Author : Nana Hafsatu Category : Love Story
tunda ummyn ta rasu ya dawo tamkar ba shi ba ya zama shiru shiru baya magana gaba daya sai ta kama. .
"Nawraah... Menene haka?" Bappah junaid yace da ita yana kallon ta
Dr. Bintu gabanta ya tsananta bugawa tayi hanzarin seseta kanta. Bappah Auwalu yace,
"Nawrah ya Isa. Ai da yardar Allah Hindu yar aljanna ce. Lokacinta ne yayi. Kuma wannan koma wanene kowacece da sukayi aika aiken nan sai dai muce ubangiji Allah ya saka mana ya biya mana hakkin mu a madakata. Allah Kuma ya bayyana mana su tin a duniya. Hajiya kiyi hakuri kinsan yarinta. Nawraah, Tunda akace a titin nan haka ta rasu kinsan tare ranar suka fita. To abun ya tabata sosai ne wallahi" bappah Auwalu ya ce da dr bintu cikin tabbatarwa
Tayi murmushi tana kallon Nawraah tace,
"Nawraah Allah ya gafartawa mahaifiyar ku kinji? Wallahi banida masaaniyar mutuwar ta ma sai da yar uwata kawata hajia qibdiyya uwar dakinta ta farko ta kirani take gayamun dazu. Wallahi sai na kasa zaune na wuce ofishin mai gidan nake sanar masa. Abubuwa sun masa yawa shi Kuma. Shine fa yace na kawo kayan abincin Kafin yazo. Kuma wallahi nima inata Kiran wayar ta a kashe don nayi mamaki ma da hajia qibdiyya tacemun ta samu wayar Hindu nan take sanar mun ai Hindu ta rasu Kuma accident nema muka kiyasata ranar da tazo gidah na ne ai . Wallahi na shiga dimuwa fiyeda yadda baki zai furta. Don kudin aikinta na wannan watan ma wallahi bata karba ba. Yana waje na, Gasu ma nace bari na kawo . Allah ya jikan Hindu ya gafarta mata"
"Ah kin kyauta. Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa .. Amin"
"Allahumma Aameen. Ni zan tafi sai mai gidan na wa yazo inshaa Allahu, Nima zan sake waiwayowa. Allah ya baku hakurin rashin ta"
"Ko ruwa baa kawo miki ba" nusaiba ta fada tana mikewa tsaye itama
Dr bintu tace da ita,
"A koshe nake karki damu. Nagode. To sai anjiman ku"
"Sai anjima, Allah yabada ladan "
Ficewa tayi da sauri nusaiba tabi bayanta tana cewa da ita,
"Angode sosai... Sai da safe."
Dr bintu ta daga mata hannu kawai alamar bye bye, ta shiga bayan mota da sauri driver yaja suka tafi. Ta saka hannunta akan kirjinta saboda yadda yake mata duka.
Tiryan tiryan maganganun Nawraah suka shiga mata yawo a kwakwalwa, Wannan wace iriyar yarinyar ce ne? Bata mantuwa? To me take tunani kenan! ? Lalle wannan yarinyar sai anyi dagaske akanta kar ta ballo musu ruwa
Duk kuwa da yadda ac din motar ke turarawa hakan bai hana tashin hankalin da Dr bintu ke ciki ba jikewa jagab da ruwan gumi tamkar tayi wanka da kayanta a jike..
Har suka koma gidah bata daina nazari akan maganar da Nawraah tayi ba...
Tirk'ashi!
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_30_
:::::::::
Tana zaune akan sallaya tun sallar asubah data tashi bata koma bacci ba, Bacci ya kauracewa idanun ta ..
Kamar ko da yaushe tana karanta wasu surori na daga cikin alqur'ani ta ciki harda su suratul Kauthar da Mulk ta roki Allah ladan ya kai wa mahaifiyar su ummy da sauran musulmai baki daya da suka rigamu da gidan gaskia ..
Mikewa tayi bayan ta karasa sauraron addu'oin ta tayi azkhar. Bandaki ta shiga ta dauraye shi kasancewar akwai wuta. Kuma da ruwa ko'ina a cike...
Ta dubi autar su Amnah dake baccin ta ahankali tana sauke numfashi. Ta rankwafa tana duban fuskar ta sosai. Daman kanwar tasu duk cikin su tafi su debo kama da mahaifiyar ta su marigayiya Hindu .
Kallon ta take tana hasaso fuskar ummyn ta su. Da tana raye da tuni yanzu tana kasa ta fara hada karin kumallo da kintsa gidah da sauran su ..
Hawaye sirara suka shiga zirara daga idanun ta ta saka kasan dankwalin ta ta goge..
Mikewa tayi ta sauka kasa don sharewa, ko'ina tas an share har da dorin kamshin turaren wuta na tsinke dake ci daga gefen wata huda..
Motsin karar kwanuka data ji ne daga kitchen yasa ta nufi kitchen din tana kiran sunayen,
"Hamma ne ko Hamma Ashfeef?" Ta karasa shiga cikin kitchen din bakinta dauke da sallama.
Ashir ne a tsaye, Yana gyara zaman kwanuka acikin kwando.
"Hamma" Ta kira sunan sa
Ya juya jin kamar an kira sunan sa. Yana hangota yayi murmushi yana goge hannuwan sa ajikin tsumma,
"Nawraah"
"Naam Hamma... Ai nayi sallama na kira sunan ka baka ji ba"
"Banji ba Nawraah. An tashi lafiya?"
"Alhamdulillah Hamma. Ina kwana?"
"Alhamdulillah Nawraah..."
"Hamma ai nace ka barshi zan dinga yi Allah. Naga har shara kayi ka gyara ko'ina"
Murmushi Ashir yayi, Yana shanya tsumma akan wani karfe yace
"Kaki damu babu komai ai.... Duk yiwa kai ne, Na gaya miki ai nace ki dinga wanke bandakin sama kawai kina gyara dakin ku dana abbiey. Kasa zan gyara inshaa Allah. Namu bandakin Kuma Ashfeef zai dinga wanke shi. Kije ki koma ki kwanta oh ba da makaranta ba yau kuna da exams?"
"Hamma Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa. Ai bana jin bacci tun Kiran sallar fari. Zan dai yi wanka sai nazo naga abunda zaa dafa"
"Kakki damu ai na dafa shayi tun jiya Kuma an sayo biredi."
Hawaye ne ya cika idanun ta taf. Ashir ya dubeta yana girgiza mata kai,
"Mayar da wannan kukan na meye?"
"Hamma dukkanin abubuwa da kake ko ummy na nan sai haka. Gaba daya baka hutawa"
"Idan banyi muku ba wanene zai muku Nawraah? Bakisan cike nake da farin ciki ba idan Ina taya wasu abubuwan na aiyukan gidah? Banda wani babban burin daya wuce naga farin ciki shimfide akan fuskokin ku. Nawraah ummy da kanta ta bani amanar ku tun da ranta... Don haka duk abunda kikaga nayi muku wallahi ban fadi ba. Fatan Allah ya buda mana duka ya yalwata mana kofofin arzuka Amin. Allah Kuma ya jikan mahaifiyar mu da dukkanin musulmai baki daya Aameen"
"Allahumma Aameen Hamma.. Tohm shikenan. Allah ubangiji ya dafa maka ya shi maka albarka ya baka mata tagari Amin"
Murmushi yayi jin ta ambaci maganar auren sa. Ta kalle shi tana murmushin itama tace,
"Hamma ko budurwa ma baka da ita fa ko meyasa oho"
"Nawraah ai yanzu ba lokacin kule kule yammata bane, Ta gidah ake yanzu bana waje ba. Idan komai yayi normal agidah sai mu duba mugani."
"Amma Hamma lokaci na kurewa ai"
"Aa fa... Komai da nasa lokacin ballantana ni bana son kule kulen yammatan nan haka. Fatana kawai Wanda zan nema ma ta kasance ita zan aura kingane? Banason yaudara. "
"Hakane kam Hamma Allah ya dafa maka adukkanin abunda ka cinma buri."
"Allahumma Aaamin Nawraah"
"Ga ruwan zafi nan a bokiti ki juye kiyi wanka zan Kara wannan da zai tafasa akai Wanda ya riga tashi bayan ke sai yayi wankan"
"Tohm Hamma yanzu kuwa. Bari naje nayi"
Ta dakko bokiti ta debi ruwan ta haye bandakin su na sama tayi wanka. Tanata sauri tana shiryawa kasancewar a yau ne zasu zana jarabawar su ta karshe ta gama sakandire.
Tana cikin shiryawa Amnah ta tashi lokacin garin har yayi haske. Tayi mata wanka ta saka mata kaya suka sauka kasan a tare
Abincin karin kumallo suka ci. Suna cikin ci Ashfeef ya tashi shima yayi wanka ya shirya zuwa kayan aiki zasuyi fenti ra fenti don sun samu aiki na fente wani site da ake ginawa...
Daga baya ba jimawa bappah junaid ya sakko sika gayshe da shi baki daya. Dakyar yaci abinci kadan ya tashi ya koma sama yayo wanka bayan Ashfeef ya Kai masa ruwan zafi sama.
Nawraah taje tayiwa bappan su sallama sai ta dawo, zata tafi zana jarabawar ta ta karshe ta kammala sakandire, Yayi musu addu'ar temako da samun nasarar jarabawar.. ya dakko kudin break ya bata, tayi masa addua ta futa rike da hannun nawrah kasancewar zata kaita gidan bappah Auwalu Kafin su dawo tunda Hamma ma dashi zaai aikin fentin...
Ta kai Nawraah gidan bappah Auwalu wajen Nusaiba. Daga nan ta jira Layla ta karasa shiryawa suka nufi makaranta don zana jarabawar..
Da misalin karfe hudu na yamma sika kammala zana jarabawar karshe ta sakandire... Sai fatan samun nasara da dinbin fatan alkhairi ga sabbabin kofofin rayuwa da zasu bude.....
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_31_
:::::::::
To haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa, Yau da dadi gobe babu sai hamdala kawai.
Nawrah ta gama zana jarabawar gama sakandire baki daya. Ashir ya sanyata a wani lesson school na marasa karfi nan kusa da su. Nusaiba ma dataga hankalin ta ta tursasa bappah Auwalu a dole ya nemo kudi ya saka Layla...
Ashir tun daya kammala sakandire Yayi national diploma bai sake cigaba ba. Malama Hindu nata ciku cikun kan zata fara tarun kudi sosai ta turashi babbar jamia yayi karatun acan Allah beyi ba ta rasu.
Ashfeef Kuma daga sakandire bai sake cigaba ba shi bayason karatun sosai. Don haka bappah Junaid ya ce a kyale shi ya huta, Nan gaba dole ya zabi daya ko karatu ko shiga kasuwa...
Amnah ce kawai bata fara zuwa makaranta kasancewar karancin shekarun ta da kuma yawan lalura da take da ita, Amman duk da haka Nawraah na zama da ita ta koya mata karatun dai dai shekarun ta..
Haka zalika bangaren gidan bappah Auwalu ma Layla tare suka gama sakandire da Nawraah. Ahmad yayan Layla, Bai cigaba ba tun da yakare sakandire daman ajin su daya da ashfeef shima yaki karatun wai yan buga kwallo yake so yayi shi da ashfeef din.
::::::::::
Dawowar su daga lesson kenan ta hango yayyun nata acikin kewayen da suke toya awara.
Kifta idanunta tayi ta sake gogesu da tafukan hannayen ta. Ba gizo bane, Yan uwan nata tagani suna kokarin hada murhun yin awara
Rabon su da yin awarar tun mahaifiyar su malama Hindu na da rai
Wasu hawaye suka ziraro mata da hanzari ta goge tana nufar su.
"Hamma..."
"Ah Nawraah kin dawo?"
"Na dawo Hamma .."
"Toh maza aje a sauya kayaki yi aikin da aka baku na karatu na gaya, Miki jarabawar jamb dinku na dada karatowa sai ki dage sosai da addua da yin karatu"
"Inshaa Allah Hamma. Amma bari nazo na taya ku awarar za'ayi?"
"Eh awara zamu cigaba da yi Nawraah. Kakki damu Ashfeef ma nace masa ya barshi ni zan toya ta tunda batada yawa yaki." Ya karasa fada yana bin Ashfeef da kallo yana grigiza Kai
Ashfeef dake gefe yayi murmushi Yana gyara itatuwan yace,
"Haba Hamma abubuwan suna maka yawa ai. Badan yunwa ta dawo da ni bama ai kullum sai dai na dawo na tarar ka kammala komai. Dan dai yau Ina gidah na tayaka. ? Inshaa Allah tun da dai zaa cigaba da yi zan dinga zama da rana zuwa sanda zamu karasa inshaa Allah" Ashfeef ya fada cikin tabbatarwa...
Hamma Ashir yayi dariya, Yana cewa,
"Gayu agaban murhu? Aa fa jeka cigaba da abubuwan ka bros. Aini nayi niya ba wani ne ya saka ni ba.",
"Aa nima inason na samu lada Hamma, Nawraah Kafin nazo fa naga ya gama komai har awarar ya yanka ya daka yaji ya sayo ledojin yayi komai ya hada wutar murhu daya zai hada wannan wadda nake yi yanzu sai gani nayi saurin karba na fara hadata"
"Wallahi Hamma Ashfeef haka Hamma yake kullum baya gajiyawa. Fatan mu Allah ya shi masa albarka kawai.”
"Haba Nawraah gajiyawa? Da ku Yan uwan nawa? Yo idan ban muku ba wa zan wa eh? Ai kune priority dina. Allah yasa mu dace"
"Aamin Hamma. Amma dan Allah kayi hakuri Zan zo na dinga zuzzubawa a leda idan an saya... "
"Shikenan tunda kikace Allah ai roko ya kare."
Shigewa cikin gidah tayi da sauri. Cikin kankanin lokaci ta sauya kayanta zuwa wata riga marar nauyi ta yafa wadataccen nayafi na ummy nema, Ta lullube kafafuwan Amnah dake bacci akan kujera , ta futa tsakar gidan inda suke hada aikin awarar ta janyo kujera ta zauna.
Nan da Nan kuwa mutane suka fara turuwar zuwa sayan awarar. Ba kadan ba daman sunyi kewar rashin yin awarar da ba ayi, Duk da sunsan iyalin suna alhini rashin mahaifiyar su ne........
To haka rayuwar ta su ta cigaba da garawa, dare ya zama safiya, safiya ta zama Rana, Rana ta zama yammaci . Yammaci ya koma dare. Lalle Allah buwayi ne gagara misali...
Nawrah sun zana jarabawar su ta jamb sun Kuma ci inda suka rubuta gurbin jami'oi biyu da polytechnic daya na:
Jami'ar Al-Haramein Naduka mai zaman kanta da ke Naduka crescent (apple island)
Jami'ar gwamnatim tarayya ta Naduka
Da Kuma makarantar polytechnic ta koyan jinya Wanda ke cikin babban asibitin na Naduka..
Cikin ikon Allah Kuma sun samu gurbin karatu a jami'ar Al-Haramein Naduka mai zaman kanta dake Naduka crescent apple island.......
Jami'ar da yayan masu farcinan Susa ne sike zuwa da manyan kusoshin gwamnati da yayan Yan siyasa Dana Yan kasuwa da manyan malamai da masu sarauta. Kai harda ma dalibai na ketare dake halartar karatun a jami'ar . Saboda tsananin kyawunta da Kuma gogayya ta yayan masu kudi. Don babu talakawa sai dai ko Yan scholarship shima tuni an dai na dauka saboda yaran masu kudin daga cikin su since basu San gogayyar rayuwa da yaran talakawa a daina kawo musu su.. abunka da masu fada aji, Nan da Nan kuwa aka dena daukar daliban tallafin ya zama sai yayan wance da wane.. who is who?!!!
Ko da Nawraah taga sakamakon inda gurbin karatun su ya fito.. tuni jikinta yayi sanyi don tasan abune da bazai taba yiwuwa ba inde ba Allah ne ya amince da faruwar hakan ba. Basuda kudin da Za’a iya kaita gurbin karatu a makarantar..
Ta kalli second choice dinsu itama jamia ce ta kasa . To idan ma ai abbiey ba zai iya biya mata ba..
Ta daga kasan kayanta kawai ta saka takardar ta cigaba da harkarta...
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_32_
:::::::::
....
_GIDAN ALH. SAMBASO_
_Yana_ daga kasan carpet a zaune rike da waya a hannun sa yana daddannawa...
Dr. Bintu na gefen sa ta rike kofin shayi a hannun ta tana sha ta dube shi,
"Kaje kuwa?"
"Ina fa?"
"Maganar me nake maka naci constantly?"
Ya dubeta yana dan daga kansa sama alaman tunani,
"Maganar zuwa Texas da kikace ?"
"Alhaji! Dan Allah ka dai na dodging idan muganar nan sarai kasan me nake nufi"
"Sanar da ni, ganar da ni",
"Ina maganar zuwan ka gidan marigayiya Hindu.”
"Ah ba nasaka a sake tura musu kayan abincin ba me suke bukata Kuma?"
"Haba Alhaji, kaje ka musu gaisuwar ta’aziyya mana"
"Ai lokaci ya kure"
"Gaisuwa bata rub'a ai... Ko shekara nawa ne kaje ka musu gaisuwa ai bata tsufa zasuji dadi, sannan kin zuwan da kake ne zargi zai shiga tsakani. Na gaya maka ai abunda yarinyar tasu Nawraah tace. Ita wadda suka zo ranar da marigayiyar ta rasu"
"Zanje kakki damu"
"Haka kake fada sau ba adadi
"Jibi inshaa Allahu zaa muje"
"Toh shikenan . Allah ya Kai mu"
"Aameen."
:::::::::::::::::::::::::
Ranar talata bayan sallar magriba. Alhaji Sambaso da mai dakin sa Dr bintu suka je gidan na Bappah junaidu.
Suka