Author : Suwaiba Muhammad Category : Bookz
a duba jikinshi dalilin Mas’ud yace bai yarda da lafiyar yaron ba.
Duk yanda Abul yayi k’ok’arin guduwa bai samu ba dalilin takunkumi da suka saka masa yanda duk wani motsinsa na idonsu, duk bandage d’in jikinshi sai da aka d’aye aka sake wankewa saboda Doctor yace bai yarda da wanda aka mishi ba. Abul yaga wahala, sai ‘wash wash’ kawai yake fad’a yana shanye hawayensa da suke son zuba.
Tests kuwa an masa har dana HIV akan washegari result zai fito. Sune basu bar asibitin ba sai k’arfe sha d’aya da rabi na dare, Haydar ya sauk’e Mas’ud a gida sannan shima ya wuce gidansa yana tunanin yanda zai samu Laila wacce ke fushi dashi.
A gajiye ya fito daga motarsa ya fito da abunda ya saya zai ci kana ya shiga sashensa. Kai tsaye d’akinsa ya wuce domin bashi da niyyar dawowa falo sai washegari dalilin gajiyan daya kwaso. Bai yi tsammanin ganin Laila kwance akan gadonshi ba, sai dai hakan ba k’aramin dad’i ya mishi ba saboda yasan kewarsa da sonshi da take yi ne yasa tazo d’akinsa ta kwanta.
A hankali ya mayar da k’ofar ya rufe sannan ya ajiye abun hannunsa a k’asa ya fara cire kayan jikinshi, daga nan kuwa ya shiga band’aki yayi wanka ya fito sannan ya zauna ya fara cin abinci yana kallon Laila wacce bata ma san ya shigo ba sai baccinta take yi hankalinta kwance.
Singlet d’insa da gajeran wandonsa ne a jikinta kamar wacce ta rasa kayan sakawa, sai dai a idanun Haydar ta mishi kyau sosai tare da tayar mishi da wani kewarta na daban. Yana gama cin abincin ya tattara gurin ya kashe wutan wayarsa kana ya isa bakin katifar ya kwanta. Addu’a yayi ya shafa a jikinshi tare da nata, jin hannun mutum a jikinta yasa Laila ta farka zuciyarta na dukan uku uku.
Tsabar rud’ewa har numfashinta ta d’age domin bata san mutum ko aljan ne ya ta6ata ba. Haydar da bashi da masaniyar ta farka ya gyara kwanciyarsa hakan kuma yasa Laila ta k’ara firgita domin wanda ya ta6ata yana kan gado kusa da ita.
Wani irin ihu tayi ta mik’e tsaye cikin sauri tana lalu6ar abunda zata yi masa lahani dashi, Haydar a tsorice shima ya tashi tsaye yana kiran sunanta tare da yin kanta don yaji meya sameta.
“Laila lafiyanki? Meya sameki? Laila.”
“Waye ne kai? Me kake yi a gidana?”
“Nine Haydar, ki kwantar da hankalinki. Kalli nan.” Ya d’auki wayarsa ya kunna haske ya ganta rungume da takalminsa wanda zata kare kanta dashi.
Wani wawan ajiyar zuciya tayi tana dafe k’irjinta domin ba k’aramin tsoritata yayi ba. Abun ya bashi dariya ya kamo hannunta yana cewa,
“Yanzu da saceki za’a yi da sai dai ki farka ki ganki a cikin buhu. Tun d’azu fa na dawo nayi wanka naci abinci sannan nazo na kwanta, duk baki ji ba? Yaushe kika fara bacci mai nauyi haka?”
“Dan Allah ka sakeni.” Ta fad’a tana mai kwace hannunta domin har lokacin bata dawo saiti ba.
“I’m sorry I scared you like this.” Ya bata hak’uri ba tare da yayi gigin ta6ata ba.
Sai data k’ara minti biyu sannan zuciyarta ta fara normal bugawa, hakan yasa ta zauna a bakin katifar ta dubeshi tace,
“Kace kwana zaka yi.”
“Yes, na gama abunda ya kaini da wuri ne shiyasa.”
“Sannu da dawowa. Ya hanya?”
“Lafiya kalau. Ya kike?”
“Hamdallah.” Ta bashi amsa tana kwanciya.
Tana son tambayarshi me yaje yi Abuja kuma a cikin kwana d’aya amma bata so yayi tsammanin bincikensa take yi. Shima Haydar kwanciyar yayi tare da kashe hasken wayar a karo na biyu.
“Me kayi a Abuja?” Ta tambayeshi duk k’ok’arinta na k’in son tambayar nashi.
“Wani abu muka d’auko.” Ya bata half answer.
“Ba kai kad’ai bane kenan?”
“Ni da Mas’ud ne.”
A nan ne Laila tayi wata wawiyar ajiyar zuciya domin har ta fara jin d’aci a ranta da tayi tunanin ko gurin mace yaje. Watak’ila a wancan zuwan nashi ya had’u da ita shine yau tace tana son ganinshi ya kuma je. Kenan duk tunaninta ba haka bane?
“Nikam Abul yana kiranki ne kwana biyun nan?” Haydar ya tambayi Laila.
“Bai fi sati ba ya kirani amma yak’i magana kamar mai jiran in fad’i wani abu. Da yaji bazan ce komai ba sai ya tambayeni wai ina kake.”
“Uhm, sai kika ce masa me?”
“Nace kana lafiya.”
“Then?”
“Shikenan sai ya kashe wayarsa. Ban gane me yake nufi ba, har na fara tsoron ko wani abun zai maka sai na tuna rashin hankalinshi bai kai haka ba.”
“Zai yi wuya kam.”
“Lafiya dai ko?”
“Lau. Ki kwanta, I’m sorry na katse miki baccinki.”
Bata ce komai ba ta gyara kwanciyarta sai dai idanunta kek’au babu alamar bacci. Shima Haydar ya nemi gajiya da baccin da yake ji ya rasa, babu abunda yafi so a yanzu kamar yaji Laila a jikinshi.
Minti biyar da haka ta mirgina ta shiga jikinshi tana ajiyar zuciya. Hannunsa yasa ya gyara mata kwanciyar sannan ya ruk’unk’umeta tsam a jikinshi yana cewa,
“I have missed you.”
“Me too. Please mu daina yawan fad’a mu ba yara bane Haydar.”
“Zamu kiyaye.”
“I need you.” Ta furta a hankali tana kai hannunta jikinshi inda tasan ba zai iya resisting d’inta ba. Kafin ta k’ara cewa komai ya kar6i jagorancin a matsayinsa na head of the house.
“I need you too like crazy Laila.”
Mun Fateey 👌
RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)
(40)
“Sun dawo da yaron gida Alhaji.”
“Good, very good.” Fad’in Alhajin yana tafa hannayensa.
*****************
Washe gari k’arfe bakwai Haydar da Mas’ud suka shiga asibitin da aka kwantar da Abul. A bakin room d’in da yake suka karb’i makullin d’akin daga gurin Nurse suka bud’e tare da kutsa kai ciki. Shigan su d’akin suka samu yana bacci mai nauyi har bakinshi a bud’e kamar wani matacce.
“Ka dubi yanda yaron nan ya dawo. It’s like kwata-kwata baya cin abinci sai kayan maye.” Fad’in Mas’ud yana mai k’arisawa kusa da gadon.
“Kayan shaye-shayen is their priority, abinci shine na biyu a gurinsu. Mu duba office d’in Doctor ko result d’insa ya fito mu kar6a.” Haydar dake tsaye a bakin k’ofa ya fad’a yana mai fita daga d’akin Mas’ud yabi bayanshi.
Bayan sun isa office d’in Doctor aka fad’a musu bai iso ba sai k’arfe takwas. Hakan yasa suka juyo zuwa d’akin Abul suka zauna.
“Yanzu daga nan meya kamata muyi?” Haydar ya tambaya.
“Zamu fad’awa Kalti da Kakarsu cewa an sameshi, idan ya samu sauk’i zuwa nan da kwana biyu ko uku sai mu kaishi Maiduguri gurin Kaala Abdi.” Mas’ud ya amsa masa.
“Hakan yayi daidai. Yanzu kam hankalin Laila zai kwanta tunda tasan inda yake, sai kuma babban abun shiryawarsa wanda sai an had’a da addu’a game da sadaka. Allah ya tak’aita masa wahala yasa daga yanzu yayi hankali.”
“Amin Amin.” Mas’ud ya amsa yana kallon Abul daya fara motsa idanunsa alamar zai farka.
A hankali Abul ya fara bud’e idanunshi yana rufewa dalilin hasken rana daya mamaye ilahirin d’akin, yana juyar da kansa yayi ido hud’u da Mas’ud wanda hakan yasa ya mik’e zaune cikin sauri tamkar wanda ya ga abun tsoro.
“Ina zaka je?” Shine tambayar da Mas’ud ya masa yana dafa kafad’unshi duka ya mayar dashi zuwa kwance.
Dafe kai Abul yayi tare da runtse idanunsa yana jin bak’in ciki a ranshi dalilin tunowa da yayi da abunda ya faru jiya, wato rabashi da suka yi da freedom d’insa. (A fad’arshi kenan)
“Kayi sallah kuwa?” Wannan karon Haydar ne yayi maganar shima yana duban Abul.
Abul bai ce komai ba haka kuma bai yi alama da zata nuna yaji me aka tambayeshi ba.
“Kai ba magana ake maka ba kayi shiru kana jin mutane?” A fusace Mas’ud ya masa maganar.
“To ai kuna gani yanzu tashina.” Ya fad’i hakan cikin rashin kunya.
“Wannan ba amsa bace. Aka ce kayi sallah ko baka yi ba?” Mas’ud yaja kwalar rigarsa ya zaunar dashi.
“Mas’ud don Allah ka barshi, gaskiyarshi ai yanzu ya tashi a gabanmu. Daa ban tambaya ba.”
Kad’a kai Mas’ud yayi kana yaci gaba da kallon Abul yace,
“Ka tashi kayi sallah. Ga band’aki nan a hanyar fita daga d’akin. And don’t even think about running away, saboda na nuna hotonka a bakin gate kan cewa in har aka ganka kai d’aya a kamaka a kirani. Sannan your condition da kuma gurbataccen k’afarka bazai baka daman guduwa ba.”
Abul na hararansu ya mik’e da kyar ya shiga band’akin ba tare da sun taimaka mishi ba. A nan ne Haydar ya dubi Mas’ud yace,
“Ya kamata Laila ta san me ake ciki don bana son tace na 6oye mata irin wannan abun har na tsawon lokaci haka.”
“Gaskiya ne. Call her.”
Da haka Haydar ya tashi ya fita daga d’akin yana danna wayarsa. A gindin wata bishiya ya tsaya yana murmusawa jin Laila ta d’auki wayar tana mishi sallama. Amsawa yayi kana yace,
“Ba dai bacci kika koma ba bayan tafiyata?”
“Ina rama na jiya ne da ka hanani yi.” Ta bashi amsa cikin murya irinta masu bacci.
“Ko in dawo ne?”
Ai da sauri ta bashi amsa,
“No, no yi zamanka a office. Ban ce ba.”
“Ya da saurin karaya haka?” Ya tambaya yana dariya don yasan meya aikata.
“Ba wani karaya, just kayi zamanka.” Ta fad’a tana dariya k’asa-k’asa.
“Raguwa kawai. Amm... ki shirya nan da minti talatin zan zo in kaiki wani guri.”
“Ina kenan?” Ta tambayeshi cikin d’aurewar kai.
“Hey, surprise ne.”
“I hate surprises. Don Allah ka fad’a mini kawai.”
“A’a, zaki gani in kin zo. Call me nan da thirty minutes. Love you.” Ya kashe wayarsa yana murmushi yana hasko yanda fuskarta zata yi idan ta kyallara ido taga Abul.
Daga bayanshi aka yi gyaran murya ya juya da sauri yaga Mas’ud ne tsaye yana ta6e baki alamar dariya yake son yi.
“Tun d’azu kana nan?” Haydar ya tambayeshi cikin mamaki.
“Eh, nazo fad’a maka wani abu ne sai naga ka fara waya, so sai na jiraka.”
“Kaji duk abunda na fad’a kenan?” Ya sake tambayarshi.
“Well... wasu maganganun har bana son in tuna. But keep it up.” Ya buga kafad’ar Haydar sau biyu kamar wanda yak’e encouraging d’insa kana ya juya ya tafi yana washe baki.
Girgiza kai kawai Haydar yayi yana murmusawa kana yabi bayan Mas’ud yana mamakin shine ya ta6a naushinsa akan Laila, amma gashi yanzu har tsokanarshi yake a kanta.
Bayan ya shiga d’akin ya samu Abul na sallah amma k’afarsa da yake d’ingisawa bata barinshi yayi zaman sallah da kyau sai a karkace ko kuma ya mik’ata gaba.
“Ko a ina aka karya masa k’afar sai Allah.” Fad’in Mas’ud yana kallon Abul cike da tausayi kamar bashi bane yanzun ya yiwa Haydar tsiya ba.
Haydar bai ce komai ba domin shima tausayin yaron ne a zuciyarsa ganin irin wahalar da yake sha. Sai da Abul ya idar kana ya dubesu yace,
“Don girman Allah ku barni in tafi, Uncle Mas’ud ku taimakeni kar ku kaini Maiduguri.”
Haydar na jin hakan ya juya ya fice daga d’akin yana cewa,
“Bari in sayo mishi abinci.”
Kafin ya fita yaji Mas’ud na mayar masa da martani,
“Can d’in ya fi maka nan kenan?”
Yana fita ya samu restaurant mafi kusa ya sayawa Abul breakfast sannan yayi hanyar gida domin d’auko Laila. Kafin ma ya isa ta kirashi ta fad’a masa ta shirya, yace ta fito waje gashi nan zuwa.
A bakin gate ya sameta sanye da hijabi mai hannu, tana d’auke da jakanta da wayarta a hannu tana dannawa.
Yana parking ta isa gaban motar ta shiga gaba tana aika mishi da murmushi ganin yanda ya shagala da kallonta.
“Baki san yanda hijabi yake miki kyau ba ko?” Ya tambayeta yana rankwafowa kusa da ita.
“Laffaya fa?” Ta tambayeshi tana kallon kwayar idanunshi cikin son kasancewa dashi.
“Shima yana miki kyau but ni kad’ai ya kamata in ganki a cikinsa saboda nan...” Ya ta6a cinyarta.
“A mota muke fa.” Ta fad’i hakan tana d’age hannunsa tana mishi harara.
“Damuwar mai gulma.” Ya fad’i hakan yana yiwa motar giya suka fara tafiya.
“Baka fad’a mini ina zamu je ba.”
“Surprise ne.”
“Shikenan mu je.”
Suna shiga cikin asibitin Laila ta kalli Haydar fuskarta babu wasa tace,
“Waye ba lafiya? Me yake faruwa Haydar? Idan wani ne bashi da lafiya ka fad’a mini I’m not some fragile Baby doll da zan fashe don naji wani nawa bashi da lafiya.”
“Kowa lafiyarsa kalau, da kuma wani bashi da lafiya da an kiraki a waya. Zaku gaisa da wani ne.” Ya fad’i hakan yana parking tare da kashe motar.
“Shine surprise d’in?” Ta tambayeshi tana fitowa daga motar.
“Not yet.” Ya d’auki abincin daya saya ya kamo hannunta suka shiga asibitin.
A bakin d’akin Abul suka tsaya ya kwankwasa tare da murd’a k’ofar ya shiga Laila ma tabi bayansa da sallama d’auke a bakinta. Sai dai mutumin data hango zaune a kan gado shiyasa ta tsaya cakk tare da rufe bakinta dalilin kukan daya so kwace mata.
A hankali ta taka ta isa bakin gadon bayan Mas’ud ya bata guri ta tsaya kan Abul tana tsiyayar hawaye. Shima ita d’in ya zubawa ido idanunsa cike da hawaye amma ya k’i bari su zubo sai cije le6ensa da yake yi yana d’aga idanunsa sama.
“Abul ne fa!” Shine abunda ta fara furtawa tana ta6a fuskarshi wacce wasu gurare suke manne da bandaids.
Kawar da hannunta yayi daga fuskarshi yana hangen bayanta inda Haydar ya jinginu da bango yana kallon reunion d’in uwa da d’anta.
“This is all because of you, kai ka fad’a musu inda nake and I hate you for that akan wanda nake maka.” Abul yayi maganar cikin k’araji tamkar ya tashi ya shak’e Haydar.
Juyawa Laila tayi bayanta ta dubi Haydar tace,
“A ina kuka sameshi kuma yaushe?”
“A Abuja, jiya muka d’aukoshi.”
Gyad’a kanta tayi tana share hawayen fuskarta ta mayar da dubanta ga Abul tana kallonshi.
“Ka rame, kayi bak’i, ka kod’e sannan ga ciwoka duk a jikinka Abul. Wannan shine rayuwar daka za6arwa kanka? Me ribar wannan rayuwa in ba asara da kaico ba?”
“Ribar shine bana kusa dake da Toy Boy d’inki.”
Haydar dake baya yayi murmushi yana tunanin waye toy tsakaninshi da Laila bayan abunda ya faru jiya da dare.
“Har yanzu bakinka bai mutu ba. Ina rok’ar maka shiriyar Allah.” Ta fad’i hakan tana murmusawa kamar ba magana mai zafi ya fad’a mata ba tana goge hawayen fuskarta cikin dakewa.
“Zan wuce aiki Laila, sai na dawo.”
Kafin ta bada amsa Abul yayi caraf yace,
“Kiji yanda yake kiran sunanki kamar bashi yake sunkuyawa yana kiranki Hajiya idan zai gaisheki ba. Wannan kuma shine abun kaico.” Ya dallawa Haydar harara wanda sai yanzu ya lura ya k’ara haske yayi k’iba.
“A dawo lafiya and thank you.” Ta gyad’a kanta alamar she mean it.
“Take care.” Da murmushin da bai bar bakinsa ba Haydar ya fita tare da Mas’ud aka bar Laila ita da Abul.
Abincin da Haydar ya shigo dashi ta tashi ta d’auko kana ta bud’e take away mai d’auke da Chips da kwai sai hot chocolate a cikin disposable cup, da kuma Apple guda hud’u da ruwan gora. A gefenshi ta ajiye mishi kana tace,
“Bismillah.”
“Bazan ci ba.” Ya bata amsa.
“Okay.” Da haka ta rufe abincin ta koma ta zauna tana kallonshi tana murmushi, can k’asan zuciyarta kuma farinciki take ji kamar zata zauce. Daa ba don Abul na d’akin ba daa ta nunawa Haydar farincikinta tare da godiya thou Mas’ud ma ya cancanci godiya amma ba irin na Haydar ba.
Abul da kallon ya isheshi ya kwanta ya juya mata baya yana mamakin yanda bata takura mishi yaci abincin ba, hasalima ya lura duk abunda ya fad’a bata mishi fad’a balle ta nuna ranta ya 6aci. Wani ciwo yaji nan take a k’irjinshi yayi saurin mik’ewa ya fara kakarin amai.
Da sauri Laila ta jawo k’afarshi k’asan gadon tana tambayarshi me yake damunshi.
Ganin amai yake son yi yasa ta taimaka mishi ya tashi yana digar da wani abu mai yauk’i a bakinsa ta kaishi band’aki ya tsugunna gaban toilet yana cigaba da zubar da abun.
“Sannu Abul. Sannu kaji?” Shine abunda take ta nanatawa tana tsaye a kanshi hankalinta a tashe. Ya kai minti biyu yana zubar da yauk’in sannan ya daina a galabaice. Laila da kanta ta wanke mishi bakinshi kana ta taimaka mishi ya dawo kan gado ya kwanta lokacin da Mas’ud ya shigo tare da Doctor.
“Ya gama aman? D’azu na shigo na jiku a band’aki yana yi.”
Laila da tarin damuwa a fuskarta ta amsa masa da cewa,
“Ehh ya gama. Doctor me yake damunshi? Amai yayi kamar majina babu alamar abinci a ciki.”
“Hakan zai iya yiwuwa saboda effect na drugs da yake sha ko wani ciwon. But ga result d’insa ya fito...”