Author : Suwaiba Muhammad Category : Bookz
Bayan sun gama magana ya ajiye wayar ya maida hankalinshi kan Laptop d’in yana karanta wani abu. Laila dake gefenshi taji haushi ba kad’an ba domin ko kallonta bai yi ba.
Minti biyar da haka ta mintsineshi a hannunsa ya juyo da mamaki a fuskarsa yana kallonta.
“Mena miki?”
Gyara zamanta tayi taci gaba da kallon tv fuskarta babu fara’a.
Shafa gurin yayi yana nurmushi don yanzu ya gane laifinsa. Sai dai bai kulata ba yaci gaba da aikinshi dalilin an bashi lokacin da ake buk’atar ya tura aikin.
Bugeshi tayi kamar bata sani ba taci gaba da kallonta. Murmusawa ya k’ara yi yace,
“Wallahi idan na gama aikin nan I will deal with you Laila. Kici gaba.” Yayi kwafa yaci gaba da aikinsa.
Minti uku da haka ya gama aikin ya tura musu, kafin ya kashe Laptop d’in yaji ta k’ara mintsininshi ya juyo yana cewa,
“That’s it! Come here.”
Hannunta ya kamo duka ya had’a guri d’aya ya fara mata cankulkuli tana rok’onshi Allah da Annabi ya bari.
“No, ai baki ga komai ba. Ba ni kike muntsina ba?”
“Na daina. Haydar ka daina, wallahi zan suma.”
“Muna da ruwa zan yayyafa miki ki farfad’o.”
Sai daya tabbatar ta jikkata sannan ya barta ya koma ya zauna yana kallonta tamkar bashi ya gama mata mugunta ba.
“Zan rama.” Shine kawai abunda ta fad’a ta tashi ta wuce d’aki domin ya birkita mata kwalliyarta.
Dariya yayi ya kwashe Laptop d’in ya bita d’aki don yaji laifin daya aikata.
Kwana uku da haka kullum Haydar baya dawowa gida sai bayan la’asar, watarana kuma sai kusan magriba zai dawo wanda hakan baya yiwa Laila dad’i. Sai dai bata ta6a k’orafi ba saboda tasan neman na rufa musu asiri yake yi, ba wai wani gurin yake zuwa ba.
Da dare suna zaune a falo tare da Mas’ud wanda ya kawo musu ziyara suna kallon News. A nan ake sanar da cewa an shiga lockdown a jihar Kano dalilin cutar Corona ta yawaita.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.” Laila ta dafe k’irji tana kallon ikon Allah.
Haydar ya dubeta ya kad’a kai yana murmushi domin tun ba yau ba ya lura tana tsoron cutar ba kad’an ba. Ido ya yiwa Mas’ud shima ya kalleta yaga yanda ta kasa zama daidai bakinta a bud’e, hannunta a kan k’irjinta cike da tsoro.
“Wai haka take da tsoro dama?” Haydar ya tambayi Mas’ud yana k’unshe dariyarsa.
“Kad’an ka gani.” Mas’ud ya mayar masa da martani sannan ya gyara zamanshi fuskarsa ta zama so serious ya dubi Laila yace,
“Kalti abun nan sai addu’a fa.”
A nan ta juyo ta kallesu zuciyarta na kad’awa tace,
“Mas’ud ko dai tashin duniya ne ya zo?”
Haydar yayi dariya mai sauti har yana rik’e cikinsa, Mas’ud ma dariyar yake son yi amma ya gimtse domin muguntar da yaso shiryawa Haydar.
“Alamomin tashin duniya kam tuntuni muna gani Kalti. Wannan d’in ma watak’ila yana ciki domin Annabi Muhammad SAW yace idan alfasha da fasadi ya yawaita to a saurari cututtukan da za’a rasa gane maganinsu. Ga HIV, ga Cancer har yau babu maganinsu sai dai a sha ayi sauk’i. Ke dai ku kiyaye. Gobe kuje kasuwa ku sayi duk abunda kuke buk’ata sai ku zauna a gida kamar yanda Gwamnati ta umurta.”
Wannan magana ba k’aramin shigar Laila tayi ba, ai kuwa ta dubi Haydar da yake murmusawa irin ko a jikinshi nan tace,
“Ka ganshi ko? Har yanzu bai yarda cewa cutar nan gaskiya bace. Daga gobe babu inda zaka sake zuwa sai an tabbatar we are all safe.”
“Sai mu gani in d’aureni zaki yi.” Ya bata amsa kana ya dubi Mas’ud wanda sai a lokacin ya fara dariya yace,
“Kai kuma ka kyauta. Sai yanzu na gane manufarka.”
“Me kuma nayi? Don na baku shawarar yin taka tsantsan? Kuma gobe kar ku manta ku sanya takunkumi wato Face Mask kafin ku fita.” Ya mik’e tsaye yana dariyar mugunta.
“Kana ji ko?” Laila ta harari Haydar yayi rolling idanunsa bai ce mata komai ba.
Mas’ud ya mata sallama amma hankalinta na kan TV tana ganin yanda ake bayanan symptoms na Covid-19.
Haydar ya raka Mas’ud waje inda motarsa yake yana kyakyata dariya.
“Kai mugu ne Mas’ud, wallahi baka kyauta mini ba. Yanzu hankalinta k’ara tashi zai yi ta hanamu sakat a gidan nan.”
“Zaka gode mini nan gaba. Ga face mask ka kai mata.” Ya damka mishi kwalin ya kunna motarsa ya tafi yana dariya.
Haydar yana komawa falo Laila ta tsayar dashi daga bakin k’ofa tace,
“Bani hannunka in d’iga maka hand sanitizer.”
“Are you kidding me Laila? Mas’ud na raka waje fa.”
“I don’t care. Kafin ka shigo ka ta6a mabud’in k’ofa ko baka ta6a ba.”
“Yes, na ta6a.”
“Bani hannunka.”
Tsayawa yayi yana kallonta, yanda ta had’e fuska babu wasa yasa ya mik’a mata kwalin face mask d’in yana cewa,
“Gashi Mas’ud yace a baki.”
“Allah sarki Mas’ud, shi burinsa yaga bana cikin had’ari. Idan na d’iga maka sai ka shafa a jikin kwalin saboda watak’ila akwai cutar a jiki.”
“Fuck me!” Ranshi ya fara 6aci ya ajiye kwalin a k’asa ya mik’a hannunsa ta d’iga masa ya shashshafa tana gyara masa yanda zai yi.
“Saura kwalin.” Ta masa nuni dashi.
“Laila bazan iya shafawa kwali abu ba. Dama kece zan iya bin duk ilahirin jikinki in shafa miki amma banda wannan.” Ya nuna kwalin tamkar zai yi ball dashi.
“Baka da kunya.” Ta fad’a tana harararsa kad’an.
“Dama ban ce miki ina da ita ba.” Ya ratse ta gefenta zai tafi.
“Ka dawo ka goge abun nan.”
Hand sanitizer hannunta ya kar6e ya ajiye a k’asa ya rik’o k’ugunta yace,
“Mas’ud was just messing with you ne. Yayi hakan ne don hankalinki ya tashi ki hanamu sakat, kuma gashi har kin fara tun kafin aje ko’ina.”
“Babu dai inda zaka je.” Ta bashi amsa tana kallon kwayar idanunsa.
Saketa yayi ya koma falo tana kiran sunansa wai yazo ya shafawa kwalin sanitizer.
“Bazan iya ba Laila.”
Kwafa tayi kana ta tura kwalin gefe da k’afarta tana cewa,
“Ai ance idan cutar tayi 9hours a jikin surface tana mutuwa da kanta. So zuwa gobe da safe zan iya d’auka.” Da haka ta d’iga kad’an a hannunta ta shafawa k’afanta inda ta ture kwalin.
“Seriously Laila?” Haydar ya sake baki yana kallon ikon Allah.
“Prevention is better than cure.”
Washe gari tare suka fita ta ajiyeshi a office ita kuma ta wuce gurin sayayya domin tace bata yarda dashi ba. Kafin azahar aka fara kora mutane gida, dama tuni Laila ta gama sayan duk abunda zata saya, office d’in su Haydar ta isa ta kirashi a waya yace mata yana zuwa ta jirashi.
Ta kai awa d’aya da rabi tana jiranshi sannan ya fito, kafin ya iso ta fito daga motar da d’iga mishi Hand Sanitizer ya shafa babu musu amma ya lura ranta a 6ace yake.
Sai da suka shiga mota suka fara tafiya sannan yace,
“Gimbiya laifin me nayi?”
“Babu.”
“Akwai dai. Irin wannan had’e fuska nasan nayi laifi.”
“Ya wuce.” Ta haka ta hau titin da zai kaisu gida yace,
“Mu koma inda kika yi shopping zan sayawa Ammi kayan abinci. Ni sai yanzu hankalina ya tashi da wannan lockdown d’in. Ya zan yi da Ammi da bata da kowa sai ita d’aya?
“Na kai mata duk abunda zata buk’ata. Sannan na samu makwabtanku sun bata wata ‘yar budurwa wai Meenat da zata zauna da ita.”
“Thank you, idan mun je gida sai ki mini lissafin kud’in in baki. But ya aka yi iyayen Meenat suka iya barinta ta zauna da Ammi?”
“Bana buk’atar sisinka, nima Ammi uwace a gurina. Ka san yarinyar kenan?”
D’an muskutawa yayi kad’an kamar mara gaskiya yace,
“Kin manta unguwarmu d’aya ne?”
“Haka fa.” Laila da bata kawo komai a ranta ba taci gaba da tafiya har suka iso gida Haydar na waya da Ammi.
“Ammi da zarar na samu dama zan zo na dubaki domin wannan lockdown d’in bai mini ba. Kina nesa ina nesa wa zai kula da ke?”
“Da kake zuwan kai kake kula dani? Ji mini shiririta! Idan dukan sojoji kake so ka fita daga gidanka. Mu nan ko k’ofar gida bama lek’awa balle har mu fita daga unguwar mu je wata.”
Laila dake gefe tayi dariya domin a hands free ya saka kiran. Harararta yayi kana yaci gaba da magana da Ammi tamkar wani k’aramin yaro.
“Na lura idan kana gaban Ammi yaro d’anye shataf kake dawowa kamar wanda aka yaye jiya.” Laila ta tsokaneshi tana zama a kan kujera bayan ya gama wayar.
“Zan dinga fita aiki 3days per week. A nan kuma zan samu hanyar zuwa gurinta.”
“Allah ya bada sa’a ya hana had’uwarka da sojoji.”
A ranar shi da kanshi ya musu girki suka ci suka zauna kallon labarai wanda ya zama sabon d’abi’ar Laila.
Zaune yake a k’asan Carpet ya mik’ar da k’afafunsa, Laila kuma ta d’aura kanta kan cinyarsa yana tura hannunsa cikin gashin kanta tana lumshe ido, a gefe guda kuma waya take yi da Sabrin tana k’ara jaddada mata matakan tsaron gujewa cutar Corona.
Bayan ta gama wayar ta sak’ala hannayenta a bayanshi ta tura kanta kan cikinshi tana numfashi a hankali. Yanayin kwanciyarta a jikinshi ya sanya masa wani irin yanayi wanda ya saba ji a kullum in yana zaune kusa da ita. Sai dai me zai yi? Hak’urin daya saba yi shi zai yi saboda ba zai ta6a mata dole ba, yasan zafin da rad’ad’in yiwa mace dole, don haka bazai ta6a yadda ya aikata hakan ba.
“Haydar.” Ta kira sunanshi wanda hakan yasa yaji kamar hura mishi iska take yi a fatar cikinshi dalilin bai sanya riga ba, wanda dama shi haka yake baya son saka kaya.
“Na’am.” Ya amsa yana k’ok’arin rabata da jikinshi amma ta k’i sakeshi.
“I’m ready.” Ta d’ago idanunta tana kallon yanda fuskarsa ta sauya cikin k’ank’anin lokaci.
“Are you sure?”
“100%.”
‘Dagota yayi ta zauna suka fuskanci juna yace,
“Why?”
“Ina tsoron kar duk mutuwa zamu yi, watakila this is the only chance da muke dashi na kasancewa tare.”
“Laila babu mai mutuwa sai lokacinsa yayi, sannan da yardar Allah babu abunda zai samemu har cutar nan ta tafi. And you are not ready yet.”
“And...” Ta fara magana sai kuma ta tsaya.
“And???” Ya tambayeta.
Mayar da kanta tayi kan cikinsa ta 6oye fuskarsa tace,
“And I need my husband.”
Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)
Littafin nan na kud'i ne a naira d'ari N100 kacal. Zaku turo kudinku ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana sai ku turo shaidar biya ta number 09023713064 a sakaku a paid group ba sai kun tsaya jiran na bati ana ja muku aji ba. Na rage kud'inshi ne don kowacce ta shigo RZ group a dama da ita. Wanda basa son hayaniyar group zamu iya tura muku ta private a N300.
(32)
Bayan Laila ta 6oye fuskarta Haydar yayi shiru bai ce komai ba amma fara’ar dake fuskarsa ba za’a iya misaltawa ba. Cizon fatar cikinshi da tayi yasa ya dawo daga kogin tunanin daya fad’a yana kai hannu gurin, amma kafin nan yaji ta hura iskan bakinta a daidai gurin data ciza.
“Bera ne yake haka Laila, idan ya ciji mutum sai ya hura iska saboda kar mutumin ya farka daga bacci.”
“So, you are saying nima Bera ce?” Ta d’ago idanunta tana hararanshi cikin wasa.
“Na isa? Ke sabuwar Amarya ce ai yau.” Ya shafa fuskarta yana jin wani mugun sonta na k’ara hauhawa a zuciyarsa.
“Better.” Ta maida kanta ta kwanta.
“Laila.” Ya kira sunanta.
“Na’am.”
“In fad’a miki wani burina?”
“Yes.” Ta d’ago idanunta tana kallon kyakkyawar innocent fuskarshi da tun farkon had’uwarsu ya tafi da ita.
Shima idanunsa na cikin nata yana aika mata da tsadadden murmushi mai sanyata shiga wani hali da take maraba dashi a yanzu.
“Ina son idan nayi aure aka kawo mini matata in ga tayi k’unshi, tayi kitso, tayi kwalliya sannan ta lullu6e kanta akan gado tana jirana. Ina son kiyi haka.”
Ai da sauri ta mik’e zaune tana girgiza kanta,
“Don Allah Haydar karka mini haka, zan yi lalle da kitson amma banda lullu6in Amarya. Wallahi kunya hakan zai bani, nifa ba budurwa bace.”
“Idan naji zan fad’a miki.”
“Ban gane ba.”
“Kiyi tunani.”
“Haydar.”
“Laila.”
“You are so stubborn wallahi. Ya Allah, mena aura?”
“Someone that will take you to cloud nine.” Ya bata amsa yana kashe ido.
“Baka da kunya.”
“Baki ga komai ba Laila, trust me.”
“An rufe gari Haydar, ya za’a yi in samu mai kunshi da kitso?”
“One of your staff gidansu a unguwar nan yake. Sai kije gidansu ta miki ko kuma ita tazo.”
“Amma kasan an hana fita ko k’ofar gida ko? Sojoji na yawo a kowanne lungu da sak’o, kuma ina tsoron Corona.”
“Ba abunda zai faru ki tashi muje in rakaki gidan.” Ya mik’e tsaye ya shige d’aki ya d’auko jallabiyarsa da hijabinta ya fito yana sakawa.
“Wallahi Haydar ina tsoron fita. Na iya k’unshi zan yi da kaina, kitso kuma kayi hak’uri idan aka cire lockdown zan je a mini.” Fad’in Laila tana tashi tsaye.
“Kin cika tsoro. Nikam ki tashi mu tafi kar lokaci ya kure.”
Ba yanda bata yi dashi ya hak’ura ba amma yayi k’ememe yace dole sai sun fita. Hand sanitizer ta d’auka tare da face masks, ta tilasta masa ya saka sannan suka fita maigadi yana musu sallama amma sai daya k’ara da cewa,
“Amma Hajiya an hana fita fa. Nima sallamar iyalina nayi na dawo nan gidan zan zauna.”
“Kash! Kasan banyi tunanin hakan ba? Gaskiya ya kamata ka koma gurin iyalinka saboda bamu san ranar da za’a d’age wannan abun ba. Zamu yi magana da maigidana, duk yanda aka yi zaka jini.”
“Shikenan Hajiya.”
Ya bisu da kallo har suka fita, har gobe bai daina mamakin wai yaron daya taimakawa shine ya zama mijin uward’akinsa ba.
Suna fita Laila ta fara zare ido tana kalle-kalle, Haydar ya rik’o hannunta ya jawota gefenshi suka fara tafiya.
“Wai ya akayi kasan ina da staff a nan unguwar?”
“Mas’ud ne ya fad’a mini.”
“Wani irin magana kuke yi a kaina da har kasan hakan? Me Mas’ud yake fad’a maka?”
“Kin cika surutu.”
Shiru tayi bayan ta harareshi suka cigaba da tafiya tana leading d’insu. Har suka isa gidan basu had’u da sojoji ba kamar yanda take tsammani, hasalima sun had’u da wasu mutane suma suna yawo kamar su.
“Ki shiga ki kiranin wacce zata miki lallen.”
“Ka mata me?” Ta tambayeshi cikin mamaki.
“Zan kwatanta mata yanda nake son ta miki kitson ne.” Ya bata amsa yana mai jingina da katangar gidan.
Ajiyar zuciya Laila tayi ta shiga gidan da sallamarta. Minti biyu da haka ta fito tare da yarinyar, har k’asa ta tsugunna ta gaishe da Haydar ya amsa da fara’arsa wanda Laila bata so hakan ba.
“Kin gane irin kitson nan da akeyi sai ya zubo ta gaban goshi?” Ya kwatanta mata da hannunshi zuwa fuskarsa.
Yarinyar bata d’ago ta kalleshi ba ta kad’a kanta tace,
“Na gane.”
“Yauwa to irinshi zaki mata. Sannan k’unshin kar ayi bak’i, ja za’ayi wanda ake shafawa sai a rufe da leda d’in nan. Sannan ayi a hannu da k’afa duka.”
Laila dake gefe tana kallon k’arfin halin Haydar tace,
“Ya Allah!”
Da haka ya ciro kud’i har dubu hud’u a aljihunsa ya mik’awa yarinyar ta d’ago ido tace,
“A’a Yalla6ai ka barshi. Hajiya tafi k’arfin haka a gurina.”
“I insist ki kar6a.”
Da Laila ta lura yariyar zata k’ara musu sai tayi saurin katseta, domin bata son suci gaba da magana duk da cewa babu mai irin tunaninta sai ita, wato na kishi.
“Na’ima ki k’ar6a tunda shi ya baki.”
Bata k’ara musu ba ta k’arba da hannu biyu tana sunkuyawa, hakan yasa Haydar ya k’ata fad’ad’a fara’arsa, ta masa godiya ta shige cikin gidansu. Laila na ganin haka ta tsuke fuska tace,
“Shikenan sai na dawo.”
“No, idan an gama ki kirani in zo in d’aukeki.”
“Haydar...”
“Laila zan zo in d’aukeki domin nasan kafin a gama miki dare yayi.” Yana fad’in hakan ya tako zuwa gurinta ya d’aura goshinshi kan nata yace,
“I can’t wait dare yayi.”
Idanunta ta sauk’e k’asa tana murmusawa, sannan ta janye jikinta ta shige gidan tana masa sallama tare da tuna mishi amfani da hand sanitizer in ya koma gida.
Sai daya tabbatar ta shiga gidan sannan ya ciro wayarsa ya kira Mas’ud, bayan an d’auka yace,
“Ya kana ina ne?”
“Ina gidana.”
“Gani nan zuwa.”
“Ohh, baka san anyi lockdown ba ko?”
“Duk karya ce, gani nan yanzu haka a waje na kai Laila wani gida nan cikin unguwarmu.”
“Kai Baaba. Ance sojoji duka suke yi fa.”
“Bari in zo.”
Minti biyu da haka ya isa gidan Mas’ud ya sameshi a waje yana jiranshi. Musabaha suka yi sannan ya masa jagora suka shiga gidan zuwa falonsa.
“Nayi mamakin