Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   10 / 12

27K to 30K   out of 33.5K words

?ara dayiwa Alhaji Alhasan addu'a.

Garzali yace "to malam yanzu tunda zaku tafi zuwa lokacin da akayi sadakan arba'in muna da bu?atar ku ?ara dawowa akwai Wan uwan baban mu guda Waya wanda yake zaune a garin Gaidan, Baffa Ado shima zamuyi magana da shi domin mu?ara haWuwa anan gabakiWayan mu asamu raba gadon abinda Alhaji ya bari kamar yadda shari'a ta tanadar mana".

Bayan duk kannin malaman sun fito ?ofar gida Alaramma Sa'ad ya bu?aci suWan dakata yace "bayin Allah abinda yasa na tsayar damu anan shine, inaso ne kuyi ha?uri muje Jakusko muduba jikin yarinyar marigayi da take kwance a asibiti sakamakon abinda ya faru".

Batare da jayayya ba duk kansu suka amince da hakan, atake kuwa suka shiga motocinsu kai tsaye suka nufi garin Jakusko, isarsu ke da wuya suka wuce asibiti a yayinda suka shiga suka tarar da Ummin Falila itakeyin jinyar Nabila tare da Jabir da ya kasamce shima kullum yana asibitin tun ranar da suka sau?a a garin Gashua tare da Daddyn sa da Mummyn sa daya samun labarin halin da Nabila take ciki, wannan yasa bai ko tsaya angudanar da jana'izar Alhaji Alhsan dashi ba duk da dalilin jana'izar suka taho tun daga ?asar Japan.

Ummin Falila.

Zaune take a gefen gadon da Nabila take zaune acikin Wakin asibitin, batayi aune ba taga mutane kwamba guda sun fara sako kayi cikin Wakin, cikin gaggawa tayi hanzari taja bargon dake rufe dav?afafun Nabila ya rufe mata har kan kafaWunta, sannan ta juya tana mai cewa "sannunku da zuwa".

HaWe baki sukayi suka amsa da cewa "yauwa sannu, ya mai jiki kuma"?

Ummin Falila ta ce, "jiki da sau?i sosai yau kam, ga tanan ma idonta biyu".

Batare da Nabila tayi magana ba suka gaisa sosai da Ummin Falila daga bisani Alaramma Sa'ad yace "ina Ammin Nabila kuma take, tana wani Waki ne"?

Ummin Falila ta ce, "Hajiya Laila ita an sallameta tana gidan Ummanta".

"Ayya Allah sarki", cewar Alaramma Sa'ad. Sannan ya ?ara da cewa "to Allah ya basu lafiya bakiWayan su, mukam yanzu zamu koma".

Juyawa sukayi Ummin Nabila tabisu abaya tana Wan taka musu har zuwa bakin motocinsu, anan Alaramma Sa'ad yace dasu "minti Waya dan Allah ina zuwa".

Da sauri ya koma Wakin ya tarar da Nabila a kwance a gurguje yace "malama Nabila naji duk kannin ?addarar da ta faru dake, amma kisani har yanzu ina nan akan bakata na maganan aurenki babu gudu babu jada baya, dan haka karma kisake kiyi kuskuren sauya tunaninki akan dan wannan lamarin ya kasance. Don haka na barki lafiya, ina yimiki fatan alkhairi".

Anan Alaramma Sa'ad ya juya ya fito ya iske abokan tafiyarsa tare da Ummin Falila suna tsattsaye suna sumayin fitowarsa a yayin da sukayi sallama, ya sanya hannunsa cikin aljihu ya Wauko bounch naira dubu dubu kimanin naira dubu Wari kenan ya mi?awa Ummin Nabila tana mai godiya ta mi?a hannu ta karSa, suka shishshiga mota suka tafi.

Jabir.

A daidai bakin gate Win Jabir yaci karo da ayarin motocinsu Alaramma Sa'ad a yayin da suke ?o?arin fita daga cikin asibitin shikuwa Jabir yake ?o?arin shiga cikin asibitin da wata motar Daddyn sa ?irar range rover launin ja, da Jabir ya ?ariso daidai inda ake parking ya faka, ya tattari tari ledodi a hannunsa wa?an da suke Wauke da balangu mai Wumi, gasassun zabbi, lemo tanjirin da ayaba, haWi da holandiya yoghourt.

Ummin Falila.

Tun daga chan nesa Ummin Falila ta hangi Jabir hannunsa Wauke da tarin ledodi ya nufo Wakin da suke yana tafiya dakyar dakyar, wannan yasa ta mi?e da hanzari ta fito ta tarye shi tana mai cewa "Jabir kai kam kullum baka gajiya da Wawainiya kenan".

Jabir ya Wanyi ajiyar zuciya yace "haba Ummi to mima nakeyi ne akan lamarin Nabila, ai yanzu ta tsinci kanta acikin yanayi ne dako da makiyinta ne dole ya tausaya mata, don haka zan iya yin komai don ganin Nabila ta dawo hayyacinta, sabida haka ban chan chanci godiya Ummi domin Nabila ta chanchanci fiye da haka".

Jin hakan yasa Ummin Filala ta ce, "to Allah ya maka albarka, ya saka maka da mafificin alkhairi akan Wawainiyar da kake tayi".

Falila.

"My halal, kwana biyun nan duk lokacin dana zauna Nabila ce take faWomin araina gaskiya ya kamata ace munje mu?ara duba yanayin jikin nata". Cewar Falila.

Malam Kabir yace "Allah sarki wannan maganar taki haka take baby, amma badamuwa zanyi ?o?ari naga munje Jakuskon acikin satin nan domin besty Nabila ta wuce haka a wurin mu".

BuWan bakin Falila ta ce, "a'a sweetheart maganar gaskiya dubiyan nan gobe ya kamata muje, bawai maganar zamuje a cikin satin nan bane, daga nan Gashua zuwa Jakusko ya kamata ace kullum ma sai munje munga jikin Nabila ne".

Jin hakan yasa Malam Kabir yace "to badamuwa muyi fatan Allah ya kaimu goben da rai da lafiya to".

Washegari.

Bayan hantsi ya Wan Waga kaWan Falila ta kammala shirya break fast a dining Win dake cikin Wan madaidaicin falonsu, sannan taje ta taso angonta ta ri?o hannunsa tamkar makaho da Wan jagora har zuwa kan dining table, tayi serving Winsa suna hirarsu har suka kammala, kafin daga bisani Malam Kabir ya tashi ya fito car park domin duba gejin motarsa ?irar advance jorker dake fake a harabar Wan madaidaicin gidan.

A yayin da ya kammala gejin motar ya koma ciki ya ?arisa kammala shirinsa, wanda yazo daidai da kammala kintsawar Falila, wannan yasa suka rurrufe Wakunan gidan suka fito suka buWe mota suka shiga kai tsaye suka nufi Jakusko.

Cikin awa Waya zuwa biyu da suka kwashe suna tafiya a hanya suka tsinci kansu a garin Jakusko, basuyi birki ako ina ba sai a cikin asibiti, sannan suka fito suka nufi Wakin da Nabila take, cikin ikon Allah kuwa suka shiga a sa'a suka tarar da Nabila ta fara yin magana, sannan kuma lamarin jikin nata ma da sau?i sosai.

Cikin alkunya Malam Kabir ya Wan dur?usa a gefe yace "Ummi ina kwana, da fatan mun sameku lafiya, ya me jikin kuma"?

Ummin Nabila ta ce, "lafiya ?alau alhamdulillah, yau kam jikin da sau?i sosai ma", ta ?ara da cewa "sannun ku da zuwa gaskiya kunsha hanya". Sannan duban Nabila tayi ayayin da take mi?o mata gaisuwa ta amsa suka gaisa sosai.

Daga bisani Malam Kabir ya bu?aci shiga cikin gari ya barsu a wurin, itama Ummin Falila ta Wan fita wani uzirinta, saura Nabila dake kwance akan gado da Falila anan ne Falila ta Wan ?ara matsawa kusa da Nabila ta ce"sannu Nabila ya kikejin ?arfin jikin naki"?

Nabila cikin tattausar murya ta ce, "jiki alhamdulillah yanzu kam, sai tarin damuwa kawai da nake ciki, wanda dalilin haka yasa yanzu na yanke shawarin na fasa zuwa jami'atul Madina sakamakon ni yanzu na tsinci kaina acikin ire iren mutanen da basu da asali arayuwarsu, dan haka ni yanzu yaWa adawa acikin al'umma ba nawa bane, sabida gudun gori akan asalina domin a duk lokacin dana fara da'awa to tamkar na fito nayi shela ne akan asalina dan nasan dole duniya zata Wauka. Bugu da ?ari lamarin aurena shima ya taSarSare duk da Jabir tun ranar da Abbana ya rasu da suka dawo jana'iza kullum sai yazo nan, kuma sai ya tabbatar min da yana sona. Haka zalika akwai ranar da Alaramma Sa'ad yazo tare da abokansa shima ya tabbatar min?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? da cewa yasan komai akan abinda ya faru amma har yanzu yana kan bakarsa akan lamarin aurena babu fashi. To ni kuma yanzu gabaWaya lamarin duniyar nan ne komai ya isheni yanzu, inba dan duk wanda ya kashe kansa ya mutu kafiri ba, to da kashe kaina kawai zanyi inaga shine zai fimin sau?i akan lamarin dana tsinci kaina".

BuWan bakin Falila ta ce, "innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Haba Nabila ina kika kai tauhidin ki, taya zaki fara bari zuciyarki tana sa?a miki irin wa?an nan munanan manufofin, a gaskiya wannan babban kuskure ne, domin imani da ?addara mai kyau ko marar kyau yana daga cikin imani don haka kiWauka wannan abunda ya faru ?addarace kawai, kuma kar hakan ya hanaki gudanar da yaWa sa?on Allah da manzonsa, domin ko da ta hanyar zina aka same baki da laifi har a wurin Allah, laifin yana kan wa?an da suka aikata to balle ma ke duk matsalarki ba irin wannan bace, abune wanda ya faru cikin kuskure kuma duk wanda yasan Abbanki ya zai masa shaidan kirki, don haka baki da laifi anan kisa a ranki kawai zaki tafi Madina karatu, batun aure kuma abinda nakeso dake ki mi?a zaSiwa Allah yayi miki zaSin mafi alkhairi kowaye ma".

A daidai nan Malam Kabir ya dawo ya iskesu suna tsaka da hira yace "sannu Nabila".

Nabila ta amsa "yauwa sannu Malam".

Malam Kabir ya dubi Falila yace "ina Ummin inaga zamu tafi ko"?

Falila ta ce, "bansan ko ina taje ba gaskiya amma gaba da baya kuka fita".

Nabila ta buWi baki ta ce, "Falila kije masallacin mata ki duba ta tana chan".

Da "to!" Falila ta amsa sannan ta mi?e ta nufi masallacin isarta kuwa tayi dace ta iske Umminta na zaune a ciki gabatanta ta buWe alqur'ani tanata karantawa, takalma Falila ta ajiye daga waje tashiga ciki ta iske Uminta tace da ita "Ummi tun Wazu ashe kina nan, to mukam munaso zamu tafi".

Ummin Falila ta ce, "ina Kabir Win, kema aikin san yana wurin bazaiyiwu na zauna ba".

Falila ta ce, "ai shima fita yayi sai yanzu ya dawo, abinda za'ayi yanzu kitashi muje kuyi sallama zamu tafi".

Ummin Falila batare da tace komai ba, ta mi?e ta sanya alqur'anin dake hannunta acikin wata drower mai Wauke da jerin littattafai, sannan ta wuce suka tafi a jere kafaWa da kafaWa har cikin Wakin, shigarsu ke da wuya sukayi sallama a gurguje suka tafi sukabar Ummin Falila da Nabila a asibitin.

Alhaji Sha'aban.

Zaune suke sunata hirarsu a majalisarsu Alhaji Sha'aban mai cewa "wato iya lamarin mutuwar Alhaji Alhasan kaWai aya ne garemu, najima banji mutuwar da ta girgizani ba irin mutuwarsa, sakamakon a yadda abubuwa suka nuna hatta iyalansa wargajewa zasuyi".

Alhaji Saminu wanda ya kasance babban amini ga marigayi Alhaji Alhasan ya buWi baki yace "abun kam ba daWin ji, sai dai muyi fatan Allah ya rabamu da mummunar ?addara kawai, Allah ya bamu ikon cin jarabawar mu duniya da lahira", sannan ya ?ara duban Alhaji Sha'aban yace "yaushe zaka koma Japan"?

Alhaji Sha'aban yace "to gani nan dai, gabaWaya jikina yayi sanyi da lamarin duniyar ne, shiyasa ko ranar komawa har yanzu ban saka ba".

Alhaji Saminu yace "hakane sha'anin rayuwa ai fata dai Allah yasa mudace kawai shine".

Hajiya Jummai.

"Garzali lokaci yayi da ya kamata kaje Gaidan kasanar da Baffan ku Ado maganar cikan arba'in Win Abban ku domin yazo araba gadonku akan idonsa sabida gudun abinda zaije ya dawo", cewar Hajiya Jummai.

Garzali cikin tattausar murya ya amsa "to Hajiya badamuwa insha Allah gobe zanyi ?o?arin naje".

Hajiya Jummai ta ce, "to badamuwa Allah ya kaimu goben".

Washegari.

Da gari ya waye Garzali ya shirya sama sama ba wani shiri har chan ba, ya Wau mukullin mota ya fita ya buWe motar a inda yayi parking Winta ya shiga ya kama hanya, tafiya ya keyi sannu a hankali har ya tsinci kansa a cikin garin Gashua, kai tsaye ya nufi gidan Baffa Ado isarsa ?ofar gidan ke da wuya yayi parking ya shiga cikin gidan yayi sallama, Sharif dake zaune akan wata kujera plastic chair ya amsa "wa'alaikumussalam", sannan ya ?ara da cewa "lallai Yaya Garzali yau kaine a gidan namu"?

Garzali yace "wallahi nine", suka gaisa sosai.

Jin muryar Garzali yasa Maman Sharif ta le?o daga cikin Waki tana mai cewa "sannu da zuwa Garzali".

Garzali ya amsa "yauwa sannu Mama", suka gaisa sosai, daga bisani yace "Mama ina Baffa kuma"?

Maman Sharif ta ce, "Baffan ka ya fita badajimawa ba, amma bana tunani yayi nisa sosai", sannan ta juya ta dubi Sharif ta ce, "Sharif jeka maza kaduba masa Babanka akan layi mana".

Da "to!" Sharif ya amsa sannan ya fita, fitarsa ke da wuya yayi dace yaci karo dashi suka juyo tare.

Bayan Garzali sun gaisa da Baffa Ado ya zayyane masa ma?asudin abinda yasa yazo ya sameshi, sakamakon abune wanda kowa ya sani Baffa Ado mutum ne mai zafin rai sosai yasa Garzali ya Wan bishi a hankali, amma kasancewar mai hali baya fasa halinsa Baffa Ado atake ya tinziro yace "yanzu kenan ku ?a?an Alhasan sai da ya mutu tukun zaku san ina da muhimmanci a wurinku kenan ko"? Sannan ya ?ara da cewa "yanzu yaushe rabonka da ?afarka ta tako gidan zaka iya tuna yawan shekarun"?

Garzali yace "wallahi Baffa abubuwa ne sukayi yawa shiyasa, kullum inna fita kasuwa tun safe wata rana gidana ma sai lokacin kwanciya nake komawa, hatta gidan mu ba kullum nake samun zuwa ba, dan haka dan Allah kayi ha?uri Baffa".

Baffa Ado ya buWi baki yace "nikam ka rufe min bakinka anan, yanzu abunda nakeso da kai shine katsaya ka kwana gobe sai mutafi tare da kai, inyaso jibi in Allah yasa an gama duk abinda ya kamata sai nadawo gida".

Da "to!" Garzali ya amsa, sannan ya mi?e ya nufi Wakin Sharif anan sukaci abinci sukayi ta hirarsu kafin daga bisani suka fita gari.

Da gari ya waye kamar yadda Baffa Ado ya faWa hakanne kuwa ta kasance ya Wan kintsa kayan sawansa a cikin wata ?ar ?irar trabling bag sannan yayi sallama da gida suka tafi tare da Garzali.

Gashua.

Isarsu gida ke da wuya Garzali ya buWewa Baffa Ado falon Abbansu nan ya shiga ya zauna, sannan ya fita ya ?arisa asalin cikin gidan yayi magana da Hajiyansa domin tazo su gaisa da Baffa Ado, batare da Sata lokaci ba Hajiya Jummai tazo suka gaisa da Baffa Ado sosai suka ?ara da yin wasu hirarrakinsu.

Washegari.

Da Wan hantsi kaWan kowa ya hallara a falon Alhaji hatta malaman da akayi alkawari dasu wanda su zasu zo su raba gadon suma duk sun samu halarta illa Hajiya Laila ne kaWai da Nabila da basa nan, wannan yasa Baffa Ado ya Wan Waga kansa yayi muzurai ya ?arewa kowa kallo a fallon sannan yace "am, ina yarinyar nan Nabila kuma da Amminta"?

Garzali ya buWi baki yace "Ammin Nabila tana gidan Ummanta a Jakusko tace ita da garin nan har abada, ita kuma Nabila tana asibiti a chan Jakuskon".

Baffa Ado yace "to Allah yasa mudace, yanzu da farko kafin araba gadon nan inaso daku ku amince gabaWayan ku ayiwa Hajiya Laila ihsani acikin dukiyar mahaifinku, sakamakon tsawon lokaci da takwashe tana tare da mahaifinku sannan kuma ta zauna daku lafiya, da wannan dalilin nake neman wannan alfarman a wurinku".

Duk kannin yaran Alhaji da suke zaune a wurin suka haWe baki sukace "wannan babu komai ai, mun amince abata kawai duk yadda akayi daidai ne".

Duba da wannan malamin da zai raba gadon ya warewa Hajiya Laila wani kaso daga ciki, sannan acikin abinda ya saura aka bawa Hajiya Jummai kaso Waya bisa huWu na dukiyar Alhaji a matsayinta na matarsa, sauran kaso uku kuma aka rabawa ?a?ansa, wanda ya zamto maza aka basu ninkin abinda matan suka samu, kamar yadda yazo mana a shari'ar muslimci.

Bayan an kammala komai da ya shafi raba gadon Baffa Ado ya buWi baki yace "to jama'a yanzu abinda nakeso daku kafin mu watse anan inaso za'a Waura auren Nabila da Wana Sharif sakamakon duk kansu ?a?ana ne don haka ga sadaki nan naira dubu Wari.

Baffa Ado ya sanya hannunsa cikin aljihu ya ciro damin kuWi ya ajiye sannan yayi umurni a malamai guda biyu daga cikin malaman da suka Waura auren a matsayin waliyan Sharif da Nabila.

Jin haka yasa Garzali yace "haba Baffa miyasa batare da an shawarci Nabila ba za'a Waura mata aure"?

BuWan bakin Baffa Ado yace "kai rasar kunya zakayi min, nine zance ga yadda za'ayi abu kace bahaka ba, to ko marigayi Alhaji Alhasan bai isa nayi magana yace bahaka ba, sakamakon duk duniya bashi da Wan uwan da ya fini, tunda da mahaifin mahaifina da mahaifin mahaifinsa uwarsu Waya ubansu Waya, ?a?an baffanu muke da dani da mahaifinku don haka yanzu baku da wanda ya fini sabida haka dole yanzu za'a Waura auren nan anan wurin".

Garzali ya buWi baki zaiyi magana kenan, Umminsa ta ce, "Garzali inka sake cewa wani abu akan abinda Baffanku ya faWa to banyafe maka ba".

Wannan dalilin yasa Garzali ya haWiye maganar da yakeson tankawa, sannan shikuwa Baffa Ado ya umurci Alaramma Sa'ad ya zama waliyin Sharif a yayin da ita kuma Nabila Waya daga cikin malaman ya zama waliyinta suka gabatar da siga kamar haka, "ni Alaramma Sa'ad ina neman auren Nabila abisa sadaki dubu Wari".

Waliyin Nabila yace "ni Malam Aliyu nabaka auren Nabila abisa sadaki dubu Wari".

Alaramma Sa'ad yace "na karSa". Sannan ya juya yace "jama'a ku shaida aure ya Wauru tsakanina da Nabila".

Cikin firgici Baffa Ado yace "kai Sa'adu kake ko waye me kake faWa ne"?

?aya daga cikin malaman yace "tabbas a shari'a aure ya Wauru tsakanin Alaramma Sa'ad da kuma Nabila sakamakon sigar a suka gabatar Alaramma Sa'ad akansa ya karSawa auren Nabila, domin idan da a Sharif ya karSa to dacewa zaiyi, ni Alaramma Sa'ad ina nemawa Sharif auren Nabila abisa sadaki naira dubu Wari. Sannan kuma a yayin da waliyin Nabila zai bada aurenta kamata yayi yace nabawa Sharif auren Nabila, shikuma waliyin Sharif sai yace na karSawa Sharif. To a gaskiya yanzu dai a shari'ance Nabila ta zama matar Alaramma Sa'ad".

Baffa Ado yace "kai! ?arya ne wallahi sai ka saketa yanzu kuwa anan Win nan".

Alaramma Sa'ad ya buWi baki yace "babu abunda zaisa na saki Nabila, don haka kabarma ?o?arin yimin barazana Baffa".

Atake falon ya kaure da hayaniya kowa yana faWin albarkacin bakinsa, bayan kwashe tsawon lokaci da suka Wauka sunata cece kuce daga ?arshe Baffa Ado yace "tunda ka?i ka saki yarinyar nan tun muna cikin ruwan sanyi to ka saurari sammaci, domin in kamin gardama anan tabbas nasan bazakayi a gaban alkali ba".

Alaramma Sa'ad yace "ni a shirye nake da muje ko ina dakai akan mamata Nabila, don haka ina jiran sammaci".

Anan Alaramma Sa'ad ya mi?e tare da zugar malaman da suke cikin falon suka fita, shikuwa Baffa Ado ya cigaba da reSa acikin falon batare da kowa ya kulashi ba har yayi ya gaji suka watse.

Batare da Sata lokaci ba fitowar Baffa Ado a cikin gidan ya mi?a shiri'a court kai tsaye domin shigar da ?arar Alaramma Sa'ad akan aurensa da Nabila, yayi dace kuwa

10 / 12