Author : Nana Hafsatu Category : Love Story
ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:02] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_36_
:::::::::
Anyi shela anyi cikiyar wadanda ke bin junaidu kudi ko wani na ajiya suyi magana a basu. Yawanci ma anfi samun wadanda shi yake binsu bashin basu biya shi ba.. duk wadanda suke binshi bashin da yawan su wasu sun yay'yaafe. Wasu kuma sun karbi wani kaso na cikin kudin sunce sun bar sauran..
Sai wani mutumi daya tashi ya taba kafadar na gefen sa suka mike. Suka ce hakika ana bin Junaidu zunzurutun kudade masu matukar yawa.
Hakan ta faru ne kuma alokacin da daya daga cikin yaran sa babu lafiya. Aka tambaye su adadin kudin sukace ai wannan magana ba tasu bace. Domin suma shedu ne na mutumin da junaidu ya karbi bashin agaban su. Kamar jingina yayi ya karbi tarin kudi...
Aka nemi ganin mutumin don sanin waye shi da yadda zaa biya da sanin ma shin nawa ne adadjn kudin daya karba? akace daya mutumin yayi tafiya sai ya waiwayo gidah nigeria tukunna.
Daya daga cikin su ya karkare magana da
"Abunda ya saka muka fada ma saboda hali ne irin rayuwa kada abar mamaci da tarin bashi akan sa. Duk kuwa da kadarar sa ya jinginar ya karbu kudin. Amman dai mun ga yakamata fadar shi yafi alkhairi Allah yasa mu dace"
"Ko zamu iya sanin kadarar daya bayar ya karbu kudin a hannun sa?" Bappah salisu ya tambayi mutumin
Mutumin ya girgiza kai sannan yace,
"Wannan batu baki daya sai an kawo takardar da faifan bidiyo da sukai yarjejeniyar ya sanya hannu tukunna shi mamacin. Kafin shima Alhajin ya rattaba nasa hannun"
"Toh Allah ya rufa asiri. Allah ya dawo dashi lafiya. Shi Kuma wannan Dan uwan namu Allah ya jikan sa ya gafarta masa Allahumma Aameen"
Suka amsa da aameen baki daya. Aka shiga yiwa bappah junaidu addu'oin samun rahamar Allah da nasarar amsa tambayoyin kabari.
::::::::;;;;;;
Sannu ahankali haka mutane suka fara darewa, kowanne yanzo daa irin kyawun halayen da yake fada game da manacin.
Hakika bappah junaidu ya samu yabo sosai daga bakunan abokanan sa, Yan unguwa, Yan wajen aikin su, makotan su, Yan unguwar baki daya dama dangi na kusa dana nesa.
An kakkawo musu kayayyakin abinci na tallafawa marayun. Saboda kallo daya zakai musu su baka matukar tausayi marar misaltuwa. Dubada duk ba wani kawo girma sukai sosai ba har shi Ashir din. Be Kai shekarun da zaa ce zai hade kawunan Yan uwan na sa ba.
Amman dake yanada zuciyar tashi ya nemi na kansa don kare daraja da martabar yan uwan nasa. Hakan bai hanashi kutsawa nan da can ba don ganin ya rufa musu asiri...wannan kenan
Haka aka nannade makoki. Akabi mamacin da addua. Hadi da dangana da hakuri da iyalan sa zasuyi. Kowa ya watse na kusa dana nesa
Idan ka tsame dangi mafi kusantana marigayin ba. Wato su Bappah Auwalu da su Bappah sani...
A parlorn Bappah Auwalu suka hallara baki daya iya yan dakin su. Sai nusaiba da tayi kanai kanai taki tashi suna magana tana tsoma baki..
Ba wanu abu ya bari da yaran zasu mori ba illa dubu biyu da dari uku dake aljihun sa Kafin rasuwar sa, sai Kuma wayar torchlight dinsa . Da wasu dari takwas dake drawer dinsa.
Toh su aka harhada dai aka gangada dai da sauran abubuwan sa aka raba gado aka baiwa yaran sa.
Wasu daga cikin kayan sawar sa bayan yaran sa maza sun dauka suna so. Sai Yan uwansa wasu ma suka dauki wasu. ragowar Kuma aka kyautar sadaka duk Wanda yazo karba sai ache masa yayiwa mamaci addua..
Baki daya a zazzaune suke suna kallon kuna. Suna magana,nusaiba na daga saman kujera tana jin abubuwan da suke fada. Wani ta saka baki baki wani tayi shiru..
Ashir ya taho daga gidan su zuwa gidan bappah Auwalu zai gayshe da bappanin na su kamar ko da yaushe yanata sauri ya karasa kofar gidan. Ya saka hannu zai murza kofar ya jiyo su suna magana haka sama sama tamkar masu rigima ko fada, Bappah Auwalu na cewa....
...
_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafawa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata Mai abarka..._
_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo tarauni dake unguwar Kano sai akira number opay dincan dake sama_
_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._
_kofa a bude take da dik Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_
[3/10, 21:02] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_37_
_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafawa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata Mai abarka..._
_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo tarauni dake unguwar Kano sai akira number opay dincan dake sama_
_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._
_kofa a bude take da dik Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_
°°°°°°
"Dukkanin mu nan uwar mu daya uban mu daya... Ba bare acikin mu idan kuka tsame Nusaiba..."
"Nima ba bare bace Auwalu . Auro ni fa kayi ka cire ni daga cikin dangi na ka dawo da ni naku. Kana da bakin cewar wani ni ce bare?" Nusaiba ta fada tana gatsine.
Yakumbo Aminatu ta tabo ta tana girgiza kai tace,
"Kash ba da wani abun ya fada ba Nusaiba. Dan Allah tashi ki koma daki. Idan muka gama kyaji duk yadda mukayi. "
Mikewa tayi tana zunburar baki hadi da kananun mita ta shige cikin daki. Ko da ta shiga ma d'age labule tayi ta kasa kunnuwanta tana jiyo abunda suke fada...
"Bappah sani, bappah Auwalu, Bappah salisu, Yakumbo Aminatu ... Kamar yadda yaran nan ke fada dukkanin su baki daya ciki harda yaran mu. Basuda wasu da suka fi mu ko suka kamo kafar mu. Mune uwar su mune uban su yanzu. Wallahi Allah sai ya tambaye mu idan bamu kula da yaran nan ba ... Bari na sake nanatawa. Acikin mu da muka rage mu hudu dinnan. Kowanne zai iya daukar yaran nan baki daya ya rike su ba wani abun bane. Zumunci ne. Naka shine naka. Ido biyun duk sun tsiyaye musu, sun rasa uwa da uba cikin kankanin lokaci baki daya ba jimawa. Zan sake nanatawa, Salisu, Sani, Ameenatou. Dukkanin ku kunfini karfi Kuma kowannen ku zai iya rike fiye da yawan yaran nan ma akarkashin sa. Allah ya hore muku. Yaran nan suna bukatar danshin iyaye atare da su. Ku temaka yanzu acikin ku wanene zai dauki yaran nan baki daya? Kuna ganin abunda mutanen nan sukazo sukace ma akan junaidu yayi jingina ya karbi kudi. Bayaga haka nace muku junaidu nima ya rantomun kudade nayi gyaran gidah har yacemun kyauta da fari nace masa wallahi bazan karba ba bashi nake so... Kunsan dai halin dan uwan mu da rufawa nasa asiri? Sam bayasan wani na waje yaji barakar mu. Zai iya salwantar da komai nasa don ganin ya sanya mu acikin farin ciki. Dan Allah kada mu bari yaran nan suyi maraicin iyayen su. Kada mu bari yaran nan su Gane Cewar bamuda hadin Kai a tsakanin mu ba zamu iya rufawa dan uwan mu asiri ba. Wanda dukkanin mu nan kowannen mu junaidu yayi masa da aljihun sa, da jikin sa da gumin sa. Bai taba gajiyawa ba..... Shin wa zai karbi rikon yaran nan su dawo hannun sa? Su hudu ne kawai, Ashir, Ashfeef, Nawraah sai Kuma auta Amnah... Wallahi summa tallahi da inada halin da zan rike yaran nan wallahi zan rike su, Amman banda shi. Junaidun dai ke rike damu duka har ni ya rasu. Dan kuwa komai na rayuwa wallahi shi yake mun ya dauke mun komai . Ba abunda zance da shi sai fatan Allah ya masa rahama yasa ya cika da kyau da imani amin "
"Aameen " suka amsa baki daya
"Sani zaka rike su?"
Bappah sani ya grigiza Kai Yana duban agogon hannun sa yace,
"Kasan halin da nake ciki yanzu. Wallahi Idan na ce zan rike yaran nan zan takura bazan iya ba wallahi."
Bappah Auwalu ya kada Kai ya dubu Bappah salisu yace dashi,
"Salisu kaifa! Nasan dai ba zaka ki ba. Kusan a bunza junaidu yafi shakuwa da Kai ma"
Bappah salisu yayi hanzarin girgiza kai yace,
"Bazan iya rike su ba gaskia. Abubuwan sai ahankali yaran gaba na kadai ma sun ishemu. Bazan iya hadawa da yaran nan ba saboda banida karfin hakan"
Bappaah Auwalu ya kada Kai cike da takaici . Ya dubu gwaggo Ameenatu yace,
"Ke fa? Aminatu ke fa? Zaki rike su ko? Nasan ke bazaki ki amincewa ba ba zaki ki tallafar ahalin junaidu ba. Ni na sani"
Gwaggo ameenatou ta sauke katuwar bahaguwar zuciya tace,
"Ba wai naki bane. Amman Auwalu a situation din da ake ciki Allah mai gidan ma baze bari na dauke su duka ba. Kaga expenses din sunyi yawa. Amma dai ni Ina son abani Amnah zan riketa. A shirye nake na tafi da Amnah. Idan yaso su Ashir, Ashfeef da Nawraah sai asan yadda zaa kula da su. Ko a rarraba su. Ni na dau Amnah, Kai salisu ka dau Ashfeef da Nawraah, sani Kai Kuma ka rike Ashir dakin nan na wajen gidan ka ku bashi ya zauna aciki ya muku tsaro ma tunda namiji ne Kuma babba, Ko duk wata wata zamu dinga harhadawa yan kudi ana kula dasu. Kowannen acikin mu sai a bashi ya kula da dan dake gaban sa yana ragewa. "
Ashir ya girgiza kai din takaici har hawayen bakin ciki yayi. Wato da iyayen su na raye bappanin nasu kamar su cinye su suna nuna suna kaunar su. Amman yau dan ba ran bappah junaidu da su ke uwa daya uba daya shine autan su Kuma 'yayan sa na cikin sa. Amma kowanne yaki amincewa ya karbe su.
Cikin zafin nama ya bude kofar ya shiga yana goge hawayen sa yana kallon su yace,
"Yakumbo ba zaki dau Amnah ba, ba Wanda zai dau kowa... Ku barshi kuje ku zauna da iyalan ku na cikin ku. Ni zan rike kanne na. Zan kula da cin su, Shan su, tufatar da su da yi musu komai Wanda mahaifi da mahaifiyar su zasuyi musu. Zan share musu kukan su. Da yardar Allah ba zasuyi na damar kukan rashin iyayen su ba a kusa. Barkan mu da rana dama gayshe mu nazo yi. Ku huta lafiya..."
Ya juya ya fice cikin zafi nama. Ransa na matukar Susa. Ya rakube a jikin wani gini Yana kuka sosai. Dama haka Yan uwantakar take? Wato idan kana raye ne akeyi da Kai da iyalan ka idan ka rasu baya ake juya musu ana kyamatar su haka? Lalle sunyi rashin bango majingina.
"Yaa Allah.... Ka dubi maraicin mu ka kawo mana dauki Aaameen." Ya fada Yana goge hawayen sa yayi hanyar gidan su jiri nata dibar sa.
Jijiyar kansa ta tashi radau ransa amatukar javula haka ya seseta kansa ya shiga gidan na su. Kai tsaye ya wuce dakin su. Ashfeef baya nan. Ya nemi katifar su ya kwanta Yana rufe fuskar sa da tafin hannun sa..
Hawaye masu matukar dumi suka shiga kwarara daga idanun sa...
:::::::::
_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafawa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata Mai abarka..._
_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo tarauni dake unguwar Kano sai akira number opay dincan dake sama_
_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._
_kofa a bude take da dik Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_
[3/10, 21:02] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_38_
:::::::::
Bappah Auwalu ya mike tsaye yana nuni da kofar da Ashir ya futa hawaye na gangara a fuskar sa yace,
"Kun gani ko? Tun ba'aje ko'ina ba. Kun fito kun nunawa iyalan sa na cikin sa ba kaunar su kuke ba. Haba haba haba wallahil azim kunban kunya. Wallahi summa tallahi da inada halin da zan rike yaran nan wallahi zan rike su.. Amman tir da halayen ku, kun yanke amanar zumuncta Allah kyauta"
"Ni dai na gaya maka uzuri na. Ai wata kusan tafi wata kusa. Har ga Allah banga ma abunda akayi anan ba. Yaran dai dama yanada tinkaho ne kawai amman me akayi anan ko salisu?"
"Gaskia nima sani banga abunda akayi ba. Magana ce fa aketa gaskia domin Allah. Magana ce ta dindinin abunda zaka dore. Ai bakyau mutum ya dau a abinda ba zai iya cigaba da shi ba. Mun fito mun fadi uzurin mu shin menene matsalar anan? Me mukayi ni gaskia banga wani aibu da akai anan ba kai ma Auwalu da son kakaro mana lefi. "
"Hmm bare ni dana amince zan rike daya daga cikin su. Ni menene aibuna? Na amince zan karbeta na riketa. Ba shikenan ba? Amman yaci ace yaron nan yazo tsakiyar mu manyan sa, da uban sa yace zai gasa mana maganganu har haka? " Yakunbo Aminatu ta karasa fada tana jan dogon tsaki...
Bappah Auwalu ya ja tsaki akaro na uku yana karkada hannu Yana nuni da ceiling dinsa yace,
"Wannan ceiling din da sabun kofofin nan/kyaurukan nan. Marigayi ne ya kawo mun kudin wallahi kyauta ma yace ya bani shi zai biya su. Nace aa wallahi bazan amince ba nafi kaunar ni na biya da Kai na idan na samu. Domin junaidu adadin bashikan da yaron nan ya biyamun Allah ba zasu fadi ba. Cin mu , suturar mu, komai namu wallahi Allah shine shahidi. Junaidu yana matukar kokari ganin ya mana dai dai gwargwadon ikon sa. Haka ma matar sa wallahi batada bakin hali kwata kwata. Hakama yaran nasu baki dayan su wallah kowanne sai sam barka. Amman tin da ga kowanne acikin ku uzurin daya kawo bazan takura muku ba. Allah ya kyauta. Ni naji na amince zan rike su"
Nusaiba ta fito daga cikin dakin da take labe. Ta daga hannu tayi guda ta nana a cinyarta tace,
"Katarar ubancan. Lalle ma Auwalu, mu sai yan hakora. Da jiki duk qashi muna tafiya da kwana acikin talauci. Kache zaka rakito mana wasu rayikan har hudu su tare awurin mu. ? Shin Ina zamu saka su acikin wannan gidan naka mai ukubar rayuwa eh? To ahir dinka. Wallahi ahir dinka. Narantse da uban da ya haifeni ban amince ba"
"Gaskia babu babbar butulu a duniya irin kiba nusaiba. Babu Allah. Menene a duniya Wanda mamatannan basu Miki ba su da yaran su.? Junaidu daki sukutum ya dauka ya baki kika saka kiwon da kike. Banda tarin alkhairin da yake mana mu da yaran mu kullum. Marigayiya Hindu baiwar Allah nan ba abunda ta rage Miki ta dauke ki tamkar kanwarta bata Miki kallon faccala dede da second daya. Duk sanda tayi awarar data fara ta sayarwa har Allah ya karbu ranta kullum yaumin sai ta aiko mana, karewarta ma ranar da zata rasu sai data shigo muka gaysa tace daman wajen ki tazo ma tamiki fada . Yaran nan wataran wajen ki zasu dawo ki rike su ma ke zaki aurar da su. Wai Amman duk wasiyyar da take bar miki din kuwa wasiyya ce dai dai da kwayar zarra baki taba ajiyar ta ba a...
"Ya Isa dakata da wannan wa'azin kurman da kake don ba saurara nake ba. Da fari kana magana yo wancen akurkin dakin ai sai da ya tabbatar dan Adam ba zai iya kwana aciki ba ko da kuwa rai daya ne bare yace zai moriyar sa shine ya jefe ni da shi. Su kansu kiwon dakyar suke nunfashi saboda azabar zafi da duhu ba ai wundo ba a dakin haba haba dan Allah... Kana maganar awara awarar banza awarar wofi Allah ya kwashewa waken soya ma albarka Auwalu, . Kana maganar suna kyautata mana to ba dole su kyautata ba kudin yafendo ne data bayar ya handame don kuwa sata yayi yasa tayi masa kyautar dole. Dake Kai zakara ne sai da tsaba ya saye ka da kananun kashin kudin da yake maka ya rufe maka baki baka iya ganin lefin sa . Wannan kai ya dama. Na fada na sake fada ba yaran da zai zauna mun agidah wallahi. Muna karime Karime to abincin da zamu ci kullum na rai hudu dakyar zaka karo mana wasu hudun? Tukun nama aina zasu kwana? Wannan gidan Mai kama da turken agwagwi. Muma bai ishe mu ba bare Karin wasu mutanen Na gama magana Allah . Ba dan da yar da zasu zauna mun " tana karasa maganar ta shiga daki ta bugo kofar.
Bappah Auwalu yayi shiru ya kasa cewa komai. Babban abunda yafi daure masa kai da Yan uwan sa uwa daya uba daya ke wajen basu tanka sun tsawatar mata ba, Amman ba wani abun mamaki bane tunda sun ki amincewa su rike yayan kanin su uwa daya uba daya .
"Allah ya kiyaye hanya idan kun tafi. Na bar ku lafiya Allah yabada ladan taaziyya