Author : Nana Hafsatu Category : Love Story
gaskia ce ai. Layla kaman taci kafar kare saboda yawo,kullum tana gidan su haba ai da gajiya "
"Gajiyar me Nusaiba? Kada ki manta da nan da can din duk tsatso daya ne. Ko yau Layla ta tattara kayan ta ta koma can wallahi gidan su ne, Haka zalika idan Nawrah ta dawo nan ma gidan su ne, Nusaiba ke fa uwa ce. Maganar dama da nazo miki kenan nace miki ke uwa ce. Ta iya yiwuwa agaba ke zaki zama mahaifiyar su gaba daya ke zaki aurar da su. Ba wai sai bayan rai na ba ko a yanzu. Yanzu ace idan rai yayi halin sa Nusaiba ke ce mafi kusantakar zama uwa agare su wadda zata share musu hawayen maraicin su Nusaiba."
"Haba Hindu maganganun me ne haka kikeyi? Ai babu Wanda yasan gawar fari sai Allah. Kuma 'yayan ki ko taki ko ta so 'yayanta ne. Haka zalika nata 'yayan naki ne"
"Kwarai dagaske baooan su. Don ni anawa rashin hankalin wallahi gani nake ko ba rai na ba zasuyi kukan maraici ba saboda Ina da ku"..
"Bar ma wannan zancen ta iya yiwuwa ma duk mu mutu mu bari ki. Yaran namu ma ke zaki cigaba da renon su . "
"Sai dai idan kai ne zaka mutu ka barta Allah . Inshaa Allah sai na zama mai uban kudi na tara dukiya na zagaye kasashen duniya , na taka nera na bada dollar na lika yan dubu dubu da kyautar motoci sai na zama babbar attajira tukui" Cewar nusaiba tana murmushi da girgiza kafa
"Toh Allah ya kyauta..." Bappah Auwalu ya fada
Malama Hindu tayi murmushi ta mike tsaya jiyo muryar nawrah tana cewa ,
"Ummy na gama ki fito mu tafi"
"Bari muje bappan su. Dama gidan aiki nazan leka. Allah ya kaddara saduwar mu"
"To masha Allah, Allah ya dawo daku lafiya"
Sa kayi ta fita. Nusaiba taja dogon tsaki tana bankawa kofar da malama Hindu tabi ta futa da harara. Ta mike tamkar jirgin sama kamar zata tashi sama ta shige dakinta tana rufo kofar da karfi ji kake 'kauuuu'
Malama Hindu ta fita suka jera sika nufi titi kasancewar direban da zai dauketa ma ba zai samu damar zuwa ba. Don haka titi suka fita ta saka sika tsaya awajen aikin kai gidan nata wato bappah junaidu.
Nawrah na daga can gefe ta basu waje tana wasa da kasan hijabin ta.
"Hindu na...."
"Naam junaidu na..... Ya aikin naku ?"
"Alhamdulillah... Ai na gaya miki mai gidan dakike aikin ogan namu sun shiga meeting dazu ai yace mu taya shi da addua wasu manyan kadarori yake so ya mallaka inde ya samu dama zai mana manyan kyauta sosai . Kinga sai mu sake gyara gidan nan sosai"
"Oh shi ya saka mai dakin sa tace ya shiga meeting kar nazo da safe sai dai da yamma kenan. Allah sarki to Allah ya amince. Amma abbiyen su ai gidan mu babu abunda ya same shi kasa ka wani damu kanka Allah "
"Shagon awara nake son na bude miki daga gefen baya dinnan zaa tada shago a dingah sayar da awarar da sauran abubuwa."
" Allah sarki junaidu. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Hakika bani da bakin godia agare ka. Ka a sani har kullum ba zan taba dai na godewa Allah da kasancewa mata agare ka ba. Allah yabar mun Kai har gaban abadan abbiyen su. Allah ya hada fuskokin mu da alkhairi yasa ko a aljanna mu kasance atare da juna. Nagode kwarai... "
"Wadannan kalaman fa Hindu? Sai kace wadda zatayi tafiya. Toh Allahumma Aminn ai komai na miki ban fadi ba Hindu. Domin duk inda matar kwarai ta Kai kin Kai kin zarce ma"
Murmushi tayi ta dan kallo gefen Nawraah taga ta juya baya tana danna wayar ummyn dake hannun ta yayinda ba maaikaci ko daya awajen. Ta rungume da shi da sauri ta sake shi tana goge hawayen dake neman zubo mata,
"SubhanAllah kukan meye wannan,?"
"Kuma dadi ne.. kukan farin ciki ne, kuka ne mai dauke da tarin ma'anoni. Kasancewa ta mata agare ka. Kasancewar uwa ga yarana. Kasancewar suruka ga su bappah Auwalu. Abubuwa da yawa. Nagodewa Allah da samun zuri'a ta gari wato hamidniyya Lebanon. Allah ya biyaka da aljanna Junaid .. Allah kuma ya cigaba da bude maka kofofin alkhairi ka cigaba da kula da yaran mu. Gasunan amana ne Allah yabamu. Kaga nj dai bana nan yanzu aiki zan tafi. Ka Kula da su don Allah.."
"inshaa Allah Hindu... Wannan kalamai haka? Yanzu zan koma karki ji komai Allah. Nasan dama saboda su kiketa maganganun akai kwantar da hankalin ki kinji?"
"Inshaa Allah. Abincin ka Yana can na bawa Hamma sallahu. Bari mu tafi kar lokaci ya kure"
"Sai kun dawo Allah ya bada sa'a ya miki albarka "
"Aameen abbieyn su . Komai dare ai inshaa Allah gidah zamu dawo"
"Tohm Allah ya amince Hindu"
Daga masa hannu tayi shima yana daga musu suka nufi tasi suka shiga ta Kai su can unguwar ta su Dr bintu
Gidan sika shiga bakunan su dauke da sallama suka gayshe da ita tana parlor itada mai gidan nata
Kitchen suka zarce nan da nan ummy ta fara hada abubuwan abincin da zata dafa yayinda nawrah ke tayata.
A haka har suka kammala komai. Ummy da nawrah suka nufi parlorn suka jera komai akan dinning
Dr bintu da Alhaji Sambaso mijinta sunata magana a parlorn dauke da wasu takardu agaban su...
Ya yinda tashar talabijin ke nuna wakar Maher Zain ta rahamatun lil alamin
Nawrah na son wakar don haka ta danna recording ta ajiye wayar daga can gefe don ta tariyo mata muryar Maher Zain da ke raira baitin
Waya Alhaji Sambaso ya daga ya gama amsa kiran ya saki Kara da karfi Yana jijjiga Dr bintu yace,
"Alhaji ateeks ya amince.... Plazas dinnan din sun zama mallaki na. Harda estates din mejesa da guzare dana Gpo da na bayan Maduki., shikenan nayiwa Dr abubakhr warwas matsiyaci duk tarin arzikin sa da sannu sai sun zama mallaki na..."
"Alhamdulillah.... Dama naki jinin munafukar matar sa sai uban izza da iyayi. Allah yasa su mutu acan duka kowa ya h...
Ji kake taratsats malama Hindu dake tafiya tana jinsu zata ajiye tray din jikinta sai rawa yake jin maganganun da suke kafafunta suka fara rawa tray din ya kufce daga hannuwanta ya fadi..
A matukar razane suka jiyo gaba dayan su suna kallon ta. Duk sai suka sha jinin jikin su,
"Me kike anan Hindu?" Dr bintu ta fada da karfi
"Ba abunda naji Dr.. Dan Allah kuyi hakuri santsi ne ya kwashe ni"
"Bangane ba abinda kikaji ba me kike nufi.?"
Nawrah na daga kitchen tana jiyo su ta fito da sauri ta janyo wayar ta,
"Menene wannan din me kike da waya?"
"Wayar ummy ce na ajiye" ta fada tana futa daga wajen recording din"
"Hajia sai da safe" malama Hindu ta fada tana kamo hannun nawrah
Dr bintu ta juya ta kalli mai gidan nata. Ya saka yatsa a hannu yana ciza shi.
"Hindu... Hindu?"
"Naam hajia dare yayi tafiya zamuyi"
"Ai baki gama ba, dama mana kunu" ta fada tana nuna mata kitchen
Jikin malama Hindu ya cigaba da kakkarwa tana yarfe yatsa tace
"Dan Allah hajia"
"Banason musu jeki dama mana kunu nace"
"Toh"
Komawa tayi kitchen ta janyo hannun nawrah jikinta na rawa suka futa tsakar gidan ta zaro nera dari ta mika mata,
"Maza maza tafi gidah"
"Ummy meyasa?"
"Ni dai nace miki ki tafi gidah ko? Tafi da wayar tawa ma "
"Idan aka kira ki fa"
"Baa wanda zai kira ma jeki yi sauri karki juyo ki, tafi gidah ki wuce kar ki dawo. Ki kashe wayar ma me kikayj awayar ne"
"Recording wakar Maher Zain nayi"
"Lokacin duk suna wadannan maganganun?"
"Eh bansani ba ni dai tun dazu na ajiye ta"
"SubhanAllah to tafi gidah dai ki kashe wayar idan kinje gidah ki bawa Hamman ku ya ajjye idan na dawo zan karba "
"Kai ummy?"
"Nawrah nace ki tafi ko?"
"Tohm shikenan. Ga tawa ki rike" ta mika naga wayar me torchlight ta ummyn ta da da ta bar mata ,
Ummyn ta girgiza kai tana kakaro murmushi tace,
"Ai dole sai kin saka na karba Kai nawrah dadi na dake KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA... Je ki Allah ya miki albarka..."
Ummyn ta karba tana cusa ta a jakarta ta hannu ... Tana kambama jarumta irin ta Nawrah tun tana karama. Lalle idan ta girma za'ai mace mai kamar maza....
Nawrah ta futa daga gidan taje titi ta hau mota ta koma gidah. Yayinda malama Hindu ta koma cikin kitchen din duk abunda da suke ashe Dr bintu na hango su... Ba dai ta jiyo maganganun da suke..
Jikin malama Hindu na rawa ta shiga aikin data sakata ta dama kunun tazuba a flask
"Hajia na karasa"
"Hindu"
"Naam"
"I don't care da rantse rantsen da kike Amma Allah idan naji magana daya ta fita wallahi sai kinyi mamaki"
"Wace magana hajia nace ba abunda naji"
"Ni dai na gaya miki"
"Inshaa Allah hajia. Ni ba zamma Kara aikatau ba wallahi daga yau da yardar Allah, na tuba dan Allah kiyi hakuri ki gafarce ni" ta durkusa kasa tana hada hannuwan ta
"Shikenan jeki sai da safe"
Hindu ta mike dasauri jikinta na rawa ta zura takalman ma wari da wari ta saka..
Tana futa Alhaji Sambaso ya mike zai fita shima,
"No Alhaji please "
"Kin aminta da ita.. ba ita ce mai aikin su ba kafin tafiyar su waje"
"Dan Allah ka kyaleta nasan ba zata fada ba"
"Okay ni ba wajenta zani ba"
"But am...
"Nace miki ba wajenta zani ba. Refreshing brain na kawai zanyi zan dan fita yanzu ba nisa zanyi ba ita kuwa ai nasan ta hau mota ta tafi ma"
"Shikenan sai ka dawo"
Fita yayi wajen gidan ya dau motar sa ya fita daga cikin gidan a hankali yake tafiya yana hango malama Hindu tana tafe tana waiwaye tana tafiya atsorace...
Tunani dankare cikin kirjinta, wannan wace iriyar rayuwa ce haka? Dama zaman cin amana suke da su? Lalle duniya abar tsoro ce... Wayar dake gurin ta ce ta fara kara mai gidan ta ne wato bappah junaidu ta dauka muryarta na rawa ta saisaita kanta tace gata nan zata dake yanzu inshaa Allah...
Daman titin yayi dubu ba street lights sun mutu..Salati ta fara yi tana karanta la'ilaha illa anta subhanaka jnni kuntu minazzalimin..
Alhaji Sambaso ya kara gudu zuciyar sa na kuna,, wato har ta fara kiran waya tana fada kenan? ya tashi kanta tana komawa gefen bishiya ya hadata da bishiyar ta daga sama can ta fado kasa tim kamar ba mutum ba ..
Ya arce dagudu ya hau babban titi. Sai bayan yan mintina tukun sannan mutane sika taru tana numfashi dakyar,..aka lalubo waya ajikinta aka Kira number data amsa Kira karshe ta bappah junaid da nawrah tayi saying da abbiey ban da nan suka kira shi suka gaya masa hankalin da ake ciki.
.
Suka nufi gidan da ita wani mutumi ya temaka aka kaita kasancewar ummyn tanata magana da kyae kan akaita gidah
Ana kaita baki daya yaran sukai kanta sunata ife ife da adduoi. Daga na suma rankaya asibiti
Likitoci sukai kanta aka saka mata oxygen kasancewar numfashin ta ya fara sarkewa.
Likitocin sunata kokarin bata temako, Bayan wani lokaci, Likita on duty ya fito daga emergency ward yana zare facemask dinsa ya dubesu kansa a kasa .
Ashir ya karasa kusa dashi yana girgiza kafadar sa,
"Ya jikin ummyn wani abun ake bukata? Jini? Kudi? magani? Me kuke so?"
Likitan ya girgiza kansa bayan ya sauke katuwar bahaguwar zuciya yace,
"Sai dai muyi hakuri Allah ya mata rasuwa...babban dadin kuma ta cika da kalmar shahada Alhamdulillahi....
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_24_
:::::::::
*ALHAJI SAMBASO AVENUE*
*Wani * tafkeken gidah suka nufi gate din sa.. Manyan masu gadi majiya karfi a mummurde su biyu ne suka taso sukayi kan motar da malam Liti ke tukawa ganin ya tunkari gate din..
Ja yayi ya tsaya da motar. Masu gadin suka leka suka saka ya bude har booth dinsa tukun sannan dayan ya janyo wata aba kamar rediyo baka ya koma gefe Yana magana. Can ya dagawa dayan me gadin hannu ya koma ya zauna
"Ku shiga" Ya fadawa malam Liti Yana rufe masa murfin booth.
Malam Liti yaja motar Yana zakin siririn tsaki yace,
"Na tsami zuwa gidan nan yadda kikasan gidan gwamna wallahi tsare tsaren su yayi yawa. Sun san nafi shekara nawa ko muzo da hajia ko ta aiko ni ni kadai amman masu gadin nan sai sun tsayar dani..."
"Kayi hakuri. Inaga yanayin aikin nasu ne yazo da tsauri haka" malama Hindu tace da shi
"Allah ya kyauta kawai. Abun nasu ne yayi yawa kam"
"Ayyah"
Ita dai nawrah na zaune tana raba idanu. Ta saba ganin hadaddun gidaje a dramas da labari idan ana basu. Amman bata taba ganin gidah me kyawun wannan ba..
"Allahumma arzuqniy" ta fada tana sake duban gidan alokacin da suka shiga harabar gidan da mota
Malam Liti ya nemi wajen parking ya faka motar. malama . Hindu suka fita da ga ciki ta riko hannun Nawraah dake kalle kallen gidan.
Murmushi malama Hindu tayi tace,
"Ai gidan hajia qibdiyya yafu wannan kyau fa? Su gate dinsu da kansa ma yake budewa Nawraah"
"Mashaa Allahu sunji dadin su"
"Mashaa Allah! Kuma Allah ya Kai ku inda zakuje ku huta sa kwanciyar hankali Amin"
"Toh Aaameen.. Amma ummy samun irin wannan gidan kan nasan ko a mafarki"
"Yi sauri kitchen astagfirullah. Waye me azurtawa?"
"Astagfirullah Allah ne"
"Waye me talautawa?
"Allah ne"
"Waye me bayarwa"
"Allah ne"
"Waye mai rayawa"
"Allah ne"
"Waye me kashewa? Ya bayar asan da yaso ya hana asanda yaso"
"Allah ne"
"To ki yi maza ki roki gafarar Allah mumini baya yanke rai ga rahamar ubangijin sa. Allahn daya basu bai manta da mu ba kina ji na?"
"Astagfirullah... Eh Ina jin ki ummy "
"Shysa a har kullum ake son ka kalki na kasa da Kai kada ka kallo na sama da kai lalle idan ka kalla na kasa da Kai Wanda ka fishi komai tanan zaka Kara godewa Allah da rahamar da yayi maka. Nawraah wasu suna nan basu da matsugunin da zasu zauna Ina nufin gidah.. wasu basu da abincin da zasuci bara suke. Nawraah wasu suna nan kayan da zasu saka ma basu da shi sutura tayi karanci Nawraah. Wasu Kuma suna asibuti ma sai dai a kwantar a tayar basusan Wanda ke kan su ba. Wasu ma hankali ne basu da shi a zare suke suna kwana a bola. Nawraah lafiya kadai ma idan Allah ya barka da ita wallahi babban arziki ne. ... Ki kasance cikin hamdala ga mahaliccin ki shi Kuma zai ninka maki bukatin ki inshaa Allah"
"Inshaa Allahu ummy"
"Yauwa Nawraah,,, mace ce ke sai kiga Allah ya daga ki ya Kai ki gidan wani hadadde Wanda baki taba zaton samu ba Allah ne kadai yabar wa kansa sanin wayasan gobe. Kuma inshaa Allah khair"
"Hakane ummy.. nagode sosai da tunatarwa"
Suna tsaye a bakin kofar tun da suka danna door bell dai baa bude musu ba sai da Nawraah ta sake saka hannu ta danna madannin tukun sannan bayan yan mintina wata matashiyar budurwa kamar Nawraah tazo ta bude musu kofar
Ta sakala earpiece a kunnenta kana jiyo karar sautin wakar da take ji.. Sanye cikin kananun Kaya riga da wando kanta ba dankwalii ta yi parking gashin nata.
Wani hadadden babban parlor ne mai girma sosai yana dauke da saitin kujeru har biyu . Yayi matukar kyau parlorn kudi yayi aiki agidan domin komai Mai tsada ne sosai.
Yarinyar data bude musu kofar wadda kallo daya zakai mata kàsan yar gidan ce dubada wani zama da tayi akan doguwar kujera ta cigaba da karkada kafa tana bun wakar da take sauraron ta earpiece.
Can sai ga wata mata fara irin fararen ne don yarinyar ma data bude irin farar nance haka. Sunada kyau ba lefi . Irin buzayen nanne yan nijar
Matar ta dashare baki tana duban su tace,
"Dan Allah ku zauna... Malama Hindu ko?"
"Eh ni ce ce. Barka da rana mun same ku kalau?"
"Alhamdulillah..."
"Ina wuni?"
Nawrah ta gayshe ta
"Lafiya kalau yammata"
"Uhm lily kawo musu ruwa please"
"Mommy ni fa ba Mai aiki bace. In kawo musu ruwa Ina Dela take takawo musu mana?"
"What nonsense coman get up. Ki dakko harda lemo ki kawo"..
"Wallahi a koshe ma muke hajiya"
"To kinji sun koshi ma" yarinyar data kira da lily ta fada. Hadi da komawa ta gyara zamanta tana harde kafafun
"Bari a kawo kayan. Ah ai dole kusha ruwa malama Hindu...takanas daga gidan kawata ai dole a karramaka . Sunana Dr. Bintu... Ke dama nasan naki hajia qibdiyya ta fada wannan ce bansan sunan taba. Yar ki ce?"
"Eh yata ce... Nawraah"
"Mashaa Allah... Sunan Mai Dadi Mai kyau kamar jta tubarkallah. Ga yata can Ilham muna ce mata Lily . Sai babban 'dana Marwaan... Lily zo ga kawa na Miki"
Lily ta juya ta dube su duka a shekeke ta tabe baki tana girgiza kai,
"Not my type.... "
Dr. Bintu ta mike ta shiga wani daki tana kwada sunan,
"Dela.. Dela"
Da alama Mai aikinta ce don da sauri ta futo daga kitchen,
"Naam hajia"
"Zo ki fito da kayan nan duka please .."
"Tohm hajia yanzu kuwa"
Suna dai zaune suna kallon sarautar Allah dela ta fito da wasu manyan buhubuna dauke da kaya kaka kala.
"Kunzo da wayar ki? Ku fara dauka*
"Eh. Nawraah daukar mata"
Nawraah ta mike tana daga kayan daya bayan daya tana daukar hotunan su