Author : Nana Hafsatu Category : Love Story
wasu budiyoyin su take yi.
Dela aiki ya kachame mata tamkar zatai hauka tazo tana cewa Dr bintu tuwo yayi ruwa gashi ko miyar bata hada komai ba.
Malama Hindu dake jin su tace,
"Bari na zo na kama Miki ko miyar ce"
"Kai harda wahala ayi haka?"
"Bakomai hajiya"
Malama Hindu ta futa tabu bayan dela suka je kitchen din. Nan da nan dama miyar kuka ce.
Malama hindu ta hada komai da zata tanada gata da saurin aiki ta fara hada miyar nan.
Baa dau wani lokaci Mai tsawo ba kitchen din ya fara tashin kamshin Miya. Nan da Nan ta gama ta ta zuba a food flask ta dauraye hannun ta ta koma inda Nawraah ke daukar hoto da bidiyo din . Suka kammala daukar
Yayinda suka lissafa Hadi da irga kayayyakin da suka haura guda biyu iri daya suka rarraba su Kashi biyu. Kowanne nawrah ta rubuta ta wayar ta ajiye.
Suna gamawa sukai mata sallama zasu tafi.. Ta bawa Malama hindu dubu biyar ta Kuma bawa Nawraah riga da skirt na cikin kayan sabbu.
Suka mata godia suka tafi. A mota malama hindu ta curo dubu daya tabawa malam Liti Dakyar ya karba yana shi mata albarka.
Nawraah ta saka aka sauketa agidan su Kuma suka wuce. Malama Hindu ta kaiwa hajia qibdiyya wayar ta Kuma nuna mata alkhairin kayan da Dr bintu ta baiwa Nawraah. Da ita kanta data Bata dubu biyar ta nuna nata ta Kuma karin tabawa malam Liti dubu daya.
Tayita yiwa hajia qibdiyya godia. Dakyar ta tsaya taci abinci aka Kuma zuba mata wani a kwanon ta.
Hajia qibdiyya ta dauki wayar bayan ta kwashe komai ta hada da chajar ta mikawa malama Hindu Wanda saboda tsabar farin ciki har kukan dadi ta saki...
:::;
Washegari malama Hindu dataje yiwa hajia qibdiyya sallama Nan take sheda mata ai Dr bintu ta kira waya tanata yaba mutinci da iya girkin malama Hindu ta kuma roki alfarmar tunda futa qibdiyya zata tafi haihuwa waje yaranta biyu Kuma zasu yi jamia. Zatayi hutu acan sosai Kafin ta dawo tana rokon Dan Allah malama Hindu ta rika zuwa tana mata abinci saboda Mai gidan ta ya yaba kwarai da miyar da tayi yanata santi..
Dakyar malama Hindu ta amince dubada yadda hajia qibdiyya keta rokon ta...
Nan sukayi sallama da su har yaran na ta da zaa Kai makaranta, junior da Hayfa. Yayinda anees Kuma zaiyi hutu tare da hajia qibdiyya zasu huta idan ta haihu har zuwa wani dan lokaci Kafin su dawo.
Har hawaye malama Hindu da hajia qibdiyya sukayi saboda tsananin sabon da sukai da juna, malama Hindu tana katse hawayen ta tace,
"Nagode hajia .. da dukkanin tarin alkhairin ki gare ni Allah ubangiji ya saka Miki da mafificin alkhairin sa ya bude Miki kofofin albarkar sa. Ya raya Miki zuri'ah ya shriya su tundaga kuruciyar su har gidan su. Allah Kuma ya sauke ki lafiya Amin. Dan Allah idan na Miki wani lefi Wanda nasan da Wanda bansani ba dan Allah ki yafe mun.Allah ya KADDARA saduwar mu ya hada fuskokin mu da alkhairi Amin"
"Ni ce da godia Hindu Allah ya daga Miki yaran ki duk kuwa da kin mun rowar ganin su Kuma bakimin lefi ko daya ba Hindu. Sai ma ni da nasan tabbas na Miki Dan Allah ki yafe mun"
"Ku gafarce ni hajia.abubuwan ne sai ahankali, Amma inshaa Allahu har sai kin gaji da ganin su ma. Ni ke Zaki aurar da su ma. Saboda ki yafemun "
"Inshaa Allahu Hindu. Allah ya yafe mana gaba daya"
Hajia qibdiyya ta rungume Hindu jikinta sukai sallama suna daga mata hannu suka shiga mota direba oga emaka yaja suka tafi.
Yayinda ita Kuma ta shiga motar malam Liti ya sauketa agidah.
Satin ta daya agida Kafin daga bisani Dr bintu ta fara Aiko direban ta yana daukar malama Hindu tana zuwa tana abinci Yana dawo da ita...
Da wannan suka cigaba da rayuwar su.sabo sosai ya shiga tsakanin malama Hindu da Dr bintu. Itaxe yiwa mijin Dr bintu abinci Kuma ya aminta da abincin sosai yana masa Dadi don har kyautar kudi yake bayarwa ayiwa malama Hindu
Wanii lokaci takan tafi da Nawraah don ta tayata wasu aiyukan na gidan aikin nata...
Ranar wata asabar da yammaci.....
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...๐_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*๐ง๐: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)๐๐ฃ_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA๐๐พ_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)๐ฆฉ๐ฆฏ_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR๐๐ฏ๐ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE๐_
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_โ๏ธ:MX_
_26_
:::::::::
*Dukkanin* su a tare ji da ganin su suka dauke na 'yan wasu daki'kai...
Ji ka ke timmmmmm... Bappah junaidu ya fadi wanwars a kasa sumamme ..
Likitan yayi kansa. Ashir ya shiga bubbuga kansa a bango... Yayinda Amnah ke duban su duka tana hawayen itama duk kuwa da karama ce ainun. Ashfeef ya rike hannun ta shima yana rera kukan sa ahankali
Nawraah ta sulale daga jikin bango ta yi zaman dab'as na yan bori...Ta saki marayan kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara....
"Ummy.... Wayyo ALLAH na ummy" Ta shiga maimaitawa tana bubbuga hannuwanta a kasa.
Bappah Auwalu yana tsaye daga bakin kofar dakin bawa marasa lafiya na gaggawa temako inda aka shigar da Bappah junaidu da yayi doguwar suma suna bashi temako don ya farfado.
Nusaiba na gefe tana girgiza kai... Mutuwar Hindu kwarai matuka ta girgiza ta. Hawaye suka shiga zirarowa daga idanun ta ..
Su Layla suka karasa asibitin itada Ahmad... Ganin su suka yi cikin yanayi marar dadi...
Jikin su yayi sanyi. Layla ta karasa wajen Nawraah dake kuka sosai kamar ranta zai fita ta zauna a kusa da ita tana kallon ta,
"Nawraah..... Meya faru? Meya samu ummy? Operation ake ma ta? Ko ciwon ne ya kara tsamari?"
Nawraah ta girgiza mata kai tana zubar da hawaye. Ta saka hannun ta ta share hawayen tace da ita, cikin rawar murya,
"Ummy ta rasu"
"Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un... Ummyn?"
Fashewa tayi da kuka sosai itama ta saka tafukan hannuwan ta akan bakin ta. Ahmad ma ya fara hawayen yana girgiza kansa cikin dimaucewa,
Har tsakiyar dare Bappah Auwalu ya futa ya kawo musu burodi dakyar ya tsawatar musu suka sha da ruwa. Wasa wasa har akayi asubah sukaci sauran burodin...
Wata nurse ta futo daga ciki tana duban su... Kowanne cikin tashin hankali. Bappah Auwalu ne kawai yake kokartawa yana kukan zuciya,
Ta karasa kusa da shi tana masa sallama. Ya amsa ta yana sharce hancin sa da hankici,
"Mashaa Allah an samu ya farfado mun masa allura saboda ya samu nutsuwa . Ita kuma marigayiya idan akwai motar da zaa sakata aciki to idan babu munada kurkura mota ta haya sai a sakata aciki, dubu biyar ne kudin kaiwa"
Ya kada kai yana sanya hannu acikin aljihu zai zaro kudin Nusaiba dake gefe tana duban su ta karasa da sauri,
"Menene ?"
"Kudin motar da za'a saka Hindu aciki ne zan biya meya faru?"
"Har nawane kudin?"
"Menene haka sai? Dubu biyar ne mana "
"Yanzu dubu biyar din zaka kwasa ka bayar?"
"Bakida hankali Nusaiba wallahi bakida hankali "
"To ai gaskia ne. Shi ya bayar mana.... Dubu biyar dinnan idan ka kwasa ka bayar ya zamuyi da sayen taliyar...?"
Dogon tsaki yayi ya girgiza kai cike da takaicin maganganun ta yace,
"Zaki matsa ko sai na hanbare ki?"
"Hanbareni halin naka zaka nuna a bainar jamaa hanbare ni Auwalu"
Kudin ya kirga da sauri ya mikawa nurse din ta koma ciki.
Ya bar Nusaiba a tsaye tanata banbamin mita. Ya nufi wajen Ashir ya riko shi
Ashir din ya fashe da kuka. Bappah Auwalu ya riko shi ya rungume shi tsam a jikinsa
Ashir ya shiga rusgar kuka tamkar karamun yaro yana kiran sunan mahaifiyar ta su
"Ummy... Ummy"
"Dan Allah ku dai na mata kuka, ku dai na zubar mata da hawaye. Addua take bukata yanzu ba zubar hawayen ku ba. Soyayyar kadai da zaku nuna mata yanzu addua ce. Sai tafi bukatar ta. Kuyi hakuri dan Allah. Uhm munyi rashi kam . Allah ya gafartawa Hindu ya kyautata namu zuwan. Bar kuka Ashir dan Allah kaji? Alhamdulillah jikin mahaifin naku ma ya farfado yanzu nurse ta fada. Kuma zamu kai gawar gidah don a sallace ta.,"
"Wayyo Allah na. Ummy na wayyo Allah " Nawraah ta shiga nanatawa tana cigaba da hawaye.
Bappah Auwalu ya shiga wajen da aka rufe gawar malama Hindu da wani yadi shudi baki daya ya rib'e ya koma kalar jini. Saboda tsananin jinin dake futa daga jikinta har yanzu. Tun sanda aka kawo ta. Daman bayan likitocin sun yi gwaje gwajen su angani ta samo karaya takwas. Hudu a kwibi. Biyu kafafun ta daya hannun ta. Yayinda dayan Kuma gefen wuyan ta. Sai internal bleeding shima data samu. Sai Kuma jini daya taru a kwakwalwar ta. Sai ciwo a gefen goshin ta da aka mata dinki har zuwa lebenta. Domin fuskar ta ma ta rabe gidah biyu. Da sauran ciwuka Wanda ba zasu kirgu ba don da tayi rai ma ba lalle ta cigaba da moruwa ba, kasancewar spinal cord dinta ma ya tsinke.
Bappah Auwalu ya saka hannu ya toshe bakin sa da tafin hannunsa alokacin daya shiga dakin yaga an lullube Hindu har kanta. Dankwalin data saka a kanta shi aka rufe fuskar ta. Tabbas kayan data saka ne dazu da ta je gayshe su.
Kwakwalwar sa ta shiga tariyo masa ashe dama bankwana take musu na tafiya tamkar wasiyya? . .
Wani siririn hawaye ya silalo masa ya sharce da bayan hannunsa sa.
Tsayawa yayi aka gama cike ciken da zaai na takardu kasancewar irin wannan idan aka kawo marasa lafiya ranga ranga haka magashiyan, To police na shiga cikin case din.
Don haka anyi dikkanin abunda ya dache daga karshe maaikatan suka Kai gawar malama Hindu cikin mota yar kurkura aka saka ganye agaba da bayan motar
Ballah Auwalu ya tattara kan su baki daya yaje su tafi gidah zaa yiwa malama Hindu wanka a sallace ta...
.
Bappah junaid da allura ta sake shi ya dubi Karin ruwan da ake masa ya fizge shi da karfi ya mike Yana dafa bango ya fita
Likitocin sukai kansa suna kokarin mayar dashi dakin hutun na marasa lafiya atafau yaki yace shi gidah zashi shima a sallaci malama Hindu da shi.
Ba yadda sika iya haka suka kyale shi bayan sun bada maganin da aka saya masa.
Akayi hayar mota ta debe su baki daya suka koma gidah
Ko da suka koma gidan ma sabon shafin alhini sika bude. Masu kuka na yi masu surutai nayi masu dukan kansu nayi.
Aka Kira yaran nasu baki daya lokacin da aka gama yiwa marigayiya malama Hindu wanka aka nadeta cikin likkafini fuskar ta kawai aka bari abude saboda yaran su gana da ita na karshe suyi mata addua. Fuskar ta takara kyau tamkar tana murmushi .
Ataree suka shiga baki daya har bappah Junaid kowanne da addu'ar da yake suna sake bude babin wani kukan mai kuna
"Allah ya jikan ki da rahamar sa Hindu Allah ya yaye Miki dukkanin zunuban ki ya sadaki da ajnabin rahama . Rabbi ya karbi bakuncin ki yasa karshen wahalar kenan. Ba abunda kikai min Hindu idan ma da akwai na yafe miki duniya da lahira Allah ya gafarta miki" bappah Junaid ya karasa fada har yana dora kansa akan gawar bappah auwalu ya fita dashi dakyar.
"Ummy ... Ummy Allah ya gafarta miki Allah ya yafe mi ki, Allah ya sa aljanna makoma agare ki ummy. Ummy na rike alkawarin ki dayardar Allah zan cigaba da rike yan uwana har karshen rayuwata ummy" Ashir ya fada shima ya tashi ya mike ya fita kamar yadda bappah Auwalu yace kowanne idan yayi sai yabar dakin
"Ummy Allah ya jikan ki Allah ya jikan ki ummy Allah ya jikan ki ya gafarta miki ya shayar da ke ruwan alkausara" Cewar Ashfeef ya mike da kyar ya fita yana boye hawayen sa
"Ummy.... Ummy na... Ummy Allah ya jikan Ki da rahama Allah ya gafarta Miki Allah ya kyautata makwancin ki Allah ya sa aljannatul firdaws makomar ki ce, ummy inshaa Allah indai har Ina raye da raina da yardar Allah sai na kwato Miki hakkin ki da dik Wanda yayi Miki wannan mummunan hukuncin . Ubangiji Allah ya dafamun ummy. Inshaa Allah, Allah sai ya tozarta su ya wulakanta su ya d'ai d'aita su. " Mikewa tayi dakyar ta futa tsna sake fashewa dakuka... Nusaiba ta bi bayanta da kallo tana nazari akan kalaman ta na karshe... Suwaye suka kร she Hindu? Nawrah tasan wani abu kenan? Lalle akwai sauran kallo a gaba idan da rai. Domin Nawraah KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA....
"Bappah... Ummy ta mutu yaushe zata dawo eh?" Amnah ta fada tana rike kafar wandon bappah Auwalu .m
"Allah ya miki albarka Amnah Allah ya raya ki ya tsare ki kinji?" Ya fada mata yana kokarin mayarda kukan daya tayo masa
Waje ya futar da ita bakin kofa. Nusaiba dawasu mata makota suka sake rufe gawar malama Hindu har zuwa fuskar ta suka daure.
Aka sanyata a tabarma aka kullubeta da wani zanun aka sanyata a makara. Bappah Auwalu ya kira su Ashir aka sallaceta aka kaita gidan ta na gaskia
Kafin a fitar da ita daga gidan sai da akayi dagaske yaran ta gaba daya da bappah Junaid sika birkice suna riko makarar suna hawaye kowanne yana surutai kamar mahaukata. Dakyar aka banbare su aka fita da ita zuwa makabarta aka binne ta
Ta samu yabo sosai daga bakunan jama'ar da suka santa. Takuma samu mutane sosai da suka halarci jana'izar ta aka sallaceta suka kaita gidan ta na gaskia.
Sannan aka dawo gidah akayi cirko cirko unguwar tayi tsiit. Yayinda zuriyar hamidniyya Lebanon tamkar ruwa ya cinye su saboda alhini . Hakika baa taba musu mutuwa data grigiza su bayan ta yafendo ba sai wannan ta rasuwar malama Hindu, Mai dakin bappah junaidu, Kuma mahaifiyar su Ashir, Ashfeef, Nawraah da kuma auta Amnah...
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...๐_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*๐ง๐: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)๐๐ฃ_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA๐๐พ_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)๐ฆฉ๐ฆฏ_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR๐๐ฏ๐ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE๐_
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_โ๏ธ:MX_
_27_
:::::::::
*Haka* rayuwar ta cigaba da garawa.... Bayan kwanaki arba'in da rasuwar malama Hindu. Dangi na kusa dana nesa duk sun Kokkoma inda suka fito. Yayinda kowanne ya cigaba da rayuwar sa idan ka cire ahalin na malama Hindu da mutuwar ta dake su kwarai matuka...
A Kwanakin ne Kuma hajia qibdiyya dake kasar waje ta kira wayar malama Hindu dake hannun Ashir.
Ya amsa mata bayan sun gaysa ne data tambayi malama Hindu yake sanar mata cewar ai Allah ya mata rasuwa tun kwanaki...
Hakika mutuwar ta daki hajia qibdiyya ji tayi tamkar da Wasa ko Kuma waswasi kunnenta yake mata sai data sake tambayar sa har sai uku Yana tabbatar mata sannan ta amince.
Kuka ta fashe da shi tun awayar tana sallallamin wallahi batada masaniya. Don kwana biyu itama wayar tata bata hannunta sakamakon ta haihu dan ba rai kuma ciwon ta ya tashi na hauhawar jini sai da mai gidan nata ya sake zuwa yayi ciku ciku ya sake canza date din ranar da zasu dawo zuwa dogon zango mai nisa.
Ashir sai ya koma bata hakuri jin tana kuka sosai mutuwar ta dake ta. Dakyar ta iya kashe wayar bayan ta bashi mai gidan ta Dr. Dollars ya musu gaisuwa. Ta Kuma bawa yaranta daya bayan daya sunyi musu gaisuwa ta wayar. Ta kashe wayar jikinta asanyaye
Sai datayi kuka ta koshi sosai har sai da zazzabin ya tasar mata ta kira Dr bintu a waya don tasan Kila batada masaniya bata gaya mata ba bayan sunyi waya jiya da su .
A handsfree ta saka wayar bayan sun gaysa. Murya a cike da alhini tache,
"Baki da labarin rasuwar da akayine Dr bintu ko kuwa mantawa kike baki sanar min?"
"Rasuwa kuma? Rasuwa fa kikace? Waye ya rasu? Kinganni a zaune Kinsa na mike a tsaye. Bangane ba waye ya rasu eh?"
"Hindu dai mai aikina da ke maki aiki a yanzu"
"Innnalillahi wa Inna ilaihi raji'un. Wallahi bansani ba. Yaushe ta rasu? Rannan tazo da yamma kamar yadda nace mata tazo da yamma tayi abinci wlh har take cewa zata dena aikatau. Naceto shikenan. Dama inata cewa kwanaki biyu shiru idan nakira wayar ta ma a kashe nache to inaga hutawar take bari nan da kwanaki kadan sai na kirata ko naje da Kai na na Kai mata kudin sallamar ta wannan watan meya sameta ? Zazzabin nan da akeyi ko Kuma