RUWAN ZUMA Book Complete Hausa Novels by Suwaiba Muhammad.docx

Author :  Suwaiba Muhammad Category :  Bookz

Chapter   3 / 44

6K to 9K   out of 132K words

aka mana ba suka fad’i gaskiya ba, kamar yanda na wancan mutanen ya wuce har aka daina maganarsu muma watarana haka za’a daina yayin maganarmu kuma zai zama tamkar ba’a yi ba. Mutanen social media haka suka zama, kowa ya 6uya a bayan keyboard ne yana fad’in k’arya da gaskiya don kawai ya jawo hankalin mutane kanshi, ko kuma don wata manufa tashi ta daban. Abunda zakiyi ki karya guiwar masu yin hakan shine ki nuna hakan bai dameki ba, ki nuna musu kin fi k’arfin su fad’i k’arya a kanki har yayi affecting rayuwarki. Ke ba yarinya bace Laila, kina da experience na rayuwa sosai, kiyi amfani da hakan sannan ki barwa Allah komai, shi zai tona asirin duk mai yin hakan. Kina jina?”

Gyad’a mishi kai tayi tana zare hannunta daga nashi kana ta share sauran hawayen dake fuskarta tana jin k’arfi a jikinta da kuma cikin zuciyarta gabad’aya.

“Nagode.” Kawai ta iya furtawa tana matsawa kad’an daga gurinshi.

Hakan da tayi bai mishi dad’i ba domin ya lura kamar bata son ya ta6ata ne. Ko dai ta manta shi mijinta ne a yanzu?

“Waya turo miki links d’in?” Ya tambayeta yana maida kanshi jikin kujeran domin yaji alamar maganin da yasha ya fara aiki.

“Ban san waye bane kuma bani da numbern. Ina gwada kiran layin Abul naga an turo mini message d’in, ni bana ma Twitter amma nabi ta link d’in nayi downloading.”

Haydar gyara zamanshi yayi ya k’ara d’aukan wayar ya shiga True caller ya duba sunan mai numbern yaga suna ne wanda bai gane ba, koda ya nuna mata itama cewa tayi bata san me sunan ba.

“Ki basu kwana biyu zasu yi su gaji su daina. Zan bincika duk wanda yayi hakan domin d’aukan pictures d’inmu da ake yi har ana editing bai mini ba.”

“Ka bari kawai ba sai ka bincika ba, koma waye ne ya yiwa kanshi.” Tayi saurin katseshi domin bata son yaje ya bincika ya gane Abul ne yake mata haka ko kuma Madu.

Ina zata kai wannan kayan kunyan ace duk wannan bak’in cikin na jikinta ne ya aikata musu haka?

Haydar da baya ganewa jikinsa ya tashi tsaye yana bata baya yace,

“Ina band’aki? Zan yi wanka.”

Laila ta mik’e tsaye tana cewa,

“Sorry, muje.” Tayi hanyar side d’in Mas’ud amma tana k’ok’arin bud’ewa taji k’ofar a gark’ame.

Ta k’ara jijjiga k’ofar ta gane key aka saka aka kulle. To waye ya kulle?

Shi kuma Haydar bai zauna ba illa ma kawar da kanshi da yayi ga barin kallonta, saboda kallonta kad’ai na k’ara jawo masa matsala.

D’akin Abul da Sabrin duk ta gwada bud’ewa amma a rufe, a nan ta tabbatar wannan aikin Mas’ud ne. Me yake nufi da hakan? Shin bai san halin da suke ciki bane da zai yi tunanin had’asu a d’aki d’aya?

Wayarta ta d’auko tayi dialing numbernshi amma a kashe. Extra keys d’in d’akunansu kaf a side d’in Mas’ud d’in ake ajiyewa incase wani ya jefar da nashi. Ya zata yi?

Haydar ta har lokacin yana tsaye ya kasa gaba ko baya yace,

“Lafiya?”

“Muje d’akina, sauran d’akunan a kulle suke.” Da haka tayi gaba yabi bayanta da kallo yana jin tamkar ya fasa ihu.

Mas’ud da Hamidu kuma tun d’azu yake tunanin me zai musu ya rama abunda suka mishi idan sun had’u gaba saboda sun cuceshi.

Sai da ya tabbatar ta shiga d’akin sannan ya bi bayanta yana doro tamkar mai ciwon baya. Yana shiga ya samu ta kwaso wasu kayanta a cikin band’akin ta jefasu a ciki wardrobe d’inta da sauri.

Halin da yake ciki yasa bai ma lura da yanayin d’akin nata ba ya tasamma cikin band’akin ba tare da ya bari ta kalleshi da kyau ba.

Yana shiga ya fara kwa6e kayan jikinshi kana ya sakarwa kanshi ruwan sanyi na minti biyu kafin nan yayi wanka. Ya jima tsaye ruwa na dukanshi sannan ya kashe shower ya nemi towel ya d’aura a k’ugunshi kana ya fito.

A cikin d’akin ya samu Laila ta kawo mishi jakarshi har ta shimfid’a k’aton bargo a k’asa ta ajiye pillow a kai. Tashin da zata yi ta hangoshi a bakin band’aki ya hard’e hannayensa a saman k’irjinsa yana mata kallon ‘me kike nufi’?

Zuciyarta ce ta buga da k’arfi ta nemi nitsuwarta ta rasa domin ba k’aramin kyau da kwarjini ya mata.

Da sauri ta fita falo ta bashi guri domin ya kimtsa, a can falon kuma wayarta ta d’auka ta gwada kiran Abul amma bai shiga ba wanda dama hakan ta san zai faru.

Sai da ta tabbatar Haydar ya gama abunda zai yi sannan ta shiga d’akin da sallamarta ya amsa, zaune yake a kan kujeran dressing mirror yana sanye da jallabiya fara sol wacce tayi masa kyau ba kad’an ba a idanunta.

Wai me yake damunta ne? Ta yiwa kanta tambayar tana kawar da kanta gefe ta bud’e wardrobe tana d’auko kayan baccin da zata saka.

“Kinyi regretting aurena?”

A bazata ta jiyo tambayar wanda yasa tayi saurin juyowa tana kallonshi a razane.

Tashi yayi ya tako har gurinta kana ya tsaya a gabanta ya k’ara cewa,

“Kinyi regretting aurena? Zaki iya za6ana a karo na biyu a rayuwarki?”

“Haydar...” Zata fara magana ya katseta.

“Just answer me. Ina son sanin matsayina ne a gurinki domin na lura tamkar ba aure kika d’auki aurenmu ba. Kamar an miki dole ne alhali ke da kanki kika yi choosing d’ina.”

“Bana dana sanin saninka ko aurenka Haydar, but halin da nake ciki a yanzu ina buk’atar space domin abubuwan da suka faru a yau sun yi mini nauyi a zuciyata. Ka daina tunanin hakan a zuciyarka.” Ta k’arishe maganan tana ra6ewa ta gefenshi zata wuce ya kamo hannunta.

“Kenan kina sona?” Yayi mata tambayar yana kallon kwayar idanunta.

“Daa bana sonka da bazan amince in aureka ba.”

“Then say it.” Ya k’ara k’arfin rik’on daya mata.

Laila tabi hannunsu da kallo yanayinta na canjawa, damuwarta na barin zuciyarta ta d’ago ido tace,

“Yes, I’m in love with you. Shikenan?”

Haydar dawo da ita yayi gabansa murmushi na su6ucewa a bakinsa a karon farko tun da ya shigo gidan amaryar tasa.

“I’m in love with you too.” Ya fad’i hakan yana had’e goshinsu guri guda yana lumshe idanunsa tamkar mai jin baccin.

“Haydar.” Ta kira sunanshi cikin kwa6a amma a hankali jin ya sumbaci kunnenta tare da wuyanta.

“Shshh.” Yayi shushing d’inta yana jawota jikinshi yayi hugging d’inta tsamm tamkar za’a kwace mishi ita.

Laila bata kwace jikinta ba domin tasan yana buk’atar ko sau d’aya ne ya gane cewa da gaske ya aureta ba mafarki yake yi ba.

Ganin labarin na neman canja salo yasa tayi saurin barin jikinshi ta shige band’aki jikinta na rawa, duk inda ya kai hannunsa a jikinta sai da tabi ta ta6a tana jin zuciyarta na tsananta bugawa, wai yau ita ce d’aki d’aya da Haydar a matsayin mijinta? Kenan mafarkan da tayi kwanaki zasu iya zama gaskiya?

Ta jima a cikin band’akin sannan tayi wanka ta saka silk nighty d’inta ta fito.

Turaren humra da bata rabo da sawa ta shafawa jikinta sannan ta fita falo zuwa gurin Haydar jin yayi kiranta. Wai da gaske ta zama matar Haydar?

A kan sallaya ta sameshi kamar wanda ya idar da sallah yace,

“Kiyi alwala muyi sallah.”

D’an k’aramin murmushi tayi tana mamakin k’arfin halinshi, haka ta koma d’aki ta d’auko hijabinta tare da sallaya suka yi sallah, a ranta kuma so take ta bashi wannan daman da zai ji ‘eh shima Ango ne ko da kuwa wani abun ba zai shiga tsakaninsu ba.

Bayan sun idar ya juyo ya mata addu’o’i ida dai kanta a k’asa, tama rasa me take feeling a lokacin a cikin kunya ko jindad’in auren wanda take so a karo na biyu.

Bayan ya gama addu’o’in ya jawo ledar daya shigo da ita ya bud’e musu yana cewa,

“Naji ance yau wuni kika yi baki ci abinci ba.”

“Bana jin cin komai ne.” Ta bashi amsa tana yamutsa fuska.

Hakan da tayi kuwa kyau ta masa ba kad’an ba, murmushi yayi mai k’ayatarwa yace,

“So cute.”

Dariya sosai Laila tayi shi kuma ya tallafe ha6arshi yana kallonta tamkar ta zama tv yana jin dad’i a ransa daya iya kore mata damuwarta har gashi tana dariya.

Ganin ya k’ura mata ido ne yasa Laila ta tsagaita dariyar tace,

“Kana da abun dariya.”

“Don nace kinyi kyau?”

“Haydar.” Ta kwa6eshi a karo na ba adadi.

“Naga alama sunan yana miki dad’i.” Ya fad’i hakan cikin zolaya.

Murmushi tayi tana tuno maganganun Ummii wanda su suke k’ara nitsar da ita akan aurenta da Haydar Idan ta tuna.

Minti kad’an da haka suka rufe kazar Laila ta d’auka tayi kitchen da ita shima Haydar yabi bayanta.

A can ya wanke bakinsa tace,

“A nan kayi alwala ko?”

“Yes. Na lek’a d’akin na samu kina ta shafe-shafe sai na fito.” Ya bata amsa yana kashe wutan kitchen d’in suka fito.

Juyowa Laila tayi tana zaro idanunta, shi kuma gaba yayi ya barta a gurin yana murmushin mugunta.

“Kace mini wasa kake yi.”

“Ni da matata. Menene a ciki?” Ya shige d’aki ya barta a gurin baki a bud’e.

Sai data kashe wutan falon sannan ta shiga d’akin ta sameshi a kan shinfid’arsa yana danna wayarsa yana murmushi.

Wani irin kishi ne ya tsaya mata a makwogoro da tayi tunanin ko da wata mace yake chatting.

Rai a 6ace tazo ta wuceshi ta hau kan gadonta tare da kashe wutan d’akin gaba d’aya tana jin d’aci a harshenta.

“Laila.” Ya kira sunanta cikin duhu.

“Na’am.”

“Nifa ban saba kwana a k’asa ba.” Ya fad’i hakan yana tashi tsaye ya hau kan gadon tare da jawota jikinshi.

A tare suka yi ajiyar zuciya kana ta fara k’ok’arin barin jikinshi ya tsayar da ita yace,

“Just in jiki a jikina nake so and nothing more.”

Mum Fateey 👌

RUWAN ZUMA 🍯

Suwaiba Muhammad

(Mum Fateey) 09023713064

(24)

Bayan Haydar ya hau gadon Laila ta lura da halin da yake ciki amma tayi kamar bata gane ba. Lokaci-lokaci yana tura kanshi jikinta numfashinsa na fita cikin sauri-sauri, ta taga abun ya fara canja mata yanayi ta matsa daga jikinshi ta koma can gefe tana cewa,

“Munyi magana akan hakan, I need space.”

“I’m sorry.”

Ya juya mata baya amma minti kad’an da haka taji ya fara juye-juye ya kasa bacci. Ita kanta babu baccin a idanunta amma why not yayi hak’uri har zuwa lokacin da taga hakan ya dace?

Tun k’arfe sha biyu yake juye-juyensa har biyun dare bai daina ba, ita kuma gyangyad’i take yi tana farkawa saboda motsinshi na hanata bacci.

“Laila.” Ya kira sunanta cikin wata murya abun tausayi.

“Umm.” Ta amsa ba tare data juyo ba amma zuciyarta ta tsinke da halin da yake ciki. Ta gane ba haka banza yake wahala ba, me yasha?

“Please ko irin dabarunku na mata ne.” Ya rok’eta yana kai hannunsa jikinta.

“Haydar me ka sha?” Ta tambayeshi tana juyowa.

“I don’t know, Mas’ud ne ya bani.”

Shiru tayi amma a ranta zagin Mas’ud take yi domin kamar da gangan yake mata haka. Don meyasa zai bawa Haydar wani magani?

“Kayi bacci.” Kawai tace dashi kana ta koma kan shimfid’in data masa a k’asa ta kwanta. Bata shirya fara mu’amala dashi ba.

Yana ganin ta koma k’asa idanunsa suka cika da hawaye har suna zuba a gefen fuskarshi. Juyawa yayi ya duk’unk’une a guri d’aya yana rocking jikinsa tamkar mai jin sanyi.

A daren yayi wankan ruwan sanyi sau uku amma babu abunda ya ragu a halin da yake ciki, k’arshe da kyar bacci ya d’aukeshi wajen k’arfe hud’u.

Ana kiran sallah asuba ya farka ya shiga band’aki yayi alwala ya fito ya wuce masallaci bayan ya zurma garen da Mas’ud ya bashi jiya.

Bai dawo ba sai da gari ya fara haske, ya shigo d’akin a daddafe domin baya iya ko minti biyu a tsaye dalilin hajijiya da yake ji tamkar zai fad’i k’asa.

Laila tana lura da hakan amma ta kasa masa magana sai ma ta bar masa d’akin ta koma falo tana tuna abunda ya faru jiya da dare. Shin ta kyauta masa?

Sai da ta tabbatar yayi bacci ta koma d’akin tayi wanka ta shirya cikin atamfa d’inkin bubu, kwalliya tayi mai sauk’i kana tabi jikinta ta turare ta fito falo wajen k’arfe taran safe, tuni masu aikinta sun mata shara sun d’aura mata breakfast.

Kitchen d’in ta shiga ta samesu su biyu suna aiki suka gaisheta ta amsa tana bud’e tukwanen da suka d’aura.

“Hajiya mun gwada bud’e shashen Oga Mas’ud zamu yi shara amma mun samu a rufe yake.” Fad’in Samira cikin girmamawa.

“Key d’inne ya 6ace, amma idan na samu za’a bud’e ku gyara. Idan kun gama aikin ku tafi na sallameku sai kuma gobe. Zan dinga yin girkin.”

“To Hajiya.” Suka fad’a a tare.

Bayan sun gama sun tafi Laila ta shirya komai a dinning table amma zuciyarta na ga tunanin Abul, ko ina ya shiga? A wani hali yake shine bata sani ba.

Tana zaune a falo k’arfe goma taji ana kwankwasa k’ofar falon tace a shigo,

“Zan iya shigowa babu komai?” Ta jiyo muryar Mas’ud cike da gatse yana dariya.

Ko meya fito dashi da sassafen nan sai Allah, bata kulashi ba ta cigaba da danne-danne a wayarta domin haushinsa take ji ba kad’an ba.

Sai da ya gaji don kansa ya shigo falon yana rufe idanunsa ta tafukan hannayensa amma yana gani ta 6ulin yatsunsa. A hakan ya k’arewa falon kallo sannan ya mayar da dubansa kan Laila wacce ta had’e fuska tamau bata ko kallonshi.

“Amarsu ta Ango mai zakin miya. Kai Ina shigowa gidan nan k’amshi girki da turare yaso ya d’agani ya mayar dani d’akin matata. To ina Angon yake?” Ya fad’i hakan yana zama kusa da ita yana bugan kafad’arta yana mata signa bakinshi a washe.

Juyowa tayi ta dalla masa harara yayi gum da bakinsa yana kawar da kanshi gefe yana kunshe dariyarsa.

“Kalti ina kwana? Kin tashi lafiya?” Yace da ita yana had’a hannayensa guri d’aya alamar ban hak’uri.

“Lafiya, ya Naana?”

“Tana can tana kwance wai baza ta iya tashi ba.”

“Ban tambayeka hakan ba Mas’ud. Wai ni yaushe ka fara rainani ne?” Ta fad’i hakan tana ajiye wayarta a gefe tana aika mishi harara.

“Kinsan komai nawa nake fad’a miki, kece dai kike 6oye mini naki.”

“Bana buk’atar kayi sharing wannan dani.”

“Shikenan, kin yiwa kanki. Amm kunyi karyawa ne? Wallahi yunwa nake ji kuma bazan iya shiga kitchen na dafa mana ba.” Ya fad’i hakan yana zuwa bakin dinning d’in yana bud’e kulolin.

“Munyi amma bamu yi daku ba.” Tabi bayanshi tana buge hannunsa ta rufe kulolinta.

“Kina nufin wannan duk na Haydar ne? Ai ya amsa yawa, ki sam mana kad’an don Allah.”

“A’a.” Tace dashi tana zama a kan kujeran dinning d’in fuskarta a kwaye.

Sai a lokacin Mas’ud ya gane halin da take ciki shima ya zauna fuskarsa na mirrowing nata.

“Abul ko?” Ya tambayeta yana mai jin zuciyarsa na k’una.

“Bana samunshi a waya Mas’ud, ban san a wani hali yake ciki ba. Wallahi ina cikin damuwa, Sabrin ma ta kashe wayarta bana samunta.”

Shiru yayi na sakanni kana ya dubeta da kyau yace,

“Kalti in fad’a miki inda kika yi 6ata a wajen bawa yaran nan tarbiyya, ranki ba zai 6aci ba?”

Gyad’a kai tayi hawaye na taruwa a idanunta.

“Tun farko kinyi sakacin nuna musu cewa zaki iya yin komai don farincikinsu, kin nuna musu sune zasu tankwaraki kiyi abunda suke so ba wai ke ki tankwarasu suyi abunda kike so ba. Kin nuna musu kina tsoron rabuwa dasu shiyasa suke amfani da hakan wajen wahalar dake Kalti, karki manta ke kika haifesu ba su suka haifeki ba. Idan kin kasa basu umurni wa kike tunanin zasu ji maganarsa? Kina d’aurawa kanki nauyin cewa wai ba zaki bari su wahala ko suyi rashin uba ba, ai wani lokacin wahala ke saita mutum ya gane cewa duniya ba gurin aji dad’i a watse bane. Ban ce karki nuna musu so ba, amma karki nunawa yaro zaki iya salwantar da farincikin ki domin shi, ki nuna mishi kema mutum ce yayi respecting d’inki for that. Ki daina damun kanki da batun Abul domin tun jiya na samu labarin halin da ake ciki na kuma baza cigiyarsa. Ita kanta Sabrin Abul ne yake juyata, domin Idan ya shiga damuwa itama sai ta damu kamar ke. I’m sorry to say that amma Abul yana juyaki Kalti.”

Shiru tayi tana tunani mai zurfi domin in wani ne ya fad’a mata hakan kai tsaye zata ce baya son ‘yayanta ne, amma tunda Mas’ud ya iya furta mata tasan gaskiya ya fad’a ba don baya sonsu ba. Saboda bata manta raino da son da yayiwa yaranta ba tun kafin su san kansu.

“Ya zanyi to? Ba’a san inda yake ba fa.”

“Na sha fad’a

3 / 44