RUWAN ZUMA Book Complete Hausa Novels by Suwaiba Muhammad.docx

Author :  Suwaiba Muhammad Category :  Bookz

Chapter   38 / 44

111K to 114K   out of 132K words

sanye cikin hijabi tana aiko musu da murmushi tana cewa,

"Marhaba, sannun ku da zuwa." Kana ta fara k'ok'arin zama a k'asa Ammi tayi saurin dakatar da ita ta ce,

"Kul, zauna a sama. Kina jego ai zaman k'asa ba naki bane Laila."

  Laila da dama tunanin yanda zata zauna a k'asan take yi ta mik'e ta zauna a kujera a hankali don har lokacin tana jin ciwon d'inkin da aka mata.

  Ammi ta mik'awa Baba jaririn wanda da kyar ya iya rik'ewa sai da ta gyara mishi kan yaron don tangal-tangal yake yi.

"Rabon dana rik'e jariri har na manta, ina ga tun haihuwar Abdul." Maganar Baba kenan da yasa kowa a mamaki.

"Lallai abun ya jima." Fad'in Ammi cikin tausayawa mijin nata, saboda tana tuna irin kwallafa rai da yayi a cikin Haydar amma Allah bai bashi ikon rik'e d'an nashi ba sai da ya girma har yayi aure.

  Gaisawa suka yi cikin marmarin ganin juna, sannan Baba ya rik'e kan yaron ya fara mishi addu'a yana tofa mishi har na wasu mintuna sannan ya gama ya mayar wa Ammi yaron ta k'ar6a. Baba ya tashi tsaye yana cewa,

"Mun ga jariri Allah ya raya mana shi. Lu’a idan kin gama ki kira Abdul ya dawo da ke gida.”

“Zan mayar da ita Baba.” Haydar yayi saurin fad’a yana tashi tsaye zai raka Baba.

Ammi ce ta mishi wani mugun kallo sannan tace,

“Maganarka za’a bi ko ta Babanka?”

Sai a lokacin Haydar ya gane yayi laifi yayi saurin gyara zancen sa da cewa,

“Ina nufin kar ya wahala ne wajen zuwa d’aukoki, tun da ni ina nan sai kawai in mayar da ke. Amma ku yi hak’uri in hakan bai muku dad’i ba.”

Baba murmushi yayi yace,

“Duk yanda kayi ya yi daidai Aliyu Haydar. Sai anjima.” Da haka ya fita daga falon Haydar ya mara mishi baya har zuwa gurin motar ya bud’e mishi suka tafi.

Yana dawowa cikin falon ya samu Laila na bawa jariri nono yayin da Ammi tayi shiru fuskarta babu fara’a ko kad’an.

“Ammi lafiya na ganki haka? Baki da lafiya ne?” Shine Abun da ya fara fad’a yana neman zama a kusa da ita.

“Koma can Ali.” Tace dashi tana nuna mishi gurin da ya zauna tun d’azu.

Babu musu ya koma ya zauna amma hankalinshi ya tashi da yanayinta yana ta kallonta.

Ammi ce ta fara magana bayan ta mayar da hankalinta kanshi ta ce,

“Yanzu kai abun da kake yi ya dace? Haihuwa aka maka amma ka kasa sanar da d’an uwanka jininka sai dai ya ji a gari? Yaushe ka zama mai rik’o haka? So kake yi ka zama mara godiya ga Allah ga duk abun da yayi maka?”

Laila ce ta d’ago kanta ta dubi Haydar wanda ke mata ido alamar ta tafi, ba shiri ta d’auki d’anta ta mik’e Ammi ta dubeta tace,

“Ina zaki je? Ai laifin bashi kad’ai bane har da naki, zauna.”

Laila komawa ta yi ta zauna tana cewa,

“Wallahi Ammi ina fad’a mishi hakan da yake yi bai dace ba, k’arshe kafa mini doka yayi ya ce kar in sake d’auko mishi maganar baya so. Na yi iya bakin k’ok’arina domin in nuna mishi fushin da yake yi da d’an uwansa yayi yawa har ina bashi misalin tsakanina da Yaya Madu yanzu babu gaba sai zumunci mun ajiye komai a gefe tamkar ba’a yi ba. Ki yi hak’uri Ammi amma abun ya fi k’arfina ne shiyasa na yi shiru.” Ta k’arisa maganan tana kallon Haydar wanda ya had’a girar sama da k’asa kansa a k’asa yana murza yatsun hannunsa.

“Ali kaine mai taurin kan kenan?” Ammi ta watso masa tambaya wacce tasa ya d’ago kanshi yana rage tsumewan ya ce,

“Ammi don Allah idan zaki mini fad’a ki daina yi a gabanta bana jin dad’in hakan. Yanzun ma ban ga amfanin zamanta a nan d’in ba tun da ni zaki yiwa fad’an ba ita ba.”

“Zaka nuna mini abun da ya fi dacewa kenan kamar yanda ka so nunawa Babanka d’azu ko? Yaushe ka zama haka ne Ali? Wallahi wannan ba tarbiyyar dana baka ba kenan.”

Shiru yayi ya sadda kanshi k’asa bai ce komai ba, Laila kuma na ganin haka ta dubi Ammi tace,

“Na yi bak’i wanda suka zo ganin jariri na taho nan bamu gaisa ba Ammi.”

“Tsoron Alin kike ji shine kike neman guduwa daga nan ko?”

Ta wutsiyar ido Laila ta kalli Haydar ta ga da gaske baya son kasancewarta a gurin kana ta mayar da dubanta ga Ammi ta girgiza kanta ta ce,

“Ba haka bane Ammi.”

“Tashi ki tafi.” Fad’in Ammi tana jin sanyi a ranta ganin Laila na bawa d’anta girma a matsayinshi na mijinta.

Tana fita Ammi ta dawo da dubanta ga Haydar wanda shima tafiyar Laila yasa ya sassauto kad’an ta ce,

“Meyasa kake mu’amala da Abdul kamar ba jininka ba? Ina son sanin laifin me yayi maka da har ka kasa koyan hak’urin zama dashi.”

Shiru Haydar ya sake yi a karo na biyu wanda hakan ya fara bawa Ammi haushi ta ce,

“Baka ji ina maka magana bane kana shiru Aliyu Haydar?”

Yanda ta kira dukkan sunanshi yasa ya gane ranta ya 6aci bana wasa ba. Tashi yayi daga in da yake ya zo ya zauna a k’asa kusa da k’afafunta ya dubeta fuskarsa gwanin ban tausayi ya ce,

“Ammi ba wai zan yi musu da ke ko kuma in nuna miki abun da kike fad’a ba gaskiya bane, sai dai ina buk’atar lokaci ne kafin in fara sake jikina dashi. Abubuwan da yayi sun yi yawan da ban hak’uri ko yafiya ba zai sa a yi saurin mancewa da su ba.”

“Idan ban manta ba kace Laila da Abul ya cutar ba kai ba, kai kuma idan za’a duba gata yayi maka ba kad’an ba duk da cewa yayi niyyar cutar da kai a k’arshe amma Allah bai bashi sa’a ba. To ita Lailan ma da ya cutar da d’anta ta yafe mishi sannan har take nuna maka rashin amfanin abun da kake yi. Abdul yayanka ne wanda jinin da ke gudana a jikinshi shi yake gudu a naka, shi kuma uban naku ko bai nuna maka a fuska ba wallahi a zuciyarsa ba zai ji dad’in yanda kake yiwa d’ansa ba duk girman laifinsa. Wani irin rahama ce Allah bai maka ba fiye dashi? Wani irin fifiko ne Allah bai maka ba? Allah ya baka Matar da Abdul yake so shi kuma ya hanashi. Allah ya bayyana maka danginka kamar yanda kaci buri ba tare da iyawarka ba. Allah ya wadataka da arziki da nitsuwa, ya kare ka daga sharrin duk wanda ya nufeka da sharri, ya kuma wadata ka da samun mace tagari sannan ya k’ara maka da albarka d’a alhali shi wanda kake fushin dashi bashi da wad’annan abubuwan, Ali wannan bai isa ya nuna maka cewa Allah yana sonka ba? Idan kuma kana maganar girman laifi ne sai ka tuna ni da mahaifinka kuma wace irin rayuwa muka yi kafin mu sameka, idan zaka cigaba da fushi da Abdul akan abun da yayi a baya ya kuma rok’i gafararka to muma zaka iya cigaba da fushi damu akan halinmu na baya wanda baka son a furta.”

“Ammi don girman Allah na rok’eki ki daina tuna mini wannan abun.” Ya yi maganar hawaye na taruwa a idanunsa yana kallonta.

“Sai ka mini alk’awarin gyara tsakaninka da Abdul don laifinshi k’arami ne a kan namu amma ka iya cigaba da zumunci da mu bayan ka samu labarin komai.”

Sadda kanshi yayi a k’asa wannan karon hawaye na zuba a fuskarsa ba tare da ya ce komai ba. Ganin hakan yasa Ammi taci gaba da magana cikin rarrashi tana cewa,

“Wata biyar kenan har da d’ori da faruwar wannan abun Haydar, Abdul ya canja ya daina munanan d’abi’unsa hatta neman mata da yake yi ya daina. Wallahi kullum idan ya zo Abuja a gidanmu yake sauk’a baya zuwa gidansa ya kwana. Yana girmamani sannan yana bani kulawa tamkar dama duk tsawon lokacin nan ya sanni kuma muna tare. Idan ya zo gida har abinci yake dafa mana duk da girmansa, kuma idan ina buk’atar wani abu kafin in sanar da Babanku shi nake fara kira ya mini ba wani ba. Ya zama tamkar d’ana dana haifa da cikina Ali. Kullum kuma maganarshi in yafewa mahaifiyar shi abun da ta mini ni kuma ban fasa jaddada mishi cewa na yafe mata ba saboda na lura hakan yana sanyaya mishi rai yana jin dad’i. Ali rashin kula d’an uwanka da kake yi yana yiwa mahaifinku zafi sai dai bai ta6a furtawa ba, akwai ranar dana d’auko mishi zancen amma cewa yayi duk laifin Abdul ne ba naka ba, amma nasan ba zai k’i ya ga kayi hak’uri kun kulla zumunci tsakaninku ba. Ita Lailan da abun ya faru a kanta ma ta hak’ura sannan taci gaba da zumunci da yayanta duk da irin muguntar da ya yi mata a rayuwarta. Shin wannan ba zai zama ishara a gareka ba cewa komai na duniyan nan d’an hak’uri ne? Tun da yayi nadama na gaskiya sai ka bashi damar da zai gyara laifukanshi ta hanyar sauk’e fushinka a gareshi. Ka kuma k’ara duba ga Rahamar da Allah Ya yi maka sai kai kuma ka gode mishi ta hanyar yafewa bayinsa abun da suka maka. Ka yi alk’awarin kulla zumunci da Abdul ko kuka in cigaba da maka fad’a ina baka misalai da rayuwata ta baya?”

“Are you trying to blackmail me Ammi?” Haydar ya fad’a yana goge fuskarsa yana murmushi kad’an.

“Na san kafin ka saurari gurin blackmailing d’in ka saurari sauran bayanai na wanda su nake so ka d’auka ba wannan ba.”

Gyad’a kai Haydar yayi kana ya ce,

“Zan gyara Insha Allah. Nagode da rashin nuna gajiyawarki wajen d’aurani a kan gaskiya Ammi. Allah ya bar mini ke ya k’ara miki lafiya da nisan kwana.”

“Amin Amin Ali. Allah ya baka ikon gyarawa kaima.”

“Amin Ammina.”

Da haka Ammi ta tashi tsaye tana cewa,

“Bari in shiga can don ban gaji da kallon mayunwacin maigidan nawa ba.”

Haydar murmusawa yayi kana ya tashi ya shige d’akinsa don shirin zuwa office wanda a yanzu shine ya zama mai mallakin Lu’a Ventures.

Ammi kuma har d’akin Laila ta shiga ta samu su Ajidde da Sabrin da wasu daga cikin ‘yan uwa a d’akin ana hira. Ganinta yasa suka fad’ada fara’arsu wanda Sabrin har tashi ta yi taje ta rungumeta tana cewa,

“Oyoyo Ammi.”

Sai da suka gaggaisa sannan Ammi ta nuna ledojin da aka shigo dasu ta ce,

“Wannan daga Baban Ali ne da ni. Wannan kuma kayan Ali ne da muka saya tun ina d’auke da cikinsa sai kuma Allah yasa bai sakasu ba, shine muka kawo d’ansa ya saka.”

Cikin al’ajabi ‘yan d’akin suka kalli akwatin wanda daga ganinta dama suke mamakin yanda aka samu akwatin daa amma kuma mai kyau da sabuntaka.

Sabrin ce ta bud’e akwatin tana ciro kayan wanda sai k’amshin Comfort detergent suke yi alamar an wankewa tana mik’awa sauran ‘yan d’akin suna dubawa.

“Ammi kun iya ajiya, wallahi kamar basu shekara talatin ba. Mun gode Allah Ya saka da alkhairi ya kuma k’ara bud’i.” Fad’in Laila tana k’arban wani daga hannun sabrin wanda ya burgeta ainun.

Wani kayan idan aka ciro sai su yi dariya ana tuna wa aka taba sakawa irinshi da yake su abun nasu ma na yayi ne. Sai da suka gama ganin sauran kayan sannan Laila ta d’auki wanda yafi burgeta ta sakawa jaririn ta kaishi gurin Babansa wanda ya fito zai tafi aiki.

“Dama yanzu nake da niyyar shiga in miki sallama. My bundle of joy, ko in tafi da kai ne?” Ya fad’a yana ajiye jakar hannuna ya kar6i yaron daga hannunta.

“Baka da abu da zaka bashi ya sha da kun tafi tare.”

“Wa yace bani dashi? Na k’irjin nawa fa?” Ya k’arisa maganan yana mata signa.

“Sarkin magana, ai babu ruwan nono.”

“Baki matsa yanda ya kamata bane.”

Dariya Laila ta yi tana kad’a kai tace,

“Baka ga kayan jikinshi ba?”

Zama Haydar yayi kana ya kwaye abun da aka lullu6e jaririn dashi yana kallon kayan yace,

“Ban sayi wannan ba. Waye ya kawo? Kuma kamar irin wanda yaran daa suke sakawa ne.”

“Naka ne wanda su Ammi suka saya maka baka saka ba shine ta kawo.”

Haydar shiru yayi ya k’urawa kayan ido sannan ya ce,

“Yayi mishi kyau sosai. Bari in tafi.” Ya mik’a mata yaron sannan ya mata sallama ya tafi.

Da rana bayan azahar Meenat ‘yar d’akin Ammi ta iso gidan mai jego, da saurinta ta rungume Ammi tana cewa,

“Nayi kewarki Ammi.”

Itama Ammi murna ne fal a fuskarta tana tambayar lafiyanta da kuma bayan rabuwa duk da cewa suna waya tun bayan da Ammi ta bar unguwar ta fara zama a gidan Ummii.

Meenat ta gaishe da sauran ‘yan d’akin sannan aka mik’o mata jaririn tana kallonshi, a ranta kuma cewa take yi da itace mahaifiyarsa amma Babanshi ya k’i aurenta.

“Baffa da kyar ya barni na taho wallahi, sai dana fad’a mishi cewa kece kika ce in zo kuma kina zuwa gaishesu sannan ya barni.” Fad’in Meenat ga Ammi.

“Ai ban yi tsammanin zaki zo ba, na fad’a miki zuwan nawa ne kawai amma akan cewa gobe zan je na dubaku da duk ‘yan unguwa. Ina su Zaliha (Matar da Ammi ta ta6a taimako har Haydar ya nema mata gidan haya bayan mijinta ya gudu ya barta da ‘yaya. Bayan Ammi ta bar gidan tasa Haydar ya d’aukota ta dawo gidan da zama.)”

“Suna can lafiyansu kalau. Ai ban fad’a mata kin zo ba.”

Ana la’asar Ammi ta musu sallama a kan sai washegari zata dawo, Haydar da dama ya dawo gida ya fita zuwa waje in da Alhaji Abdul ke jiran Ammi ya kwankwasa mishi glass d’in window ya bud’e yana mamakin ganinshi.

“Ka zo dauk’an Ammi kenan?” Haydar yayi maganar nevously yana kallon yayan nashi wanda yake cikin mamaki.

“Eh, tace mini tana fitowa.”

“Ka shigo ka ga Baby.” Haydar ya fad’a yana jin kamar zai shak’e da yawun bakinsa. Domin zai iya cewa wannan ne karo na farko da suke magana wacce bata shafi kasuwancinsu ba.

“Kar ka damu ba sai na shiga ba, saboda na san Ammi ce ta matsa maka. Bana son a yi maka dole a kan abun da baka so.”

“Ammi bata san da cewa zan maka magana ba.” Ya fad’i hakan yana kallon bakin gate in da Ammi ta fito tare da Meenat suna hira gwanin ban sha’awa.

Alhaji Abdul ma bin su yayi da kallo amma hankalinshi yafi karkatuwa ga yarinyar da ke manne da Ammi tana mata magana kamar ta dad’e da saninta har tana d’aura kanta a kan kafadarta tana dariya. ‘She’s so young and innocent’. Ya fad’a a ranshi.

Kafin su Ammi su iso gurinsu ya bud’e marfin motar ya fita yana cewa,

“Ok to. Mu je.” Fuskarsa d’auke da murmushi domin ya gane cewa hakan yin kan Haydar ne ba wai tilasta mishi aka yi ba.

Ammi da ta gansu tare sai da zuciyarta ta buga tana fatan Allah yasa Haydar ba maganar banza ya mishi ba akan fad’an da ta mishi d’azu.

“Ammi ku shiga motar, bari ya ga Baby sai ya zo ku tafi.”

Gyad’a kai kawai Ammi ta yi don ta kasa magana suka wuce gurin mota, Meenat kuma mamaki take yi dalilin da yasa wannan mutumin da zai mayar da su gida yake kallonta don dai tasan yayi sa’an babanta babu k’arya.

Haydar a falonshi ya sauk’ar da Alhaji Abdul sannan ya d’auko mishi ruwa a cikin fridge d’in da ke falon ya ajiye mishi a gabanshi yana cewa,

“Bari a kawoshi.”

Alhaji Abdul tsabar murnar wannan karramawar da Haydar ya yi mishi kasa cewa komai yayi illa gyad’a kai da yayi yana murmushi tamkar zai tsaga fuskarsa gida biyu. Wai yau shine a gidan Haydar har yana kawo mishi ruwa? D’aukan goran ruwan yayi ya bud’e duk da cewa baya jin k’ishi ya bud’e ya fara sha yana jin kamar RUWAN ZUMA yake sha don bai yi tsammanin akwai ranar da Haydar zai bashi ruwa ba.

Yana ajiye goran Haydar ya shigo hannunsa d’auke da Baby yayin da Laila ke bayanshi itama tana tahowa.

Alhaji Abdul shima bai iya rik’e jariran ba sai da Haydar ya gyara mishi. Murmushin da yake yi kuwa k’aruwa ta yi yana kallon fuskan Baby yana jin kamar a bashi kyautarsa.

“Da gaske yana kama da kai. D’azu da Baba ya fito yake fad’a mini har ya tura mini hotonsa. Allah ya rayashi a kan addinin musulunci yasa addini yayi alfahari dashi.”

“Amin Amin.” Su Laila suka amsa.

Kallo d’aya da Alhaji Abdul ya yiwa Laila bai sake d’ago kanshi ba har suka gaisa ta fita. Haydar na lura da hakan sai yaji sanyi a ranshi don ya lura da gaske yayan nashi ya canja.

Wayarsa ya d’auka ya yiwa Babyn hoto yana cewa,

“Wanda Baba ya d’auka bai fito sosai ba hannunsa na karkarwa kuma camerarsa bata da kyau.”

Dariya ce ta su6ucewa Haydar ba tare da ya sani ba kana ya girgiza kai yace,

“Zan fad’a mishi.”

Alhaji Abdul dad’i ne ya k’ara lullu6eshi ya ce,

38 / 44