THE GOVERNOR'S-MATAR GWAMNA --Document Complete .txt

Author :  Azizat Hamza Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   19 / 21

54K to 57K   out of 62.2K words

ya yiwa Asiya alƙawarin binciko mata abin da take nema cikin ƙanƙanin lokaci...






Asiya na zaune akan kujera ta harɗe ƙafafuwanta, hannunta ɗaya riƙe da waya tana karatu, ɗayan kuma soyayyiyar gyaɗa take ci da shi. Lokaci lokaci ta kan yi dariya. Wannan karan da ta fara dariya harda tunkuɗe kwanon gyaɗa da ke gefenta.






Sumayya da ke rubutu a kan carpet ta ɗago ido ta kalli 'yaruwarta tana tambayarta ko lafiya. Sai da Asiya ta yi dariya ta isheta kafin ta ce "wani waƙar KaSaSa nake karantawa wai Attaruhu, kin ji abin dariya. Kai matar nan Allah ya bata baiwar tsara waƙa. Bari ki ji na karanta miki..."






Sallamar Uwani ya katseta. "Ranki shi daɗe kinada baƙi a falo"






"Su waye?"






"Yaya Bello ne da wani tsoho"






Asiya ta kalli Sumayya, Sumayya ta kalli Asiya, dukkansu suka haɗa baki wajen faɗin "Ale".






Asiya ta sako hijabi ta fito yayinda Sumayya tace fir bazata fito ba. Ale na zaune yana kora lemu Asiya ta shigo falon.






"Matar Gwamna" Ale ya faɗa da ƙarfi kaman wani Yaro.






Asiya ta haɗe rai ta zauna nesa da su tace "Baba lafiya?"






"Haba Asiya Shahidan Baba. Babu gaisuwa sai tambaya"






"To ai ni ban taɓa jin inda aka yi aure sati biyu Baban Amarya ya fara bibiyar 'yarsa ba, sai dai idan babu lafiya ne"






"Lafiya ƙalau muke, su Baffanki ma sun ce na gaisheki"






Yaya Bello ya miƙe yace "barin barku ku tattauna"


Asiya ta harareshi dan ta san shine zai yiwa Ale kwatancen gidanta. Sai kuma ta tuna Ale da Yaya Bello basa shiri.






"Tunda na miki maganar kwangila kika dena ɗaukan kirana. Haka ake yi, ko kin shigo daula kin manta da iyayenki ne"






"Ban manta da iyayen da tunda nayi aure suke aiko mani da addu'a ba. Amma na manta da Uban da ke maula a wajen mijin 'yarsa"






"Asiya!" Ale ya faɗa yana miƙewa a fusace.






Basu ji shigowar Gwamna falon ba sai da yai sallama.


Asiya ta kalleshi ta kauda kai yayinda Ale ya shiga gaishe shi jiki na rawa.






"Asya" ya kira a hankali. Ta ɗago ido ta kalleshi


"Follow me"






A tsakiyar falonsa ya tsaya, ya juyo ya kalleta. Yana tattare da fushin Bilkisu da Nana abinda ma ya hana ya fara wucewa chan gidan kenan, ya biyo nan ne saboda ya ɗan huce kafin ya je gida, kada garin fushi zuciyarsa ta sa shi aikata abinda bai dace ba. To gashi ya zo nan ma itama wannan Attaruhun tana yiwa mahaifinta rashin kunya.






"Disrespecting your father Asya. Kin san darajan Uba kuwa, kin san mutane nawa ne a duniya ke kukan rashin Uba. Ba zan lamunci wannan ba, ki je ki bawa mahaifinki haƙuri"






"Ba abinda zan yi. Ba a chanja Uba amma ni na chanja ranan da ya sayar maka ni. Idan ba zaka lamunta ba ka sake ni mana, ai kasan yadda nake sarai amma ka nace sai da ka aureni saboda zalin....ci"






Numfashinta sai da ya kusa ɗaukewa saboda matsowa da Gwamna yai daf da ita. Kallo ɗaya ta yiwa ƙwayar idonsa ta san babu wasa tattare da shi.






"Na gaya miki iya zaman da za mu yi tare dole ne ki riƙe matsayin Matar Gwamna da kyau, which means duk wani rashin kunya, shirme da shiririta za ki ajiye su gefe. Ki je ki bawa mahaifinki haƙuri kafin raina ya ɓaci"






Ai da sauri Asiya ta bar falon. Bata manta kashedinsa ba, daren farko da aka kawota gidan. Ya riga ya san abu ɗaya take tsoro, kuma da shi ne kawai zai iya maganinta.






Ale na zaune yana jujjuya maganganun Asiya a ransa, Asiya ta shigo falon.






"Kayi haƙuri Baba" Asiya ta faɗa ba tareda maganar ya kai zuciyarta ba. Ta tsani halin mahaifinta fiye da soyayyar da take mishi.






"Ya zan yi da 'ya'yan zamani. Allah ne ya baki wannan matsayi Asiya, ni ba sayar da ke nayi ba.






"Na ji daɗi da kika kawo Bello kusa da ke, ina fata za ki nutsar da shi ya dena shaye-shaye, yai ƙoƙarin ajiye Iyali. Na barki lafiya"










"Baba" Asiya ta kira da muryar kuka.


Ale ya juyo ya kalleta jikinsa a sanyaye.






"Ka yafe min dan Allah"






"Na yafe miki, nima ki yafeni in Allah ya so ya yarda ba zan sake yi miki maula ba"






"Haba Ale Faruƙu na gidan Tabawa da Gwani Lukman. Ni fa ban ce kana maula ba, inaga dai daga TV ka ji wannan maganar"






Ta yi maganar tana kamo hannunsa ta zaunar da shi a kujera. Wani abu ta gani a idonsa lokacin da yai maganarsa ta ƙarshe. Bata taɓa tunanin Ale zai ji kunya ko yai danasanin wani abu ba, amma yau ta ga kunya a idonsa, ya yi danasanin neman alfarma da ya zo yi.






"Baba barin shiga kitchen da kaina na maka girki"


Ale yai dariya yace "Ina Sumayye? ko ta je makaranta"






"Barin kira maka ita".






Asiya ta shiga kitchen ta zage ta yiwa Ale girki. Tuwon shinkafa miyar kuka da ya ji naman kaza ta yi, ta haɗa masa da tacaccen juice ɗin Kankana da Abarba.






Ale ya ci abincin sosai ya kuma sa albarka. Da zai tafi ya ce ta gaishe masa da Gwamna ya ajiye mata kyautar da ya kawo wa Gwamna na tacacciyar Zuma a cikin jarka 5 liter.






Ga mamakin Asiya lokacin da ta shiga falon Gwamna sai ta sameshi a dining table yana cin abincin da ta girka.


Ta san dai ta ɗebi abincin Ale sannan ta barwa Sumayya ta kwashe sauran. Yaushe Sumayya ta haura sama ta kawo masa abinci bata sani ba?. Tukunnama dama tuntuni bai fita bane. Ita ba sanin ranakun ta yi ba balle ta gane yau kwananta ne ko ba nata bane. Bata taɓa masa girki ba, idan ya zo gidanta bata san ya yake cin abinci ba, bata ma san su waye ke gyara masa sashensa ba.






Gaskiyar Sha'awanatu Bacchi ne da tace dole ta koma gidan Gwamnati. Idan suka cigaba da zama irin haka ba zata rinƙa samun bayanai akansa ba.






"Babana ya wuce, ya bayar da wannan a baka"


Ta ajiye jarkar kusa da ƙafarsa. Bata san ya akayi ta tsaya kallon ƙafarsa ba, babu takalmi a ƙafarsa, jallabiya ya saka hakan ya sa zaman da yai ya bayyana silangarinsa da ƙafafuwansa. Ta kan ce Ya Ubayd na da marteten ƙafa, mai kauri, mai faɗi. Har tana tsokalarsa idan suka yi aure sai dai ya dinga saka safa saboda ƙafarsa ba ta da kyau.






Ta zubawa doguwar ƙafarsa ido, ƙafar a mulmule take da gani zai yi laushi, yanada dogin yatsu cike da baƙin gashi zara-zara da suka ƙarawa ƙafar kyau.






"Ƙafar ne yai miki kyau ko neman wajen da zaki ɗaura min jarkar kike?"






"Allah sawwaƙa, mi zan yi da baƙin ƙafa kamar na Burgu"










Murmushi yai har saida haƙwaransa suka fito. Asiya ta yi saurin ajiye jakar ta juya.






"Ki shiga min da shi ɗaki, Please"






"Ban san wanne ne ɗakin ka ba"






"Kin taɓa tambaya ba a nuna miki ba?"






"Zan nema da kaina"






Ɗakin farko da ta duba a kulle yake, na biyu ma haka, na ukun da ta shiga ta ajiye masa jarkar kusa da gadonsa. Ɗakin ya mata kyau sosai, tun daga design zuwa furnitures da aka saka.






Ta buɗe ƙofa kenan tayi kiciɓis da Gwamna zai shigo.


"Har kin gama ganin ɗakin?"






"Babu abun kallo ai"






"Na ɗauka za ki tsaya muyi wanka tare ai"






Yai maganar yana kanne mata ido. Ƙirjinta ya shiga lugude. Iya zaman da za ta yi da shi ba abinda zai shiga tsakaninsu, jikinta da ruhinta duk na Ubayd ne.


Ta tsane shi, daga nesa zata gama cika baki akansa amma yana zuwa kusa da ita ƙwaƙwalwarta sai ya juya ya fara kawo mata wasu tunani daban.






Matsawa yai ta fice daga ɗakin ba tare da ta iya furta komai ba.














***










Umaru Kwom na zaune a guest house ɗinsa tareda wasu mutane guda biyu. Ɗaya member ne na House of Assembly, ɗayan kuma mai bashi shawara ne.






"Idan har aka tsige Saifuddeen Kachallah banida matsala da Alhaji Yamai, saboda tamkar na lashe zaɓe ne an gama"






"Kana ga za a tsige Saifuddeen Kachallah? Mutumin nan fa ba shida wani aibu, he's totally clean"






"Senator Bashari kenan. Ai idan Saifuddeen Kachallah bashida wani datti, mu zamu yaɓa masa dattin, burinmu ai duniya ta ganshi da datti ne"






"Da kamar wuya Alhaji Umaru" Senator Bashari ya faɗa. Ya cigaba bayan ya kurɓi giya "Alhaji Sani Kachallah ba zai taɓa bari a tsige ɗansa ba"






"Ko ba a tsige Saifuddeen Kachallah ba, na yi alkawarin shi da kansa sai ya yi resigning"






Mai bashi shawara yace " ban ƙi taka ba Excellency, amma koma mi zamu yi ya kamata muyi da sauri tunda sati uku masu zuwa za a yi primary election daga nan kuma ba wani lokaci garemu ba, Kamfen za a fara gadan-gadan"






"Kar ku damu komai zai zo cikin sauƙi, an riga an fara aiki akai"





*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....













*©Azizat Hamza*





wattpad Azi_zat










Bismillahir Rahmanir Rahim

















Book one













17










Lokacin da 'yan fensho (pension) suka yi zanga-zanga jaridar Climax ce ta fitar da labari mai jan hankali akan haka. Kusan jaridar Climax ta maida hankali ne wajen nuna gazawar Gwamna Saifuddeen Kachallah. Tunda jaridar ta fitar da labarin birthday ɗin 'yar Gwamna sai mutane suka maida hankalinsu wajen karanta jaridar. Kafin Umaru Kwom ya sayi jaridar Climax, jaridar ta disashe, ba kasuwa. Yanzu kam a Jahar Congo tana ɗaya daga cikin jaridar da mutane ke marmarin karantawa saboda labarai masu zafi da take fitarwa.









"Har yanzu ba a san wanda ya sayi Jaridar Climax ba?" Gwamna ya tambayi COS daya kawo masa jaridar.






"Umaru Kwom"






"Umaru Kwom? Hmmm wannan mutumi dai ya ɗau aniyar ɓata mini suna kafin zaɓe"







COS yai shiru yana nazari, ya faɗawa Gwamna waye mai rubuta labaran nan ne ko kuma ya gayawa Kachallah. Idan ya faɗawa Gwamna zai shiga tashin hankali, amma ba abinda zai iya yi akai. Lokacin da ya gayawa Kachallah cewa Asiya ce 'yar jaridar da ta saurari maganansa kwanaki ba abinda aka mata dan haka zai yi shiru ya zubawa dukkansu biyu ido zuwa lokacin da zasu gano da kansu wanda ke ɓata musu suna a jaridar Climax.






"Ina son sanin waye ɗan jaridar da ke rubutun nan"







"Angama Excellency, za a nemo koma wanene" COS ya faɗa yana murmushin mugunta.










***







Asiya tana zaune ta shirya kayanta tsaf tana jira Sumayya ta gama haɗa nata kayan su tafi.






"Ni kam Anty Allah bana so mu bar nan, a chan fa takura za mu yi"






"Idan ba za ki bini ba, kya iya wucewa hostel daga nan" Asiya ta faɗa tana hararanta.






Babban labari take bibiya kuma dole sai tana gidan Gwamnati za ta samu. Irin kira da saƙonnin da Nana ke tura mata ya sa tayi zargin ko yarinyar 'yar maɗigo ce. Har a whatsapp idan tayi hoto sai ta turawa Asiya wai ta gani ko tayi kyau.






Yaya Bello ne ya kaisu gidan. Asiya ta shiga gidan tana addu'ar Allah ya sa ta samu ta gama komai cikin ƙanƙanin lokaci.







Masu aikin gidan sun ganeta sai dai ganinta da kaya yasa suka tsaya cirko cirko. Babu wanda ya faɗa musu Amaryar Gwamna za ta zo. Gashi Gwamna da Bilkisu ba sa nan balle aje a tambayesu.






Hansa'u da ta fito ta kalli Asiya zaune a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, gabanta kuma akwatuna ne guda uku. Hansa'u ta yi murmushin gefen baki dan ta hango drama idan Bilkisu ta dawo.






"Hajiya Barka da zuwa, a shiga miki da kayan ciki ne?"







"Kira min Nana" Asiya ta faɗa tana danna wayarta






Hansa'u ta wuce ɗakin Nana da gudu.


Lokacin da ta shiga cacar baki ta samu Nana da Zunnairah na yi.







"A wani dalilin za ki ce ta dawo gidan nan idan ba soyayya ku ke ba"






" Tana da ikon zama a gidan nan saboda itama matar Daddy ce. Sannan idan ma soyayyar muke ina ruwanki. Ke mata nawa kike da shi. Yes ina sonta"







Hansa'u tayi gyaran murya, dukkansu suka juyo suna dubanta. Ta taɓa kamasu suna aikata maɗigo tun farko-farkon fara aikinta a gidan. Sun mata kashedi akan kada ta kuskura ta faɗawa kowa, sai dai ba kashedinsu ne ya sata yin shiru ba. Aikinta bai bata daman tona musu asiri ba sannan ta lura Bilkisu gafalalliyar Uwa ce. Wani lokaci tana gani suna abinda bai dace ba amma sai tayi shiru.






"Hajiya Asiya tana neman ki "






"Ina zuwa"



Nana za ta fita Zunnairah ta riƙe hannunta tace " wallahi duk ranan dana kamaki da ita sai na gayawa Daddy komai"






" ni kuma sai na faɗawa kowa cewa ke ɗin 'yar shegiya ce, da cikin ki Mommynki ta yi aure"






Zunnairah ta kaiwa Nana duka Nana ta goce ta fice daga ɗakin da gudu.







Zunnairah ta dunƙule hannu tana huci.


Tun ranan da ta saurari faɗan iyayenta abin ya taɓa mata ƙwaƙwalwa. Tana shekara shaɗaya a lokacin ta buƙaci mahaifinta ya kaita karatu ƙasar waje, lokacin yawanci 'yan ajinsu 'ya'yan manya da suka gama firamare tare iyayensu sun kaisu ƙasar waje.


"Ni zan kashewa shegiya kuɗi" amsar daya bata kenan data faɗa mata buƙatarta. Ta wuce ɗakin mahaifiyarta tana kuka. Daren ranan bayan ta kwanta ta jiyo Iyayenta na faɗa inda mahaifinta ke cewa ba lallai bane ace cikinsa ne tunda ba budurwa ya sameta ba, sannan koda suke tare ai tanada wasu samarin. Yayinda mahaifiyarta take cewa idan bai yadda Zunnairah 'yarsa bace ya je ayi gwajin DNA.







"Koma minene dai ba zan kashe mata kuɗi ba. Idan ba zata boarding school da aka sama mata ba ta haƙura da karatun"






Da wannan aka tura Zunnairah boarding school a nan kuma aka koya mata maɗigo...







Nana na zuwa falo ta rungume Asiya tana dariya. Ita ta mata jagora har ɗakin da ke kallon nata tace ta zauna a ɗakin idan Daddy ya dawo sai ta zaɓi ɗakin daya mata.






Bilkisu bata shigo gidan ba sai chan yammaci. Tana zuwa kuwa aka ce mata Asiya ta zo, ta haura sama kaman za ta tashi sama.






Ɗakin Nana za ta shiga ta ga Zunnairah ta fito daga ciki.


"Ina take?"






"Wa?"






"Shegiyar da ta shigo min gidana"






Zunnairah ta nuna mata ɗakin da Asiya take.






Bilkisu ta banko ƙofa ta shigo ɗakin tana huci.


Nana da Asiya da Sumayya ne ke zaune akan gado suna hira.






"Ku bamu waje"






"Mommy daga zuwanki" Nana ta faɗa tana tura baki.






"Ki fata ko na ci miki mutuncin, wawuya kawai"


Kafin ta gama magana ma Sumayya ta fice daga ɗakin, yayinda Nana ta fice tana buga ƙafa.






"Ehen, mi ya kawo ki?" Bilkisu ta faɗa bayan su Nana sun fita.






"Mi ya kawoni kuma?"






"Uban wa ya baki damar zuwa gidan nan?"






"Inaga dai kin manta cewa ni da ke matsayinmu ɗaya. Yadda kike da iko da gidan nan haka nake da shi"






"Never. I am the first lady of the state, ba ki da matsayi a nan. Ki koma inda kika fito kafin na sa a maida ki ta ƙarfi"






Asiya ta miƙa mata wayarta tace "gashi, kira shi ki ce masa ba zaki bi umurninsa ba"






"Shi...shi Saifuddeen yace ki tattaro ki dawo nan?" Bilkisu tayi tambayar ta kasa gaskata hakan. Gwamna ba zai taɓa kawo Asiya ba bayan ya san ba ta so.






"Ki tattara kayanki ki koma inda kika fito"






"Idan kinga na tafi, to Excellency ne da kansa yace na bar gidan nan"










"Asiya kike ko wa. Ki fita a gidan nan kafin rayuka su ɓaci"










"Bismillah, Bilkisu Kachallah" Asiya ta faɗa tana dariya.










Bilkisu na fita daga ɗakin ta shiga kiran Gwamna, bai ɗauka ba hakan ya sake tunzurata. Lokacin daya kira bayan minti talatin ihu ta fara masa a wayar kan a wani dalilin zai cewa Asiya ta dawo gidan Gwamnati. Gwamna yace koma minene ta bari ya dawo.


Bilkisu har ƙarfe shaɗayan dare haka ta zauna zaman jiran dawowar Gwamna. Lokacin da ya shigo gida shabiyu saura a falonsa ya samu Bilkisu tana zaman jiransa.






"Ina ji, miya kawota gidana?"






Da rana bayan sun yi waya da Bilkisu, kiran Asiya yai dan ya ji dalilin dawowarta Gidan Gwamnati amma sai tace tana son zama a gidan ne, tana son sanin ya ake ji idan ana zaune a gidan gwamnati a matsayin Matar Gwamna.






"Saifuddeen ina jin ka"






"Bilkisu ke ba yarinya bace, ku ba yara bane. Ka da ku ɗaga min hankali dan Allah, akwai abubuwa dayawa a kaina"






"Haka ma zaka ce...haka ma zaka ce ko"






Gwamna ya wuce ɗaki ya barta a wajen.


Da sun san abinda ke damunsa yanzu da ba za su fara faɗa akan gida ba.


Ya kasa biyan albashin 'yan fensho da suke bin gwamnati har na wata huɗu, ga kumadu 'yan secretariat da malaman Sakandare duka sai dai ya biya su kaso hamsin na albashinsu wannan watan.






Lokacin da yayi wanka ya kwanta, bacci ƙaurace masa yai. Yana so koda kaɗan ne ya samu ya rintsa amma zuciyarsa tana cikin ƙunci nan da kwanaki kaɗan idan bai biya albashi ba mutane zasu fara magana. Ƙarshe dai sai daya sha maganin bacci kafin bacci ya ɗauke shi.














***






Da sassafiya kira ya shigo wayar Asiya tana dubawa taga numbar ƙasar waje . Tana ɗauka aka kira sunanta "Aseey"






"Ya Allah! C Y?, kana nan, ya kake ya jiki"






" lafiya Excellency, jiki da sauƙi"






"Gaskiya na ji daɗi C Y, ya hannunka"






"An samin na roba"






"Sorry ka ji"






"Ki tayani yiwa Gwamna godiya, he's a good man Wallahi, na ji daɗi da aka ce kin aure shi"






"Tsaya, tsaya, CY kana asibitin ma gulma kake. Waya gaya ma na auri Gwamna?"






CY ya ƙyalƙyale da dariya yace " har video ɗin dinner ɗinku na gani"






"Magulmaci, yaushe za ka dawo?"






" sunce za su sallameni nan da sati biyu haka"






"Na missing ɗinka sosai"






"Rufa min asiri kar Gwamna ya sa a harbeni"






Asiya ta sa dariya.






Kaman haɗin baki suna gama waya da CY sai ga kiran Fou'ad Salisu. Kafin ta amsa kiran sai da ta shige banɗaki ta kulle ƙofa.






"Ina jinka Fou'ad"






Daga ɓangaren Fou'ad ya fara yi mata bayani "akwai wani account mai suna Sa'ad Kachallah, inaga na Gwamna ne. Lokacin da Gwamna ya bayar da takardar shaidar kuɗi da dukiyar daya mallaka kafin a rantsar da shi bai haɗa da wannan account ɗin ba, sannan account ɗin duk wata akwai miliyoyin kuɗi da ake turawa ciki. Zan ƙarisa bincike na tabbatar da gaskiyar komai"






Asiya cike da farin ciki tace " idan aka tabbatar account ɗin nashi ne za a iya tsige shi kenan?"






"Za'a iya"






Asiya ta yi murmushin jin daɗi...






***










Sumayya tana gama lectures na ƙarfe shabiyu ta hau keke ta wuce

19 / 21