RUWAN ZUMA Book Complete Hausa Novels by Suwaiba Muhammad.docx

Author :  Suwaiba Muhammad Category :  Bookz

Chapter   34 / 44

99K to 102K   out of 132K words

tunda aka gane cewa shi d’in jininsu ne kuma d’an cousin d’insu.

Sai da Haydar ya cinye tuwon sannan Laila ta kawo mishi bowl da ruwa ya wanke hannunshi yana kallonsu duka yace,

“Irin wannan so da kulawan da ake nuna mini sai yasa in k’ara gudu gobe.”

“Don’t even try it.” Fad’in Mas’ud. Laila kuma tace,

“Zaka k’arisani kenan?”

Murmusawa yayi ya kad’a kanshi kana yace,

“Ina Ammi take?”

Nan suka nitsu Laila ta musu jagora zuwa falo suka zauna, shi dai Haydar bin su yake yi da ido domin bai ga dalilin da zai sa daga tambayar ina Ammi take ba sai su nemi ya dawo falo a zauna, kenan magana mai muhimmanci za’a yi. Kasa hak’uri yayi dalilin zuciyarsa data fara tsoritashi a kan cewa ko Ammi tana kwance ne bata da lafiya yace,

“Me ya samu Ammi?”

“Babu abun da ya sameta amma bayan tafiyanka abubuwa da yawa sun faru Haydar, ciki har da bayyanar mahaifinka.”

K’ura musu ido Haydar yayi yana karantar su, ganin babu alamun wasa a fuskarsu yasa yace,

“Da gaske kuke yi? Ina mahaifin nawa?” Zuciyarsa kuma tuni ta tsananta bugu amma a waje sai ya dake yana jiran amsarsu.

“Alhaji Abdul yayanka ne babanku d’aya.”

“No, no. Ta yaya? Yaya hakan zai kasance?” Ya cire hularsa ya ajiye a gefe yana jin gumi na tsatstsafo mishi ta ko’ina a jikinshi.

A nan Mas’ud ya fad’a mishi duk abunda ya faru bai rage komai ba sannan ya k’arisa da cewa,

“Yanzu Ummii da Ammi suna can Maiduguri.”

Shi kuma Haydar kallon Laila yake yi da yaji labarin har gayyatar Alhaji Abdul tayi gidanta bayan duk munafurcin daya mata ya lalata mata d’anta, yace,

“Meyasa zaki nemeshi Laila? Bakya tsoron ya k’ara cutar dake?”

“Yayi nadama Haydar, yana k’aunarka yanda baka tsammani a yanzu. Try and get to know him shi da Babanka a nan zaka gane irin son da suke maka bana wasa bane.”

A nan itama ta bashi tarihin Alhaji Abdul wanda ya fad’a mata har ta yarda da cewa ba zai ta6a gigin cutar dasu ba. Shiru Haydar yayi yana tunani sannan yace,

“Bazan ta6a yafe mishi halin daya saka Abul a ciki ba, wannan cutar tafi kowanne bak’anta mini rai Laila. Ya cuci rayuwarsa wanda hak’uri yayi kad’an ya gyara 6arnan da yayi. Zan nemi mahaifina amma tsakanina da Abdul babu zumunci har abada.”

Shiru su Mas’ud suka yi domin a yanzu da yake kan gadon zuciya ko menene suka fad’a mishi ba zai sauraresu ba. Amma idan lokaci yayi shi da kanshi zai neme Abdul d’in saboda su ‘yan uwan juna ne wanda ruwa ba zai wanke jininsu ba haka kuma wuk’a baza ta yanka ba.

Suna zaune suna tattaunawa Haydar ya d’auko wayarsa dake cikin jakarsa ya kunna ta. Sak’onni ne suka fara shigowa babu k’akk’autawa wanda hakan ya hanashi kiran wanda yake son kira. Sai da suka gama shigowa ya duba yace,

“Su waye suka turo mini messages haka?”

“A cikinsu akwai wanda na zageka, so kar ka 6ata rai.” Fad’in Mas’ud yana sosa k’eyarsa.

“Meyasa zaka zageshi Mas’ud?” Laila ta zaro ido tana dubanshi.

Kafin ya bata amsa suka ga Haydar ya kara waya a kunnensa yana cewa,

“Hello.”

Alhaji Abdul da yake d’ayan gefen kasa magana yayi illah tashi da yayi tsaye ya nufi d’akin da Babanshi yake yana cewa,

“Baba ga Haydar.”

Hannu na rawa Baba ya k’ar6i wayar ya k’ara a kunnenshi yace,

“Aliyu Haydar.”

Kasa magana Haydar yayi dalilin ruwan daya taru a idanunsa ya juyawa su Laila baya sannan yace,

“Na’am Baba, kana ina?”

Mintuna talatin da haka Haydar ya shiga tangamemen gidan Alhaji Sammani wato Babansa shi da Alhaji Abdul. A bakin k’ofa ya tarar da tsohon wanda ko jira bai yi motarsa ta tsaya ba ya tako cikin sassarfa ya bud’e marfin gaban motar inda yaga Haydar yake zaune. Ai kuwa yana fitowa Baba ya rungumeshi tsam a jikinshi yana cewa,

“Allah nagode maka, Alhamdulillah d’ana ya dawo gareni.”

Shi kuma Haydar daurewa kawai yake yi amma kuka ne yaji yana son ku6uce mishi ganin wai yau gashi tare da mahaifinshi wanda a daa har ya cire rai da zai had’u dashi.

Sai da suka tsagaita sannan Baba da kanshi ya mishi iso zuwa cikin falonsa ba tare da ya sake hannun Haydar ba. Alhaji Abdul da yake can gefe yana tsaye murmusawa kawai yake yi cikin farin ciki kana ya shige motarshi ya fita daga gidan zuwa gyaran abunda ya 6ata na biyu.

Suna shiga falon Baba ya zaunar da Haydar kusa dashi kana ya k’ura mishi ido yace,

“Kafi kama da k’anina Alhaji Shettima wanda ya kar6a maka aure, suna zuwa yanzu da duk ‘yan uwana.” Yana rufe baki kuwa suka ji k’aran bud’e gate nan da nan motoci zafafa suka fara shigowa suna parking a farfajiyar gidan wanda zai d’auki motoci fiye da ashirin.

Lokaci guda falon ya cika da mutane manya da yara wanda Baba da kanshi yake nuna mishi su tare da sunayensu. Yawancinsu ‘yaya da jikokin Alhaji shettima ne tunda Baba Alhaji abdul kad’ai ya haifa kuma ya k’i aure har yanzu, Hajiya Hadiza k’anwarsu kuwa ‘yayanta 6 ne sai tarin jikoki.

“Ga k’anina Alhaji shettima sai k’anwarsa Hajiya Hadiza, mu kad’ai iyayenmu suka haifa wanda a yanzu basu da rai Allah ya musu rasuwa. ‘Yayan Shettima goma sha uku da jikokinshi talatin da biyar. Sammani mai sunana shine babban d’ansa yana da ‘yaya bakwai, sai dai baya gari zai dawo yau daya samu labarin an sameka. Wannan k’anwarsa ce Aisha tana aure a nan Kano da ‘yayanta hud’u, sai........”

Haka Baba yayi ta k’irgawa Haydar ‘yan uwansa da kuma sunayensu, wani gurin idan yayi 6atan suna sai jikokin su gyara mishi suna mishi dariya wai yayi expire. Haydar dai bin kowa yake yi da kallo yana jin zuciyarshi kamar ta fashe tsabar murna da farinciki, suma ido suka zuba masa suna murnar ganinshi kowa na son yayi hira dashi amma hakan babu dama don yawansu.

Hajiya Hadiza da tun shigowarta take zaune kusa dashi tace,

“Aliyu Haydar ina mamanka?”

“Tana Maiduguri gurin ‘yan uwanta.” Haydar ya amsa mata yana mamakin yanda yake d’ibi da ita kad’an musamman idanunsu da girarsu.

Alhaji Shettima kamar yafi kowa murna don tun ranar daya d’aurawa Haydar aure da Laila yaji yana son yaron. Halin Alhaji Abdul na neman mata yasa suka tsani halinshi suke hantararsa, amma a yanzu da Haydar ya kasance nasu zasu jawoshi jikinsu ya gane cewa yana da zuriya.

Kanshi ne ya fara ciwo domin mutanen sun mishi yawa gashi tun d’azu bak’inshi ya kasa rufuwa, Baba ne ya fara lura da hakan ya cewa ‘yan matan zuriyar nasu su shiga kitchen su musu girki.

“Zamu dafa amma sai anyi alk’awarin aure.” D’aya daga cikin jikarsu Iman ta fad’a cikin tsokanan Kaka da jika.

“Ku dai dafa sai ayi maganar auren, amma ni bazan auri wacce bata iya d’aura zani ba.” Ya mayar da martani wanda kowa ya gane da Iman yake yi wacce bata iya d’aura zani ba ko da pieces ne.

Dariya sauran ‘yan uwanta suka mata ta koma gefen Haydar tace,

“Kaga Babanka ko?”

“Tsakaninku babu ruwana.” Ya bata amsa yana dariya.

Kiran sallah da ake yi yasa Haydar da ‘yan uwansa maza wanda wasu sun fishi yayin da wasu kuma sa’anninshi ne suka wuce masallacin dake jikin gidan, iyayensu maza ma suka rufa musu baya.

Matan kuma empty rooms d’in da ke gidan suka shiga suka bar Aisha babbar addarsu a falo tana musu order na abinci a wani restaurant. Hajiya Hadiza kam d’aki ta samu cikin tarin d’akunan da suke gidan tace kar a dameta zata yi bacci, jikokin da suka san halinta na masifa babu wanda yayi gigin zuwa inda take kowa ya kama sha’anin gabanshi.

Kafin su Haydar su dawo gida har yayi aboki a cikin ‘yayan Alhaji Shettima wanda hankalinsu yazo d’aya kuma sa’annin juna ne sunanshi Yunus, a nan Yunus yake bashi labarin budurwar da zai aura wanda har an saka date next month.

“Kace zamu sha biki.”

“Ba sosai ba saboda bana son bidi’a yayi yawa a biki.” Yunus ya amsa yana murmushi.

“Kuma hakan yafi, less bidi’a more albarka a aure. In bidi’a yayi yawa sai kaga ana ta tashin hankali saboda tun a auren albarkar shaidan aka nema bana Allah ba.”

“Kuma gaskiyanka fa.”

K’anin Yunus wanda kanshi ke rawa mai suna Na’eem yace,

“Mu dai namu sai kaff yan Kano sun san anyi aure.”

Dariya Haydar yayi yana jin kanshi cikin annushuwa wai shine yake having conversations da danginshi, shi kuma Yunus hararan k’anin nashi yayi yace,

“Ka samu matar tukunna.”

Da haka suka shigo cikin gidan Alhaji Sammani na tambayar ina Alhaji Abdul yake, kowa yace bai ganshi ba. Hakan yasa ya kirashi a waya yace yana son ganinshi yanzu.

Minti ashirin da haka Alhaji Abdul ya shigo gidan ‘yan uwanshi na gaisheshi yana amsawa fuska babu yabo babu fallasa. Haydar kuwa yana ganinshi ya had’e rai sosai domin babu abunda yake tunawa sai lalata tarbiyyar Abul da yayi. Alhaji Sammani da Alhaji Shettima su suka ja ‘yan uwa biyun zuwa wani falo a uptairs suka ajiyesu guri d’aya domin sulhuntasu.

Masu karatu zaku iya bawa Alhaji Abdul second chance?

Mum Fateey 👌

RUWAN ZUMA 🍯

Suwaiba Muhammad

(Mum Fateey)

(49)

  Alhaji Sammani ya dubi ‘yayan nasa ya fara magana kamar haka,

“Aliyu Haydar ban yi rayuwa da kai ba amma a ‘yan awannin da na kasance tare da kai na lura kai mutum ne mai hankali, nitsuwa da kuma dattako. Ina da labarin duk abun da Abdul yayi maka tare da kuma matarka bai 6oye mini komai ba, yayi laifi matuk’a wanda nima nayi fushi dashi bana wasa ba saboda yayi amfani ne da k’arfin arzikin da na tara wajen aikata sharri gare ku. Ban ji dad’in abun da yayi ba, kuma na mishi fad’a, sannan na mishi nasiha duk don in nuna mishi laifin da yayi ba kad’an bane. Dalilin da yasa na tara ku a nan shine don in baka hak’uri a kan duk wani abu da Abdul ya muku sannan ina neman mishi yafiya a gurin ku ba don ya cancanci a hakan ba sai don ina tsoritar masa fushin Allah da kuma girman alhakin ku daya d’auka. Abdul yayi nadama ya kuma yi dana sani a kan gur6ata tarbiyyar d’an matarka da yayi, wallahi rana bata gushewa kullum sai ya sanar dani irin tsanar kanshi da yake yi a kan laifukansa a gareku. Ka yafewa d’an uwanka sannan ka mishi jagora ya nemi yafiyar matarka da kuma yaron idan har zasu iya yafe masa. Don Allah kar hakan yasa zumuncinku ya 6aci tun kafin a k’ulla, ku kad’ai Allah ya bani wanda nake fatan ko bayan raina zaku had’a kanku ku zama tsintsiya mad’aurin ki d’aya. Hakan kuma ba zai faru ba har sai kun sasanta junanku kuma kun yi hak’uri da duk abun da ya faru a baya. Rok’on ka nake yi Aliyu Haydar ba wai ina baka umurni bane, sannan a yau idan ka nuna ba zaka iya hak’urin ba wallahi zan fahimceka saboda Abdul ya yi laifin da ya wuce minzali ya wuce gona da iri.”

Tun da Baba ya fara magana Haydar kanshi ke k’asa yana jin ina ma basu d’auko maganar ba a wannan ranar, saboda shima a yau ya samu labarin makircin Alhaji Abdul wanda yake jin shi sabo a zuciyarsa. Sannan da ba don a gaban Baba suke ba da ya yiwa Alhaji Abdul abun da yafi na Madu, yanzu ma ya tsani ganinsa balle har ayi tunanin zai iya yafe masa duk da cewa bashi ya cuta ba kai tsaye. Amma ai jinin Laila jininshi ne, Abul danginshi ne na jini sannan d’an matarsa ne. Kuma ko ya iya yafe mishi Laila da Abul baza su ta6a yafe mishi ba dalilin mugun cutar dasu da yayi. Sannan ta yaya zai iya huld’a dashi a karo na biyu har yarda da amincin da Baba yake fata ya wanzu a tsakaninsu? Ai abun kamar da wuya wai gurguwa da auren nesa.

Haydar kasa cewa komai yayi dalilin kunya da kuma ganin girman Babansa da Alhaji Shettima da yake yi. Ina zai iya kallon tsabar idanunsu yace ba zai iya hak’uri da d’ansu ba? Ya san cewa Alhaji Abdul yafi samun gurbi mafi yawa a zuciyar Babansu, saboda shi kad’ai Baban yake gani a matsayin d’a, shi kuma rana tsaka da bayyanarsa ba zai sa a yi mishi wannan soyayyar ba saboda rashin sabon dake tsakaninsu.

Ganin shirun yayi yawa yasa Alhaji Shettima yin gyaran murya ya ce,

“I understand how you feel Haydar, sannan zai fi kyautuwa mu baka lokaci kayi tunani a kan hakan. Sai dai don Allah zamu rok’eka kar ka bari wannan abun da ya faru ya shiga tsakaninka da d’an uwanka, kayi fushi, kayi fad’a amma kar ku raba zumunci. Allah ya baka hak’uri Haydar.”

“Amin.” Kawai Haydar ya iya cewa amma bai d’ago kanshi ba.

Alhaji Abdul da tun daya shigo gidan yake jin k’aunar k’anin nasa yace,

“Kayi hak’uri da duk laifin da na aikata a gareka da kuma dangin matarka, nayi nadama sannan baku cancanci hakan daga gareni ba ko da kuwa kai ba jinina bane. Ina rok’an yafiyarka sannan ina neman ka mini izini zuwa gidanka in bawa Laila hak’uri kuma in nemi yafiyarta. Kar kasa a ranka zan k’ara kallon Laila mai nuni da soyayya, wallahi tun ranar da na gane kai k’anina ne na ji na hak’ura da ita saboda k’aunar da nake maka zai iya sawa in bar maka komai ko da kuwa zan rasa raina ne. Hakan yasa na yanke shawarar barin duk wata dukiya da Baba ya damk’a mini ta dawo hannunka, sannan zan yi nisa da ku, nisa mai yawa saboda I want you to feel free and secured. Lu’a Ventures an ginashi ne da sunan da Baba ya rad’awa Ammi, sauran companies d’inmu na kayan gine-gine da kuma yin kwangila duk sun dawo k’ark’ashin ka sai yanda kayi dasu. Sannan zan iya rantse maka da sunan Allah babu haram a cikin dukiyar nan, sai dai a daa na kashe da yawa daga cikinta ta hanyar neman mata da shan giya wanda a yanzu na daina har abada kuma ina so ku tayani da addu’a Allah yasa kar in koma halina na da. Ina son barin duk rayuwar da nayi a baya amma hakan ba zai yiwu ba har sai na samu sauk’i game da sukuni a zuciyata ta samun yafiyarku. Don girman Allah ka yafe mini.”

“Na yafe maka duniya da lahira, zaka iya zuwa ka nemi yafiyarta da kuma Abul saboda sun fi cutuwa sama da ni. Bana buk’atar dukiyar ka sannan kar kace kaima zaka tafi domin hakan ba zai gyara komai ba, and Baba will always need you.”

Baba da Alhaji Shettima farin ciki ne fal a ransu musamman Baba da yake taraddadin lalacewar zumuncin ‘yayansa, ya ce,

“Allah ya muku albarka ya had’a kanku ya kuma shiryi yaron.”

“Amin.” Kowa ya amsa kana suka cigaba da tattaunawa game da dukiyar da Alhaji Abdul yace zai barwa Haydar yayin da shi Haydar d’in ya kafe da cewa baya so kuma baya buk’atan hakan. Ganin jayayyar ta yi yawa yasa Baba ya dakatar dasu kan a bar maganar sai daga baya. A nan ya dubi Haydar yace,

“D’ana tun lokacin da Ammin ka ta bayyana na nemi ta amince a mayar mana da aurenmu, dalili kuwa bayan 6acewarta da shekara biyu na saketa saki d’aya saboda bana son tana yawo da aurena a kanta. Na san zaka ji haushin rayuwar da muka yi a baya wanda bana fatan a sake furtawa saboda k’azantar dake ciki ta yawaita har ta ta6a d’ana Abdul wanda shima yanzu yake nadamar halayyarsa. Duk yanda na kai ga neman ganawa da ita ta hana k’arshe cewa tayi in barta da halin da take ciki na 6acewarka, a yanzu da ka dawo ina so kai ka mini iso gareta da ‘yan uwanta don in samu aurenta wannan karon cikin mutunci da albarkar iyaye.”

Haydar zai iya cewa wannan ne magana mai dad’i da yaji tun zaman su a wannan falon, domin kuwa baya son Ammin shi ta k’are a haka babu aure duk da cewa ita ma rayuwar da tayi a baya ta k’azanta kuma Allah Ya nuna mata kuskurenta ta hanyoyi daban-daban. Ya sani cewa itama ta yi nadamar halin da ta saka kanta a ciki domin yana tuna nasiharta a gareshi akan ya nisanta kanshi daga aikata zina domin tana wargaza rayuwar mutum ta kuma hana shi samun rahamar Allah, hakan yasa ya taso baya ko sha’awar zina balle har ya aikata. Zai d’auki hakan a cikin rahamar Allah saboda daga Babanshi, mamanshi har yayanshi basu kaucewa wannan k’addarar ba. Kenan shi Allah ya ku6utar dashi ya kuma mishi Rahama da har ya bashi Laila ya kuma bayyana mishi ‘yan uwansa da dangin shi a lokacin da bai yi tsammani ba.

Murmusawa Haydar yayi yana godiya ga Allah da ya nuna mishi wannan so da k’aunar yace,

“Baba ka saka rana in maka jagora zuwa Maiduguri neman auren mahaifiyata a karo na biyu. Allah ya bar ku tare.”

Laila ce zaune a falo da yamma tana jiran mijinta wanda take mugun kewa tare da son kasancewa tare dashi

34 / 44