Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   4 / 12

9K to 12K   out of 33.5K words

har bakin mota, bayan duk kansu sun shiga mota sun zazzauna, Nabila ta dawo ta Sangaren Jabir yake ta Wan sunkuya ta dubeshi ta ce, "nagode sosai da ziyara, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sauke ku lafiya".

Jabir ya Wan saki murmushi yace "amin mungode da addu'a", yaja motar suka fita, kai tsaye suka nufi makaranta, akan hanyarsu ta komawa makaranta Jabir yace "wato yau ko mahaukacine akayi masa abinda Nabila tayi min ya san tana sonsa".

Jin hakan yasa Aisha da Falila duk sukayi shiru tamkar ba kowa acikin motar, wannan abu ya taSa zuciyar Jabir hakan yasa yace "yau ya tabbata ina cikin alkhairi dumu dumu, don haka daga nan har cikin makaranta a rufe ido zan kaimu", batare da Jabir ya gama rufe bakinsa ba, yaji sun haWe baki suna cewa "a wayyyo! Dan Allah kayi ha?uri, wallahi bamu shirya mutuwa yanzu ba".

?wafa kawai Jabir yayi ya Wan jijjiga kai ya ?ara giya a motar ya take ta 180 har cikin makaranta, parking Winsa ke da wuya ya buWe musu ?ofa batare yace uffan ba yaja motarsa ya ?ara wuta.

Washegari.

Falila tana zaune a department, kamar a mafarki sai taji muryar Nabila tana ambaton "my besty", Waga kanta tayi kamar wasa ta hangi Nabila tana kusanto inda take zaune, da hanzari ta mi?e tayi kanta da gudu tana mai cewa "oyoyo", suka rungume juna.

Suka samu wuri suka zauna Falila ta fara da cewa "besty jiya bayan munbar gidanku munga abun mamaki kam".

Nabila ta ce, "to ikon Allah, me kuma ya faru"?

Falila ta ce, "tunda muka hau kan hanya Jabir yake murna yana maganganu akan soyayyarki, dani da Aisha dukkan mu mukayi shiru, tamkar ke da bakya wajen, ashe yaji haushi, akan haka dai tun jiya ko kulamu bayayi yanzu, lamarin irin son da Jabir yake miki yakai ?ololuwa Nabila ya kamata ki fahimci haka".

Nabila ta Wanyi shiru ta ce, "bawai ban fahimta bane, na fahimta sosai ma, domin ko Ammina jiya bayan kuntafi itama tace min gaskiya ita bataga laifin Jabir ba yaron yana da hankali, itama ta yaba dashi sosai".

Falila ta ce, "to kiji fa, miye ne yasa bazaki bashi dama ba"?

Nabila ta ce, "a rayuwa dukkannin wani Wan adam baya taSa cika cikakken mutum har sai yana da manufa acikin rayuwarsa, a yanzu burina da nasa a gaba a rayuwata bazan samu damar cika shiba in har ya kasance na auri Jabir".

Jin hakan yasa Falila ta ce, "shin amma minene dalilinki akan haka"?

Nabila ta ce, "har kullum ina faWamiki mata da yawa sun rasa farin cikinsu ne, ta sanadiyar auren wa?anda basu dace da rayuwarsu ba. Ni nataso da arayuwata bani da burin da yawuce na zama likitar yara, amma sabida rauni irin namu na ?a?a mata wannan burin nawa ya rushe, a yanzu kuma bani da burin da yawuce na zama malamar addinin islama, na samu damar na ri?ayin da'awa a gidan mijina, idan ta kama ina yin wa'azi a wuraren walima, da dai sauransu. Sannan kuma abu na biyu ina da bu?atar samun miji wanda zai kasance a kusa dani ako da yaushe ba wanda zayi nisa dani ba. To kinga anan idan zamuyi duba da tsarina akwai bu?atar na samu miji mai son hidimar addini sosai, domin shine zai ?arfafamin idan munyi aure domin yaga na cika burina, sabida ya san muhimmancin abun".

Jin hakan yasa Falila ta ce, "besty kin manta ne tun muna secondry fa Jabir ya sauke alqur'ani, sannan kuma abune wanda kowa ya sani bashi da matsala a Sangaren mu'amala da mutane".

"Duk nasan da wannan", cewar Nabila, ta ?ara da cewa "matsalar dama itace, shi Jabir ya kasance Wa Waya tilo a wurin iyayensa, sannan kuma mahaifinsa Alhaji Sha'aban babban Wan kasuwa ne, ya kwashe tsawon shekaru yana international business, babban burinsa kuma anan gaba shine yaga Jabir ya gama makaranta ya mi?a masa ragamar dukiyarsa ya cigaba da gudanar da ita abisa tsarin ?asa da ?asa. To Falila kinga idan mukayi duba da wannan lamarin akwai babban ?alubale acikinsa domin kuwa, idan har mukayi aure da Jabir anan gaba to bazamu zauna a Nigeria ba, hasalima sai dai yau muna wacchar ?asar gobe muna wata daban, to kinga in har haka ta kasance tofa babu tayadda zan cika burina na yaWa da'awar addinin islama. Abu na biyu kuma shine, idan ya kasance ya barni anan shi yatafi ?asashen harkokinsa to kinga zan takura a Sangaren rashin rashin samun kulawar mijina akusa dani, domin ni nafi kowa sanin kaina".

Bayan shiru da Falila tayi na ?an mintuna ta ce, "to amma kisani shi kansa aure ibada ne, haka zalika yaWa da'awa ibada ce, amma dai akwai bu?atar kije kizauna ki ?ara tunanin sosai akan wannan lamarin".

Nabila ta ce, "to naji kuma nagode insha Allah zan duba nagani".

"To Allah yasa mudace", cewar Falila, ta ?ara da cewa "amma nayi mamaki da naga kinzo makaranta yau, baki duba time table bane ki kazo"?

Nabila ta ce, "na duba mana miyake faruwa"?

Falila ta ce, "yau fa departmental muke dashi, ko dai kin manta H.O.D ne yake Waukan mu course Win"?

Nabila tayi salati ta sanarwa ubangiji ta ce, "tab, lallai na tafka kirinSa dana taso nazo, amma bari kawai na tashi na koma gida".

Anan sukayi sallama Nabila ta wuce gida ita kuwa Falila ta shige class, anan ta iske Jabir a zaune, batayi ?asa a gwiwa ba ta?arisa har inda yake ta ce, "Jabir dan Allah miyasa kake fishi dani, ka faWamin"?

Jabir yace "miyasa bazanyi fishi dake ba Falila, kin sani inason ?awarki sosai, mun taso tare tun muna ?uruciya har kawo yanzu, amma kin kasa bani wata muhimmiyar gudumawa da zan shawo kan Nabila a matsayinki na aminiyarta, duk da irin tasarin da ?awaye suke da shi wajen sauya ra'ayi, don haka abun tambaya anan shine, minene aibu na a rayuwa, ki faWa min"?

Falila ta buWi baki ta ce, "Allah sarki Jabir ni ba abinda kamin wallahi, kuma ina maka albishir da cewa Nabila tana sonka, kawai dai ita ta kasance tana da matu?ar alkunya, don haka karka Waurawa kanka presure ka Sata rawarka da tsalle".

Jin hakan yasa Jabir ya Wan saki murmushi yace, "amma gaskiya Falila baki taSa birgeni irin na yau ba, tun farko wannan shine irin abinda ya kamata kina yimin kenan, ki rin?a ?arfafa min gwiwa, sannan kuma kina mutuntani sosai, musamman a gaban Nabila, yin irin haka zai na ?ara tasirin soyayyata acikin zuciyar ta".

Falila ta ce, "indai dan wannan ne angama baka da matsala dani, don haka daga yanzu ma ina mai tabbatar maka da sunanka ya koma Yaya Jabir a wurina".

Kallonta Jabir yayi yana murmushi yace "wallahi har kinsa na rasa abinda zan faWamiki tsantsar farin ciki da kika sani".

Falila ta ce, "haba Yaya Jabir ai kawuce haka, kai dai kawai yanzu katashi le?a wurin lecture mugani ko H.O.D yazo".

"A'a dole kece zaki fara yin gaba, domin banaso mutumin nan ya gan mu tare dake, sabida tsaro badan tsoro ba", cewar Jabir. Anan sukayi sallama suka rabu.

Bayan wata Waya.

Alhaji Alhasan yana zaune a farfajiyar gidan yana shan iska gefe dashi ga Hajiya Jummai suna hirarsu, mai gadi ya shigo ya dur?usa daga nesa yace "Alhaji wani ne yake sallama dakai a waje".

Alhaji yace "to kace ina zuwa".

Mai gadi yatashi ya juya daga baya Alhaji yabi bayansa fitarsa ya iske wani ustaz ne ke zaune a benci tare da mai gadi, ganin Alhaji yasa ya mi?e yace "barka da fitowa Alhaji".

Alhaji ya mi?a masa hannu suka gaisa sosai.

"Ni sunana Malam Idris, nine senior master na islamiyyar su Nabila, wanda yanzu haka ma nazo ne akan magan ta, sabida jiya mun samu takarda na sakamakon musaba?a da aka fitar wanda aka gabatar kwanakin baya na jiha, to cikin ikon Allah sunan Nabila na Waya daga cikin yara uku da sukayi nasarar tsallake matakin jiha wanda ba da daWewa ba zasu halarci national musaba?a. To wannan shine dalilin da yasa hukumar makaranta tayi zama akaga ya kamata a dawo da Nabila islamiyya sannan kuma acigaba da bata horo na musamman, a matsayinta na Waliba Waya tilo da ta taka rawar gani a makarantar mu".

Alhaji ya buWi baki yace "masha Allah, najidaWin jin wannan magana da kazo min da ita, muna fata ku da kuke malamansu Allah ya ?ara muku haza?a, sukuma Allah ya ?ara taimakonsu akan lamarin karatun, Malam Idris nagode, nagode sosai, har gida zan aikama tukwicin wannan albishir da kazo min insha Allah".

Anan sukayi sallama, senior master ya wuce, shikuwa Alhaji ya shiga gida, ya tarar da Hajiya Jummai zaune a inda ya barta, Alhaji ya zauna shima sannan yayi umarni wa Hajiya Jummai "tashi maza ki kiramin Nabila da Ammin ta kuzo tare".

Da "to!" ta amsa ta nufi side Win Laila, bayan wasu ?an mintuna duk kansu suka gurfana a gaban Alhaji suka zazzauna akan garduman dake malale a a farfajiyar wurin tare da cewa "gamu nan munzo Alhaji".

Alhaji ya dubesu yace "to dama albishir zanyi muku, Auta takasance tana Waya daga cikin yara guda uku da zasu halarci national musaba?a na bana insha Allah, Wazun nan wani senior mastern su yazo ya sanar dani, don haka hukumar islamiyya ta amince da Auta zata koma islamiyya gobe in Allah ya kaimu".

Jin hakan yasa Nabila ta juya ta fiskanci al?ibila tayi sujuda domin godiya ubangiji da ya nufeta da yin nasara, bayan ta Wago ta ce, "alhamdulillah".

Hajiya Jummai dake zaune a gefen Auta ta ce, "tabbas wannan nasara ce babba agaremu bakiWaya don haka muna fata Allah ya ?aro dubun nasarori anan gaba, Allah ya miki albarka Auta".

Duk kanninsu suka haWa baki sukace "amin thumma amin".

Alhaji yace "gobe da safe idan Mubaraq yazo kaiki makaranta, kisanar dashi nace ya buWe store na kayan abinci ya Wauki buhun shinka Tyland ya kayi gidan senior master ya haWa masa da dubu Wari injini, wannan tukwicinsa ne na albirshir da yazo yamin".

Nabila ta ce, "Abba amma sai dai gobe free day ne bamu da lecture, hasalima yanzu tesis mukeyi ba kullum muke zuwaba, sai ranan da muke da test nake zuwa nayi na dawo".

"To badamuwa, zan kwatantawa Ubale driver gidan ya kaimasa kawai", cewar Alhaji.

Anan duk kanninsu suka watse kowa yaje ya cigaba da harkokinsa.

Washegari.

La'asar Win fari Nabila ta kimtsa tsaf ta fita ta tafi islamiyya batare da Yaya Mubaraq ba, isar Nabila ke da wuya, hukumar makaranta ta haWa gangamin taron Walibai (assembly), wanda ya haWa da kowa da kowa daga kan Walibai har malamai.

An saurari jawabi daga bakin head master Malam Abbakar, inda ya fara da cewa "yau wannan assembly ya ban banta da sauran irin wanda mukeyi abaya, sakamakon wannan makaranta tamu mai albarka ta taka matakin da darajarta ya ?ara Waguwa a idon duniya bakiWaya. Da wannan nake ?ara jan hankalin Walibai daku Wauki wani darasi da ya faru anan, akan koran Nabila wanda gashi yau ta dawo, sanin kanku ne a tarihi bamu taSa korar wani Walibi kuma ya dawo daga baya ba sai Nabila, wanda itama kuma kwazonta ne da jajircewarta ya jawo mata hakan. Ina kira ga duk kan sauran Walibai daku zamto masu koyi da Nabila, sannan ku zamto masu addu'a akan wannan nasara tamu. Daga ?arshe inayiwa kowa fatan alkhairi".

A daidai nan aka kawo ?arshen assemblyn kowa ya watse, a yayinda Nabila ta koma aji Walibai sukayi dandazo akanta suna taya ta murna akan nasarar da tasamu wanda ta kaita ga samun daman dawowa makaranta, haka dai Nabila takasance cikin annushuwa na tayata murna da ake tayi har aka tashi a makaranta".

Kasancewar Falila bata samu zuwa makaranta ba yasa daga aka tashi batare da Sata lokaci ba Nabila ta kama tafiya ta nufi hanyar gida, akan hanyar Nabila ta tafiya gida ne ta iske wasu mutane a daura da hanya suna tsattsaye a wurin wani mutum mai facin tayu da alamun dai matafiya ne, har bayan Nabila tawuce ta shiga wata kwana da zata kaita gida WoWar taji alamun tafiyar mutum a bayanta juyawarta yace "?an mata barka dai".

Nabila tayi halin ko in kula, ta cigaba da tafiyarta tamkar bada ita yake ba.

Bayyi ?asa a gwiwa ya ?ara cewa "am, ina mai baki ha?uri domin nasani ba kimar ?a mace mai tarbiya ne irinki ta tsaya tana magana akan hanya ba, to amma sai dai nima hakan ya zamemin dole ne agareni, sakamakon daga ganinki jikina ya bani kece mace tagari da na daWe ina ro?on Allah ya bani a matsayin matar aurena. Don haka ko da bazaki tsaya ba dan Allah baiwar Allah kiyi ha?uri ki sanar dani sunanki da kuma inda gidan ku yake".

A fusace Nabila ta juya ta ce, "malam da kata dan Allah, to niba irin wa?an matan bane, da zaka ganni haka kawai kazo kafara min za?in baki, ina kasanni da har kasancewa ni mace tagari ce? To ya isheka haka, karka sake ka ?ara bina".

Nabila ta juya tacigaba tafiya, shima ya bita yana mai cewa "tabbas najidaWi da ki ka?i ala?anta kanki da irin wa?an chan matan, domin nima bana fatan Allah ya haWani da irinsu, amma sakamakon yau ne karo na farko da na fara zuwa garin Gashua a rayuwa, kuma yanzu ma hanya ce ta kawo mu zamu tafi wa'azin ?asa garin Mai Gatari chan bodan Nijar, to ni zan juya daga nan wurin kamar yadda kika bu?aci hakan, ?an uwana suna chan na barsu a baya suna jirana. Abu na ?arshe da zan faWa miki shine ni sunana Sa'ad, ni mutumin garin Damaturu ne, zanje na cigaba da addu'a idan ke alkhair???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i ne a gareni watarana zamu ?ara haWuwa, don haka na barki lafiya".

Nabila wucewa tayi ta?arasa gida da sauri sauri, da shigarta kai tsaye ta nufi Wakinta batare da kowa ya san shigowarta ba, akan gadonta ?irarar 6/7 ta zauna sannan tasa hannu ta buWe side drawer dake jikin gadon nata ta Wauko wayarta ?irar iphone 16 launin ruwan zuma (golden colour), mai Wauke da punch purple, domin ya kasance shine best colourn ta. A take ta kunna wayar ta Wan jira tayi searching ta gama, sannan ta lalimo lambar Falila wanda ta sanyawa my besty ta danna kira, tayi dace kuwa ta shiga ringing Winta biyu Falila ta Waga ta ce, "hello besty".

Nabila ta amsa "hello ya kike"?

Falila ta ce, "lafiiya ?alau alhamdulillah, ya Ammi"?

Nabila ta ce, "tana lafiya ?alau", ta ?ara da cewa "yanzu dawowana a islamiyya kenan, sakamakon yau naga bakije ba yasa na kira ki naji ko lafiya"?

"Wonderful, besty taya akayi suka yarda kika koma islamiyya"? Cewar Falila.

Nabila ta Wanyi ajiyar zuciya ta ce, "ke dai bari kawai labarin yana da tsawo sai in mun haWu, yanzu dai fatan kina lafiya"?

Falila ta ce, "lafiya ?alau, niWin ma tun lokacin da aka dakatar dake naji gabaWaya duk lamarin makarantar ya wanke min araina, shiyasa kawai idan naga Daddy baya nan nake Wan taSa fashi, to amma yanzu tunda Allah yasa kindawo fashi ya ?are insha Allah".

Nabila ta ce, "to masha Allah, Allah yasa mudace".

"Amin", cewar Falila. Sannan ta ?ara da cewa "kinyi waya da Yaya Jabir ne"?

Cikin mamaki Nabila ta ce, "what! Yaya wama ki kace"?

Falila ta nanata "Yaya Jabir".

Nabila ta ce, "lallai sai a gaisheki Falila".

Falila ta ce, "to yanzu dai duk ba wannan ba, akwai papers Win test Winki har guda uku a wurinsa, don haka sai kiyi ?o?arin gobe kafin a shiga test ki sameshi ki karSa".

Da "to!" Nabila ta amsa, sukayi sallama ta katsar da wayar, atake ta mi?e da hanzari ta nufi falon Abbanta, da shigarta ta iske Amminta da Hajiya Jummai duk kansu suna sallan magriba, batare da ta tsaya Sata lokaci ba, ta nufi banWanki tayi alola tazo ta gabatar da sallah, sannan daga bisani suka kafa hira acikin falon wanda ta Wauke tsawon lokaci sunayi kafin suka shiga kowa ta kwanta.

Washegari.

Nabila ta samu halartar makaranta tun saura 1 hour kafin su shiga test Win chemistry 101, amma duk da irin sammakon da tayi taje ta iske Jabir na zaune akan boot Win motarsa, daga nesa Nabila ta hangi Jabir sanye da jarket riga da wandon jeans up and down launin skay blue, kayan sun zauna masa ajikinsa, sakamakon Jabir irin mutane wankan tarwaWan nan ne, ma'ana, shi ba ba?i ba, kuma shi ba fari har chan ba, kai tsaye Nabila ta nufin inda Jabir yake, ta?arisa tayi masa sallama.

Bayan ya amsa sallamar yace "yau jiki yayi sau?i kenan"?

Cikin tattausar murya Nabila ta ce, "eh yanzu kam jiki ya ware alhmdulillah".

Jabir yace "sau?i sosai sosai, ko dai sama sama"?

Nabila ta Wan saki murmushi ta ce, "sau?i sosai sosai".

Jabir ya ?ara da cewa "yanzu kina nufin idan muka tsera dake daga nan zuwa labry zaki iya wuce ni"?

Nabila ta Waga kai ta Wan gallawa Jabir kallon gefe ta ce, "taya ina matsayin soja kana civilian zakace zakayi tsere dani, lallaima ashe zaka sha bulala kenan".

Yanayin maganan da Nabila tayi yasa Jabir yaji ya tsinci kansa cikin shau?i, wani murmushi na musamman ne ya bayyana a fiskarsa, ganin hakan yasa Nabila ta ce, "oh, dariya ma nabaka ko"?

Atake Jabir ya haWe fiska, ya Wan ?ame hannayen sa yace "easy, permision to carry on".

Ganin yanayin yadda Jabir ya ?ame yasa wata irin dariya mai tattare da nishaWi ta kwacewa Nabila wanda har sai da ta buWi baki ta ce, "amma wallahi ba?aramin dariya kasani ba".

Jin hakan yasa Jabir yace "haka nakeso dama kullum na ringa ganinki cikin farin ciki".

Nabila ta Wanyi shiru ta ce, "miyasa kakeso ka ringa ganina cikin farin ciki"?

Jabir yace "sabida ina sonki Nabila".

Nabila tayi shiru, chan ta Wanyi ajiyar zuciya ta ce, "amma miyasa kake sona"?

Jabir yace "dalilaina suna da yawa, amma ga kaWan daga ciki kamar yadda yazo mana a cikin koyarwar manzon Allah (s.a.w). 1.ina sonki sabida asalinki, ke ?ar dattawa ne wanda kowa ya san haka a garin nan. 2.sabida tarbiyarki. 3.sabida ilimin ki. Duba da iya wa?an nan abubuwa guda uku kaWai sun isheni hujja akanki har a gaban Allah, domin na tabbata ?a?anki nan gaba zasuyi alfahari dake amatsayin mahaifiyarsu".

Nabila ta ce, "to naji kuma nagode, amma inaso kabani lokaci zanyi shawara, duk abinda na zartar zan sanar dakai insha Allah".

Jabir ya buWi baki yace "Nabila dawa kuma zakije kiyi shawara, bayan wannan abune wanda ya shafeki a karan kanki"?

Nabila ta ce, "bada kowa zanyi

4 / 12