Author : Suwaiba Muhammad Category : Bookz
da nake ciki yasa na sake hannunta nabi class by class ina duban yaran da ake koyawa karatu. Office d’in headmaster Ammi ta shiga dani bayan ta kamo hannuna muka samu guri muka zauna. Namiji ne wanda har in mutu bazan ta6a mantawa da fuskarsa ba mai suna Mr Eze. Bayan sun gama magana da Ammi ya fad’a mata kud’in makarantar ta ciro a jikin zaninta ta bashi muka tafi a kan cewa bayan kwana uku in an d’inka mini uniform zan fara zuwa makaranta. A ranar murnar da nayi ba’a cewa komai, itama Ammi tayani farin ciki take yi har ta saya mini biscuits da sweets. Kwana biyu da haka na fara zuwa makaranta Nursery one, na saka kayan da nake buri har da socks da sandal, sai dai duk abunda ake koya mana bana ji bana rik’ewa domin hankalina na ga window ina ganin yanda mutane ke wucewa zuwa wajen sana’arsu ina tunanin ko ina Ammina take a yanzu.”
“Har aka tashi ban san me ka koyar ba, sannan duk yaron da yaso ya mini magana bana kulashi saboda Ammi ta hanani yiwa kowanne yaro magana balle har mu saba. Kin san menene abunda take tsoro? Kar in saba da kowa har in fad’a mishi wani abu daga cikin rayuwarmu mak’iyanmu su ganmu. Ana tashi na samu Ammi a bakin makarantar tana jirana da kayan sana’arta a kanta, a gefe ta saka na cire kayana na mayar dana gida muka kama hanya zuwa gurin sana’armu. Bayan mun dawo ne take tambayata me aka koya mana nace mata babu komai. Fad’a ta mini tace idan bana maida hankalina a kan karatu zata cireni inyi ta zama haka. Jin hakan yasa na tsorita washe gari duk abunda aka koya mana nazo na fad’a mata ta saka mini albarka tana jin dad’i.”
“Ban dad’e ina zuwa makarantar ba, wata rana bayan mun dawo nake wak’an da ake koya mana na Father Mother and children, can na dubi Ammi na tambayeta waye Father? Tace mini namiji ne Baba. Na k’ara tambayarta cewa ni ina Father na? A nan ne na fara ganin tashin hankali domin rud’ewa Ammi tayi ta fara suratai tana rik’e jikinta guri d’aya tana jijjiga. Hakan da take yi ba k’aramin tayar mini da hankali yayi ba, na isa gurinta zan rik’eta ta tureni gefe na bugu da langa-langan d’akinmu, ashe buguwan da nayi na caki wani guri sai jini ya fara zuba a goshina. Kukan da nake yi yasa Ammi ta dawo cikin hayyacinta ta d’aukeni tana kuka itama ta fita dani zuwa wani chemist a can nesa damu. A nan aka wanke mini ciwon k’arshenta har da d’inki aka mini guda uku wanda har yau ina da ta6onshi.”
Laila ta mik’e zaune tana duban fuskarshi ya nuna mata gurin tasa hannunta tana shafawa a hankali idanunta na ciko da kwalla.
“Haka kayi rayuwarka?”
Kad’a kai yayi cikin takaici yana cije le6e yace,
“Wannan mai sauk’i ne Laila, baki ji komai ba.”
“Haydar idan hakan zai sa ka tuno wani abu da bakya son tunawa ka bar labarin haka don Allah.”
Girgiza kai yayi yace,
“Tunda na fara ki barni in k’arasa Laila.”
Kad’a kai kawai tayi kana ta gyara zamanta tana fuskantarshi yaci gaba da bata labarinshi tana saurara.
“A kan hanyar mu ta dawowa wasu mutane suka tare Ammi ta rik’o hannuna gam taci gaba da tafiya cikin sauri sauri, binmu suka yi Ammi ta sa6ani a baya tana gudu, k’arshenta a haka suka cim mana suka fara kwatoni daga bayanta wanda hakan yasa ta daina gudu ta juyo tana rok’ansu su bata ni. Tsakaninsu suka dinga cillani suna ca6ewa, wani daga cikinsu ne yayi bayan d’akunanmu dani Ammi tabi bayanshi tana ihu tana neman taimako amma babu wanda ya iya fitowa a cikin unguwarmu ya zo ya taimakemu.
Sai da suka yi nisa suka bar cikin mutane sannan biyu daga cikinsu suka kama Ammi d’aya kuma ya rik’eni suka fara farka mata kayan jikinta. A gaban idanuna Laila maza uku suka yiwa mahaifiyata fyad’e ba tare da nasan menene abunda suka mata ba sai daga baya da nayi hankali, but all i know is Ammi bata son abunda suke mata and that they should stop doing it.” Hawaye ne ya gangaro kan fuskarshi yayi saurin sharewa ita kuma Laila hani’an take kuka ta rufe bakinta.
“A gurin na kwana kusa da Ammi bayan sun gudu sun barmu, duk tashinta da zan yi tak’i tashi k’arshenta ni na gyara mata kayan jikinta na kwanta a kan hannunta ina kuka ga zafin rad’ad’in da ciwona yake mini.”
“Haydar.” Laila ta kirashi tana kamo hannayensa. Girgiza mata kai yayi yaci gaba.
“Ina ga sanyin asuba ne ya farkar da ita ta tashi tana kuka ta jawoni jikinta, jawoni da tayi yasa nima na tashi daga baccin da nake yi ina tambayarta meya sameta tace mini babu, da haka ta tashi muka koma gida, a d’akin namu muke wanka sai dai kuma in zamu yi bayan gari ne zamu nemi leda muyi a ciki sannan muje mu jefar a bola. Ni na rufewa Ammi kwanan da muke wanka tayi wanka sannan tayi sallah, duk wannan abun da take yi kuka take yi ni kuma har na gaji dayi nayi shiru. A ranar ban je makaranta ba kuma haka Ammi bata je sana’arta ba. Kwana uku da haka muka farka cikin tashin hankali domin gwamnati ce ta aiko motar rusau tazo zata kwashe duk gidajemu wai za’ayi titi a gurin. A lokacin zan iya cewa bakwai na safe yayi, Ammi na tonon gurin da take ajiyar kud’inta muka ji motar ta d’aye gefen d’akinmu wanda saura kad’an a had’a da Ammi wacce ke tsugunne a gurin tana tonon rami. Ganin hakan yasa naje na jawota ta k’arfi muka fito a guje ba tare da mun tsira da komai ba sai suturun jikinmu. Muna tsaye a can gefe aka wargaza gidajenmu ya zamana tamkar mutane basu ta6a zama a gurin ba. A nan ne kuma muka fara tunanin ina zamu je mu zauna. K’arshenta sauran ‘yan unguwan namu muka bi babu mai yiwa d’an uwanshi magana muka je k’ark’ashin gada muka samu guri muka zauna. Bayan kwana biyu da haka Ammi taji ana labarin za’a je unguwar squatters a tono kayayyakinmu. Tare dasu muka je kowa yayi inda yake tunanin a nan gidansa yake aka fara tone k’asa ciro kayan sakawanmu da sauransu. Burina d’aya a wannan lokacin shine a fito mini da uniform d’ina in koma makaranta. Cikin sa’a kuwa aka samu kayan nawa da sauran kayan abincinmu har da tire d’in Ammi na sana’a. Sai dai duk tonon da Ammi tayi na neman kud’inta bata samu ba, k’arshe ita da kanta ta hak’ura muka kwashi abunda muka tsira dashi muka koma k’ark’ashin gada.”
Mum Fateey 👌
RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)
Littafin nan na kud'i ne a naira d'ari N100 kacal. Zaku turo kudinku ta 5139579011 fcmb Suwaiba Babagana sai ku turo shaidar biya ta number 09023713064 a sakaku a paid group ba sai kun tsaya jiran na bati ana ja muku aji ba. Na rage kud'inshi ne don kowacce ta shigo RZ group a dama da ita. Wanda basa son hayaniyar group zamu iya tura muku ta private a N300.
(27)
Haydar yaci gaba da bawa Laila labarinshi.
“Bayan mun koma ne nake tambayan Ammi meyasa aka rusa mana gidanmu? Tace dama ba filinmu bane, kuma gwamnati ta sha aika mana notice kan cewa mu tashi amma bamu tashi ba. A wannan gurin Ammi ta had’a mana d’akin leda kamar tent muna kwana a ciki, sai dai in zamu fita dole mu d’auki duk valuable abunmu idan ba haka ba zamu zo mu samu an kwashe, kuma koda Ammi zata kwana tana tambayar wa ya d’auka baza a kulata ba. A hakan naci gaba da zuwa makaranta har na shiga nursery two Ammi na cigaba da sana’arta. Watarana headmaster yace in fad’awa Ammi yana son magana da ita, koda tazo d’aukana na fad’a mata tace sai gobe idan tazo ajiyeni sai ta shiga. Hakan kuwa akayi, washegari da safe suka had’u a office d’insa yake fad’a mata yana buk’atar mai aiki a gidansa idan tana so domin matarsa tana da ciki kuma an hanata aikin wahala. Ko da Ammi taji zai bata gurin zama sai ta yarda washegari muka tattara kayanmu muka isa gidansa. Ba wani tsararren gida bane kamar yanda nayi tsammani, asali shima talaka ne sai dai yafi k’arfin abinci da gurin kwana. Wani d’aki aka bamu d’an k’arami muka zauna a ciki, wannan shine karon farko dana fara kwana a cikin d’aki na gaskiya ba langa-langa ba.”
“Ammi ta daina sayar da plantain ta fara kula da matarsa da kuma yayansa uku wanda biyu daga cikinsu tare muke zuwa makarantarsa. Ban fad’a miki sunana da aka sanni dashi ba ko? Idan ana kiran sunan students a register kika ji sunan Chijioke Towolawi nine zan amsa, sai daga baya Ammi ta sanar dani dalilinta na bani wannan sunan yare biyun, wai saboda koda fad’a ya tashi na tsakanin k’abilu zan tsira saboda duk na tara sunan Yoruba da Igbo. Zamanmu a gidansa zama ne na jin dad’i domin bayan d’akin da muke kwana a ciki ita matar gidan bata tsangwamarmu ko da wasa. Ammi ce take yin komai na gidan har girki kuma ta kwasa ta bamu muci mu k’oshi. Bayan wata bakwai da komawarmu gidan matarsa ta haihu a asibiti. Washe gari zata dawo gida Ammi tana gyare-gyaren tar6anta Mr Eze ya shigo gidan ya sameni ni da yaransa muna wasa a tsakar gida, kudi ya bamu yace muje mu sayi minti sai mu zauna a waje muyi wasa kar mu shigo cikin gida. Da murna muka kar6i kud’in muka tafi shago mafi kusa damu, shi kuma a wannan lokacin ne ya samu damar yiwa Ammi fyad’e a d’akin matarsa. Muna tsaka da wasanmu naji ina son komawa gida domin Ammi bata ta6a bari nayi nisa ko na jima a waje, hakan yasa na koma da gudu na samu matar gidan ta dawo a cikin Taxi tare da ‘yan uwanta mata biyu. Ganina yasa ta bani wasu abubuwan na shiga dasu cikin gidan, sai dai jin kukan Ammina yasa na sake abun hannuna k’asa na ruga zuwa d’akinsa naga abunda yake yi. Ban san menene na d’auka na kwad’ayin mishi a kanshi ba amma dai na fasa masa kai wanda hakan yasa ya sauk’a daga jikinta yana ihu yana dafe kanshi.”
“Laila a ranar matar gidan da ‘yan uwanta ne suka mana duka ni da Ammi. Domin cewa yayi Ammi ce take seducing d’insa ni kuma na shigo na fasa masa kai don mu mishi sharri mu 6ata masa aure. Su suka watsar mana da kayanmu waje da warning d’in kar su sake ganin mun shigo unguwar balle gidansu. Shiyasa da naga kayana a watse a falo na tuno da wannan labarin.”
“I’m so sorry Haydar, I have no idea haka kayi fama da rayuwarka. Sannan ina baka hak’urin abunda Abul yake maka wanda nasan kaima ka sani baya cikin hayyacinsa ne. Kuma na kwashe kayan na adana maka, I’m sorry.” Ta fad’i hakan tana ta6a gefen fuskarshi.
Kwantar da kan nashi yayi a hannunta yana runtse ido kana ya d’ago yaci gaba,
“Daga nan komawa k’ark’ashin gada muka yi, muka samu babu gurin zama mai kyau domin duk mutane sun cike. A hakan muka zamu gurin tsugunnawa muka fara jinyar jikinmu. Washe gari da safe bayan da yawa daga cikin mutanen gurin sun fita bara ko sana’arsu Ammi ta fito da kud’in data tara tana k’irgawa. A nan take fad’a mini zaman Lagos ya isheta zata koma arewa amma kud’inta ba zai kaimu inda take so ba. Bayan kwana d’aya mun samu k’arfin jikinmu muka je babban titi domin yin bara ko zamu samu cikon kud’in da muke buk’ata. Farko da muka fara nine na rufe idona Ammi kuma tana rik’e da sandana, sai dai dana ji tsayuwar mota sai in bud’e idona a ga cewa k’arya nake yi, hakan yasa wasu suka fasa bamu kud’i wasu ma suka bimu da zagi.” Ya k’arisa maganan yana d’an dariya kad’an.
Murmusawa Laila tayi tana share hawayen fuskarta yaci gaba.
“Ganin zan 6ata mana plan ne yasa Ammi ta k’ar6i sandan ni kuma na rik’e ta rufe idanunta. A haka muka samu kud’i mai d’an dama domin da gaske nake kuka ina cewa a taimakeni Mamana bata gani bata da abincin bani. Ana hakan ne wata babbar mota ta tsaya aka mik’o mini kud’i na k’ar6a sai naji an kira sunan Ammi cikin k’araji ‘SUWAIBA’ hakan yasa ta bud’e idanunta cikin razana tayi arba da mutumin da yake ciki. Ina tunawa a guje Ammi ta jani muka bar gurin mutumin na binmu a baya. Sai dai da yake Ammi ta fishi sanin lungu da sak’on Lagos sai muka 6ace mishi. Daga nan tasha muka nufa cikin sauri domin a yanda naga Ammi ta razana da ganin mutumin nan nasan yana d’aya daga cikin mak’iyanmu masu son ganin bayanmu. Awa biyu da haka motarmu ta tashi zuwa Abuja, daga nan muka canja mota zuwa Kaduna muka fara neman gurin kwana. Da yake Kaduna ba kamar Lagos bane da ko’ina ka samu zaka kwanta sai gurin kwanciya ya gagaremu muka yi ta gagaramba a gari, da kyar muka samu wani dattajon arziki ya bamu shagonshi muka kwana washe gari yace mu san inda dare ya mana. Tasha muka k’ara zuwa muka hau motar Jos. A ranar farko da muka sauk’a a garin Ammi ta samu aikatau a gidan wata babbar ma’aikaciyar gwamnati. Motarta ce tazo wucewa muna bara dalilin kud’inmu ya k’are tasa aka tsaya tana kallona wai na mata kyau, hakan ne yasa ta d’aukemu ta kaimu gidanta tare da bawa Ammi aikin wanki da guga na masu gidan. Boys quarters muke dashi na ma’aikata a gidan wanda na mata daban haka na maza daban.”
“Albashin Ammi na farko ta sakani a makaranta naci gaba da zuwa lokacin ina da shekara takwas. Bayan mun dawo Jos ne Ammi ta fara koya mini addinina tace mini mu musulmai ne gaba da baya, kuma a nan ta daina 6uya idan zata yi sallah. Lokacin sanyi yana zuwa sauran ‘yan uwanta masu aiki suka matsa mata ta kira wanzami ya mini kaciya wanda daga ni har ita kuka muke yi an kasa samun mai rarrashin wani. Bayan na warke naci gaba da zuwa makaranta har na gama primary. A nan ne na fara matsawa Ammi da maganar ina Babana da dangina suke, dukan data mini ne yasa na daina tambayarta kwata-kwata har na shiga secondary school. A nan ne kuma Ammi ta fad’a mini sunana na gaskiya wai Aliyu Haydar ba Chijioke Towolawi ba. Ita kuma tace mini sunanta Suwaiba ba Mama junior da ake kiranta dashi ba.”
“Bayan gama secondary school d’ina na lura Ammi na cikin damuwa, koda na tambayeta dalila sai cewa da tayi wai zama guri d’aya risk ne, mak’iyanmu zasu iya gane inda muke. Babu wanda ya sani muka tattara kayanmu zuwa tasha muka hau mota har zuwa nan Kanon Dabo. A nan Ammi ta saya mana d’an k’aramin gidan da muke ciki a hannun wata dattijiya wacce mijinta ya rasu ya barta babu d’a babu jika ta koma garinsu. Da kyar na samu shiga Jami’a bayan wahalan da muka sha na neman addmission Ammi na soya k’osai da doya a bakin titi har na gama makaranta. Kar kice na daina tambayan Ammi inda mahaifina yake, ban daina ba kullum idan abun ya ciyoni sai nayi maganar kuma sai ta mini fad’a ko kuma ta daina shiga harkata har sai na bata hak’uri. Na daina tambayanta su waye muke guduwa, domin nasan tana fad’in hakan ne don kawai in yarda cewa akwai masu son ganin bayanmu. Ranar dana dameta da maganar har na furta mata wata kalmar da bana fatan sake maimaitashi Ammi ta fad’i ta kamu da ciwon zuciya. Ikon Allah ne kad’ai ya tada kafad’unta Laila, tun daga ranar ban sake mata maganan mahaifina da dangina ba sai da kika shigo rayuwata na k’ara jin son sanin waye ni. Laila har yau har gobe ban san wanene ni ba, ban san daga ina nake ba, haka kuma bansan waye mahaifina ba. Kuma nayi alk’awarin har in bar duniya bazan sake tambayar Ammi akan hakan ba, domin dana rasata gwara na mutu a haka ba tare dana san komai a kaina ba. Wannan shine tak’aitaccen labarina dana sani.” Ya sauk’e ajiyar zuciya yana kallon kyakkyawar matarsa Laila wacce ta aureshi ba tare da tasan komai a kanshi ba.
Itama ajiyar zuciyar ta sauk’e kana ta jawoshi ya kwanta a kan cinyarta tana shafa gashin kanshi tana jin tsananin tausayinshi da k’aunarshi na ratsa dukkanin jikinta.
“Bari nima in baka nawa labarin duk da nasan ko kad’an ba zai kai naka bak’in ciki ba.”
A nan ta bashi labarinta ta k’are da cewa,
“Naga wasu jarabawar rayuwa amma a hakan Alhamdulillah ina cikin ‘yan uwa da dangina. Sannan na gane me kake son fahimtar dani, na gane Haydar.”
Juyo da kanshi yayi yana kallon fuskarta yace,
“Shiyasa nake son auren matured mace wacce zata d’auki labarina ba abun kyama da gudu ba sai dai a matsayin jarabawar rayuwa. Ina son tara iyali Laila, tunda bani da kowa ina son ya kasance ni kad’ai na tara zuriyata sun yi yawan da baza suyi kewan danginsu ba.”
Wannan magana ta Haydar ba k’aramin tsoro ya bawa Laila ba, ina ita haihuwan yara da yawa a shekaruntan nan? Ko ba yau ba zasu yi wannan maganan domin zai yi wuya ta haihu ne gaba d’aya.
“Baki ce komai ba.” Yace da ita yana mintsinin tumbinta.
“Lokacin sallar isha yayi.” Ta fad’i hakan tana d’age kanshi