Author : Nana Hafsatu Category : Love Story
shiga tamkaar wasu mutanen kwarai musamnan Alhaji Sambaso da harda hawayen makirci wai na tausayin iyalin data bari.
Su bappah junaidu suma sun karbe su hannu biyu. Bayan ya tashi zasu tafi ya dakko kudi ya bawa Amnah .
Inda yake ta mamakin ai bai ma san Bappah junaidu mijin marigayiya Hindu bane kasancewar a kamfanin sa yake aiki na kera makeri na gidaje aluminium da sauran su...
Ya sake dakko wani kati ya mikawa bappah junaidu yace da shi ya Kira wannan number yazo zai bashi wani aikin dayafi wanda yake yi..
Suka shiga yi musu godiya Alhaji Sambaso yanata kada mukullin hannun sa na mota yace,
"Zamu shiga cikin case din zamu gano Wanda yayi wannan aika aikan . Amman Kafin sannan ku kwantar da hankulan ku ku bar mana komai a hannun mu. Ni zan samu dakarin farin kaya na tsaro na kasa zamuyi magana sosai zaa zurfafa bincike inshaa Allah"
"To shikenan angode Allah ya saka da alkhairi"
"Aaameen Alhaji. Angode kwarai” Cewar bappah Auwalu.
Suka musu rakiya har kofar gidah bappah Auwalu yanata kambama mutincin su.
Alhaji Sambaso ya ja motar suka koma gidah zuciyar su fari fat ya dubi dr bintu yace,
"Kinga ai na wanke su. Nan gaba kadan ma zan sake zuwa na yi musu wani hidimar"
"Ka debi a hankali Alhaji ba damuwa."
“Ai ni banida masaniyar mai gidan ta. Ai a karkashi na yake aiki a kamfanin yankin dalla. Zan bashi babban aiki gaskia”
“Yauwa hakan ya yi..”
::;;;
To haka rayuwar ta cigaba da garawa.
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_33_
:::::::::
Amnah yau lafiya gobe babu. Sunata zuryar asibiti duk kudaden hannuwan su suka kare.
An mata tasa tasai an gani tanada ciwon tonsils shi ke sakata amai da yunkurin aman. Sannan typhoid ta mata illa..
Bappah junaidu bayasan bin mutane ko yan uwan sa yana cewa su temaka masa. Don haka ya saka gidan su jingina bada masaniyar kowa ba ya karbu kudin aka yiwa Amnah aiki da shi aka kwantar da su a asibiti sukayi jinya sosai.
Sai bayan da aka sallamo su ne bappah junaidu ya shirya ya tafi ofishin da Alhaji sambaso ya bashi katin.
Ya nufi unguwar har kamfanin akace ya shiga. Ya nufi ofishin zai shiga ya ja ya tsaya jin da akwai mutane aciki suna magana.
Har zai juya yaji an ambaci sunan sa da na matar sa. Sai kuma ya jiyo suna maganar tarin dukiyar dr Abubakar dollars dayake so ta zama mallakin sa har ya saka hannu. Can kuma yake gayawa mutumin, Tsautsayin daya same shi na niyyar illata Malama Hindu sai kuma ya kasheta har lahira. Kafafun Bappah junaid suka gaza daukar sa. Ya sanya hannu a baki ya toshe saboda wani abu daya taho masa. Kafafun sa suka gaza daukar sa. Ya nemi jikin kofar ya jingina saboda wani yanayi na tashin hankali daya samu kansa aciki.
Alhaji sambaso suka gama magana da mutumin na ciki sukayi sallama. Mutumin ya tashi ya nufi kofa zai tafi.
Laptop din Alhaji sambaso ta fara karan shigowar waya ta app ya dauka yana murmushi kasancewar video call ne…
Alhaji ateeks na daga masa hannu yana bude kofar sai ga Bappah junaidu fuskar sa shabe shabe da hawaye. Alhaji ateeks ya dube shi ya wuce dan baisan waye ba ma.
Alhaji sambaso ya ja hannun sa ciki yana rufe ofishin. Ga video call din nata tafiya. Na ciki yanata 'hello hello' yana duban sa.
“Meyasa ka kashe mana Hindu? Me ta maka?”
Alhaji sambaso ya bude baki yana shafo keyar sa yana hura iskar bakin sa mai zafi yace...
"Bangane me kake nufi akai ba. Hankalin ka daya kuwa kasan me kake cewa?"
"Na sani mana, da hankali na duk na ji dukkanin abubuwan da kuke fada, Kai da abokin ka. Kun hada kai kun kwato duniyar Dr abubakhr dollars ta karfin dole. Kun kashe Hindu meta muku? Shin akan wani dalili kuka kashe mana hindu? Ashe kai ka bigeta a mota ka kasheta Alhaji? Yanzu duk wadannan kayan abinci da kake aika mana da sauran su dama duk toshiyar baki ne? To Allah ya tona asiirin ku wallahi Allah kuwa daga yau zaka kwashe kashin ka a hannu"
Ya saka hannu akan mabudin kofa da niyyar murzawa ya fita Alhaji Sambaso yayi hanzarin riko hannun nasa yana duban sa sosai,
"Ka tsaya muyi magana ta hankali ba abunda kake tunani bane"
"Babu abunda zanji. Kuka samu kanku gaban hukuma zakuyi bayani, yanzu a yau zan bankada dukkanin kofofin sharrin ku. Mugaye kawai. Allah ya yi wadai da halayen ka"
Ya sake kai hannu zai fita Alhaji Sambaso ya tare hanyar ya riko shi yana duban cikin idanun sa yace,
"Kasan wanane ni kuwa! ? Na ga alamar ba hankalin ka kake ba, wannan zantukan, Idan kudi kuke bukata zan baka ishasshe yanzu. Dan naga alamar rashin su ya fara taba maka kwakwalwa kake ta surutun magana da sambatu acikn ta"
"Wai ka dauka kudi na sayan mutane? Ka dauka dukiya itace kwanciyar hankali? Ka dauka dukiya itace maganin damuwa? To ka bude kunne ka kaji. Daga yau kwanan ka a doren duniya cikin gidan ka babu kai babu kwanciyar hankali. Inshaa Allahkashin ka ya bushe. Police station zan tafi wallahi wallahi " ya fada yana duban sa cikin tsantsar tsana.
Alhaji Sambaso yayi hanzarin riko kafadunsa. Bappah junaidu ya fuzge. Alhaji ya sake riko shi. Suka shiga kici kici har zuwa wajen wata baranda. Bappah junaidu ya jinga a jikin bango yana magana cikin fushi
Jiyuwar nan da Bappah Junaid yayi Alhaji Sambaso ya hada shi da karfen baranda yana dukan cikin sa.
Ya daga hannu cikin tsantsar tashin hankali da tsana ya shararawa masa mari
Alhaji Sambaso ya rike kuncinsa, Yana duban bappah Junaid daya sake daga hannu zai kauda masa wani , Alhaji Sambaso ya jinginar da shi a jikin baranda, bappah junaid ma ya tattake ya buga shi da kofar.
Alhaji Sambaso cikin hazalar fushi ya cakumi wuyan bappah junaid ya hankada shi da karfunan barandar.
"Kashe ni zakai? Nima ka mar yadda ka kashe matata?"
Alhaji Sambaso ya saka hannu, Yana rufe bakin bappah Junaid dayaki ya sake cakumar sa. Alhaji Sambaso ma ya riko tasa yana sake cakomar rigar sa yace,
"Shashasha"
"Kai ne shashasha, Mugu, Azzalumi...."
Garin riko shi zai naushe shi ya hankada shi. Bappah junaidu ya fada kasa ji kake 'Timmmmm
Kamar kara ya fada, Take kansa ya fashe bai shura ba ya mutu awajen alokacin....
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_34_
:::::::::
Rufe bakinsa yayi da sauri, yana zare idanuwa jin muryoyi suna kururuwa daga waje lalle da alama mutumin ya mutu....
Tun sanda mutumin ya shigo dama yayi hanzarin danna recording kiran na video call da sukeyi....
Alhaji Sambaso ya saka hannunsa ya shafo kasan keyar sa, Yana rufe bakinsa da tafin hannun sa....
"Naga kaman labarai kake kalla ko? Bari na kashe na sake kira yanzu nima zanyi abune?"
Ya jiyo murya daga cikin laptop. Dama bai katse video call din ba? Ai baki daya ya manta.
Ya dafa teburin yana kallon sa ta cikin system din yace
"Dama baka kashe ba? Me kake nufi da labarai? Ka saurari maganganun da nake fada ne?" Alhaji Sambaso ya tambaye shi cikin tsananin tashin hankali
Ya girgiza kansa yana bashi amsa da
"No da naga Jana kallon labarai ne kome. Magana sama sama sai na tashi na shiga bandaki fitowata kenan kuma naga kaman da kanta ma muna waya"
"Ka tabbatar abunda ka sani kenan?"
"Eh mana... "Ya kakaro daria ya sake cewa,
"Futsari na tashi nayo ma sai na tsaya na karba parcel dina da aka kawo yanzu"
"Oh okay. To shikenan zamuyi magana, yanzu zamu shiga meeting ne " ya katse kiran yana rufe laptop din baki daya..
Zagayawa yayi ta kofar baya emergency exit dinsa wanda ba kowa bane ya sani a kamfanin ya fita ta ciki ya koma kasa...
Nan da nan maaikatan wajen suka fara taruwa akan gawar bappah junaidu....
Da sauri wasu maaikatan suka nufi ofishin nasa suka bude baya ciki. Aka dudduba bayan ko'ina
Nan suka shiga fara kiraye kirayen wayar sa. ... Ya fito daga cikin wani guri a kasan kanfanin da suke kira da lodge .
Daki ne da parlor da bandaki inda manyan maaikatan suke shiga su huta.
Nan ya futo daga ciki yana mitssika idanu,
"Ah ranka ya dade ashe baka cikin ofishin na ka?" Cewar wani leburan kamfanin daya nufe shi yan yana tambayar sa. Duk sauran maaikatan suka yayyabe su.
Alhaji Sambaso ya saka hannu yana rufe bakinsa alaman hamma ce tataho,
"Alhaji ayi hakuri amaana afuwa, Ashe hutawa ma kake"
"Wallahi kuwa bansamu bacci bane gaba daya nache bari na dan huta. Bayan tafiyar Alhaji ateeks"
"Ranka ya dade wani mummunan labarin ne ya faru"
"SubhanAllah Allah yasa muji alkhairi meya faru kuma?"
"Wani ne ya fadi daga barandar ofishin ka...
Kafin su karasa maganar da suke. Alhaji Sambaso ya katse su cikin buda baki yace,
"Ba dai junaidu ba da yazo duba gyaran da zaa mun a barandar"
"Allahu Akbar kabiran. To shine... Bawan Allahn nan yazo dazo yake tambayar mu wajen ka muka nuna masa ofishin ka . Dama bakuwar fuska ne kam. Amman daya nuna katin ka dinnan nasan babban bako ne shysa ma muka kyale shi ya shiga. Ashe ashe ajalinsa ne ke kiran sa. Kuma akwai tsani fa a bayan kofar bai duba ba kenan ya taka karfen dama karfen ai girgidi yake"
Alhaji Sambaso farin ciki ya taho masa ya danne don kar su gane. Ba kadan ba yaji dadi da daya ji daya a cikin maaikatan yace dama karfunan barandar suna girgidi..
Wucewa yayi gaba tamkar Wanda yake cikin tsananin tashin hankali .mutanen suka rufu akansa sam ba dadin ganin gawar ma ta bappah junaid. Aka dakko kyalle aka rufe shi.
Alhaji Sambaso ya sanya aka kirawo ambulance nan da tazo aka fara wucewa aasibiti aka gyara shi sannan aka kira gidah da number Ashir dake cikin wayar ta bappah junaidu.
Nan ake sanar dashi zaa kawo gawar mahaifin su ya fado daga benen barandar me tsananin tsayi ya rasa rayuwar sa yanzu ma gasunan akan hanyar motar kwana kwana sun biya ta asibuti an gwada gwaje likitoci sun tabbatar ya rasa ransa..
Ashir baki daya dama suna zazzaune a parlor ne. Ya na tsaye wayar ta fadi daga kunnen sa yana salati
"Menene Ashir? Menene ?"
"Hamma menene?"
"Ashir Ashir menene?" Bappah Auwalu ya shiga girgiza kafadun Ashir. Ashir yana zubar da hawaye duk tsananin dauriyar sa jikin sa na rawa yace,
"Abbiey ne..."
"Abbieey din. Meya same shi meya samu junaidun?"
"Bappah.... Abbiey ya ra su... Abbiey ya rasu bappah "
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.......
Bappah junaidu ya ambatada da karfi gwiwoyin sa sun gaza daukar sa ya zube awajen ya fara kuka sosai tamkar karamun yaro ...
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:01] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_35_
:::::::::
Nawraah na sama ta sakko rike da bokiti a hannun ta da kaya aciki. Tana murmushi tana taka kafafun benen tana sakkowa tace,
"Hamma! Yau ni ma na rigaka Ina son na samu lada.... Na wanke kayan abbiey daya cire jiya. Yana dawowa zan gaya masa"
Tana sakkowa ta tsaya tana duban su. Yadda sukai cirko cirko masu kuka nayi masu salati nayi.
"Menene?" Ta tambaye su jikinta a sanyaye ..
Duk sukayi shiru suna kuka sosai. Ta karasa kusada da Layla ta dafa kafadarta,
"Meya faru ? Eh? Menene? Wane ne ba lafiya ko wani abun ne na daban?"
Layla ta daga fuskarta sharkaf da hawaye ta saukar ta akan Nawraah tace,
"Bappah ne?"
"Bappah sani Bappah salisu ko bappah Auwalu? Meya same su bappahn?"
Layla ta sake girgiza mata kai tache,
"Bappah junaidu?"
"Bashida lafiya? Wani abun ne ko? Daman yadda kwana biyu abbiey yake yi nasan bashida lafiya. Me akace ya same shi?"
"Nawraah. Abbieyn ku Allah ya masa rasuwa"
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un..." Ta fada da karfi ta zube awajen a sume.
Sukai kanta da sauri. Bappah Auwalu ya saka aka kawo ruwa aka yayyafa mata. Ta farfado da kyar tana wani irin sauke numfashi mai nauyi tamkar zata shide..
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un... Bappah Auwalu ku tasheni daga baccin da nake.. wai abbiey ya rasu? Abbiey fa kukace? Abbiey ya rasu fa kukace? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un. Wannan wane irin wasa ne? Layla meyasa zaki ce abbiey ya rasu akan wane dalilin abbiey zai rasu eh?" Ya karasa fada tana sakin dariya harda tafa hannuwa tamkar sabuwar marar hankali, can kuma ta saki kara mai razana ta fashe da wani irin kuka tana birgima.
"Wayyo Allah na. Abbiey. Wayyo Allah na! Wayyo Allah na Ummy. Wai abbiey shima shikenan ya rasu ya bar mu? Abbiey ya tafi shima? Ummy ma tarasu fa? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un. Waya kashe mana abbiey? Kashe abbiey sukai. "
"Kiyi hakuri Nawraah babu Wanda ya kashe junaidu kinji. Lokacin sa ne yayi. Kinaji daga wajen aiki ne wai a karfen baranfa ya taka shine ya fado rai yayi halinsa sun akai shi asibiti ma ance ya cika. Yanzu sun taho kawo shi gidah. " Ya karasa fada mata shima yana sake barkewa da wani kukan
Baki daya sai suka bude shafukan kuka. Nusaiba daga can gefe tayi shiru itama kanta a kasa. Hakika mutuwar kanin mijin nata junaidu ta razananta kwarai matuka. Agubi agubi anyi musu mutuwa biyu kenan ajere ba daukar lokaci.
"Shikenan Hamma bamuda iyaye? Abbiey da ummy sun rasu? Shikenan bamuda sauran gata ko Hamma? " Ashfeef ya fada yana girgiza kai.
Ashir ya katse hancinsa Yana goge hawayen fuskar sa yace,
"Ga mota can inaga sune..."
Dunguma sukai suka fita wajen ...ambulance ce ta kawo shi har kofar gidan suka shigar dashi gidan bisa jagorancin maaikatan..
Daya daga cikin leburan dake kamfanin na Alhaji Sambaso yace,
"Ina wunin ku? Kuyi hakuri fa. Allah ubangiji ya gafarta masa.ya kyautata namu zuwan Allah Kuma ya baku hakurin rashinsa...wallahi Yana gyaran wani bangare ne dake babbar barandar ofishin mai gidan mu. Ashe bai hau tsaani ba sai yahau karafunan barandar a haka ya taka. Su Kuma dama rawa sukeyi shine ya fado Allah yayi masa rasuwa. Domin kwanyar kansa ma afashe take... Inshaa Allahu aljanna makoma ce agareta shi. Yanzu zamu jira a gama wanke shi sai mu sallah shi mu Kai shi gidan gaskia baki daya daku iyalan sa..."
Bappah Auwalu ya fara kiraye kirayen dangi na kusa dana nesa Yana sanar musu rasuwar junaidu. Auta daga iyalan yafendo. Dangin Hamidniyya Lebanon.. Hakika kowannen su mutuwar ta dake shi .
Alkalani yayi kadan wajen bayyana adadin alhini da dangin suka shiga baki dayan su. Musanman iyalan sa na cikin sa sun shiga cikin dimuwa marar misaltuwa.
Haka aka yi masa wanka. Anayi jini na fita daga jikinsa har da guda guda. Haka aka nannade shi duk da hakan jinin yaki tsayawa.
Aka Kira iyalan sa daya bayan daya suka yi masa sallama. Kowanne da koke koke aka futar da shi.
Aka dauke gawar junaidu aka sanya a makara aka sallace shi aka kai shi gidan sa na gaskiyar wato makabarta.
Allahu Akbar wata bishiya ce ta raba tsakanin kabarin marigayi Bappah junaidu da mai dakin sa marigayiya malama Hindu. Allah ya jikan su ya gafarta musu ya musu rahama..
Hakika junaidu ya samu sheda daga bakunan iyalan sa na cikin sa, dangin sa su bappah Auwalu bappah sani da matayen su baki daya dai dangin hamidniyya Lebanon. Sannan mutanen wajen aikin sa dama yan unguwar baki daya sun yabe shi. Ya Kuma samu mutane sosai da suka sallace shi suka kai shi makabarta.
A farfajiyar gidan aka shinfida tabarma aka fara makoki dukkuwa da ahalin Hamidniyya Lebanon basa zaman makoki, Amma mutane na zuwa yi musu ta'azyiya wasu tundaga birnin bunza na kusa dana nesa...
Suma yan yankin bunza sosai sun yi alhini da jimamin rashin junaidu. Domin yanada halaye na kwarai bai taba fada da wani ba .. kowa nasa ne ga temako .
_Yanzu zamu sake tsunduma cikin labarin:_
_KWANKWASON JIMINA MAI WUYAR SHAFAWA... Ayi hakuri da yadda rubutun yake zuwa... Labarin na gaba In shaa'Allah_
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE