Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   7 / 12

18K to 21K   out of 33.5K words

ya Saci kinji"?

Kai tsaye da Ubale ya Wauki Falila a mota baitsaya ako ina ba sai da isa ?ofar gidan yayi parking sannan Falila ta buWe ?ofar motar ta fita tana mai godiya yaja motar ya tafi, ita kuwa ta shige cikin gida, ta iske Umminta duk hankalinta ya gama tashi ganin shigowar Falilan yasa Umminta ta mi?e cikin firgici ta ce, "Falila ke daga ina yanzu"?

Jin hakan yasa Falila ta tsaya chak cikin sanyin jiki ta ce, "naje gidansu Nabila ne".

Ummin Falila ta ce, "amma wa kika tambaya kika fita, bayan kinsan dokar Daddynki bayaso kuna fita waje ko da aikane balle kuma fita da babu dalili, tun Wazu nake zaune anan addu'oi kawai nakeyi akan Allah yasa kar yarigaki dawowa gidan domin nasan za'asamu matsala".

Falila ta Wan ?arisa daf da Umminta sannan ta dur?usa ta ce, "Ummin ki gafarce ni dan Allah, banyi haka dan na Sata miki rai ba, kiyi ha?uri kinji"?

Ummin Falila ta Wan sanya hannunta akan kafaWar Falila ta ce, "ni kaina nasani ba Wabi'arki bace irin haka, yanzu ma nasan dalilin aurenki ne yasa duk hankalinki ya tashi, gashi yanzu ma da ganin idanuwanki alamun kuka kikayi Falila, amma abinda nakeso dake mudai mune iyayenki bazamuso abinda zai chutar dake ba, don haka ki saki ranki, shi lamarin aure duk wanda zaki aura, duk kuWinsa ko mulkinsa, ko ?arfin soyayya da sha?uwa da fahimta dake tsakaninki da wanda zaki aura to dole sai kin haWa da addu'a domin yau da gobe yawuce wasa Falila, don haka kimi?a lamarinki ga Allah kisaki ranki kinji ko"?

Falila ta ce, "to naji Ummi, insha Allah daga yanzu bazan ?ara saka damuwar komai arai na ba".

"Yauwa najidaWin jin hakan, Allah ya miki albarka", cewar Ummin Falila.

Washegari.

Da Falila ta tashi taje ta gaida Daddynta kamar yadda ta saba, sannan tayi gyare gyren Wakinta haWi da Wakin Umminta, ta ?ara da karya kumallo daga bisani ta kintsa ta fito direbansu ya Wauketa zuwa makaranta, a yayin da suka isa suka tarar da Nabila na zaune akan cool down dake daura hanya ta zabga tagumi, alamu da kaganta kasan hankalinta baya jikinta, wannan yasa Falila tayi sallama da direbasu sama sama ta sau?a motar da hanzari ta?arisa inda Nabila ke zane ta ce, "haba Nabila yau dan Allah miyake da munki haka, da zaki kama ki zabga irin wannan tagumin"?

Nabila ta Wan sauke ajiyar zuciya ta ce, "kibari kawai, ai dole nashiga damuwa domin bana mantawa tun ina ?ar yarinya ?ara lokacin ana kaina islamiyya muna aji Waya Ammina take cemin ?an matan Ammi Allah dai ya nuna min ranar da zakiyi sau?ar alqu'ani mai girma, haka takasance cikin irin wannan fatan, tare da yimin addu'oi na alkhairi, to yau gashi an wayi gari Allah yayi nayi sau?a sannan kuma za'ayi waliman sau?armu Ammina tana Saudiyya lokacin, haWi da aurenki guda nan ma bata nan, wannan yasa nakejin wani irin idan na tuna".

Falila ta ce, "haba besty kece kullum kike faWin ina mi?a duk kan al'amurana ga Allah, amma kuma yau ke gashi akan abunda bai kai ya kawo ba, kin zauna kin zabga tagumi irin wanda duk wanda ya ganki sai ya Wauka mutuwa akayi miki, don haka kibar wannan tagumin domin bashi da amfani, kitashi muwuce class kawai".

Mi?ewa Nabila tayi suka Wan haWe hannayensu wuri guda suka kama tafiya, suna daf da shiga department daga chan gefe guda suka jiyo muryar Jabir yana cewa "dama ana ganin amare ne, a irin wannan lokacin"?

Jin hakan yasa sukayi birki, Jabir ya ?ariso inda suke ya ?ara da cewa "amma a gaskiya Falila kin bani matu?ar mamaki sosai, banyi tunanin bani da amfani agareki ba kwata kwata har sai da naga invitation auren ki a gidan mu akawo a Daddy nah, wanda ko a wasa baki taSa faWamin aurenki yayi kusa ba".

Duban Jabir Nabila tayi sannan ta ce, "abunde duk bana ?orafi bane, domin bawani hidima za'ayi ba, kuma Waurin auren ma inda kalura ajikin invitation Win zakaga a islamiyyar mu za'a Waura auren ranar sau?ar mu, batun sau?a kuma najima ina faWamaka kasani ai".

Jabir yace "to amma ?anwata miyasa bakiyi mana ko da family and friends bane a bikin"?

BuWan bakin Nabila ta ce, "walatajajjasu, (karka tsananta bincike) wannan ingantacen hadisi ne, don haka kai dai kayi fatan alkhairi kawai".

Jabir ya Wanyi murmurshi yace "uhm! To nayi shiru, abunka da manyan malamai komai sai an kafa hujja da hadisi ko aya, to Allah yasa mudace".

Duk kansu suka haWa baki sukace "amin thumma amin", sannan suka shiga class domin rubuta test.

Fitowarsu a test Win ke da wuya, Falila tayi bankwana dasu da zimmar cewa "nifa daga yau bazan ?ara zuwa makaranta ba, har sai bayan aurena insha Allah".

Jin hakan yasa Nabila ta ce, "ko nima gaskiya ba lallai ba, domin gobe Ammina zata tafi Damaturu jibi kuma jirginsu zai tashi insha Allah".

Bayan Sati ?aya.

An wayi gari shirye shiryen walima yayi nisa, ranar gabatar da taron walimar kaWai ya rage ake jira, a kwana a tashi har aka wayi gari ranar wata asabar za'a gudanar da taron walima, duk kannin Walibai sun fito a cikin ayari cikin shiga ta ?aya iri Waya kowacce na ri?e da allonta a hannunta, aka gama da abunda ya shafi sau?ar karatu, sannan daga bisani aka Waura auren Falila da Malam Kabir a wurin, abisa sadaki dubu Wari, dubban mutane da suka halarci taron daga Sangare daban daban sun gabatar da add'oi sosai, sannan daga bisani kowa ya watse.

Alaramma Sa'ad

Yana Waya daga cikin dubban mutanen da suka halarci taron walimar, bayan antashi a taron bayyi ?asa a gwiwa ba, kai tsaye ya bu?aci wani daga cikin malaman islamiyyar da yayi masa jagora har gidansu Nabila, isarsu kenan shima Abban Nabila ya dawo ko cikin ma bai shiga ba, daga nan suka gaisa daga bisani ya basu daman suka shiga har cikin falon sa, bayan sun zazzauna Alaramma Sa'ad ya gabatar da kansa, sannnan yace "Alhaji dama bawani abu bane ya kawo mu illa maganar Nabila, nidai bantaSa aure ba, ina aiki a ministry of health kuma naga Nalbila na yaba da hankalinta, shine mukazo idan har ya kasance ba ayi magana da wani ba, to ina bu?atar abani izinin fara tsayuwa da ita ko Allah zaisa mu fahimci juna".

Jin hakan yasa Alhaji yace "to a gaskiya naji daWi sosai da zuwan ku, kuma a yanzu haka dai babu wata sahihiyar magana a ?asa dangane da lamarin Nabila, don haka na baka dama ako da yaushe zaka iya zuwa domin ku tattauna".

Alaramma Sa'ad ya buWi baki yace "masha Allah, muna godiya sosai da irin wannan karamci Alhaji, babu abinda zamuce face Allah ya ?arawa rayuwa albarka".

Duk kansu suka haWa baki sukace "amin summa amin". Suna masu raha a junansu sukayi sallama.

Bayan Wata ?aya.

Allah yayi Ammin Nabila ta samu dawowa daga ?asa mai tsarki cikin ?oshin lafiya, mutane kowa yayi murna da hakan, musamman ma Nabila da ta kasa zaune ta kasa tsaye tun ana saura kwana biyu kafin tasowar jirginsu Amminta daga Saudiyya.

Falila.

Falila zaune take acikin Wan madaidaicin falonta wanda aka ?ayatashi sosai da kayayyakin ?awa kala daban daban, batayi aune ba taga Nabila tamkar anjeho ta daga sama, cikin mamaki Falila ta ce, "besty idonki kenan, rabona dake tun ranar walima fa".

Nabila ta Wan saki murmushi ta ?arewa Falila kallo ta ce, "tabbas lallai aure ni'ima ne, kinga yadda kika murje kike she?i kuwa"?

Falila tayi dariya ta ce, "ke dai bari kawai idan ana sallah ba a magana, amma ai ni zan faWamiki aure ni'ima ne".

Nabila ta Wan zauna kusa da Falila ta ce, "a'a ?awata bani labari na sha,wai miye sirrin ne"?


Falila ta ce, "wato bantaSa samun cikakken farin ciki da natsuwa ba har sai da nayi aure, kuma wallahi rayuwa sirri ce, domin kinsan akwatina 6 nazo na samu acikin Wakin nan, sakamakon Daddy nah ne da kansa ya Waukoni a mota ya kawo gidan nan, kaya set 50 ya min, ga takalma son barka da jakakkunansu, sannan kayan kwalliya suma tarinsu guda babu abinda babu, murna da farin ciki ya lulluSeni, da dare yayi bayan abokansa sun rakoshi sun tafi, ya Wauko takardun gidan nan ya dam?amin yace na Soyesu a wuri mai kyau da na duba naga gidan mallakin Malam ne, atake na Waga hannu sama nayi godiya ma Allah, abun bai tsaya nan ba washegari ya mi?a min iphone 17 pro sabuwa gal a kwalinta, harna rasa ma ta yadda zan gode masa, ?arshe dai da ya fahimci irin mamakin da nakeyi sai ya bani labari, ashe kwashe shekaru yana aiki NGOs wanda a ?alla duk wata albashinsa ya kai dubu Wari uku, banda kuma alawansis Winsa, akwai device wanda yake gunar da ayyukansa ta cikinta, a kullum yana turamusu report wannan yasa yake da ishashen lokacin zuwa islamiyya ako da yaushe. Ni dai a yanzu kullum ?ara godewa Allah nakeyi da ya bani miji daidai dani wanda yake riritani, yake sani farin ciki ako da yaushe, a gaskiya aure duniya ne Nabila, domin a yanzu dake da hoto baki da banbanci".

Nabila ta ce, "uhm, lallai kin samu duniya besty harda kirana hoto, wato yanzu ni dan banyi aure ba shikenan bani da amfani ma, to Allah ya baki ha?uri ni dama na kawo miki tsarabar Hajiya nah ne na dawowanta daga Saudiyya tunda Allah yasa nazo na isar da sa?o ni bari intafi".

Cikin raha Falila ta rungume Nabila ta ce, "haba my besty wai fishi kikayi kenan, amma dai ai kema kinsan wasa ne".

Da sauri Nabila ta Wan galla mata harara ta ce, "ta yaya zakice wasa kike min, bayan kingama cimin fiska".

Falila ta ce, "to kiyi ha?uri bazan ?ara ba aminiya", sannan ta ?ara da cewa "ya labari makaranta nasan abubuwa sungama Waukan zafi yanzu kam ko"?

Nabila ta ce, "a'a kidai tsaya karkina karatu zaki sha mamaki ai".

Suna cikin tsaka da hira sukaji shigowar Malam Kabir, ya ?ariso ya iskesu a falo ya buWi baki yace "yau besty ne a gidan namu, ai mukan har munyi fishi dake daga ni har mar'atussaliha, tunda sai yau kikaga dama kikazo mana".

Nabila ta ce, "lah Malam bahaka bane wallahi, sakamakon lokacin da akayi auren ai Ammina tana Saudiyya wannan dalilin yasa bana zuwa ko ina, har sai da ta dawo tukun, yanzu ma na kawo muku tsarabarku ne, kafin daga bisani kuma muzo tare da ita".

Malam Kabir ya buWi baki yace "lallai muna godiya sosai, tsarabar nima har dani, to kicewa Hajiya mungode sosai, kuma har gida zamuzo muyi godiya insha Allah".

Nabila ta ce, "to bakomai insha Allah zataji, nikam zan gudu nabarku lafiya".

Bayan Nabila ta dawo gida, ta tarar da Amminta na zaune a falo tana ta ?o?arin Waure wata babbar dealer mai Wauke da tarin kayayyakin tsaraba wanda suka haWa da sallaya da jallabiyoyi da dai sauransu.

Cikin mamaki Nabila ta ce, "Hajiya wannan tarin kayan kuma na minene"?

Ammin Nabila ta Wan Wago kai ta ce, "wannan tsarabar ?an uwan Abbanki ne, wa?an da suka garin Jakusko, inaso ne zuwa jibi akayi musu chan garin".

BuWan bakin Nabila ta ce, "ayya Hajiya nikam da kibari sai anyi hutu a makaranta sai in tambayi Abba mukayi tare, domin nima inason zuwa garin sosai".

Ammin Nabila ta ce, "a'a aiba zaiyuwu ba Nabila, dole ne yanzu za akai musu, amma sai dai na Wauka miki alkawarin duk lokacin da kukayi hutu za muje tare insha Allah", ta ?ara da cewa "sannan Wazu kuma Abbanki ya sanar dani na faWa miki kishirya akwai wanda sukayi magana dashi ya bashi izinin akan gobe zaizo ku gaisa".

Cikin firgici Nabila ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!"

Da sauri Ammin Nabila ta ce, "ya naga duk kin firgita, to kisaki jikinki ai neman izini ba bayarwan aure bane, kawai muslimci ya tanadar mana da hakan ne domin arin?a bada daman samun fahimtar juna a tsakani ta hanyar da tace, sannan ba laifi bane idan ba a fahimci juna ba sai ayi ha?uri, don haka wannan bakomai bane kitabbatar kinshirya da zuwansa gobe da zarar ya iso kikayi falon Abbanki ku gaisa a chan".

Nabila ta Wanyi chan ta ce, "to naji, Allah ya kaimun goben".

Jikinta da sanyi ta mi?e tabar Amminta a wurin ta nufi Wakinta taje ta faWi akan gadonta yiriiiiif, tana mai huci, daga nan ta shiga tunanin, "miyasa na hana Jabir ya turo iyayensa? Tabbas na tafka babban kuskure da nayi sake wani daban ya fara zuwa gidan mu neman aurena a wurin mahaifina wanda bashi bane zaSina, domin a wannan matakin komai yana iya faruwa akan lamarin aurena nasani. Abu na biyu kuma shine a yanzu ko da zansa Jabir ya turo to ya zama nema acikin nema kenan, wanda kuma yin hakan a muslimci haramun ne, ya Allah gani gareka kafini sanin abinda yake daidai a dangane da lamurana don haka ina ro?onka kayi min zaSi da duk abinda yafi alkhairi a gareni ya rabbi".

Haka Nabila ta kasance cikin Wimuwa har zuwa wayewar gari, daga bisani ta daure ta tashi tayi wanka batare da kwalliya ba ta Wauki dan?areren swiss less ta sanya, wanda ya samu Winkin fited gown daga kwararriyar telarta mai suna Zahratul-Qalam, sannan Nabila ta?ara da sanya jalbaf akan dogowar rigar wanda ya sau?a mata har ?asa, tana ta zaune cikin sake sake chan kawai taji ana knocking Win ?ofar Wakinta, batare da Nabila ta tashi daga kan gadonta da take zaune ba ta buWi baki ta ce, "waye ne"?

"Nine", cewar mai gadi, ya ?ara da cewa "Ammin kice tace na sanar dake kinyi ba?o yana falon Alhaji".

Nabila ta ce, "kace ina zuwa".

Da "to!" Mai gadi ya amsa jikinsa yana Sari ya juya ya tafi, ita kuwa Nabila ta ?ara gyara zama tamkar bada ita ake ba, bayan ta kwashe tsawon lokaci tukun ta tashi ta ?arisa falon ta iske Alaramma Sa'ad na zaune daga gefe akan wata kujera ?irar 1 sitter, tayi ?arfin hali tayi masa sallama, sannan ta zauna a ?asa kan carpet Win dake malale a cikin falon.

Da murmushi Alaramma Sa'ad ya amsa sallamar, suka gaisa sosai sannan yace "malama Nabila nasan zakiyi mamakin ganina anan, amma nasan zaki tuna na faWamiki zanbi duk wani mataki domin naga na taka matakin aurenki bisa ka'ida, to a yanzu dai na taka matakin farko kenan wanda shine ya bani daman samun irin wannan karamci da aka nuna min a yau. Don haka abu na ?arshe shine, a yanzu goyon bayakin kaWai nake nema, domin shine zai bani damar cika burina akan soyayyarki, don kije kiyi tunani, ni zan tafi".

Muryar Nabila da nauyi ta ce, "to nagode sosai, a sau?a lafiya Allah ya tsare". Sukayi sallama Alaramma Sa'ad ya tafi, kai tsaye daga falon itama ta ?ara komawa side Winta.

Washegari.

Jabir na zaune hannunsa Wauke hand out yana Wan duddubawa a wani keSantaccen wuri bayyi aune ba ya ga Nabila akansa, cikin firgiji Jabir ya Waga kai yaga Nabila yace "lafiya kuwa, miyake haka"?

Nabila ta ce, "ba lafiya ba, domin akwai wani lamari da wasa wasa yana neman zamemin gaskiya, na taSa haWuwa da wani mutumin wanda ya nuna yana sona amma ban bashi dama ba, haka dai ya cigaba da bibiyar rayuwata, akwana a tashi har yahe ya nemi izini a wurin Abba nah, kamar wasa jiya ya zoshi har cikin falon Abbana da amincewar iyayena, a raina banaso amma haka nabi umurni na saurareshi".

Jin hakan yasa Jabir ya ajiye takardar dake hannunsa, sannan ya mi?e yace "Nabila kunnuwa basa iya tantancemin kalamanki wani irin sa?o kikeson isar min ne kifaWamin kai tsaye kawai".

Nabila ta ce, "ina nufin anzo wani mataki da duk yadda za'ayi kayi ?o?arin katuro Daddyn ka, domin ya samu Abba nah akan maganan auren mu".

Jabir yace "Nabila kenan, abaya babu yadda banyi dake ba akan zan turo shi, amma sam kikace sai Amminki ta dawo daga Saudiyya, tun a wanchan lokacin nakasa gane dalilinki na zartar da irin wannan hukuncin, domin Daddy nah Abbanki zaije ya samu ba Amminki ba, kuma ke kanki kin sani bazaiyuwu ayi auren mu Amminki tana Saudiyya ba, amma sai yin maganan a tsakaninsu shi zai tabbatar da muna tare da junan mu ko zuwa bayan shekara nawane, kuma bazaiyiwu wani yazo abashi dama ba, to amma sam kika?i amincewa. To gashi yanzu kuma Daddy nah yana Japan daga Itali yawuce chan, kuma babu alamun dawowarsa akusan nan domin yayi mana visa dani da Mummy na, jira kawai akeyi mu kammala exam Win semestern nan mutafi a chan zamuyi hutu gabaWaya".

Jin hakan yasa Nabila ta fara zubda hawaye tana mai cewa "Jabir amma kasani zuciyata ta saba da kai, ban san ta yadda zan fara gudanar da rayuwa babu kai ba, ya kamata kayi wani akan wannan lamarin dan ganin mun rayu atare har abada".

Jabir yace "my dear banaso kina zubda hawayenki ba daidai bane kyakkyawar mace irinki ace kina asarar hawayenki mai shegen tsada, don haka kiyi ha?uri kiyi goge hawayenki ni nasan me zanyi akan lamarin don haka yanzu daga nan kawai gida zan wuce".

BuWan bakin Nabila ta ce, "nima tare zamu tafi a motarka sai ka ajiyeni a gida kawuce, amma inaso ta tsohuwar kasuwa zamubi sakamakon Abba na yana store Winsa na chan don haka nakeso ya gammu tare da kai".

Jabir yace "to badamuwa buWe ki shiga mutafi".

Kai tsaye Jabir bayyi birki ako ina ba sai abakin katafaren storen Abban Nabila a yayin da suka iske shi yana kan plastic chair Jabir ya buWe ?ofar motar ya fito itama Nabila ta buWe ta fito sannan suka ?arisa gaban Abbanta Jabir ya dur?usa yace "sannu Abba, ina kwana"?

Abban Nabila ya amsa "lafiya ?alau Jabir", ya ?ara da cewa "ku daga ina haka"?

Jabir yace "mu daga makaranta ne Abba, sakamakon muntashi kuma Yaya Mubaraq baizo ba, nikuma zan tafi shiyasa nace ta shiga motana sai nabi ta gida na ajiye ta na wuce, muna cikin tafiya kuma Mummy nah ta kirani a waya ta bani sa?o zuwa kasuwa, shiyasa da muka shigo nace to bari mu?araso na gaishe ka".

Abban Nabila ya buWi baki yace "ayya Allah sarki, ka kyauta kuwa, Daddyn ka ai kwanan baya ya kirani a waya ya cemin ya shigo Nigeria yana gida, to kuma bamu haWu bama naji labarin ya sake tafiya".

Jabir yace "eh haka akayi anyi masa kiran

7 / 12