RUWAN ZUMA Book Complete Hausa Novels by Suwaiba Muhammad.docx

Author :  Suwaiba Muhammad Category :  Bookz

Chapter   17 / 44

48K to 51K   out of 132K words

da kuma kod’ewar da yayi wacce ta saka ya zama baki kamar wanda ya k’one a gobara.

Fuskarsa ta tanik’e kumatunsa sun burma ya zama tamkar k’ashi da rai yana yawo kwararo-kwararo neman abinci da kuma kud’in da zai sayi kayan maye. Abunda ya faru a rayuwarsa a baya shi kanshi baya son tunawa dalilin bak’ar wahala da azabar da yasha.

Yana nan tsaye har mutane suka k’are sannan yaja k’afarshi da yake d’ingisawa ya shiga Chemist d’in.

“A bani Codein.” Shine abunda ya fara fad’a musu bayan ya shiga.

Wani irin wawan kallo masu shagon suka watsa masa sannan d’aya daga cikinsu wanda daga ganinshi kaga Ustaz yace,

“Akwai amma ba zamu baka ba saboda amfani dashi da zaka yi ka 6atar da hankalinka. Ka gyara rayuwarka ka tuba zuwa ga Allah domin wannan rayuwar daka jefa kanka a ciki baza ta haifar maka mai kyau ba.”

“Banza shashasha. Wa’azin uban me zaka mini da wani gemunka kamar bunsuru ka d’agashi sama kana mak’e murya? Idan ba zaku sayar mini ba akwai Chemist dubbanni da zasu sayar mini.”

D’ayan mutumin wanda k’ani ne ga wanda Abul ya zaga ya tashi a zuciye zai gaurawa Abul mari yayanshi Ustaz d’in ya dakatar dashi.

“Idan kace zaka dinga saurin 6ata rai da irinsu to da kai dasu baku da banbanci, idan basu da hankali kai kayi amfani da naka hankalin kar ka biye musu.”

“Yen yen.” Fad’in Abul yana barin shagon bayan ya tofar musu da yawu a bakin k’ofa.

“Yaya kana gani ya zubar mana da yawu kan tiles?”

“Ka barshi, ka kuma mishi addu’a Allah ya shiryeshi domin yana cikin jarabawar rayuwa. Alhamdulillah bi ni’imatil lah.”

Jikin k’anin ne yayi sanyi tunowa da yayi da rayuwar yayan nasa kafin ya zama Ustaz d’in. Shima ya fuskanci jarabawa ta sace-sace kafin Allah ya shiryeshi, ya zamana kaff yaran gidansu babu mai hankali da kuma nitsuwarsa.

“Hakane Yaya. Allah ya shiryeshi da kuma masu hali irin nashi.”

“Ameen thumma Ameen.”



Abul yana barin gurin ya koma ainihin unguwar da yake zama da k’afa tsabar rashin kud’i. Dalilin da yasa yaje wancan Chemist d’in shine wanda yake sayar musu a unguwar nasu yana binshi bashi har na dubu daya amma bai biyashi ba. Kuma yace matuk’ar bai biyashi duka kud’insa ba bazai sake sayar mishi da magani ba.

Yanzu dolenshi zai je ya rok’i Imaa ya taimakeshi ya bashi saboda babu inda ya sani inda zai je a bashi magani babu prescription. Zaman Abuja kenan sai wanda ya shirya.

A bakin shagon Imaa ya samu abokan shashancinsa suna shan taba ya wucesu ba tare daya musu magana ba.

“Imaa bani Codein mana.”

“Sai ka biyani kud’ina don ubanka.”

“Nace ka daina zagin ubana, ka zagi uwata amma banda wancan daya mutun.”

“Gerrout before a bash your head for this wall.” Wannan karon cikin fushi yayi maganar domin ya tare mishi k’ofar tsukakken Chemist d’in wanda ta nan yake shan iska.

“Please na, kaga yau nazo da kudina zan biyaka.” Ya ciro d’ari biyu da hamsin wacce aka bashi bayan kwadagon da yayi a kasuwa.

Kamar walkiya Imaa ya wafce kud’in ya soketa a cikin aljihunsa yana zare masa ido.

Abul da sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa yayi saurin shiga shagon yana cewa Imaa ya bashi kud’inshi amma tuni Imaa ya hankad’oshi waje, sai gashi ya zube a k’asa a gaban abokan nashi.

“Dan iskan yaro lalatacce ni zaka nunawa rashin kunya?” Fad’in Imaa yana naushin cikinshi da k’arfin da Allah ya bashi.

Wata siririyar k’ara Abul yayi mai tattare da wahala ya dunk’ule guri d’aya yana rik’e da cikinshi. Wanda suke zaune a bakin shagon suka tashi tsaye suna kallonshi sai dai sun san shiga fad’an Imaa death wish ne, domin zai iya had’asu duka yaci uwarsu ba tare daya gaji ba ko kuma suyi nasara a kanshi ba.

K’ato ne, bak’i mummuna kuma mai tsayi. Baya shan kayan maye amma ya fisu hauka dalilin rashin imaninsa da kuma rashin tsoro. Wata naushin ya k’arawa Abul wacce tasa ya fara kakarin amai, Imaa na ganin hakan ya jawo kwalar rigarshi ‘kiiii’ ya kaishi bakin kwatan unguwar ya watsar dashi.

Amai Abul ya fara yi wanda yake fitowa kore kamar ganyen bishiya kuma mai yauk’i. Yanda yake aman kamar ranshi zai fita ya bawa Banney tausayi, ya tako ya iso gurinshi ya tsaya a kanshi.

Sai daya gama aman da taimakon Banney ya mik’e tsaye suna layi dukansu suka wuce d’akin da suke kwana wanda shago ne k’arami, k’ofar shagon da yake na katako ne k’asan ya bangare yanda mutum ko dabba zasu iya shiga koda kuwa an kulle.

Banney ya watsar da Abul kan tsummokaran kayansu kana ya koma lungun da yake kwanciya ya toni rami ya d’auko chocolate snickers ya bawa Abul.

“You are sick man. Typhoid ne yake damunka daga ganin aman da kayi. You should see a Doctor asap.”

Murmushin yak’e Abul yayi kana ya 6are chocolate d’in ya fara ci bai yi magana ba. A ranshi kuma cewa yake yi duk cutar da take jikinshi sai dai ta kasheshi saboda bashi da kud’in neman magani.

Banney da shima k’addarar rayuwa ta jefashi a halin maye ya dubi Abul yace,

“Ka koma gida, zaman nan bai dace da kai ba.”

A fusace Abul ya juyo yace,

“Kai don uwarka meya hanaka komawa? Da yanzu ka zama d’aya daga cikin successful Doctors d’in da ake ji dasu a Nigeria.”

“Do not bring my past into this.” Yayi warning d’in Abul yana masa mugun kallo.

“Nima karka sake mini maganan komawa gida. I have no family left.”

Da haka suka yi shiru Kowa da abunda yake sak’awa a ranshi, a yayin da Banney ke tuna dalilinshi na barin gatanshi shi kuma Abul tuna wahalar da yasha yake yi har rana mai kamar ta yau kamar haka;.....

Mum Fateey👌

RUWAN ZUMA 🍯

Suwaiba Muhammad

(Mum Fateey)

Littafin nan na kud'i ne a naira d'ari N100 kacal. Zaku turo kudinku ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana sai ku turo shaidar biya ta number 09023713064 a sakaku a paid group ba sai kun tsaya jiran na bati ana ja muku aji ba. Na rage kud'inshi ne don kowacce ta shigo RZ group a dama da ita. Wanda basa son hayaniyar group zamu iya tura muku ta private a N300.

(35)

Bayan Abul ya fakaici idon Mas’ud da yaran shagonsu sai ya fara d’aukan kud’i ba tare da sun gane ba. A ranar daya shirya gudu, ya d’auki jakarsa ta Laptop ya sanya kayansa kala uku a ciki da kud’in daya sata sannan suka tafi shago shi da Mas’ud kamar kullum.

Mas’ud bai kawo komai a ranshi ba game da jakar Abul saboda ya san shi mayen Computer ne kuma yana fita da ita kullum. Lokacin sallar azahar yana kawowa ya bud’e Laptop d’in ya fara danne-danne mutanen gurin na tsokanarsa wai Computer Guru yana murmushi.

Har suka yi alwala domin gabatar da sallar azahar shi yana zaune bai daina aikin da yake yi ba. Hakan yasa Mas’ud da sauran suka tafi suka barshi a kan in ya tashi ya rufe shagon su sun wuce masallaci.

Sai daya tabbatar sun isa masallacin sannan ya bud’e jakarsa ya juye kaf cinikin da aka yi a ranar ya fita daga shagon a hankali kamar ba wanda yayi 6arna ba. Daga nan bai nufi tasha ba domin yasan zasu iya bin kadinshi su gane motar ina ya shiga.

Babban titi na k’arshen gari ya nufa ya tsaya can motoci manya da k’anana na zuwa suna wuceshi ba tare da sun tsaya kamar yanda yake d’aga musu hannu ba.

A nan ne ya kira Laila da sabuwar sim d’in daya saya ta d’auka yace,

“Nine Abul. Kuma ina miki albishir da cewa na bar garin Kano da zama kwata-kwata har sai kin kashe aurenki da wannan matsiyacin yaron sannan zan dawo. Kar kusha wahalar nemana domin ba zaku ta6a sanin ina nayi ba.”

“Allah ubangiji ya shiryeka.” Shine kad’ai abunda Laila ta samu fad’a ya kashe wayarsa.

SIM card d’in ya cire ya karya sannan ya watsar a cikin ciyawin bakin hanyar. Daga nan ya kai awa biyu tsaye sannan da kyar ya samu wata Sharon da zata je Abuja ta tsaya aka d’aukeshi. A takure ya isa Abuja domin motar cike take da Lawashi da Albasa a bayan booth da kuma seat d’in baya. Seat d’in tsakiya ne kad’ai mai d’auke da mutane hud’u sai shi da Driver a gaban motar.

Suna isa tasha ya d’auki jakarshi sannan ya sanya wata sabuwar Sim Card ya kira abokinsa Faisal d’an wani hamshak’in mai kud’i a nan Abuja. Mota zugegiya aka zo aka d’aukeshi da ita wanda Faisal na bayanta yana busa Shisha yana sauraron wak’ar Naira Marley.

Suna ganin juna suka tafa kowannensu d’auke da murmushi domin wannan ne karo na farko da suka ta6a had’uwa.

“Sai gaka a Abuja. I’m glad you come Man.” Fad’in Faisal yana komawa cikin motar.

Daga nan suka wuce gidansu Faisal a wata unguwar masu ji da kud’in Nigeria, gida ne babba wanda daga gani zaka gane na wani hamshak’in mai kud’i ne wanda baya jin zafin kasheta.

Faisal d’a babba a gidan Cabin house aka gina masa a can lambun gidan wanda babu mai zuwa gurin sai shi da kuma wad’anda ya gayyata. A can aka sauk’e Abul wanda yake bin tsari da kyawun gurin. Living room ne babba guda d’aya sai d’akuna biyu da toilet guda d’aya dake tsakanin d’akunan.

Furnitures d’in da suke ciki masu kyau da tsada wanda basu cika yawa a ba dalilin mai Cabin d’in baya son hayaniya a tsarin gurin zamansa.

“You live here?” Abul ya tambayeshi yana zama kan Sofa dake cikin falon.

“Ina son zama a secluded area shiyasa Babana ya gina mini nan, sometimes na kan manta a cikin gari nake domin bishiyoyin da suke zagaye dani kan sa in d’auka a real forest nake. Bana son damuwa da hayaniya, bird chirps sun fi mini dad’in sauraro akan maganan mutane. Da fatan baka da surutu? Domin bazan shirya da kai ba.”

“No. Nima bana son yawan magana nafi son zama a gaban Computer like you.”

“Yeah.” Da haka Faisal ya isa gurin wani cabinet dake falon ya d’auki wata wayar hannu ya nunawa Abul.

“Duk abunda kake son ci ko kake buk’ata na rayuwa ka rubuta ka tura a nan za’a kawo maka a lokacin da kake so, zasu ajiye maka a bakin k’ofa domin na hanasu shigowa gurina in ba weekly cleaning ba. Ina da bak’uwa a d’akina, don’t disturb us.” Da haka ya fara takawa ya isa bakin d’aya daga cikin rooms d’in kana ya juyo yace,

“Next room is your as long as you want.” Ya shige ciki.

Haydar tashi yayi ya isa gurin da wayar take ya rubuta abunda yake so da time d’in da yake son a kawo mishi kana ya tura.

D’aukan jakarshi yayi ya shiga d’akin da aka ce nashi ne, sai dai yana shiga ya fara jiyo muryoyin Faisal da budurwarsa a wani hali na intimacy wanda hakan ya takurashi nan take. Yana ajiye jakar bai ko tsaya k’arewa d’akin kallo ba ya fice cikin sauri saboda irin kalaman da suke amfani dashi ya girmi kwakwalwarshi.

Minti sha biyar da haka yaji alamar an ajiye abu a bakin k’ofar ya tashi ya bud’e ya shigo da kwandon abincin.

Kamar yanda ya fad’a haka aka masa chips da scrambled egg sai black coffee wanda babu cream babu sugar. Yana gama cin abincin ya tattara ya kai kitchen island da yake wani gefe a falon kamar kitchen.

Bayan ya dawo ya zauna ya kunna Netflix yana kallo amma hankalinshi na kan Mamanshi wacce ya tabbatar yanzu tana cikin zullumi da kuma dana sanin auren da tayi. Kwafa yayi a zuciyarsa kuma murna yake yi da Allah ya had’ashi da Faisal a Dark Web d’insu har suka bayyanawa junansu suna da kuma inda suke, wanda ba’a cika hakan ba a duniyarsu.

Yana zaune Faisal ya fito gefenshi wata yarinya ce da bazata wuce shekaru sha shida ba tana shafa k’irjinsa. Wata riga ce iya cinya a jikinta shara-shara da bata 6oye komai ba na jikinta.

Kai tsaye gurin da wayar take suka yi Faisal na rubuta musu abunda suke buk’ata, Abul kuma daya lura da shigan yarinyar sai ya kawar da kanshi, a lokacin ne ya rage murnarsa domin da alama haka zai dinga ganin ‘yan matan Faisal and zasu takurashi.

“Abul this is Beeba my girlfriend.” Faisal ya fad’i hakan yana zama a sofa dake kallon Abul ita kuma Beeba ta hau cinyarshi tana shafa kanshi da kunnuwanshi.

Abul da bai ta6a kallon hakan a zahiri ba sai ya tsorita zuciyarsa ta fara bugawa yayi saurin kawar da kanshi gefe yace,

“Hey Beeba.”

Juyowa tayi ta masa kallon sama da k’asa sannan ta sanya yatsanta a bakinta tace,

“Hey Bull.”

“It’s Abul not Bull.” Faisal ya gyara mata yana sanya hannunshi cikin rigarta.

“I prefer to call him that.”

Abul da yaji haushin had’ashi da tayi da Shanu sai ya tashi ya koma d’akin da aka bashi domin ya lura kamar basu gama abunda suke yi ba.

Sai daya tabbatar sun fita daga gidan sannan ya fito ya shiga band’aki yayi wanka da alwala kana ya koma yayi sallah. Yana zaune a kan sallayar yaji yana buk’atar abunda zai kawar da hankalinshi. Jakarsa ya jawo ya fara bincike ko zai samu sauran kwayarsa, yana binciken ya samu wata kwayar da sau d’aya Micheal ya ta6a bashi yasha saboda k’arfinta da tsadarta.

Waye ya iya sayan mai yawa haka har ya sanya mishi a cikin jakarsa? Ya gama kaf tunaninshi bai tuna lokacin daya saya ko aka bashi ba. Ganin zai 6ata lokacinsa yasa ya d’auki biyu ya harba kana ya kawar da duk abunda zai iya yiwa kanshi illa dashi ya kwanta a kan gado yana jiran ta fara aikinta ta kaishi duniyar da babu damuwa sai farin ciki da jindad’i.

Bai iya komai ba bayan ta fara wargaza masa kwakwalwa illa bud’e bakinsa da yake yi yana rufewa, can kuma sai ya rufe idanunsa sai ya bud’e yana murmushin jindadi shi kad’ai. Wani lokaci kuma zai gwada tashi amma daya duba k’arkashin gadonsa sai yaga rami ne mai duhu babu gurin takawa. Hakan yasa yayi kwanciyarsa akan gadon har bacci ya kwasheshi mai cike da mafarkai iri daban-daban.

Haka rayuwarsa a gidan Faisal ta kasance, da safe kafin su tashi zai rigasu tashi yayi amfani da band’aki ya kuma yi order d’in abinci a kawo masa yaci. Daga nan kuma zai shige d’akinsa yana danna Laptop d’insa inda yake samun labarin duk wani motsi na uwarsa da mijinta. Yamma tana yi zai sha kwayarsa yayi mankas ya kwanta a kan gado yana zaro harshensa waje har bacci ya d’aukeshi.

Faisal bai damu da sanin ina Abul yake ba domin shima harkar gabansa kawai yake yi da Beeba budurwarsa. Idan kuma suka had’u falo in dai ba wata babbar magana ba basa kula juna. Beeba na yawan kallon Abul tana kuma jan hankalinsa idan Faisal baya ganinta, Abul daya lura ta fara seducing d’inshi sai yayi saurin gama abunda yake yi ya bar musu falon.

Yau satinsa biyu a gidan, a nan ne kuma kwayarsa mai kwantar masa da hankali da sakashi nishad’i ta k’are. Kud’insa da yake dashi ya fitar ya fito falo ya samu Faisal da Beeba a wani hali da bai so gani ba. Ya kai seconds goma yana kallonsu sannan ya kira sunan Faisal ya juyo.

“What bro?” Faisal ya amsa masa ba tare daya daina abunda yake yi ba.

“Ina son fita supplies d’ina sun k’are.”

“Go to my Driver.” Daga nan ya maida hankalinshi kan abunda yake yi ya rufe idanunsa yana cije fuska.

Abul hanyar k’ofa yayi amma bai san dalilin da yasa ya juyo ba hankalinshi na kan Beeba dake k’asan Faisal tana aiko masa da kallo mai cike da fassara iri-iri.

Shi ba gwanki bane koda yana shan kwaya yana buk’atar mace a rayuwarsa, ganinsu da yayi kuma cikin wannan halin yasa yaji shima yana buk’atar hakan. Sai dai wa zai samu? A yanzu daya 6ata rayuwarsa ma baya buk’atar k’arin yin zina. Zai sha kwaya amma ba zai yi zina ba, da haka ya isa gurin da motocin Faisal suke Driver ya d’aukeshi suka fita daga gidan.

Babu inda bai zaga ba amma bai samu inda ake sayar da kwaya ba, Pharmacy babba ko k’arami sun hanashi magani sunce sai da prescription. Ya fito a wani Chemist na shida da suka je ne wani ya biyoshi ya masa kwatancen shagon Imaa dake can kwararon unguwar ‘yan iskan garin marasa galihu.

Da k’afarshi ya k’arasa shagon domin Driver yace motar baza ta iya shiga unguwar ba, a bakin shagon ya samu samari hud’u zaune suna busa sigari, daka gansu zaka san suna shan wahalar rayuwa. Duk abunda yake buk’ata ya saya a shagon Imaa na murna domin yayi ciniki sosai ba kad’an ba. Sai dai bai samu kwayarsa da yake sha tun zuwanshi Abuja ba.

Bayan ya fito ya bawa samarin kud’i wanda ciki har da Banney dake binshi da kallo

17 / 44