Author : Azizat Hamza Category : Top Hausa Novels 2025
kawo muku hira ne da wani shahararren ɗan boko, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wato mai girma Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah inda zai bamu cikakken tarihin rayuwar sa da yadda aka yi har ya kawo wannan matsayi. Ni Asiya-Shahidah Faruƙ Baba zan gabatar da shirin a madadin abokin aikina wato Comrade Faisal Kamaye"*
Sakataren Gwamna ne ya ƙariso wajen da sauri ya ɗan rankwafa yai wa Gwamna magana a kunne. Hakan ya sa C Y ya dakatar da ɗaukan shirin.
Gwamna ya kalli Asiya ya ce "za'a dakatar da shirin zuwa ƙarfe shaɗaya Insha Allah"
Bayan Gwamna ya tafi sannan Asiya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda fara yiwa kanta fiffita da hannu dan duk iskar wajen ta mata kaɗan.
CY ya matso wajenta yana yi mata dariya tareda tsokanarta kan cika bakin da tayi kafin zuwansu sai gashi ganinta kusa da Gwamna ta ruɗe.
Tun suna jiran Gwamna zai dawo ƙarfe shaɗaya har su ka fara sarewa ganin har ƙarfe ɗaya saura.
"CY anya ba za mu tafi ba. It seems wannan Gwamnan ya manta da mu fa"
Kafin CY ya bata amsa Sunusi driver yai saurin ɗaga murya da cewa ko ƙarfe nawa ne za su jira Gwamna tunda ya ce su jira shi.
"Bar Aseey, tana mana baƙin cikin kyautan da Gwamna zai mana ne" CY ya sa baki.
"Wannan maƙon ne zai baku kyauta?. Keep dreaming Clement".
"Allah idan aka bamu banda ke aciki tunda naga adawa ki ke da Gwamna" Sunusi ya faɗa yana ƙarisa sauran maltinan da Asiya ta rage.
Bayan Gwamna ya bar wajen su Asiya kai tsaye office ɗinsa ya wuce inda Alhaji Sani Kachallah ke jiransa. Idan ba shi ɗin bama waye zai shiga office ɗin Gwamna kai tsaye haka bayan Gwamna baya zaune a kujera.
"Baba sannu da zuwa" SSK ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa. Bayan sun yi musabaha sannan ya je ya zauna a kujerarsa yana kallon Alhaji Sani. Sun gama maganar naɗa mataimakin Gwamna tunda ya naɗa wanda su ke so bai san kuma mi ya kawo sirikin nasa office ɗinsa ba wannan safiya.
Bai yi mamaki ba da Alhaji Sani ya kawo maganar allowance na cabinet members daya riƙe. Sai dai duk da kunyan Alhajin daya ke ji hakan ba zai sa ya aiwatar da wannan baɗala ba.
"Baba tunda na hau kujeran nan na ke tsoron haƙƙin mutane da ke kaina. Idan na basu kuɗin nan tamkar na ci amanar wannan Jaha ce. Bayan ɗimbin albashi da sauran allowance da doka ta tanadar a basu miyasa zan sake ɗaukan maƙudan kuɗi na basu bayan akwai tarin ayyuka a gabana"
Gwamna yayi maganar ne a sanyaye saboda darajar Alhaji amma idan da zai fidda tiriri da zuciyar sa ke yi to ba ƙaramin amon wuta zai yi ba.
"Saifu kenan. Kaga siyasa lamari ne daya ke buƙatan hankali da takatsantsan. Kwata-kwata abun da za ka yi a wannan kujera kafin a sake wani zaɓe bai kai shekara ɗaya ba. Idan kuwa hakane dole ne ka tafi da mutanen nan yadda aka riga aka ɗaura su akai. Idan muna da rai kaci zaɓe sai ka fara naka sabon tsarin"
Gwamna yai shiru yana kallon Alhaji Sani. Yadda yai maganar cin zaɓe ya bashi mamaki. Domin zaɓe dai ba ayi ba balle a san ko zai koma kan kujerarsa ko ba ze koma ba.
"Baba da kamar wuya. Kuɗin sun yi yawa"
"Ka biya kaso 70% na kuɗin"
Gwamna ya tauna leɓensa na ƙasa tareda sauke ajiyar zuciya. Yadda Alhaji Sani ya shawo kansa akan maganar naɗa Bala Yamai a matsayin Mataimakin Gwamna baya tunanin wannan karanma zai bar ofishinsa har sai ya samu abinda ya ke nema.
"Zan biya su kaso 40%"
Alhaji Sani ya ɗan ɗaga ido sama na ɗan daƙiƙu kafin ya sauke akan Gwamna Saifuddeen ya ce "mu rufe shi kaso 50% Saifu".
Bayan fitan Alhaji Sani daga office ɗin Sakatare ya shigo ya sanar da shi Contractors da za ayi meeting da su sun iso. Gwamna ya miƙe ya fita.
A chan wajen meeting ɗin ma wani ɓacin ran ya tarar domin kusan kaso saba'in da biyar na ayyukan da marigayi Gwamna Saminu Bacchi ya fara duk akan bashi ne. 'Yan Kwangila suna son a biyasu kuɗaɗen su idan ba haka ba sun dakatar da duk wasu ayyuka har sai baba ta gani.
Gwamna ya duba COS ɗinsa sannan ya maida dubansa ga Mr Paul. Waɗannan biyun sun fi kowa ɗaga jijiyar wuya akan maganar allowance amma yanzu ana maganar ayyukan cigaba na Jaha amma kowannen su yayi tsit.
Kuɗin allowance ɗin nan da su ke buƙata idan da za a haɗa na wata huɗu zai biya gaba ɗaya basussukan da contractors ɗin nan su ke bin Gwamnati.
Haƙuri Gwamna ya basu tareda mu su alƙawarin zai biyasu dukkan kuɗaɗen su zuwa wani watan sai dai wannan wata za su fara ne da kaso 25% na kuɗin da zai biya su. Basu ɗau lokaci ba suka amince da maganar Gwamna.
A take a lokacin Mr Paul ya miƙa masa wasu takardu tareda check Gwamna ya saka hannu sannan aka miƙawa jagoran contractors ɗin wato Mr Azad Sahib Khan.
Gwamna na komawa kan kujerarsa Mr Paul da COS suka biyo bayansa da takardar da suke son ya saka hannu. Gwamna ya duba takardan a walaƙance sannan ya kalli fiskar Mr Paul wanda ƙarara ta nuna bai ji daɗin kaso 50% ɗin da za a basu ba ya ce " Mr Paul ina fata baka manta maganan ƙarin albashin malaman makaratan firamare ba"
"Your excellency na sani"
"Good".
Kusan ƙarfe biyu saura kwata da Gwamna zai fita sallar Azahar Sakatare ya tuna masa da su Asiya da ke jiransa tun ƙarfe goma.
Gwamna ya girgiza kai ya ce su dawo gobe dan akwai inda zai je idan yayi sallah.
Idon Asiya ɗar akan wayarta lokacin da wani security ya iso ya ce musu Gwamna ya ce su dawo gobe ƙarfe goma.
"Kan Uba..."
"Mungode zamu dawo gobe ɗin" CY ya faɗa yana hararan Asiya.
Har suka isa ma'aikatarsu Asiya bata bar zagin Gwamna ba kan walaƙantasu da yai. Har iƙirari ta yi akan gobe ba za ta koma ba sai dai Comrade Faisal ya je yai tunda dama asali shirinsa ne. Sai dai MD bai bata damar hakan ba dan cewa yai ita ɗin dai yakeso tayi hiran da Gwamna goben.
Da dare da Ubayd ya zo hira kaman ta shaƙeshi dan yadda ta ke masifa tamkar shine Gwamnan.
"Mine, sunana Ubaydullah ni Likitan Ido ne ba Gwamnan Jahar Congo ba. Ki ajiye fushinki a gefe please"
"Dan shi Gwamna ne sai akace ya maidamu Awakai. He treat us like goats fa. Ya shanya mu for good 4 hours munata jiransa"
"My Asiya Gwamna fa akace. The first citizen of the state"
"And so bloody what!"
"Shikenan. Yayi haka a chanja hiran"
"Da wani shegen idonsa a wajen..." ta ƙarisa ƙarshen jimlar a hankali saboda wani abu da ya zo ya dabaibayeta. Idon da ta ke zagi shi dai ta gani yau ta birkice, ta rasa nitsuwarta. Idon ne dai da ya ke sukanta kamar kibiya lokacin da ta ke zaune daura da shi kafin CY ya gama haɗa camera.
Ba ta gayawa Ubayd wannan ba ƙila shiyasa ta dage kawai akan cin mutuncin da Gwamna ya mu su. Sai da Ubayd ya sako zancen kayan lefenta da yake haɗawa kafin ta ture maganan Gwamna a gefe ta koma ta rayuwar da su ke shirin farawa tare nan da watanni kaɗan.
***
Taron gaggawa Mr Paul ya kira a gidan Yallaɓai tunda suka haɗu kuwa aketa cacar baki sai da Yallaɓai ya tsawatar kafin sukayi shiru.
"Mr Paul ina sauraronka"
Mr Paul ya ɗaga takardar da Gwamna SSK ya sa hannu yace "Yallaɓai tunda Saminu Bacchi ya hau kujera bai taɓa chanja tsarinmu ba amma gashi nan wata biyu da hawan Saifuddeen ya hanamu allowance lokacin da ya ga daman bamu kuwa kaso hamsin ya bayar. Ka gaya min ta ina zamu yarda da wannan cin mutunci. Idan har ba zai iya ba to kuwa yai resigning a ɗaura Bala Yamai"
"Ka ci gidanku Eugene Paul. A gabana kake cewa Saifu yai resigning saboda baka da hankali"
"Alhaji Kachallah ka kama girmanka, ka san bana yarda da cin mutunci a gidan nan"
"Ayi haƙuri Yallaɓai amma Paul ya sani cewa an ɗaura Bala Yamai ne ba dan shi ba sai dan kawai lokacin saka mutumin Agun ne a matsayin mataimakin Gwamna. Ya kamata kuma ya sani cewa ba zan lamunta a ci mutuncin ɗana ba"
Bayan duka ɓangare biyu sun gama gabatar da ƙorafinsu sannan Yallaɓai yai magana.
"Kowani Gwamna muna bashi wata shida dan ya aiwatar da abinda ya ga dama a farkon tenure da kuma ƙarshen tenure ɗinsa. Lokacin Saifuddeen ne yanzu, Mr Paul ka barshi yai abinda yake so"
"Amma..." Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu hakan ya sa shi datse maganarsa.
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
06
Washegari Asiya ba ta shirya da wuri ba dan sai takwas da rabi ma ta fita daga gida. So take MD ya tura Comrade Faisal da CY gidan Gwamna amma kash! MD ya nace sai ita ɗin zata je. Yau kan maimakon riga da wando data saba sakawa Atamfa ta saka riga da skirt da ƙaton mayafi daya kai mata gwiwa. Shikansa MD sai da yai wa Asiya kallon mamaki ganin shigar da ta yi, rabon da Asiya ta yi shigar Atamfa zuwa office har ya manta. Suna tafiya a hanya CY ya dinga tsokalarta wai tayi shigan matan aure. Asiya bata kulashi ba dan gaba ɗaya gabanta faɗuwa yakeyi, ta rasa dalilin hakan kuwa.
Koda suka isa gidan Gwamnati ƙarfe goma saura minti shabiyar. Wajen da aka ajiyesu jiyan dai nan aka sake zaunar dasu. Basufi minti goma da zuwa ba fitsari ya kama Asiya, cikin ranta sai dana sanin shayin da ta sha kafin su fito take. Ƙarshe data ga abin zai dameta ta miƙe ta tafi wajen wata mata da ke da office a corridor ɗin lobby ta tambayeta ina ne banɗaki, matar da keta tauna cingam kamar zata haɗa da harshenta tayiwa Asiya kwatance tana haɗe rai, Asiya ta wuce tana mamakin matar da fiskarta ya gama soyewa saboda bleaching.
**
"Na san ka san matsayinka a wannan Jaha. Kuma ka san baya daga cikin ayyukan ka abinda ka aikata"
"Your excellency..."
Gwamna ya ɗaga masa hannu ya cigaba "kar hakan ya ƙara faruwa Mr Lamara Damana. Matsayin Chief of Staff zai iya faɗawa hannun kowa nan gaba. Ina fata ka fahimta"
"Yes your excellency. Hakan ba zai sake faruwa ba da yardar Allah"
"Good. Now ka duba min ko kwamishinan ayyuka ya fara aikin da aka bashi"
Lokacin da COS ya fita Gwamna ya jawo takardar da ya ajiye ya kekketata sannan ya watsar. Ba zai taɓa lamunta da wannan ba. Fitar COS keda wuya Sakatare ya shigo ya sanar da Gwamna cewa 'yan jaridan jiya sun dawo.
COS na shiga office ɗinsa ya cillar da file ɗin hannunsa takardun ciki suka watse. Ya dunƙule hannunsa kamar mai shirin dambe, ya kira sunan Gwamna da ƙarfi "Saifuddeen Kachallllaaaaah!"
Yana cikin huci ya tuna da wani abu nan da nan yai saurin lalubo wayarsa a aljihu ya shiga danna kira, ba aɗauka ana farko ba sai a kira na biyu.
"Akwai matsala Kachallah" abinda ya fara furtawa kenan da kakkausar murya. Bai bari wanda yake maganar ya ƙarisa ba ya katse shi da cewa " har Gwamna zai yi iƙirarin cireni a matsayina. Ya manta ne? Ya manta ne?"
Yai shiru yana sauraron bayani daga ɗaya ɓangaren sannnan ya ɗaura da cewa
"idan har bai san yadda akayi aka ɗaura shi akan kujera ba to kuwa lallai ƙaddarar da ta hau tsohon Gwamna za ta sameshi. Ta inda aka hau tanan fa ake sauka Kachallah... eh inaji.... sai dai abu ɗaya na sani idan har Saifuddeen ya cireni a matsayina saina gayawa duniya cewa Saifuddeen Sa'ad Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna..."
Saura kaɗan recorder da ke hannun Asiya ta faɗo saboda firgita da tayi. Tayi saurin toshe bakinta saboda kar mutumin da take naɗan maganarsa ya jiyo nishinta. Ta fito daga banɗaki kenan za ta koma inda aka ajiyesu ta hango Chief Of Staff ya zo ya shige wani lungu a bircike. Curiosity nata na 'yar jarida ya sa ta bi bayansa. Wani office taga ya shige hakan ya sa ta bi bayansa da zimmar ko za ta iya gano dalilin fushinsa tunda hanyar da ta ga ya fito tanan ne office ɗin Gwamna, koma minene ya ɓata masa rai yanada nasaba da Gwamna ɗin.
Ihun da ta jiyo COS yayi yana kiran sunan Gwamna yasa ta laɓe ta fidda ƙaramar recorder ɗinta ta fara naɗan maganar sa.
Ganin yayi shiru yana sauraron bayanin da ake masa ya sa tayi saurin jan jiki ta bar bakin ƙofar.
Ba ta ji ƙarshen maganar sa ba.
"Eh...ina sane amma... shikenan zan kiyaye sai dai gara a nuna masa cewa mune muka buɗa masa hanya har ya samu ya hau kujeran, idan aka cigaba da ninke shi a baibai zai yi abinda zai jawo masa dana sani... to shikenan zamu haɗu idan na tashi a office"
Da ƙyar Asiya ta iya komawa wajensu CY dan a tsorace take, abinda ta jiyo ya girgizata matuƙa yayinda tsanar Gwamna Saifuddeen ya dira a zuciyarta, dama ya aka ƙare balle kuma...
Ta samu CY na faman saita camera, shi da Sunusi suna taɗi shiyasa hankalinsu bai kai gareta sun lura da chanjawar yanayinta ba.
Bayan minti biyar sai ga Gwamna ya iso fiskarsa ɗauke da annuri. Kallon tsana Asiya ta bishi da shi tana ji a ranta kamar ta shaƙeshi ya mutu kawai.
Maimakon jiya da za a naɗi shirin sannan a editting na shi kafin a ɗaura a tasharsu yau kam live za a saka shirin a gidan talibijin na su.
Yau kam ba kamar jiya ba babu tsoro ko fargaba a tattare da Asiya, cike da nitsuwa ta fara gabatar da shirin. Tambayoyin da aka amince ta masa su takeyi sai da aka kai tsakiyar shirin sannan ta sako zancen tsohon Gwamna wanda ba Gwamna kaɗai ba hatta CY sai da ya sha jinin jikinsa da tambayar
"Gwamna Saifuddeen duba da yadda mutuwar tsohon Gwamna ya zo bagtatan ko za ka iya sanar damu yadda mutuwarsa ta zo maka?" Tambayar offscript ne baya cikin jerin tambayoyin da akace za a masa shiyasa ya ɗan ji abin banbaraƙwai amma ya dake ya amsa da cewa.
"Kowanni halitta dake doron ƙasa sai ya ɗanɗani mutuwa. Dukkanmu lokaci muke jira. Haƙiƙa mutuwar tsohon Gwamna ta girgizani matuƙa saboda yadda ya zo mana lokaci guda..."
"Excellency baka ganin ya kamata a duba mutuwar tasa kodai akwai lauje cikin naɗi duba da cewa Gwamna nada 'yan adawa dayawa"
Ba dan shirin kai tsaye aka ɗaura shi ba da CY tuni ya katse ɗaukan shirin saboda yadda Asiya take chanja alaƙar shirin nasu.
Gwamna ya kalleta cikin zargi amma bai bari hakan ya bayyana a fiskarsa ba yace " Malama Asya mutuwa koda ciwo ko babu ciwo sai anyita. Likitoci sun tabbatar da cewa hawan jini ne yai ajalin tsohon Gwamna Allah ya jiƙan rai"
"Ya yanayin alaƙarka da shi kafin rasuwarsa?"
"Munyi zama na amana da shi, Allah ya gafarta masa kurarensa da ma namu gaba ɗaya"
"Amin"
"Tambayata ta gaba ko miyasa Gwamna ya zaɓi Alhaji Bala Yamai a matsayin mataimakinsa duba da cewa ana zarginsa da cin hanci da rashawa har ma shekarun baya hukumar EFCC sun kama shi?"
Kafin Gwamna ya bada amsa daga chan ma'aikatarsu aka katse shirin aka saka talle saboda a samu daman katse ɓaranɓaramar da Asiya ke yi.
"Jesus! Aseey lafiyanki kuwa?"
CY ya faɗa da ɗan ƙarfi, kafin ta bashi amsa MD ya kirata tana ɗauka ya shiga surfa mata masifa kaman zai zo wajen ya bindigeta. Tana ajiye wayar tareda sauke ajiyar zuciya ta haɗa ido da Gwamna. Duk da tsanar da take masa hakan bai hana tasirin kallon sa gareta ba.
"Yaudara na ɗaya daga cikin abubuwan da na ke ƙyama. Miss Asya na yarda da wannan interview ne saboda babu maganar siyasa a cikinta, kar ki manta da wannan"
A yadda ransa ya sosu da abinda tayi niyyarsa ya miƙe ya bar wajen saidai idan har yai haka ya sani daga lokacin 'yan jarida zasu murɗa labarin da cewa Gwamna ya ƙi amsa tambaya saboda bashi da gaskiya. Ya sani Alhaji Bala Yamai ba shine candidate ɗin daya so ya zama mataimakinsa ba sai dai kamar yadda Alhaji sani ke yawan faɗa masa cewa a siyasa dolene ka yi abinda bature ke kira compromise. Ba zai manta lokacin da Alhajin ya kirashi ya ce masa mataimakinsa shine Alhaji Yamai ba. Ya faɗi maganar kamar bashi da zaɓi, kamar ba shine mai ikon naɗa duk wanda yakeso ba.
"Alhaji Yamai yanada record na rashawa, Baba" ya faɗa da murya mai sanyi.
"Ka zo gida muyi magana" Alhaji Sani ya faɗa. Koda ya sameshi a gida bayani ya masa wanda hakan ya birkita shi har sai da asthma ɗinsa ta fara barazanar tashi.
Ya sani tun kafin ya kawo wannan matsayi Alhaji Sani Kachallah yana ɗaya daga cikin wanda suke riƙe ko yace suke juya jahar Congo. Tun zamanin mulkin soja ake damawa da shi har aka dawo mulkin farar hula.
"Mutane huɗu ne keda alhakin zaɓan Gwamna da Mataimakinsa. Wannan karan ɓangarena ne da Gwamna, ɓangaren Mataimakinsa yana hannun ɓangaren Yellow Group kuma sun zaɓi Alhaji Yamai. Kar ka damu, Alhaji Yamai hoto zai zama kawai" yadda Alhaji Sanin ya faɗi kalmar hoto sai ya tuna da yadda shima watannin baya yake kamar hoto a matsayinsa na mataimakin Gwamna. Ya so yaja da hakan amma bai samu ƙwarin gwiwar yi ba. Tun lokacin da Alhaji Sani ya gabatar da shi a jam'iyyarsu ya sanar dashi ma'anar tutar Jahar Congo. Kalar Baƙi da ta fi yawa a jikin tutar ita ke ɗauke da kaso 45% wanda Yallaɓai ke shugabanta yayinda kalar Blue ke ɗaukan 25%, kalar Red ta ɗauki 18% sai Yellow 12%.
kalar blue ta Alhaji Sani Kachallah ne hakan na nufin da shi ake damawa a Gwamnati, hakan na nufin Saifuddeen ba shi da ikon yin komai sai da yardar sa.
Yanzu da aka dawo daga tallen da aka saka wanda ta kai kusan minti takwas bai ɓata lokaci ba ya amsa tambayar Asiya da cewa ya