ne. Na farko aikinta da za a dawo mata da shi (ta tsani aikin editting ɗin nan). Na biyu kuma cimma burinta da ta yi.
Idan za ka lissafo halayen Asiya to dole ka sako cewa ita ɗin mace ce mai son cimma duk wani abu da ta sa a gaba.
A cikin dictionary ɗinta babu kalmar impossible. Akoda yaushe slogan ɗinta shine *it's possible but.... HOW*
Kafin ta bar office ɗin MD sai da ya ce ta drafting tambayoyin da za ta yiwa Gwamna ta kawo mishi kafin a tashi...
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
05
Tunda Gwamna SSK ya zauna ya ke sauke numfashi akai-akai saboda maganganun Baffan na sa daya saka mishi rashin nitsuwa har ya ji ƙirjinsa ya cunkushe. Ƙarshe hannu ya sa a aljihu ya lalumo inhaler yai saurin jijjigata sannan ya kai bakinsa ya matsa.
Alhaji Sani ya sassauta muryansa ya ce "sannu Saifu. Har yanzu yana damunka sosai ne?"
"Nagode Baba" abinda ya iya faɗa kenan
Alhaji Sani bai matsa da cigaba da maganar da su ke ba ganin SSK yana buƙatar hutu sai dai kafin su rabu ya jaddada ma sa cewa tabbas zai kai ma sa ziyara zuwa office ɗin sa gobe.
Bayan Gwamna ya bar Kachallah house kai tsaye gidansa ya wuce dan har yanzu ba su koma gidan Gwamnati ba saboda gyararraki da ake yi.
Bayan wannan dogon rana ba abunda ya ke buƙata irin bacci cikin kwanciyar rai amma yana isa falonsa ya iske Bilkisu tana zaman jiran sa.
"Excellency Darling" ta faɗa tana manna ma sa kiss a kumatu.
"You're just here on time, yanzu na gama parking kayanka. May be mu je ka gani ko akwai abubuwan da za ka buƙata"
"Parking?"
"Dont tell me ka manta jibi Asabar za mu koma Government house"
"An gama gyaran ne?" Gwamna ya faɗa yana zama a kan kujera
"Darling yaushe ka fara mantuwa ne. Jiya fa na ke gaya maka an gama gyaran gidan za mu iya shiga yanzu"
"Bilkisu ki miƙo min ruwa mai sanyi please"
Sai da ta ɗan tsaya kaman mai shirin shawara da zuciyarta kafin ta miƙe. Ya sani da a falon ƙasa su ke sai dai ta kira ma sa Hansa'u ko ɗaya daga cikin ma su yi mu su aiki.
Ko da ta kawo ruwan ba ta barshi ya sha da daɗin rai ba ta cigaba da maganar komawar su gidan Gwamnati.
"Hansa'u da Uwaji za su bimu, sauran za su zauna a nan tunda dai ba za a bar gidan kango ba"
Kallon da ya ke mata kallon ki barni na huta ne amma ita Bilkisu sam ba ta karanci hakan ba. Sai ma cewa da ta yi "ko akwai wanda ka ke so a tafi da su bayan su Hansa'un?"
Bai amsa ma ta ba, sai ma kauda zancen da yai da cewa "ina yarana?"
"Duk sun yi bacci. Mahira ma ta dawo yau da yamma"
Gwamna ya miƙe tsaye yana faɗin "sai da safe"...
***
"Ya Ubayd ina tsoro, mafarkin danayi jiya ya tsoratani sosai"
"Wani mafarki kenan?"
"Na yi mafarki wai..." sai kuma ta yi shiru. Ta ina za ta fara ce ma sa ta yi mafarkin marigayi Kakanta Gwani yana ɗaura aurenta da Gwamna Saifudden Kachallah. This is absurd ai, ba abune da ya ke da daɗin faɗa ba. Balle ta san halin kayanta da shegen kishi.
"Ance ba kyau faɗin mummunan mafarki dan haka ka barshi kawai"
"Yau kuma?" Ya faɗa yana taɓe baki
"Mu bar zancen kawai. Ya maganan aikin kitchen ɗin nan an saka sink ɗin nan kuwa?"
"An gama Yallaɓiya. Kin matsu ko? Saura wata huɗu da kwana ɗaya tak"
Yana maganan ta ji ƙirjinta ya buga hakan ya sa ta yi saurin faɗin "Insha Allah" shima Ubayd ɗin ya maimaita kalmar.
Bayan sun gama hira da Ubayd ta shiga ɗaki ta iske Umma na duba wasu kulolin abinci. Umma na ganinta ta mata magana da hannu akan ta zo ta duba kulolin ko sun yi kyau. Asiya ta zauna tana dubasu tareda faɗin kulolin sun yi kalan 'yan ƙyauye.
"Umma ni ban san miyasa kike siyan kaya a wajen Laraba dillaliya ba. Ga kayanta tsada gashi ba wani kyau ne da su ba. Indai ni kika siyawa gara ki mayar mata dan ba su min ba" ta ƙarisa maganar tana turo baki
Umma ta taɓe baki tana kallon Asiya.
"Allah Umma ko kin saka a kayana kyautar da shi zan yi, dan wannan kulan ba zai zauna a dining table ɗin gidana ba ehe"
Umma ta yi murmushi sannan ta mata bayani akan gudummawar da ta ke son bayarwa 'yar maƙotan su da za a aurar ne nan da sati biyu.
"Yanzu na ji batu Umma na" ta yi maganar tana rungume Umman ta...
Yau ma dai mafarkin data yi ne ya tasheta daga bacci, abin mamaki irin mafarkin jiya ne sai dai wannan karan Gwani ya haɗa hannunta dana Gwamna yana ma ta nasiha akan mahimmancin haƙuri da kuma yarda da juna a rayuwar aure.
Ba ta cika yin mafarki ba hakan ya sa a mafiya lokuta idan ta yi mafarki za ka ga abun yanada nasaba da rayuwarta.
"Allah ka sa wannan mafarki ba gaskiya ba ne. Ubayd na ke so ya Allah" ta faɗa a hankali tareda sauke ajiyar zuciya sannan ta koma ta kwanta sai dai bacci ya gagareta...
***
Asiya ta fito daga kitchen a fusace saboda ruwan wankanta da aka juye.
"Wani marar imanin ne ya juye min ruwana?"
"Waye a banɗakin nan ne?" Ta faɗa tana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin kaman za ta ɓalla shi.
"Mutum ya tashi da Asuba ya saka ruwa azo a juye ma sa, a hakan ba za a saka masa wani ba. Koma waye yau sai ya biyani ruwana"
Kusan minti uku sannan Hindatu ta buɗe ƙofa ta fito ɗaure da zani.
"Miye ne kike ta buga ƙofa kamar wata sabuwar mahaukaciya"
"Ke ce mahaukaciyar ai. Na saka ruwa a heater kin zo kin juye min saboda tsabar iya shege"
"Dama akwai wanda ya kafa dokar idan kana gidan ubanka sai ka nemi izinin Agola kafin ka yi amfani da abun gidan ne?"
Asiya ta buɗe baki za ta yi magana amma ta fasa saboda ɓata lokaci ne biyewa Hindatu da sassafen nan. Ba ta san mi ta tsarewa wannan Hindatun ba. Ta rasa kishi ta ke da ita ko kuma haka kawai tsantsar ƙiyayya ce.
Banɗakin ta shige ba tareda ta tankawa Hindatun ba, ta fito da bokiti ta je ta ɗebo ruwa mai sanyi. Kafin ta ce za ta haɗa wuta ta ɗaura wani ruwan wankan lokaci zai tafi dan haka kawai ta daure ta zo ta yi wanka da ruwan sanyi. Tana fitowa kuwa da gudu ta je ta shige ɗakin su ta kullo ƙofar da ƙarfi
Umma ta kalleta ta ce lafiya? da hannu
"Sanyi Umma" ta amsa tana ƙarisawa wajen jakar kayan kwalliyarta.
Ƙarfe bakwai saura kwata Asiya ta fito daga gidansu sanye da wandon jeans blue, baƙin riga sai farin blazer jacket da ta saka sannan ta yane kanta da light blue gyale. Keke ta nema ta wuce ma'aikatar su.
Tana zuwa office ta fara duba tambayoyin da ta tsara wanda jiya da daddare MD ya kirata ya ce ta ƙara da tambaya ɗaya wato miyasa Gwamna ya naɗa tsohon Kwamishinan ayyuka Alhaji Bala Yamai a matsayin mataimakinsa.
Kusan komai ya tafi daidai. Zuwa ƙarfe tara Asiya da CY su ka kama hanya zuwa gidan Gwamnati.
Lokacin da su ka zo an ajiye su a waje na musamman kafin Gwamna ya fito.
A cikin ofishin Gwamna kuwa COS ne ya ke ganawa da Gwamna.
"Your excellency ina so ka dai sake tunani akan wannan lamari, yanke wannan allowance ɗin dai dai ya ke da fushin cabinet members ɗinka"
"Wani ɓangare ne cikin magana na baka gane ba?. Kana sauraron kanka kuwa?. For God's sake bayan ɗimbin ayyukan da ke gaban mu har kuna da zuciyar da za ku tambayi wani allowance"
"Excellency wannan allowance ɗin tun kafin administration ɗinka ake bayarwa idan ka ce ba za ka cigaba da bayarwa ba za a samu matsala"
"Look Mr Damana. Ba zansa hannu a wannan ɗimbin kuɗin ba bayan munada abubuwa dayawa a gaban mu. Ka ƙara jaddadawa Mr Paul cewa bazan biya kuɗin nan ba. Now please leave my office"
COS ya miƙe jiki a sanyaye.
Bayan fitan COS Gwamna ya kira Sakatare
"Malam Baffayo ka haɗa meeting da Contractors ɗin nan ƙarfe goma"
Sakatare yai saurin cewa "Excellency akwai hiran da za ka yi da 'yar jarida daga Hill TV ƙarfe goma, sun ma iso lokaci su ke jira"
Har zai ce a ce su dawo wani lokaci sai kuma ya fasa yace ya maida meeting ɗin sa da Contractors ɗin ƙarfe goma da rabi saboda minti talatin kacal zai yi da su Asiya.
Asiya na tsaye tana yiwa CY magana Gwamna da tawagarsa su ka iso.
Ganin CY yayi saurin miƙewa ya sata juyawa ba shiri.
"Your excellency Sir" CY ya faɗa yana murmushi. SSK ya miƙa ma sa hannu CY yai saurin saka hannu biyu ya damƙi hannun SSK yana faɗin " myself Clement Yohanna"
"Welcome Mr Yohanna" sannan ya miƙawa Sunusi hannu dreban daya kawo su Asiya.
"Allah ya ja zamanin Gwamna. Allah ya kare ka, Ubangiji ya maka jagora" Sunusi ya dinga sunbatu kamar zai haɗiye Gwamna saboda farin cikin sun yi musabaha da Gwamna SSK.
Tunda Asiya ta juya ta ganshi bakinta ya kafe. Yadda kasan an tura mata dunƙulen Auduga a maƙoƙoro haka magananta ya toshe ya ƙi fitowa. Sau ɗaya su ka haɗa ido amma gaba ɗaya ta rasa nitsuwarta. Kaifin idanunsa gareta sun karya ma ta duk wata laka da ke jikinta. Abin mamaki wai ita Asiya-Shahidah da ta ke iƙirarin ba mutumin da ba za ta iya magana a gabansa ba sai gashi kusan minti biyu da zuwan Gwamna wajen ta kasa ko da gyaran murya ne. A baya duk lokacin da aka yi maganar ƙwarjinin SSK ƙaryatawa ta ke yi sai gashi yau ta gani a zahiri.
Bayan Gwamna ya gama darawa bisa surutun Sunusi da CY sannan ya maida hankalinsa ga Asiya.
*"Asya?"* Ya kira sunanta da sigar tambaya
Ji tayi jiri yana shirin kwasarta a wajen saboda irin yadda taji wani abu ya ratsa jijiyoyin jikinta lokaci guda. Taya ma zai iya kiran sunanta da daɗi haka?
Ta yi kusan sakan goma kafin ta iya haɗiye koma minene daya toshe mata maƙoƙoro ta ɗan yi ƙaramar gyaran murya sannan ta ce " your excellency, Asiya Shahida Faruƙ Baba"
"Of course. The famous Asya ta tashar Hill tv"
"Sit" ya faɗa yana nuna mu su kujera. Sai da ya zauna kafin suma su ka zauna
"Wannan location yayi ko za a chanja wani?"
CY yai caraf ya amsa da cewa "yayi your excellency. Barin saita camera sai a fara ɗaukan hiran"
Da rawar jiki CY ya miƙe ya fara saita camera yayinda Asiya ta sunkuyar da kanta ƙasa tanajin kamar idanun Gwamna yana yawo a duk ilahirin jikinta. Sai yanzu ta yi dana sani da hijabi ta saka ba gyale ba.
Kusan minti shida kafin CY ya gama saita komai ya ɗagawa Asiya hannu yana faɗin one, two.... "ina zuwa CY" ta faɗa sannan ta yi saurin ɗaukan ruwan da aka kawo mu su ta tsiyaya a kofi ta kafa kai sai da ta shanye. Ta sake tsiyaya wani ta shanye.
CY ya ɗaga gira sama yana faɗin "Aseey are you nervous?"
Asiya ta yi saurin girgiza kai tareda yin gyaran murya ta ce "muje, na shirya "
CY na ɗaga ma ta hannu ta tattaro duk ƙarfin halinta ta fara bayani kamar haka *"ma su kallon mu barkar mu da warhaka, barkan mu da sake saduwa da ku a cikin shirin nan mai suna 'Siyasar mu a yau'. A yau dai za ku ga sauyin tsari, domin shirin namu kwacokam zai