Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   6 / 12

15K to 18K   out of 33.5K words

tabbatar miki kuwa yau da kinsha bulala kinyi kukan da gaske".

Cikin shagwaSa Nabila ta ce, "uhm, uhm, Malam bulala fa kace"?

senior master yace "ke wuce nikam mutafi dan Allah, musamu mu koma gida".

Damaturu, Yobe State.

Sau?arsu kenan a filin tashi da sau?ar jirgi na Damaturu, Alhaji da ahalin gidansa bakiWaya harda ma Aunty Na'ima da Aunty Basira tare da ?a?ansu Ubale ya Waukosu acikin wata mota doguwar bus ?irar coaster, ya kawosu air port domin tarbar Nabila da senior master, suna sau?a a jirgi duk kansu suka yanyan me Nabila tamkar zasu haWiye ta tsantsar farin ciki, da haka suka Wunguma suka shiga mota har gida, anan suka tarar da Yaya Garzali da Yaya Mubaraq suma sunata kai kawo a tsakanin kitching zuwa babban falon gidan.

Wata irin liyafa ta alfarma aka shirya, wanda ta ?unshi zallan nama ne kawai, sai kuma kindirmo da zuma da aka haWesu wuri guda aka damasu, tsarin liyafan an shirya tane tsarin Webi da kanka, wannan ya bada dama a senior master ya zage yayi cin yaushe gamo a naman wani ban?arraren rago da aka tura masa gabansa.

Bayan anci, an sha, kuma anbatse senior master yace "to masha Allah", ya dubi Alhaji ya ?ara da cewa "Alhaji Allah ya ?ara arzi?i kawai zamuce, ke kuma Nabila Allah ya miki albarka, nikam inaso zan wuce gida kuma".

Alhaji yace "amin ya rabbil alamin senior master, babu abinda zamuce face Allah ya saka muku da gidan aljanna dangane da ilimi da kuke koyarda yara, muna godiya sosai, kuma insha Allah da kaina zanzo har makarantar taku".

Senior Master ya mi?e Alhaji yayi masa rakiya har hararbar gidan, sannan yayi umurni a Ubale da ya kaishi gida, shikuwa Alhaji ya juyo ya dawo falon a yayin da Alhaji yayi sallama, kowa ya risina suka amsa masa, sannan ya nemi wuri ya zauna gefe da Nabila.

Aunty Basira ce, ta buWi baki ta fara da cewa, "Hajiya Nabila kamar yadda kika ganmu mun haWu a wannan wuri ?wan mu da ?war?wata duk mun haWune dominki, badan komai ba sai dan mutayaki murna a matsayin mu na ?an uwanki, don haka muke fatan Allah ya ?aro dubun nasara". Duk kanninsu da suke cikin falon suka haWa baki sukace "amin thumma amin".

Nabila ta ce, "Aunty Basira, Hajiya Nabila fa naji kin kirani"?

"Eh mana", cewar Aunty Na'ima da ke gefen Yaya Mubaraq.

Nabila ta ce, "a'a gaskiya, zuwa Saudiyya aikin hajji bana bai kamani ba, Ammina ita tafi chanchanta taje a madadina, don haka nabata kyautar kujerar hajjin".

Jin hakan yasa Ammin Nabila dake zaune daf da Hajiya Jummai, kwalla ya fara fita daga idaniyanta, sannan tayi salati ta ce, "Alhaji kaji fa abinda Nabila take cewa, ya kake ganin wannan lamarin"?

Alhaji ya Wan numfasa yace "eh wannan aiba wani abu bane, yadda ta faWa Win hakan kawai za'ayi insha Allah, ita kuma daga baya in Allah yasa ta tafi jami'atul Madina ai zatayi aikin hajji kam".

Laila kawai ta ?ara Sallewa da matsanancin kuka, wanda ya janyo duk hankalin kowa ya koma kanta suna masu bata ha?uri, tana mai share hawaye Laila ta ce, "kubarni kawai nayi kukana na more, domin kukan daWi nakeyi, abinda na jima ina mafarkine yau ya tabbata min a zahiri".

Alhaji Sha'aban.

Mutane ke chinchirindo babu dare babu rana a wani katafaren gida dake tsakiyar federal lowcost a garin Gashua, ankwashe tsawon shekaru Alhaji Sha'aban yana hidimtawa al'umma a duk lokacin da ya kasance yana ?asa Nigeria, ta hanyar ciyar da bayin Allah abinci har ma da kuWi na bu?atun yau da kullum, abune wanda yayi ?aurin suna ata wannan Sangaren birni da ?auye kowa yana alason barka, kamar ko yaushe dai, yau ma Alhaji Sha'aban ya samu dawowa gida lafiya, kuma cikin ikon Allah da yardarsa ya Waura daga inda ya tsaya.

Bayan Kwana Uku.

Nabila zaune take tana ?o?arin sanya lalle a ?an yatsunta, shigowar kiran waya taji, batare da ta duba suna ba, ta Waga ta kara wayar a kunnenta, cikin tattausar murya taji ance "hello besty".

"hello besty", cewar Nabila itama.

Cikin shau?i Falila ta ce, "besty kice Allahu akbar".

Nabila ta ce, "Allahu akbar, miya faru"?

Falila ta buWi baki ta ce, "wato H.O.D ya daWe yana yaWa Sarna a makaranta, amma dubunsa ya cika, kin san yarinyar da ya bata class rep bayan Yaya Jabir ya ajiye Win nan, itace tayi ciki tajeta wurin zubarwa a Damaturu, ashe likitan yasan babanta sakamakon babban mutum ne a garin Gombe, shine ya kira shi a waya ya sanar dashi halin da ?arsa take ciki a yanzu haka a Damaturu, Wazu kawai mun tashi a makaranta mun fito bakin gate, sai ga hukumar D.S.S sunyi ram da H.O.D, atake suka sanya masa sar?ar hannu suka jefa shi a mota suka tafi".

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Cewar Nabila, ta ?ara da cewa "amma wannan labari na cike da ban tausayi gaskiya, sakamakon yaci zarafin yarinyar nan, tunda a ?alla yanzu H.O.D zai kai shekara 50, wanda ita kuma yarinyar nan ko shekara 20 bazata kai ba, amma ya ruWeta yayi mata irin wannan aika aikan, tun tana matakin aji Waya a jami'a har tasan taje ta zubar da ciki to ya kike tunanin kafin muje aji biyar adadin yara nawa zata kashe ta hanyar zubar da ciki bisabilillahi"?

Falila ta Wanyi shiru sannan ta ce, "uhm, gaskiya dai abun kam bayyi tsari ba, domin kowani irin hukunci aka zartar masa a yanzu ya riga da ya gurSata mata rayuwa, aikin gama ya gama, don haka nake ganin hukuncin irin wa?an nan gurSatattun mutanen acikin al'umma shine kisa, amma muna fatan Allah ya ganar dasu sugane gaskiya, idan kuma bamasu shiryuwa bane to Allah ya haWa ire irensu da masfar da tafi ?arfinsu tun anan duniya".

"Amin ya Allah", cewar Nabila.

Falila ta ce, "yanzu dai koma miye sai zuwa gobe, sakamon gobe ne sati biyu cif da gama rubuta exam Winki, kuma a yanda suka faWa gobe ne zasu fidda result Winki, don haka muna fatan Allah yasa muga alkhairi, kuma zanyi iya ?o?rina domin naga direban mu ya biyo dani ta gidanku, sabida nazo nabaki cikakken bayani akan yadda duk lamarin ya kasance insha Allah".

Nabila tana mai godiya sukayi sallama, ta katsar da wayar.

Bayan Nabila ta katsar da wayar ta cigaba da chanchaWa lallenta wanda ya Wauketa tsawon lokaci kafin ta samu ta kammalashi, sannan ta ?ara jira na tsawon wasu mintuna daga bisani ya bushe ta wanke shi, a yayin da dare har ya Wan fara shiga lokacin, da?yar Nabila ta ?o?arta ta haWa sallah magriba da isha'i ta kwanta, wanda ba ita ta tashi ba tsantsar gajiya har sai da gari yayi haske sosai, alamun rana ta fara fitowa tukun Nabila ta samu daman tashi ta fito ta fara ?o?arin yin alola domin yin sallar asuba, a gurguje Nabila ta sanu ta gabatar da sallar sannan ta koma Wakinta ta haWa kakkauran shayi, tajawo wani bredi a cikin lokarta wanda ya samu isashen bota da kwai, ta karya kumallo dasu, daga bisani da ta Wan huta ta Waura dayin tilawar alqur'ani mai girma. Nabila tana cikin tsaka da tilawa batayi aune ba, kwatsam taga Falila ta shigo Wakin batare da tayin sallama ba, tana mai cewa "albishirinki besty".

Nabila ta ce, "goro fari tas tas".

Falila ta Wan saki jikinta daga tsaye ta faWo akan Nabila ta ce, "an manna result Winki kuma kinyi passing exam Winki duka, sannan kuma an manna ankori H.O.D".

Nabila ta ce, "masha Allah, nagodewa Allah dama kullum sai nayi ?iyamullaili na kayi kukana wa Allah akan wannan lamarin, a gaskiya najidaWi sosai kuma ina fata Allah ya ?ara bamu ikon tsare mutuncin mu".

"Amin", cewar Falila. Ta ?ara da cewa "to daman kisa aranki gobe sai makaranta in Allah ya kaimu", sannan ta mi?e tana mai cewa "nikam zan wuce domin dakyar na samu direban mu ya yarda ya biyo dani ta wurinki".

Dubanta Nabila tayi ta ce, "daga zuwa kamar ana korarki sai tafiya, dama ina cike dake domin tunda nadawo daga Abuja baki le?o gidan nan ba".

Falila ta ce, "haba besty kefa kinsan yadda tsarin gidan mu yake, ba a taSa barin mu mufita inba dalilin makaranta ba, kuma na tambayi Ummi nah inaso zanzo wurinki lokacin da kika dawo ta cemin nabari zata tambayi Daddyn mu sai muzo tare da ita, ?arshe kuma haryanzu bata ?arayi min maganan ba, don haka koma miye kiyi ha?uri kiWauka yawuce kawai, bari in samu naje kar ya gaji da jirana, sai mun haWu gobe a school".

Washegari.

Nabila tun tashinta da asuba bata koma bacci ba, tanata ?o?arin kintsawa domin tafiya makaranta, cikin ikon Allah kuwa ta samu ta kammala kintsawarta tsaf akan lokacin da ya dace, kasancewar Yaya Mubaraq bai san da zuwan Nabila makaranta ba yasa ta fita domin hawa taxi, isarta akan babban layi tayi dacen samun taxi direct har University, anan tashiga ya kaita har bakin gate sannan ta sau?a ta sallameshi yawuce itakuwa ta shige cikin makaranta.

Nabila tana cikin tafiya, Jabir ya taho ya tare gabanta da mota yayi parking, sannan ya buWe ?ofa ya fito yayi mata sallama, bayan ta amsa Jabir yace "malama tah".

Nabila cikin tattausar murya ta ce, "niba malama bace, domin bankai matsayin malama ba".

Jabir ya Wan saki murmushi yace "haka dai kikace, amma nikam ai naga zahiri a gidan tv inda balarabiya take bayyana sunanki a matsayin gwarzuwar data lashe gasar karatun alqur'ani mai girma, don haka ya tabbata ke malama ce".

Nabila ta Wanyi ajiyar zuciya ta ce, "to gaskiya nikam bani bace sai dai ko in sunan mune yazo Waya da wanda kaji".

Jabir yayi dariya yace "kedai my dear, kullum ba arabaki da zolaya", sannan ya ?ara da cewa "to yanzu dai duk ba wannan ba my dear, Daddy nah ya dawo a satin da ya gabata, kuma kinsan tsawon shekaru munatare da juna duba da wannan nake ganin anzo matakin da yakamata kibani dama nayi magana da Daddy nah yaje ya samu Abbanki akan maganan auren mu, sakamakon karmu yawaita soyewa har mu ?one gabaWaya".

Jin hakan yasa Nabila har sai da takasa Soye dariyarta ta fito da ita fili sannan ta ce, "to in banda abunka ba, aiko Laila da Majunun ma basu ?one ba ballantana mu".

Jabir yace "lallai ma my dear wai yanzu kina nufin bamu fisu ba kenan"?

"Eh", cewar Nabila, ta ?ara da cewa "amma dai insha Allah inasa ran in mukayi aure zamu fisu, domin ina maka tanadi na musamman, abu na biyu kuma shine, kamar yadda kayi maganar tura magabatanka gidan mu wannan abune mai kyau, amma sakamakon a satin nan Ammina zata tafi Saudiyya zanso kaWan dakata tukun har sai in Allah ya dawo da ita lafiya".

Jabir yace "to bakomai, fatan mu shine Allah yakaisu lafiya ya dawo dasu lafiya, yasa kuma muna raye lokacin malama tah".

"Amin ya Allah habibi nah", cewar Nabila.

Duba da yanayin lokacin lecture yayi daga nan Jabir ya bu?aci Nabila da tashiga motar su?arasa class, da farko dai Nabila ta?i amincewa daga bisani kuma ta amince ta shiga sukatafi.

Bayan Nabila Tadawo Gida.

Kai tsaye ta wuce side Win Amminta, a yayin da taje ta isketa tana tattare kayan sawanta daga cikin wall drof tana shishiryasu acikin akwati, Nabila ta zauna tayi shiru ta zurawa Amminta ido har sai da ta dakata da aikin, ta?ariso daf da ita ta ce, "Nabila lafiyarki kuwa, miyake damunki"?

Nabila ta ce, "Ammi wato?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? a duk lokacin dana tuna zaki tafi kibarni, sai naji duk jikina ya mutu, sakamakon ina tuna irin kaWaicin rashinki da zanyi, domin tunda na taso bantaSa rabuwa dake na tsawon kwana biyu ba, gashi yanzu kuma zaki tafi tsawon wata guda, amma dai ni daWin da nakeji kawai shine, zaku dawo lokacin muna hutu inyaso sai ki tambayi Abba ya barmu ki kaini muje naga ?an uwanki ko"?

Ammin Nabila tayi shiru harna ?an da?i?a sannan ta ce, "Nabila nima da kike ganina ban san kowa nawa a duniyar nan ba, sakamakon na tashi na buWi ido kawai na ganni a gidan marayu, anan na girma har nakai munzalin aure, a lokacin ne aka dam?amin file Wina a hannuna naga asalin yadda akayi na tsinci kaina a gidan a rubuce. Watarana ?an sanda guda biyu suka kayini gidan marayu tare da likita guda Waya tun ina kwana Waya da haihuwa a duniya, jami'an tsaron da likitan sun shaidawa hukumar gidan marayu cewa, mahaifiyata ta kawo kanta haihuwa ne asibiti batare da wani Wan uwanta ba, kuma da alamun mutumiyar ?auye ce, gashi kuma bayan ta haifeni Allah ya karSi rayuwarta sanadiyar yoyon jini da ya?i yatsawa, wannan dalilin yasa sukayi ?o?arin yaWa hotunanta ko Allah zai Sullo da wani Wan uwanta, amma shiru ba labari, shine sukayi jana'izarta nikuma suka yanke shawarar kaini gidan marayu dake garin Damaturu, wanda yake ?ar?ashin kulawar bayin Allah masu hannu da shuni, wanda daga cikin attajiran da suke tallafawa ake kula da wajen har da mahaifinki Alhaji Alhasan. Abisa tsarin wurin kuma duk shekara akwai bikin yaye Walibai marayu da ake haWawa na sau?ar alqu'ani mai girma tare da aurar da wasu daga cikin marayun. A shekarar da mukayi sau?ar karatune mahaifinki na daga cikin manyan bakin da suka samu halartar wurin, anan ya ganni yace yana sona zai aureni, to kasancewar ni marainiyace babu uwa babu uba yasa hukumar gidan marayu ta bashi aurena aka Waura a wurin, ya Waukoni a matsayin matarsa ya taho dani gidansa, munkwashe tsawon shekauru biyu munatare Allah ya nufa na haifeki. To kinji wannan shine ta?aitaccen tarihina wanda bantaSa sanar dake ba sai yanzu".

Atake Nabila ta fashe da kuka, wanda ta kwashe tsawon lokaci ta nayi batare da Amminta ta bu?aci ta daina ba, duban Amminta Nabila tayi tana mai kuka ta ce, "tabbas Ammi kin fiskanci ?alubale a cikin rayuwarki", da sauri Ammin Nabila ta tari numfashinta ta ce, "Nabila karkina faWin irin haka, domin kowa da kike gani a wannan duniyar yana rayuwa ne gwargwadon abinda Allah ya tsara masa, don haka karki kitaSa saka damuwa aranki akan lamarina kawai addu'a ne zamuyitayi Allah yasa mudace duniya da lahira".

Nabila ta ce, "amin thumma amin".

Jabir.

Sallama Jabir yayi sannan ya bankaWa labule, "wa'alaikumussalam", cewar Daddyn Jabir dake zaune a cikin katafaren falon tare da Mummynsa, Daddyn Jabir yace "Jabir zo mana, wai ni miye yake damunka ne tun dawowa na nake ganinka kamar ba lafiya sosai"?

BuWan bakin Mummyn Jabir ta ce, "ai Jabir yanzu ya zama Wan soyayya shiyasa, baza kagane masa ba, domin yanzu soyayya kawai ya keyi babu kama ?afar yaro".

Cikin mamaki Daddyn Jabir yace "ya salam, da ?ar gidan waye haka Jabir yake tare"?

Mummyn Jabir ta ce, da Nabila ce, yarinyar Alhaji Alhasan".

"ohhhh, ha'a Nabilan kam har tagirma haka"? Cewar Daddyn Jabir.

Mummyn Jabir ta ce, "Nabila ai yanzu ta zama budurwa sosai, kuma yarinyar gata da nutsuwa ga ilimi".

Daddyn Jabir yace "ikon Allah, to badamuwa yaran Alhaji Alhasan kam ai ?a?ana ne nima, don haka ka kwantar da hankalinka Jabir, sakamakon akwai wasu kayana da aka kirani a waya Wazu ake faWamin an kama a gaSar kogin Itali zuwa gobe da sassafe zanbi jirgi naje wurin kayan, idan Allah yasa na dawo lafiya, sai naje na samu Alhaji Alhasan muzauna muyi maganan aurenku ko"?

Cikin annushuwa Jabir ya dubi Daddynsa yace "to Daddy nagode sosai, Allah ya kaika lafiya yasa kadawo lafiya". Duk kaninsu suka haWa baki sukace "amin".

Falila.

"Yau besty lafiya na ganki da sanyin safiyar nan a gidan nan"? Cewar Nabila.

Falila ta ce, "lafiya ba lafiya ba, sakamakon gaskiya nifa tunda akasa ranar sau?ar karatun mu, kwata kwata bana cikin natsuwa".

Cikin firgici Nabila ta ce, "ban fahimce kiba besty"?

Falila ta ce, "ina nufin ina cikin matsananciyar matsala ce, domin ranar sau?ar karatun mu ya tabbata za'a Waura aurena da Malam Kabir, tunda har an buga invitation, amma ina mai tabbatar miki har yau Win nan, ni bantaSa tsayuwa da Malam Kabir a matsayin hira ba, sannan kuma bamu taSa yin waya dashi da sunan hira ba, gashi duk wani tsari na al'adun mu na hausawa Daddyna ya hana ayi min, bugu da ?ari ni bansan wata sana'ar da yakeyi ba bayan koyarwa a islamiyyar mu, to dan Allah yanzu a irin wannan zamani da muke ciki komai yayi tsada ma'aikatan gwamnati suna kuka da lamuran rayuwa haka zalika ?an kasuwa suma suna kokawa, to balle kuma malamin islamiyya. Shin zamuci ustazanci ne kam, kidai dubamin wannan lamarin"?

Jin hakan yasa Nabila ta ce, "hm, Falila kenan, abinda nakeso kigane anan shine, hira ko yin waya ga masoya bashi da wani tasiri a cikin auratayya, hasalima idan sukayi yawa acikin soyayya Sarna suke jawowa, ko ta hanyar aikata alfasha na maganganun banza acikin wayar ko kuma a zahiri, kuma yawaita haWuwa da juna yana haifar shau?uwa mai tsanani irin wanda ake iya wuce gona da iri kuma kiga an Wauki hakan ba abakin komai ba, domin ana ganin ta irin wa?an hanyoyin ne za a tabbatarwa juna da soyayya a tsakani. Abu na biyu kuma shine, karki kuskura kiyi tawaye a iyayenki akan wannan lamarin domin wallahi in har kika?i zaSinsu to duk wanda kika aura kisa aranki bazaki taSa jin daWin zaman aure dashi ba, ke kam sai dai kiji wasu mata suna bada labari, amma babu tayadda za'ayi kiyi nasara alhali kina tare fishin iyayenki".

Kuka Falila ta shigayi tana mai cewa "irin wannan rayuwa ina zansa kaina ne, wallahi da duk ganin lamarin nakeyi kamar wasa, to yau gashi an wayi gari aurena bai kai sati uku ya saura ba, har zuwa yanzu babu wani shirye shirye da aka fara gudanarwa".

Nabila ta buWi baki ta ce, "wannan duk ba abun damuwa bane, kedai kawai addu'a zakiyi tayi, sai kiga abun ya zame miki alkhairi, amma maganan bijirewa iyaye arayuwa ba wannan maganar, domin duk wanda kikaga yayi nasara a cikin rayuwarsa to yabi iyayensa sau da ?afa, sannan a duk lokacin da iyeyen mutum suke fishi dashi to Allah (swa) da kansa yana fishi da mutum, duk kannin wani Wan Adam yana samun cikakken yarda ne a wajen Allah ta hanyar samun yardar iyayensa, don haka kawai kibi iyayenki akan duk abinda suka zaSamiki wanda baisaSawa Allah ba'.

Batare da Falila tace uffan ba, Nabila ta ?ara da cewa "abinda za'ayi yanzu kitashi muje nasa Ubale ya mayar dake gida, karma kidaWe sosai ran Umminki

6 / 12