RUWAN ZUMA Book Complete Hausa Novels by Suwaiba Muhammad.docx

Author :  Suwaiba Muhammad Category :  Bookz

Chapter   39 / 44

114K to 117K   out of 132K words

/>
“Kar mu yi haka da kai.” Shima yana dariya.

Sai da suka nitsu sannan Alhaji Abdul ya dubi k’anin nashi with serious face, yace,

“Nagode daka bani wannan daman kuma I promise baza ka ta6a regretting hakan ba. Thank you.”

“Allah yasa.” Kawai Haydar ya fad’a kana ya kar6i yaron bayan Alhaji Abdul ya mik’o mishi suka fita tare.

Har bakin motar ya rakashi sannan ya k’ara musu sallama ya koma gida.

A hanya Ammi ta fad’awa Alhaji Abdul in da zai kaisu wato tsohuwar unguwarsu zata mayar da Meenat gida. Shi dai tun lokacin da yarinyar ta gaisheshi ya ji ya kasa nitsuwa yana ta kallonta ta wutsiyar ido don a gaban motar ta zauna kamar yanda Ammi ta umurceta ta yi.

Suna isa suka shiga ciki wanda minti goma da haka suka fito tare Meenat d’auke da jaka a hannu ta matafiya tana ta murna. Mutumin da ya gani a bayansu yana magana da Ammi cikin mutuntawa yasa ya gane shine Babanta. Hakan yasa ya fito daga cikin motar ya mik’a mishi hannu suka gaisa Ammi na cewa,

“Wannan d’an maigidana ne Alhaji Abdul, kuma Yaya yake ga Ali.”

“Masha Allah, ai kullum na tuna cewa kin samu ‘yan uwanki sai na ji dad’i a raina. Ali kam ba’a ganinshi ya daina ziyartarmu, tun lokacin da ya kawo Zaliha gidanku ya tafi bai k’ara zuwa ba. A fad’a mishi Ina mishi murnar samun k’aruwar da yayi.”

“Insha Allah zan fad’a mishi kuma zan aikoshi ya zo. Ai kun wuce makwabta a gurinmu sai sai ‘yan uwa. Allah ya bar zumuncin da ke tsakaninmu.”

“Amin Amin.” Fad’in Baban Meenat yana gyad’a kanshi.

Da haka suka yi sallama suka shiga mota Meenat sai murna take yi zata je gidan Ammi hutu har na sati d’aya. A gidan Alhaji Sammani na Kano Alhaji Abdul ya ajiyesu sannan ya tafi ya barsu zuciyarsa cike da tunanin wannan yarinyar Ammin.

Washe gari driver ya kai Ammi da Meenat gidan su Laila wanda basu wuce minti talatin ba suka tafi akan zata je ziyaran dangin mijinta sai an kusa suna zata zo. Ammi ta zaga duk dangin Alhaji Sammani a cikin kwanaki hud’u tare da Meenat ‘yar d’akinta. A rana ta biyar ne suka k’ara komawa gidan Haydar in da ake hada-hadan suna washe gari, Ammi ta kai kayan sunan da ta yiwa Baby akan cewa ita baza ta zo suna ba. Ana sallan isha Haydar ya mayar dasu gida, har zai tafi Ammi ta tsayar dashi ta ce,

“Baza ka fad’a mini Sunan yaron bane har sai na tambaya?”

Murmushi yayi har hakwaran shi na bayyana ya fad’a mata. Cikin farin ciki ta nuna yayi k’okari sannan ya mata sallama ya koma gida.

Misalin k’arfe sha d’aya da rabi Laila ce zaune a bakin katifar Haydar tana had’a kayayyakinta da zata saka washegari ranar suna, tun da ta san d’akinta ba zai mata dad’in canja kaya ba saboda jama’a.

Haydar ne ya fito daga cikin band’aki ta ce,

“Baka fad’a mini sunan Bundle of joy ba Haydar.”

“Yayana na yiwa mai suna.” Ya bata amsa yana kwanciya a gefenta ya jawota yana tura kanshi jikinta.

Zuciyarta ce ta buga ta k’arfi domin bata ta6a tsammanin zai yi hakan ba, ya rasa wanda zai yiwa takwara sai Alhaji Abdul? Duk da cewa ya canja halinshi sannan ta yafe mishi, kuma tana son mijinta yayi zumunci dashi bata ga cancantar da yayi a mishi takwara ba. Sai dai baza ta nuna mishi hakan da yayi bai mata dad’i ba saboda ya fita iko da yaron fiye da ita.

“Haydar me kake yi haka?” Ta tambayeshi da taji ya zuge zip d’in rigarta yana neman cireta gaba d’aya.

“Dabarun mata nake son a mini, na so in yi hak’uri amma kullum na ganki sai kin birkita mini lissafi da kyan ki da kuma k’amshin da baya barin jikinki Laila.”

“Haydar jego nake yi fa.” Ta fad’a tana rik’e hannunshi wanda ke wasa da k’irjinta.

“Sai aka ce kar mace ta biyawa mijinta buk’ata in tana jego? Ba fa jikinki zan shiga ba Laila.”

Shiru ta yi bata motsa ba, hakan yasa ya dakata daga abun da yake yi ya koma can gefe ya kwanta kamar wani abun tausayi.

Hakan ba k’aramin tausayi ya saka mata a ranta ba, sannan ta san abun da yake buk’atan ba laifi bane don ta mishi. Kwanciya ta yi tana manna mishi k’irjinta a bayanshi tana cewa,

“Mik’o mini Vaseline d’inka.”

Washegari da asuba aka rad’a sunan jariri a masallaci aka raba goro, dibino da sweets. Mas’ud sai da yayi hawaye da ya ji shi aka yiwa takwara, ai kuwa har gida ya biyo Haydar yana mishi godiya kamar zai had’iye shi tsabar murna da farin ciki.

Laila tana zaune a falo a lokacin gari ya fara haske tana magana da wad’anda aka yi hayansu zasu yi girki akan kulawan Marwa da Hajja ta ji shigowan su, wanda hakan yasa k’irjinta ya buga don za’a fad’a mata sunan d’anta Abdul K’adir ne.

Sallamarsu ta yi kana ta k’ak’alo murmushi ta gaishe da Haydar tana kallon Mas’ud wanda ya ke cikin farin ciki kamar wanda aka yiwa babban kyauta ta ce,

“Kai kuma me ka samu kake ta murna haka?”

Mas’ud kallon Haydar yayi cikin rashin yarda yace,

“Dama bata sani bane?”

Girgiza kai Haydar yayi yana mik’awa Sabrin sauran dibinon wacce itama ta kasa kunne tana son jin sunan k’anin nata.

“Ni ya yiwa takwara Kalti. Duk mutanen duniyan nan ni kad’ai ya za6a ya sakawa d’anshi sunana.”

Sabrin zuwa ta yi ta rungume Mas’ud cikin tayashi murna sai dariya take yi ta kasa tsayawa guri d’aya, ita kuma Laila kasa motsi ta yi tana kallon Haydar idanunta sun ciko da hawaye ta ce,

“Meyasa ka za6eshi?”

“Saboda shi ya bani aurenki ya kuma mara mana baya ba tare da ya kyamaci tarayyarmu ba Laila. Mas’ud ya cancanci fiye da haka, ya zama d’an uwana, abokina kuma mai sunan d’ana.”

“Nagode sosai Baban Mas’ud Allah ya saka maka da alkhairi. Nima Mas’ud ne ya zama tamkar k’ashin bayana duk tsawon shekarun da muka d’auka muna rayuwa. Yayi mini komai ya kuma so duk abun da nake so ciki har da kai Haydar. Ka wanke mini zuciyata kuma ka cika mini wani buri nawa wanda tun ina da k’uruciya na yi alk’awarin yi wa Mas’ud takwara sai Allah yasa ban saka haihuwa ba sai yanzu. Nagode sosai.”

“Ki daina mini godiya saboda ke kika wahala bani ba Laila, and you deserve more than that.”

“Awnnnnn. Allah ya barku tare lovebirds.” Fad’in Sabrin tana narkewa a jikin Mas’ud irin abun ya burgeta d’in nan.

Dankwalon Laila ta aika mata kana ta share hawayen fuskarta ta shige cikin d’akinta in da ta jiyo kukan Mas’ud junior.

Bikin suna ya k’ayatar don dangi da abokan arzik’i sun taru ana ta hidima cikin farin ciki da annushuwa. Duk wanda ya zo aka fad’a mishi sunan yaron sai ya kad’a kai ya ce,

“Dama Mas’ud ya fi kowa cancanta.”

Dangin Haydar kuwa zuga suka yi na kwansu da kwarkwatansu suka zo a lokaci d’aya wanda yasa dole aka bud’e musu falon Haydar saboda yawansu. Kayan da suka taho dashi kuwa sai da Laila tace yayi yawa a rage amma suka k’i.

Aunty Aisha ce ta ce,

“Ana haihuwa a zuriyar Aunty Hadiza da kuma Babana amma ba’a ta6a yi a zuriyar Baffa Sammani ba sai wannan karon. Wannan kad’an ma kika gani don ga makullin gida da mota daga Alhaji Abdul ya ce a bawa d’anshi.”

Laila kasa magana ta yi sai ‘yan uwanta ne suke ta godiya tare da saka albarka aka mik’o mata keys d’in ta rik’e tana cewa,

“Allah ya saka muku da alkhairi ya kuma bar zumunci.”

“Amin Amin.” Suka amsa kana aka fara shigo musu abinci da drinks kamar ba zai k’are ba.

Rengem kam wannan karon bata samu shiga ba saboda abincin Shuwa irin su Danderu, Shurba da Gahwa su suka ci saboda basu ta6a cin irinshi ba kuma ya burgesu.

Ana cikin hira sai ga Umma da Muna wanda daga ganin yanayin fuskarsu zaka gane dole ce ta saka suka zo. Laila ce ta tar6esu cikin fara’a don ta yi mamakin ganinsu, tana tuna rabonta da Umma tun lokacin da su Haydar da Nazifi suka kai Abul Maiduguri. Umma bata bari suka gaisa ba ta ce,

“Yanzu ‘yar nan da girmanki tsofai-tsofai da ke sai da yaro mara asali nan ya miki ciki? Kuma don rashin ta ido har tara jama’a kuka yi ana hidiman suna? Ni kam in ba don Nazifi ya matsa mini ba bazan zo ganin wannan kayan takaicin ba.”

Sosai Laila ta ji zafin kalaman Umma saboda cikin baynar jama’a ta yi maganar ciki har da ‘yan uwanta da kuma abokan arzik’i. Kunya ce ta rufeta ta ji kamar ta rufe idonta kowa ya 6ace a gidan.

“Cikin shege shi ake 6oyewa ake kuma ala wadai dashi ba cikin sunnah ba wanda ya fito daga tsatso na gari. Girman mace kuma ba shi zai sa idan ta haihu ta zama abun kaico da nunawa a idon duniya ba. Sannan zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ha-maza-ha-mata sai ya yi. Wanda kike kira mara asalin ga can ‘yan uwansa a falon can ki duba ki gani in sun yi kalar takaici, sannan ki gyara halinki don kullum tsufa kike yi amma masifa da bala’i ke cinki kin kasa kwantar da hankalinki, k’arshenta a haka zaki tafi in baki yi babban rabo ba. Allah ya kyauta.” Wannan fad’in Hajiya Maryam kenan wacce dama tun asali take cike da halin Umma a kan Laila.

Umma kamar zata yi magana amma ta rufe bakinta babu kunyan idanun mutane ta shiga falon Haydar ta ga jama’a birjik wanda gani d’aya zaka musu ka gane ‘yan gayu ne na k’arshe, gefensu kuma can akwatuna ne shida da kuma ledoji kala kala wanda ta tabbatar kayan suna ne a ciki wanda aka kawowa Laila.

“Su basu d’auki haihuwata a matsayin kaico ba shiyasa suka mini hidima irin haka har da kyautar mota da gida Umma.” Laila ta fad’awa Umma wanda ita kad’ai ta ji kana ta d’aga muryarta tace, “Aunty Aisha ga Kakarsu Abul da Sabrin ta zo gaisheku.”

Nan idon ‘yan falon ya dawo kan Umma suna binta da murmushi ana d’aga mata gaisuwa tana cewa,

“Lafiya. Lafiya. Lafiya.” Kawai amma mamaki ne shimfid’e a fuskarta. Jiri ta fara gani ta yi saurin dafa k’ofa tana rufe idanunta.

Hakan yasa ‘yan d’akin suka farga wasu suka yiwo kanta aka rik’eta ana mata sannu. Hajiya Maryam ce ta bada shawaran a mayar da ita gida wai hayaniyar ce bata so. Hakan kuma aka yi, ana neman wa zai mayar dasu gida Aunty Aisha ta ce,

“Ga can Ahmad a waje ya kaisu mana. Ga motoci birjik a waje har sai an tsaya ana nema? Mu ma ai ‘yan uwa ne.”

Muna dama bata bi Umma zuwa falon Haydar ba don tana da masaniyar bayyanar dangin Haydar da kuma cewa wai ‘yan uwa ma suke shi da Laila.

Aunty Aisha ce ta kama kafad’ar Umma suka fita da ita waje Muna na rik’e da silifas d’inta tana binsu a baya kamar zata tsala ihu. A cikin motar Aunty Aisha aka sakata ta zauna sannan aka kar6o jaririn daga hannun su Ahmad aka mik’awa Umma wanda sai k’amshi yake yi ya cika yayi kyau cikin kayan alfarma.

“Na ga har zaku tafi baku ga jaririn bane shine na kar6oshi a hannun dangin babansa. Tun lokacin da suka zo yaron yake hannunsu, to abun ka da gudan jini suna marmarinsa. Wannan d’in sunanta Aunty Aisha kuma ‘yar Baffan Haydar ne, wanda zai mayar daku gida kuma d’anta ne. Ahmad idan ka sauk’esu akwai kayansu a booth ka cire musu.” Hajiya Maryam ta d’age yaron a cinyar Umma ta rufe musu k’ofar.

Cikin girmansa Ahmad ya ce,

“To Aunty Maryam.” Kana ya ja motar suka fara tafiya bayan ya kunna a.c.

Muna da Umma kuwa suna bayan mota a.c na bugarsu sai zare idanu suke yi, Umma ce ta yi k’arfin hali ta ce,

“D’an nan ku d’in dangin mijin Laila ce?”

Murmusawa Ahmad yayi bai kawo komai a ranshi ba ya ce,

“Eh, shi kawuna ne k’anin mamana. Ina zan kai ku?”

Umma ce ta mishi kwatance ya kaisu har bakin k’ofar gidan sannan ya fitar musu da take away d’in su tare da souvenirs ya kai cikin gidan sannan ya fito ya koma gida. Yana fita Umma ta saka kuka wanda ya sa Nazifi ya fito daga d’aki yana tambayar ko lafiya?

“Ashe an gane dangin mijin Lamla shine baka fad’a mini ba? Kai wannan abun bai mini dad’i ba ta bani kunya a cikin jama’a ana ta mini dariya.”

Dafe kai Nazifi yayi yana tausayin mahaifiyarsa da irin tsanar da ta yiwa Laila har bata son farin cikinta.

Dangin Haydar sai yamma suka tafi aka cikasu da take away da kuma souvenirs. Laila rufe side d’in Haydar ta yi suka koma sashenta aka cigaba da hidiman suna. Suna zaune ana hira sai ga Shema’u y’ar Tabawa ta shigo falon.

Tun bayan rasuwar Babansu Tabawa ta sayarwa Madu takunta da na ‘yarta na gidan gadon nasu sannan suka koma Wudil in da iyayen Tabawa suke da zama. Tun auren Shema’u da su Laila suka je aka musu wulakanci basu sake komawa ba, haka suma basu nemesu ba a haka zumuncin nasu ya lalace.

Bayan an gaisa ana tambayar bayan rabuwa Shema’u ta ce,

“Marwa ce ta je har Wudil ta fad’a mana kin haihu tare da rok’on muci gaba da zumuncin mu kar mu watsar. Mama tace a gaisheku ciwon k’afa ba zai barta ta zo ba.”

Da haka ta ciro rigar yaro da kuma zanin abunku ta mik’awa Laila tace ga abun sunansu ita da mamanta. Har cikin ranta Laila ta ji dad’in wannan kaya ta kuma kai cikin wardrobe d’inta da niyyar d’inkawa duk da cewa zanin wankanta ya fishi tsada.

Sati d’aya shema’u ta yi a gidan Laila sannan ta bi Yayarsu Ajidde gidanta a kan itama zata mata kwana biyu sai ta koma Wudil, aka bar Laila ita kad’ai da mijinta da kuma Bundle of joy d’insu.

Haydar bai dawo d’akin Laila ba yace ya gaji da je-ka-ka-dawo tsakanin sashenshi da nata. Dolenta ita ta shigo sashensa suna kwana tare, idan abun nashi suka motsa sai ya d’age Bundle of joy ya nemi a mishi dabarun mata tun da har lokacin bata gama bik’i ba.

Wata biyu da haka Laila ta fara ziyara ga ‘yan uwa da abokan arzik’i a matsayin yawon arba’in. Daga nan har Wudil suka je gaishe da Tabawa in da suka kawo ta asibitin Kano ganin ciwon k’afar tata yana wahalar da ita. Shema’u ke jinyarta yayin da Haydar ya d’auke nauyin komai bayan yayi k’aramar musu da Mas’ud akan cewa shi zai biya. Tana samun sauk’i suka koma garinsu suna zuwa ganin Likita idan lokacin komawarsu yayi.

Mas’ud Junior wanda ake kiranshi da sunanshi na yanka ya cika wata shida har yana rarrafe, yaro ne d’an lukuti kyakkyawa gwanin ban sha’awa kuma ga shiga rai. Kulawan da yake samu daga kowa yasa yake da son mutane da kuma son a d’aukeshi a fita yawo. A wannan ranar ne kuma Kaala Abdi ya kira Laila ya fad’a mata Abul yana hanya zai dawo gida.

Laila kasa zama ta yi tsabar murna da kuma fargaban yanda Abul zai yi idan ya zo ya sameta tare da d’an Haydar duk da cewa yana da labarin ta haihu, zata iya cewa rabon da ta yi magana dashi tun ranar da ta fad’a mishi ta haihu ya d’auki fushi da ita yau wata biyar kenan. Ko da ta je Maiduguri dubashi kuwa bai d’ago kai ya dubeta ba balle d’an dake hannunta.

Haydar ta kira a waya ta sanar dashi ya dawo gida yana tayata murna amma sai ya lura ita damuwa take ciki.

“Menene damuwar ki Maman Mas’ud?” Ya tambayeta yana jawota jikinshi tare da d’ansu wanda ke wasa da gemun babansa.

“Abul.” Kawai ta fad’a ya kuma gane me take nufi.

“Karki damu. Insha Allah babu abun da zai faru. Me da me za’a shirya mishi?”

Haydar shi ya taya Laila girkin da zata sauk’i Abul dashi duk ta bata da tabbacin ko zai ci. Har yamma liss suna zaune suna jiranshi suka ji k’arar bud’e k’ofa Laila tayi saurin isa bakin window tana lek’awa.

Abul ta gani tare da Baba maigadi suna gaisawa fuskarsa d’auke da fara’a kamar bashi ba. Yayi k’iba ya tara gemu da saje yana rataye da jakarsa a bayanshi ya nufo mashigar falon Laila ta yi saurin sake labulen ta koma gefen Haydar ta zauna zuciyarta na bugu.

Abul yana shigowa suka dubeshi cikin fara’a amma shi hankalinshi na kan yaron da ke hannun Haydar wanda ya tabbatar shine d’an mamanshi.

Mas’ud junior na jin k’arar bud’e k’ofa ya kalli wanda ya shigo ya 6are baki yana dariya yana tafa hannayensa alamar a d’aukeshi a tafi yawo. K’arshe sauk’a yayi daga jikin babanshi ya rarrafa zuwa gurin Abul ya kama wandonshi yana ja yana gwalantoyi.

Laila tsoro ne ya kamata kar Abul yayi kwallo da d’anta amma Haydar ya rik’o

39 / 44