Author : Nana Hafsatu Category : Love Story
kwantan kwatankwacin rabin rabin rabin rabin abunda ake bi basu hada ba. Haka ya hakura ya sanya kudin a asusu kawai gab daya.
Ranar wata talata da safe kanin Alhaji Garbosai yazo yace lalls su tashi su zubar masa gidah na zuwa da yamma. Suka karasa komai nasu tun da safe Ashir ya zuciya suka fita daga gidan
Bappah Auwalu ya ce suje gidan su. Su koma gidan sa baki daya da zama shi bai wulakanta yayan Yan uwan sa ba. ...... Ya kwankwasa
[3/10, 21:02] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_43_
:::::::::
"Wallahi summa tallahi yaran nan bazasu dawo mun gidah da zama ba. Aina zasu zauna rai hudu? Zagada zagada, dakuna biyu ne kawai jallin jal. Daya muna ciki. Daya Layla . Ahmad kuwa a parlor yake kwana saboda babu wajen kwana. To akan mu kakeson wannan rai hudun sun kwana ko meye? Sannan munada halin ciyar dasu ne eh? Muma da Yaya muke samun abincin da zamu saka acikin mu hudu ballantana ka karo rai hudu? Kanzo zaa jika a basu ko menene? Duk acikin Yan uwan ka Kai ne koma baya. Kowanne yafi ka hali nesa ba kusa ba. Amman sika kekashe idanun su. Suka bada musu kasa kowanne yace shi ba zai iya daukar su ba da dawainiyar su saboda halin rayuwa. Amman sai Kai uban dan sarkin son birgewa ba kada ko sisi kana tafe tamkar iska zata hure ka saboda yunwa har Kaine zaka je ka jajibi mana rayuka uku saboda San asani da nuna birgewa aljihu ba ko sisi. To narantse da Allah bazan rike yaro ko daya ba. Kuma babu yaron da zai zauna mun agidah. Wallahi" nusaiba ta fada tana kururuwa tamkar zata hau kansa da duka.
Bappah Auwalu da maganganunta duk sun cika shi ga kunya daya dabaibaye shi yadda take gasa masa magana agaban yayan sa na cikin sa. Duk da sun saba ji su da su nawrah din Amman dai da kunya. Don haukanta na ranar yafi na ko yaushe...
Hannunta Yaja ya shigar da ita ciki ya rufe da mukulli. Suka shiga fadan kache nache tamkar zasu cinye juna don masifa musanman nusaiba dake masa tsiwa tamkar zata rufe shi da duka
"Hamma daman su bappah ca sukai suma na zasu rike mu ba kenan?" Ashfeef ya tambaye Hamma Ashir da kansa ke a sunkuye idanun sa sun kada sunyi jazir
"Hamma wai hakane? Su bappah fa da Gwaggo Aminatu ko ba ka sani ba Hamma?"
Ashir ya saka hannu ya goge hawayen dake zuba a Idon sa Yana Jan majina. Sam bai gayawa Yan uwan nasa bappanin su sinki daukar su ba saboda bayasan suji haushin su saboda zumunci. Amman tunda sun rigada sunji da kunnen su yanzu. Bashida wani dabarar da zai ce baai haka ba. Don idan ya karyata ma yayi kuskure don haka ya kada yai Yana sharce idanun nasa yace
"Abune ya fadamun a idanu na. Anyi haka. Amma ba da wani abu suka fada ba. Kunsan rayuwar yanzu tayi tsada ne gashi muna da yawa. Ku tashi mu tafi. Yan kudaden nan da aka sayarwa gwangwan kayan mu ya Isa mu kama ko da dakine da parlor awani wajen mu koma. " Mikewa yayi Yana goya jakar Amnah a bayan sa.
Suna shirin buda kofa su fita sai jin muryar bappah Auwalu ya kira sunayen su daya bayan daya,
"Ashir Ashfeef, Nawraah, Amnah Ina zuwa ? Ku dawo ku zauna mana ga ruwan"
"Ai bappah daka basshi wallahi. Zamu je inda zamu samu wajen kwana ne Kafin mu nemi wuri sosai akwai kudin awaje na"
"Ah karmuyi haka da ku ahsir Dan Allah. Kada ku bari maganganun wannan sakaryar suyi muku tasiri a kwakwalen ku gidah dai nawane don haka nike da iko da gadara akan sa. "
"Ita nusaiba da Layla su kwanta akatifa daya. A dakko babbar katifar can dakin a sakata aciki Nawraah da Amnah su kwana tare da su. Dakin Layla Kuma sai Kai da Ashfeef da Ahmad kub dinga kwana aciki. Ni kaga kujerar nan ta bayan ka ta ishenuli daman wani lokacin ma akanta nake kwanciya har safe iska parlorn ga dadin bacci".
Ashir yayi murmushi yana grigiza Kai yace,
"Dan Allah kayi hakuri bappah Amman wallahi bazan iya dawowa gidan nan da zama ba tabbas gaskiyar Aunty yayi mana kadan"
"Yauwa Ashir kaji yace gaskiyar ta. Yo mu kanmu Ina gidan nan zai dauke mu bakidayan mu"
"Zan mugun saba miki nusaiba Allah kuwa. Ashir....
Kafin bappah Auwalu ya karasa maganar dazai Ashir ya katse shi ta hanyar zube gwaiwoyin sa akassa yace,
"Dan Allah kayi hakuri bappah. Ka dubi girman Allah ka saurari abunda Zan fada. Kuma dan Allah ka amince da abunda Zan fada din. "
"Inasauraron ka Ashir"
"Bappsh gidan nan wallahi ba zai dauke mu ba yayi kadan wallahi Anty tayi gaskia. Na biyu dama wallahi bada niyyar zaman agidan nan muka biyo ka ba yau din. Dama akwai tsare tsare. Da nake akai na.kayi hakuri yau din na amince akan dare yaja zamu kwana anan, Amman daga gobe inshaa Allah ba zamu sake kwana ba. Zamu samu waje kusaa da nan din. Idan Allah ya amince na mun samu kudaden da zamu biya wancen mutumin shikenan sai mu karbi gidan bappah mu biya shi. Dan Allah karma ka ki amincewa bappah. Idan kaki amincewa akwai matsala. Dan Allah Kai ne mahaifin mu albarkar ka muke nema" ya rike kafafun bappah Auwalu ya faraa hawaye dumin su na diga a kafar bappah Auwalu.
Sunkuyawa bappa Auwalun yayi ya riko hannuwan Ashir yace dashi,
"Shikenan na amince Ashir. Amman sai idan inda aka samu din anan zagayen layin yake ko nan yankin idan baa samu ba to gaskia ban amince ba. Haka zaku dawo nan mu cigaba da rayuwa tare watarana ma duk mutuwa zamuyi ashir. Dan Allah Nima Ina rokon wannan alfarmar kaji?"
"Shikenan bappah. Na amince"
"Yauwa ko kaifa Allah yayi muku albarka kaji? "
"Aaameen bappah wa iyyakum"
Nusaiba sai Harare hararare take bappah Auwalu yasa ta dakko zannuwan gado Ashir da su Ahmad sukayi shimfida a parlor suka kwanta.
Nawrah da Amnah da Layla Kuma suka kwanta a adakin layla. A haka sukayi bacci kowanne da abunda zuciyar sa ke saka masa....
Ashir da asubah ya futa tunda akayi sallah Bai dawo gidah ba. Ya sayi biredi wajen takwas na safe da madara da sukari ya Kai musu duka gidan suka ci
Nan ya shiga neman gidan haya kain dana in anan yankin.. Amma Allah cikin ikon sa baa dace ba. Gashi Ashir bayason ketare maganar manya don haka ya cewa bappah baa samu ba . Ya Kuma nemi gafarar sa daya barsu su nema a unguwar kusa da su. Bappah Auwalu yace sai nan gaba amman ba yanzu ba.
Tunda nusaiba ta jiyo su ta fara hauka kamar sabuwar tabi. Har da fashe fashe na kofuna tana nanawa kanta wuka zata kashe kanta kan lalle Auwalu ya zabi daya ko ita ko su.
Ganin haka yasa Ashir yace da kannen nasa su tashi su dakko kayan su duka suka fito. Bappah Auwalu ya biyo su Yana hawaye,
"Dan Allah Ashir karku yanke mana zumuntar mu ku nake kalla naga kamar junaidu don Allah . Kayi hakuri ka janye maganar ka ni ku na zaba ba ita ba. Ita tamkar riga ce da zan cire na sako wata haka take awaje na. Aurota nayi ,Dan haka iya rabuwa da ita na auro wata ku kuwa Yaya na ne bazan iya taba yanke zumuntar mu ba har gaban abadan. Jini ya wuce gaban komai"
Ashir Ya goge hawayen sa Yana rasa Mai zace Duk suna tsaye cirko cirko da akwatinan su a hannu...
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[3/10, 21:02] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_42_
:::::::::
_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me naira hamsin me naira dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._
_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_
_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._
_kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_..
:::::
°°°°°
Ya sake kai hannun sa ya kwankwasa a karo na biyu. Yana riko hannun Amnah acikin nasa.
Nusaiba dake zaune a kujera taja tsaki ta mike tana mita,
"Auwalu kenan. Kawai saboda kasan yanzu Ina hutawa ne. Zaka dinga wani bugo kofa don na tashi lalle na bude? To gaskia ba komai agidan gwara ka shigo mana da biredi ka koma Layla ta kwanta Kuma na san yunwa ce. " Ta fada tana bubbuga kofar itama
Bappah Auwalu yaja tsaki cike da takaici yace,
"Bude mana. Ba ni kadai bane"
Nusaiba ta gyara zaman dankwalin ta. Ta dauka bako yayi ko zai basu dan kudi su samu suyi abinci.
Ta gudu ta shiga dakin Layla ta tasota,
"Tashi dan uban ki. Inaga mutumin rannan abokin baban ku ne yazo. Je parlor ki zauna idan kin gayshe shima karki tashi nasan idan suka gama hirar su kamar rannan. Zai baki ko yar dubu biyu ce"
Layla ta tashi tana murza idanu saboda baccin dake kanta tashiga bandaki ta dauraye bakin ta,
"Ba Zaki sauri ba. Wane irin wulakanci ne?"
"Umma yanzu zan tafi ai"
Nusaiba ta zauna a kujera. Alokacin bappah Auwalu ya cika yayi fam. Layla ta saka hannu ta bude kofar tana cewa,
"Ina wuni?"
"Lafiya. Ke Kuma wa kika dauka? Akace kinyi bacci. ? Nusaiba wane irin wulakanci ne wannan tun dazu saboda Allah nake cewa ki bude mana Amman shine kika ki sai da kika taso ta tazo ta bude. Wato ban Isa kizo ki bude mana kofar ba kenan ba ko?" Bappah Auwalu ya karasa fada yana jan tsaki."
Nusaiba ta mike har tana ball da kofin ruwa agabanta tana mai nuni da su Ashfeef da kowanne ke rike da akwatin sa a hannu tace,
"Bangane ba. Wadannan nan Ina zasu? Wanne bappanin ne ya amince ya rike su? Bappah salisu ko sani ko kuwa Gwaggo Aminatu ce? Ko gidan aikatau dinne suka ce zasu karbe su?"
Tsaki yaja dogo yana nuni da yan kujerun parlorn na su yace
"Ku zauna Nawrah"
"Ka wayar mun da Kai mana Auwalu. Ga ka ga yara rabe rabe kowanne da kayan akwatin sa dashi. Shin wani gidan suka sauya da yafi wannan? Hmm to Auwalu ai gwara Kai ma kasan abunda ke maka ciwo kullum jiya iya yau. Sai dai kache wanin ka. Ba zaka tashi ka nemi na kanka ba."
Bappah Auwalu ya grigiza Kai Yana yatsina fuska yace,
"Dan Allah ya isheki haka. Yi shiru. Haba sai magana kiketa ratattakawa. Meye haka eh? Haba banason irin wadannan abubuwan wallahi ,yara dan kin gansu acikin gidan nan ai yaya nane suma ko kin ki ko kin so inda kara kema ai baki ne. Bayaga haka. Tun ba yau na gaya miki. Ba Kuma wai amincewar ki ko kin amincewar ki zan bi ba. Wadannan Yara da uban su da ni uwar mu daya uban mu daya. Don haka na dawo dasu gidah na da zama baki daya har zuwa sanda Allah zai warware mana matsalolin mu."
Nusaiba ta saka hannu a baki taja guda tana watsa hannu sama cike da bakar masifa tace
"Ah lalle. Nace mekace a karshen zancen ka! Ka san ba kasafai maganganun ka suke ratsa kunne na ba"
"Nace Yara sun dawo gidan nan. Ba na neman amincewar ki ko kin amincewar ki"
"Kan babban balastin. A wannan kungun gidan Mai kama da ramin cinnaka zaka ce zamu zauna da yara zagada zagada har hudu? Wallahi summa tallahi bazan yarda ba. Bazan amince ba. Wallahi kaji rantsuwar musulmai kenan."
"Gidan ki ko nawa? Ni Kuma nace yara sun dawo nan gidan da zama kiyi abunda Zaki. Ku zauna Ashir bari a kawo muku ruwa"
Kitchen ya nufa. Nusaiba tabi bayan sa tana ife ife tamkar zata rusa gidan hannunta daya akan kofar kitchen tana kwaso rantsuwa tana bubbuga hannunta cike da tsantsar masifa tace...
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:02] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_44_
:::::::::
"Zamu iya kwana nan Bappah..." Ashir ya fada yana nuni da dan dakin da Bappan su ya bawa nusaiba take zuba kiwon ta . Tamkar akurkin kaji.
'ah haba ahsir. Ya za'ai rai na dan Adam ya iya zama nan? Ai ba zeyiwu ba"
"Allah Bappah zai yiwu. Zamu zauna har ya zuwa sanda zaa samu dan waje na kamawa anan yankin. Idan har zuwa nan da yan lokacin dana bari ya cika bamu samu ba. To kayi hakuri ko da awani unguwar ne zamu kana waje mu koma. Kuma zumuncin mu har aljanna inshaa Allah. Haka na dai yanke bappah .. Daurewa zai ayi"
"Ashir ka kalli dakin nan kuwa."
Nusaiba dake binsu dadi fam ranta ta nufesu tana murmushi,
"Kalau daki yake. Tumakan kawai zaa janye. Kajin Kuma a mayar da kejin su gefen can haka daga ciki ai yayi"
Bappah Auwalu ji yake tamkar ya Kai mata gula aciki ya hanbare ta baki daya. Cike da takaici yace,
"Bar nan nusaiba"
"Naje Ina? Ko ka manta mallaki na ne nan din? Ai na wa ne"
"Mahaifin su ne dai ya baki kada ki manta. Ke butuluce wallahi Allah"
"To daya banu yanzun ai nawa ne ko na baka ta rabaka da kayan ka. Allah na tuba nan din dan ya bani har wani abun birgewa ne...
"Da kata anty.ya isa hakaa. Kada ki tabo abbiey ko ummy. Maganar ta tsaya akan mu please." Ashir ya katseta Yana kada Kai.
Bappah Auwalu ya juya ya dankara mata harara,
"Ai ga irin ta Nmnan" ya fada Yana Jan dogon tsaki ya dubi Ashir yace,
"Amma da sharadin zaayi gyara sosai acikin sa da sauran su. Don daii ka hadamu da babban bango ne kace Allah bazan iya musu ba. Amman kasani har cikin raina banji dadin kasancewar ku anan dakin ba wallahi Allah ne sheda. Dakinda ake saka kiwon tumaki da kaji daa harda zomaye ma ace dan Adam ne zasu kwana acikin sa?"
"Bakomai bappah Allah. Mungode hakan ma ta mana kokarin"
"Kokarin me bayan mahaifin ku nema ya bata ba wai kudi ta saka ta saya ba"
"Kuma dai ai ba roka nayi ba da zaka ce haka. Allah na tuba dakin da kiwon da duk mutuwa suka dinga y kamar an canfa shi. Ni dai ga daki nan nace su zauna aciki ba Kuma kyauta na bayar ba ban amince Kuma ayi wani fàshe fashe ko gine gine acikin sa ba batare da izini na ba gaskia. "
Tana gama magana ta koma ciki kamar Zata tashi garin,
"Kifi ruwa gudu ma nusaiba. Aikin kawai" bappah Auwalu ya fada Yana hararo bayanta data tafi
Ashir yayi gaba Yan uwan na biye da shi abaya aka bude dakin. Ba lefi Yana da Dan girman sa. Sai dai kofa ce kawai babu window a dakin. Sai kashin tumaki Dana kaji da kazanta dai sosai.
Ashir ya kade hannunsa yana duban nawrah yace,
"Muje keda Amnah . Idan muka gama zamu kira ku. Sai anyi gyara sosai"
"Hamma zan tayaku"..
"Aa jeki zauna da amnah"
"Toh shikenan Hamma Allah ya bada sa'a"
"Aamin"
Tafiya tayi ... Ashir da Ashfeef da Ahmad da b. Auwalun suka fara kaude kauden kayan wajen zasu gyara nusaiba ta leko tana kiran Ahmad.
Tunda ta kiraa shi bappah Auwalu ya girgiza kai kawai don ya tabbatar Kiran sa tayi ta hana shi aikin.
Ai kuwa suna fita ta rufe shi da fada,
"Dan uban ka a wannan kurar,wannan shekararren akurkin dakin da ba bil adama ke kwana aciki ba kaje ka baje hanci kana tayasu aiki. Wuce muje gidah. Kuma wallahi ka sake ka fito sai na ci haka kaza ta uban ka"
"Kai umma"
"Zakaa wuce ko sai na sharara maka Mari"
Ciki ya nufa,Yana kananun mita. Ta shiga ta rufe kofar harda mukulli ganin haka yasa nawrah rike hannun Amnah suka koma can gefen famfo suka zauna.
Sannu ahankali suka fara gyara dakin suka wanke shi. Ya bushe suka saka katifun da suka rage akayan da basu sayar ba.
Suka raba dakin biyu da labule. Rabi daya na Ashir da Ashfeef. Dayan Kuma Nawrah da Amnah sai yama tamkar ciki da parlor don sai ka daga labulen zaka Isa wajen su Amnan.
Suka jajjera Yan abubuwan su da suka taho dasu. Suka jinginar da akwatunan