Author : Suwaiba Muhammad Category : Bookz
ba.
Su Ajidde ne suka d’auko Naana amaryar Mas’ud aka kawota gidan Madu aka yi bud’an kai da yamma, ana sallan magriba aka kaita gidan da Mas’ud ya gina shi da kanshi shima a cikin Jakara wanda tafiyar minti uku zai kawoka gidan Laila.
Bayan isha kowa ya watse aka bar amarya da kawayenta kafin angwaye su shigo.
Daga masallacin jumma’a Haydar yaje gurin aikin Nasir wanda tun bayan abunda ya faru da Laila ya ja baya dashi, wai yana tsoron kar a kulleshi.
Yana ganinshi suka yi musabaha cikin d’okin ganin juna kana ya gaisa da sauran mutanen gurin suka zauna.
“Kana nan abunka?” Fad’in Nasir yana mik’a mishi coke mai sanyi.
Haydar ya k’arba tare da yin godiya yace,
“Ina nan. Yau aka d’aura aurena da Laila.”
Nasir da ya kur6i Coke d’inshi ya shak’e ya fara tari Haydar kuma yaci gaba da sipping nashi a hankali tamkar bai ga Nasir ba.
“Kai mugu ne d’an iska.” Nasir ya fad’a tsakanin tari.
“Maganin mai gudun abokinsa don tsoro. Wallahi kaji kunya! Yaushe rabon da kazo gidanmu? Tunda Ammi ta dawo gida baka k’ara zuwa duba jikinta ba.”
“Ba ina maka waya ba?” Ya amsa masa bayan tarin ya tsagaita.
“Waya bai isa ba.”
“Sue me.”
Haydar ya ajiye goran coke d’in a saman counter yace,
“Wallahi ba wasa nake maka ba. An d’aura mini aure da Laila yau.”
A nan ya bashi labarin abunda yaga zai iya fad’a masa ba tare da ya fad’i abunda ‘yayan Laila suka yi ba, saboda 6oye sirrin ‘yayanta.
“Kai Haydar!”
“Baka yarda bane?”
“To uban me kake yi a nan kana Ango d’anye shataf?”
“Ina kake son in je?” Ya tambayeshi yana tsura mishi ido.
“I don’t know, amma dai ba nan ba kuma ba cikin tsofaffin kaya ba.”
“Sue me.”
Bai bar gurin ba sai bayan isha bayan ya nacewa Nasir ya rok’i ubangidansu ya dawo dashi aiki a kantin tunda ya daina aiki a Lu’a Ventures.
Yana isa unguwarsu yaga motar Mas’ud a k’ofar gidansu yayi saurin shiga don jin meya kawoshi.
Samu yayi Mas’ud na zaune a kan tabarma shi da wani abokinsa d’aya suna hira da Ammi cikin yaren Shuwa wanda har yau shi bai iya ba.
Sallamar da yayi yasa suka dakata da maganan da suke yi kana suka amsa ya samu guri ya zauna yana mik’a musu hannu suka yi musabaha.
“Ali ina kaje tun d’azu ana ta nemanka? Mas’ud bana fad’a maka ana yin isha zai dawo gida ba?”
Mas’ud ya gyad’a kai yana kallon Haydar yace,
“Ai kuwa Ammi.”
Haydar dai shiru yayi yana jiran da wacce suka zo domin har cikin ranshi ya raya cewa Laila ce ta aikosu ya bata takardarta tun kafin auren ya kwana.
“Ka had’a kayanka ku tafi.” Cewar Ammi tana mik’ewa ta shige d’akin Haydar don tayashi had’a kayansa.
“What? Ammi ban gane in had’a kayana ba sai kace wata mace.” Yabi bayanta yana mata magana amma har ta fara jawo kayanshi masu dotti da wankakku tana ajiyewa a gefe bata ce mishi kanzil ba.
Dariya Mas’ud yayi amma yayi saurin k’unsheta yana kasa kunne shi da Hamidu abokinsa.
“Mu da aka kai mana mata shi kuma shi za’a d’auka a kaiwa matarsa. Bari mu ga ko zai yi kuka in yazo rabuwa da Maman nashi.” Mas’ud ya k’ara fashewa da dariya yana sauraron draman Ammi da Haydar.
“Ammi don Allah karki ta6a mini gajerun wandunana masu dotti, ki bari zan had’a kayan da kaina. Ammi!.” Ya fad’i hakan yana kwacewa daga hannunta cike da kunya.
“Ammi nifa babu inda zan je in barki ki kwana ke kad’ai.” Ya fad’i hakan bayan sun gama had’a kayan.
“Yau na saba kwana ni d’aya? Lokacin da ka tafi bautar k’asa a can kudu da waye nake kwana? D’auki jakanka ku tafi karka 6ata musu lokaci.” Fad’in Ammi kenan tana turashi gaba.
“Ammi ki bari gobe zan je da kaina muyi maganan inda zata zauna, zan nema mana gidan haya.”
“Mas’ud yace ya baka gefenshi ka zauna a gidan tare da matarka har Allah ya hore maka kayi naka.”
“Amma kuma bai yi shawara dani ba ina matsayin namiji sai ke yake fad’awa hakan?”
“Tun bayan magriba suke gidan nan, yana son maganan da kai amma baka nan wayarka ma bata shiga, shiyasa suka zauna zaman jiranka.”
K’arshe dai haka suka fito daga d’akin Mas’ud na k’unshe dariyarsa domin hakan ba k’aramin dad’i ya masa ba, kuma ya samu abun tsokanan Haydar kenan.
“Haydar kar kayi kuka fa, kasan rabo da iyaye akwai zafi, amma kullum zaka dinga zuwa kana ganinta ai. Ko Ammi?”
Ammi ta shafa kanshi tamkar k’aramin yaro tace,
“Kwarai kuwa. Ai bamu yi nisa ba.”
Haydar ya rufe idanunsa na sakanni goma yana danne 6acin ransa domin yasan da gayya Mas’ud ke mishi haka.
Tun kafin suyi bankwana da Ammi ya figi jakarsa yayi waje yana cewa,
“Sai da safe Ammi.”
“To ka tsaya kuyi bankwana da kyau mana, ko baka son a ga kukan da kake yi ne?” Fad’in Mas’ud yana zura takalmansa yana kecewa da dariya.
Ammi da har lokacin bata gane gayya ake yiwa d’anta ba jikinta yayi sanyi tace,
“Kuka yake yi ko? Allah sarki Ali.”
“Babu komai zamu rarrasheshi. Ai kamar kunya yake ji ma.”
Haydar da yake waje duk yaji maganganunsu ya cije le6e cikin takaici.
Har waje Ammi ta biyosu ta musu bankwana kana ta koma gidanta ta rufe cike da kewan d’anta tilo data fi so a duniya.
A hanya Mas’ud ne ke tsokanan Haydar amma ko kad’an bai nuna yasan yana yi ba, k’arshe wayarsa ya d’auka ya fara danne-danne gudun kar ya mayar masa da martani domin bai mance halaccin daya masa yau ba na bashi auren Laila.
A Pharmacy d’insu suka yi parking suka fito Haydar na mamakin me ya kawosu gurin. Sai da suka shiga Mas’ud ya sallami duk masu aikin gurin akan sai gobe su zo su bud’e shagon.
Shagon ya rage daga Mas’ud, Hamidu da Haydar wanda tun shigowarsu ya samu guri ya zauna.
“Angon Laila.” Mas’ud ya kirashi cikin tsokana yana zama kusa dashi da syringe a hannunsa.
“Mallam me zaka yi da wannan d’in?” Haydar ya tambayeshi yana matsar da fuskarsa baya.
“Zamu gwada jininka ne ko kana da STDs, bazan kaiwa Laila kai haka ba tare da an maka gwaji ba. Domin kafin a d’aura auren ma an buk’aci ganin takardunka na asibiti nace duk na sani.”
“I’m clean man, bani da ko malaria balle HIV.”
“Bani hannunka domin bazai d’auki minti goma ba.”
Haydar ya mik’a hannunshi ba tare da tsoro ba aka ja jininshi. Minti sha biyar da haka Mas’ud ya fito daga d’an k’aramin Lab d’insu dake cikin shagon yana cewa,
“You are clean.”
Daga nan shagon aski suka wuce, shi dai Haydar na kallon ikon Allah yana kuma binsu ne kawai.
A can aka masa aski da gyaran fuska wanda Mas’ud yaso a kwashe sajenshi Haydar yace in aka cire masa shima sai ya cire na Mas’ud. Da dariya suka fito daga gurin tamkar wasu abokai kana suka wuce gurin sayan kazar Amarci.
“In ba don kai ba da yanzu na jima a d’akin matata wallahi.” Fad’in Mas’ud yana biya musu kud’in kajin da drinks d’in da suka sayo.
Bayan sun dawo cikin mota ne Hamidu ya mik’awa Mas’ud wani kullin magani a takarda yace,
“Goga kar ka manta da ita fa.”
Mas’ud yayi saurin k’ar6a ya barbad’a a bakinsa ya shanye haka ba tare da yasha ruwa ba. Haydar ya kallesu cikin rashin yarda yace,
“Wannan d’in menene?”
“Maganin zaman lafiya ake bawa angwaye a daren farko. Ko zaka sha?” Hamidu ya mik’a mishi wata takardar Haydar ya girgiza kai yace,
“Nagode.”
“Ka bada maza wallahi, tsoro kake ji?” Fad’in Mas’ud yana k’ara barbad’a wani garin a bakinshi.
Jin wannan kalma ta ‘tsoro’ da ya tsana yasa ya wafci uku daga hannun Hamidu ya had’iyesu duk a lokaci d’aya suka dubeshi suna zare ido.
“D’aya ko biyu ake sha ba uku ba.” Fad’in Hamidu cikin kad’uwa yana maida sauran cikin aljihunsa.
“I challenge you Mas’ud ka k’ara d’aya in ba tsoro kake yi ba.” Haydar yayi challenging Mas’ud.
D’an zaro ido kad’an yayi ya dubi Hamidu wanda yayi saurin girgiza masa kai tare da masa alamar yanke kai, kana ya kalli Haydar yace,
“You won.”
Haydar yayi dariya yana jin kanshi suka cigaba da hira irin tasu ta maza.
Sai da suka iso gidan Laila sannan ya dawo hayyacinshi ya fara tunanin yaya Laila zata kar6eshi da auren nasu gabad’aya.
Hamidu da dama shi yake driving aka barshi a mota, Mas’ud kuma ya rako Haydar har cikin falon Laila ya zauna.
Mas’ud ya shiga part d’inshi na daa ya kulle kana ya dawo ya kulle d’akin Sabrin dana Abul ya jefa keys d’in a aljihunsa ya shiga d’akin Laila.
A bakin gado ya sameta rik’e da waya tana danne-danne. Ganin Mas’ud da tayi yasa ta ajiye wayar a gefe da k’ak’alo murmushi tace,
“Ango me kake yi a nan? Na d’auka tuni ka shiga gidanka.”
“Na kawo miki naki Angon ne tunda na lura kunya kike yi baki tambayeshi ba.”
“No karka mini haka, kace mini wasa kake yi.” Ta fad’i hakan tana dafe k’irjinta.
“Yana can falo. Sai da safe don bacci nake ji sosai.” Ya fad’i hakan yana gyara garenshi kana yayi saurin fita daga d’akin.
Haydar ne ya rakashi har bakin mota kana Mas’ud ya lek’o ta window yace,
“Abunda kasha d’in nan yayi maka yawa, ka tabbata ka rage zafi idan ba haka ba wallahi gobe zaka kasa fitowa cikin jama’a, kaji na rantse maka.” Yana fad’in hakan Hamidu yaja motar suka fita daga gidan suna kyakyatawa da dariya.
Haydar da sai a lokacin ya gane me yasha yayi saurin dafe kanshi cikin dana sani. Yafi minti biyar tsaye a gurin yana tunanin me zai yi amma kwata-kwata hankalinshi bai bashi idea d’aya kwakkwara ba.
K’arshe juyawa yayi ya koma cikin falon ya samu Laila zaune a kan kujera ta dafe kanta hawaye na tsiyaya a idanunta.
Mum Fateey 👌
RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)
Littafin nan na kud'i ne a naira d'ari N100 kacal. Zaku turo kudinku ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana sai ku turo shaidar biya ta number 09023713064 a sakaku a paid group ba sai kun tsaya jiran na bati ana ja muku aji ba. Na rage kud'inshi ne don kowacce ta shigo RZ group a dama da ita. Wanda basa son hayaniyar group zamu iya tura muku ta private a N300.
(23)
Ko da Haydar ya shigo ya samu Laila tana hawaye tsayawa yayi daga bakin k’ofa yana kallonta domin bai san dalilin kukanta ba. Zuciyarsa ce ta karaya na wannan hali da suka tsinci kansu a ciki.
Laila ta d’ago ta dubeshi tana share hawayen fuskarta tace,
“Dama tun farko burinka kenan ka auri babbar mace?”
“Ban gane ba.” Ya iso cikin falon ya zauna a gefenta cikin d’aurewar kai.
“Duba nan.” Ta mik’a mishi wayarta ya kar6a ya fara karantawa.
A shekarar daya gabata ne wato 2019 a shafin Twitter wata babbar mata ta auri saurayi k’asa da shekarunta mutane suke ta kushewa, wasu sun maida hakan abun dariya wasu kuma suna ganin hakan bai dace ba, a cewarsu yafi kamata mace ta auri namijin daya fita a shekaru saboda wasu dalilansu. A cikin wannan muhawaran ne Haydar shima ya tsoma baki yake cewa,
‘Ni banga abun kushewa a nan ba, shi yaga mata yace yana so kuma ya aureta. Kowanne mutum da ra’ayinsa, bro Allah ya baku zaman lafiya.’
A k’asa abokinsa Nasir ke cewa,
‘Kai kam dama tun farko kafi son matan da suka girmeka. Ko In tayaka neman sugar mummy ne ta riritaka Alhaji?’
Haydar yace,
‘I hope to find one.. bana son yara ne kawai, I dislike their inexperience and lack of understanding of life. Sai ya zama kamar kana raising yaro ne ana ta maka shirme a gida.’
A nan hirar ya k’are ya ajiye mata wayan a gefenta.
“Yes burina kenan saboda bana son yarinta ko kad’an. ” Ya bata amsa yana kallon cikin idanunta domin ta yarda dashi.
“Kenan tun farkon had’uwarmu k’udurinka kenan?”
Girgiza kai yayi yace,
“Ganinki na farko da nayi nasan kin fi k’arfina kuma ban kawo hakan a raina ba ko kad’an. A zaman da muka yi tare ne na fad’a sonki ba tare da nayi shawara da zuciyata ba.”
Shiru suka yi na wasu sakanni sannan tace,
“Ka duba sauran links d’in da aka turo mini ka shiga kaga abunda aka fad’a a kanmu.”
Haydar ya d’auki wayar ya duba yaga har yayi locking kansa,
“Me password d’in?” Ya tambayeta.
Daburcewa tayi na ‘yan sakanni kamar mara gaskiya tace,
“Aliyu.
Wani Aliyu? Shine bai sani ba kuma bashi da niyyar tambayanta domin bashi bane a gabansu ba.
Yana bud’e wayar ya shiga text messages d’inta ya duba links d’in da aka turo yabi d’aya bayan d’aya yana karanta mummunan sharrin da aka musu, ana had’awa tare da hotunansu da aka d’auka a kwanakin baya wanda take bashi labari.
Yana karantawa ransa na 6aci zuciyarsa na k’una tamkar zata fashe saboda k’azafin zina da aka musu tare da sharri kala-kala.
‘Gulma da d’umi-d’uminta. Wannan shine Aliyu Haydar matashi d’an shekara ashirin da biyar da aka kamashi turmi da ta6arya tare da Hajiya Laila mai shekara arba’in kuma mai zaman kanta. Sakamakon kamasu da aka yi ne Alhaji Abdul CEO Lu’a Ventures ya fasa aurenta bayan ya samu labarin cewa tana can tare da Haydar a wani Hotel da sunan sun je yiwa juna bankwana, kenan ba yau suka fara aikata alfasha ba. Saboda gudun tonon asiri yasa kaninta da yayanta suka d’aura mata aure da yaron ba tare da saninta ba.
“Waya juya zancen nan haka Haydar? Wa yake son 6ata mini suna ne? Me na yiwa mutane?” Tayi tambayar idanunta na tara wasu hawayen tana jin bak’in ciki mara misaltuwa.
“Yanzu kowa yaga wannan abun, abokan kasuwancina, ‘yan uwana har da surkina da yake ganin girmana yanzu shima zai fara wasiwasi a kaina. Wallahi ban ta6a zina ba, ban ta6a yinta ba Haydar.”
Haydar kwantar da kanshi yayi saman kujera ya runtse idanunshi yana maimaita sharrin da aka musu tare da maganganun mutane, wanda wasu sun yarda da hakan har suna tsine musu wasu kuma fatan shiriya kawai suka musu.
Ya za’ayi ya goge wannan abun daya faru ya zama tamkar ba’a ta6a yi ba? Yasan za’a soki aurensu tunda yana ganin irin hakan a social media sau da yawa, amma bai ta6a kawowa a ransa za’a jefesu da k’azafin zina ba.
D’ago da kanshi yayi yaga ta d’auki wayar tana cigaba da karanta sak’onnin mutanen yayi saurin kar6ar wayar ya ajiyeta a gefe. Hakan da yayi yasa hankalinta ya dawo kanshi tana kallonshi cikin mamaki.
Gyara zamanshi yayi ya dubeta cikin nitsuwa yace,
“Laila.”
Kamar baza ta amsa ba amma ganin yanda ya nitsu sai taga ya mata kwarjini ainun tamkar ba Haydar d’in da take yiwa kallon yaro ba.
“Na’am.” Ta amsa tana kawar da idanunta gefe.
“Tambayarki zanyi ina son ki bani amsoshinsu. Kin ji?”
Gyad’a mishi kai tayi yace,
“Good. Shin a cikin duniyan nan akwai wanda ba’a ta6a zaginshi ba?”
“Babu.”
“Shin a cikin mutanen da kika sani kike tare dasu kuke harkokin yau da kullum zaki iya bugan k’irji kice dukkansu sonki suke yi na gaskiya?”
“A’a.” Ta fad’i hakan a sanyaye tana jiran taji ina maganarshi ta dosa.
“Shin d’an Adam yana iya kaucewa k’addararshi ko kuma ya rayu ba tare da Allah ya jarabceshi ba?”
Wanna karon girgiza kai tayi tana jin wani nauyi da yake kanta na raguwa, domin ita take yiwa mutane tuni da hakan amma yau gashi ita ake yiwa tuni.
“Shin kin ta6a aikata abunda ake zarginki a kai?”
“Ban ta6a ba.”
“Kenan bai kamata ki damu har kiyi kuka da idanunki don wani bawa yaga daman miki sharri ba. Kowanne mutum da kika gani a duniya yana tafiya ne da tashi jarabawar, sannan komin mulkin mutum, iliminsa, kyawunsa, arzikinsa ko sa6aninsu ba zai ta6a kaucewa maganan mutane ba sai an samu wanda zasu zageshi, koda kuwa tunda yazo duniya bai ta6a aikata laifi ba. Kiyi duba ga Annabi Muhammad SAW masoyin Allah, wanda aka yi duniya dominsa amma a hakan wasu suna zaginsa suna binshi da sharri, har aka samu masu iya jifanshi da duwatsu. Ki fad’a mini idan har shi aka iya mishi haka mu kuma su waye da zamu kaucewa hakan? A tunaninki Allah ba zai kwato mana hakkinmu bane a kan sharrin da aka mana? Ko kuma gaskiya ba zata fito ba duk daren dad’ewa?”
Ya kamo hannunta wanda yau ne karon farko da ya fara yin hakan a rayuwarsa. Wannan lokacin kallonshi take yi cikin yadda da maganganunsa ba tare da ta mance ko kalma d’aya ba.
“A hakan Laila ba’a rasa wanda suka k’aryata sharrin da