Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   2 / 12

3K to 6K   out of 33.5K words

mai cewa "sadaka fa Daddy na ya ba dani kenan"?

Nabila ta ce, "Falila kenan, to miye sadakan"?

Falila ta ce "wallahi ni yanzu duk ustazain duniya ma na tsanesu, duk munafukai ne".

Dubanta Nabila tayi ta ce, "haba Falila miyasa kike furta irin wa?annan munanan kalaman, ya kamata kisani Daddyn ki bazai taSa zaSa miki abinda yasan cewa zai chutar dake ba, domin iyayen mu da kike gani sunfi son farin cikin mu akan nasu, shi auren mutumin kirki yana da matu?ar tasiri babba, tayiwu sai anan gaba zaki fahimci tasirin hakan. Misali Waya kuma da zanyi miki shine, ya kikeji aranki idan kika tuna cewa Daddyn ki shine chief imam na gabaWaya garin nan? Wallahi ko baki faWa ba nasani kina jindaWin kasancewarki ?ar limamin garin nan. Don haka idan duk garin Gashua za acika miki da kayan lefe da sauran kayan ?yale ?yalen duniya idan baki auri mutum nagari ba wallahi ya zama aikin banza, don haka Falila ya kamata ki natsu kidawo hayyacinki, ki yawaita askar da karanta alqur'ani domin akwai shairin shaiWan a cikin lamarin kin nan, duk kinbi kinsa kanki damuwa kin rame kinfita a hayyacinki".

Jin hakan yasa Falila ta ce, "haba Nabila kefa kinsan ina da wanda nakeso, amma miyasa bazaki tausayamin ba"?

Nabila ta ce, "kullum zaSin mafi alkhairi muke nema a wurin Allah kuma tunda kikaga an bada aurenki a Malam Kabir to ki Wauka kawai shine mafi alkhairi agareki kizamto mai biyayye game da zaSin iyayenki, sannan kuma kina addu'a Allah ya tabbatar muku auren da alkhairi a cikinsa, kiyita ?o?ari kiga kincire soyayyar duk wani saurayinki a ranki sai kiga kin zauna lafiya".

Ana cikin haka Malamin hadith ya shigo, atake kowa ya mi?e tsaye suka gaishe shi, bayan kowa ya zauna ya hangi Nabila yace "kai kai, Nabila ke daga ina haka, rabonki da ajin nan tun muna hadith na 87 yanzu yau har zamu shiga na 130 tukun kike dawowa, to tabbas dole zaki fiskanci hukunci mai tsanani, don haka kitashi ki fita waje".

Batare da Nabila tace uffan ba, ta tashi ta fita ta zauna a bakin barandar ajin, har lokacin tashi yayi suka fito, anan ne Malamin hadith ya samu Nabila ya ?ara da cewa "Nabila lallai kitabbatar gobe idan za kizo kintaho tare da wani babba daga gida". "To! Malam", cewar Nabila.

Sannan ta juya ta kama hannun Falila dake tsaye a gefen ta cikin tattausan murya Nabila ta ce, "besty ina mai ?ara baki shawara ki saki jikinki dan Allah, a wannan zamanin mata da dama rashin samun nagartattun mazaje shiyayi sanadiyar salwantar rayuwarsu. Don haka ina tayaki murnar samun Malam Kabir a matsayin miji, domin ina da ya?inin zai kulamin dake insha Allah".

Duk da irin tasirin kalaman Nabila, basusa farin ciki ya bayyana a fiskar Falila ba. Amma Nabila batayi ?asa a gwiwa ba ta dafa kafaWar Falila ta ce, "besty wai ke ko kinfi so kiji ana kiranki da matar Alhaji ne, ba matar Malam ba? To duk dai damuwarki nasan bazatawuce kiga kuna Wan fita outting kuna Wan tafiya honey moon dadai sauransu ba, to duk ki kwantar da hankalinki idan Allah ya horewa Malam babu abunda bazaiyi miki ba, sakamakon indai magana ake ta soyayya to ustazai ma?ura ne wajen nuna kulawa da iya soyayya, don haka kinyi nasara nake faWamiki tawan sa hannu mukashe".

Ajiyar zuciya Falila tayi tare da alamun murmushi da ya bayyana a fiskarta ta ce, "uhm! Besty ke kam Allah ya shiryeki wallahi".

Suna cikin tsaka da tattaunawa sai suka hangi shigowar motar Yaya Mubaraq.

"Kinga chan Yaya Mubaraq yayi birki, bari na ?arisa na sameshi nikam mukwan lafiya", cewar Nabila. "To Allah ya tashemu lafiya besty".

Anan Nabila ta wuce ta bar Falila a wurin, tana tsayuwar dakon mai zuwa Waukarta itama. Nabila ta ?arisa inda Yaya Mubaraq yayi parking ta buWe motar tayi sallama ta shiga ya amsa "wa'alaikumussalam", sannan ya tada mota suka fara tafiya.

Bayan sun kwashe tafiya mai tsawo batare da sunyi magana a junansu ba Nabila ta ce, "oh Yaya Mubaraq yau fa Wazu da Malamin hadith Win mu ya shigo aji korata yayi da zaiyi darasi, ?arshe ma bayan ya kammala darasin da ya fito cemin yayi sai najeni da wani babba daga gida, basa bu?atar na ?ara zuwa ni kaWai".

Yaya Mubaraq yace "babbar magana kenan, to abinda nakeso dake shine ba sai kin sanar da Abba ba, gobe idan Allah ya kaimu kiahirya kawai idan na kaiki islamiyyar sai nayi magana dasu".

Batare da Nabila tace komai ba Yaya Mubaraq ya ?ara da cewa "ai Wazu bayan na ajiyeki a islamiyya na koma gida Abba ya aikeni nakai takardunki a Baffa Saminu, ashe dama biochem kika cika cika a jamb Winki"?

Nabila ta ce, "eh mana, Yaya kamanta ne, ai da ina da burin na zama likitar yara ne, to sakamakon babu course a Uni Gash yasa Abba yace min lallai sai dai na chanja na zaSi wani course wanda akeyi a Uni Gash domin bazai lamince na tafi karatun jami'a nesa ba, sai dai na jona Uni Gash ina zuwa ina dawowa kullum yana ganina. To kaji wannan shine dalilin da yasa na zaSi biochemistry".

Suna cikin tsaka da zance kawai suka iso gida, kasancewar magriba ta kawo kai Yaya Mubaraq yana ajiye Nabila ya juya ya nufi masallaci, ita kuwa Nabila ta wuce cikin gida ta ajiye jakar islamiyyan ta cire hijaf Winta tayi haraman alola, bayan tayi alola ta koma falo tayi sallah a yayin da kammala askar Winta yazo daidai da kammala tuwon shinkafa miyar kuSewa da Hajiya Jummai ta girka a lokacin taci tuwon ta Waura da tilawa, kafin daga bisani tayi sallar isha'i ta kwanta tayi bacci.

Washegari
Da sassafe Nabila ta shirya abun karya kumallo, daga bisani tayi wanka ta chanchaWa kwalliya ta fito ta zauna a falo tana jiran fitowarsu Abban ta, kafin daga bisani suka fito Nabila ta gaishesu Waya bayan Waya kamar yadda ta saba, sannan ta ?arisa dining table tayi serving Winsu suna masu raha a junansu sukayi break fast suka gama.

Haka Nabila ta cigaba da sauran ayyukan cikin gida har lokacin tafiya islamiyya yayi tayi wankanta ta shirya tsaf abinta ta zauna tana tsumayin zuwan Yaya Mubaraq ya kaita, jim kaWan sai ga Yaya Mubaraq ya shigo batare da Sata lokaci ba Nabila ta fito ta shiga mota suka nufi islamiyya.

Isarsu ke da wuya Yaya Mubaraq ya umurci Nabila da ta zauna a cikin motar, shikuwa ya fita ya ya nufi staff room dake daura da ofishin prinspal, sallama yayi ya shiga ya tarar da tarin malamai a zazzaune kowa da abunda yake gudanarwa, wasu nayin marking Win takardun yara wasu suna duba roster.

Senior Master

Wa'alaikumussalam, bayan sun amsa sallamar Waya daga cikin malaman dake zaune akan wata babbar kujera wanda shine senior master a makarantar yace "sannu da zuwa, bismillah ga wurin zama", yana mai nuni da ?ar yatsar sa.

Ya zauna ya fara da gabatar masa da kansa "sunama Mubaraq A Alhasan, ni Yaya ga Nabila, nazo ne domin jiya da ta koma gida ta sanar cewa akwai malamin su na hadith da yace da ita ta turo wani babba daga gida".

Senior Master yace "eh hakane, sakamakon idan kaduba jikin form Win makarantar nan zakaga Walibi idan yayi fashin sati guda a jere batare da wani kwakkwaran dalili da hukumar makaranta ta sandashi ba to lallai Walibin ya kori kansa duba da yanayin yadda muka tsara salon koyarwan mu, to ita kuma Nabila an wayi gari ta kwashe sama da tsawon wata guda bata zuwa makaranta, don haka duba da wannan doka hukumar makaranta ta kori Nabila bisa laifin karya doka".

Numfasawa Yaya Mubaraq yayi yace "to amma Senior Master babu wata alfarma da za'a iyayi mana akan hakan, ayi ha?uri ta dawo karatu"?

Senior Master yace "ina ai wannan doka ce wanda duk makarantar nan babu wanda ya isa ya karya ta, ha?uri kawai zakuyi".

Yaya Mubaraq ya Wanyi shiru chan yace "to ba matsala shikenan mungode", sannan ya mi?e ya juya yace da sauran malaman dake cikin staff room Win "to sai anjiman ku".

Fitowa yayi ya tarar da Nabila zaune kamar yadda ya barta acikin motar, shiga yayi ya ta da motar batare da yace mata komai ba suka nufi gida.

Isarsu gida sukayi dacen iske Abbansu ya dawo gida yana zaune tare da mai gadi a ?ofar gida, Yaya Mubaraq yayi parking suka fito ya ?irge ma Abbansu duk yadda sukayi da Senior Master, shiru Abbansu yayi na ?an da?i?a daga bisanin ya numfasa yace "to Allah yasa haka shi yafi alkhairi". Duk kanninsu suka haWa baki sukace "amin ya Allah".

Cikin sanyi jiki duk kansu suka shiga gida Nabila kai tsaye taje ta zube akan Aminta dake zaune a wata garduma a farfajiyar gidan ta fara kuka tana mai cewa "wayyo shikenan Ammi nikam bazan cika burina na sau?ar alqur'ani mai girma da nasa a gaba ba, yau kam an koreni a islamiyya".

Duban Yaya Mubaraq dake tsaye a gefe Ammin Nabila ta juya tayi sannan ta ce, "Mubaraq wai miyake faruwa ne"?

Mubaraq yace "wato an samu matsala ne sakamakon daina zuwa islamiyya da tayi na tsawon kwanakin da Abba ya hanata zuwa, sabida hakane sukace bazasu amince taciaba da zuwa ba, sai dai a nema mata wata makarantar".

Jin hakan yasa Ammin Nabila ta ce, "ayya to kiyi ha?uri kiyi shiru haka Auta, batun yin sau?ar karatu insha Allah zakiyi, domin nasan Abbanki zai kaiki duk irin islamiyyar da kikeso insha Allah, dan haka ke dai kiyi fatan Allah yasa haka shi yafi alkhairi kawai".

Haka dai Ammin Nabila tacigaba da shafa kuncinta dake kan cinyoyinta tana yimata nasiha tana rarrashinta har sai da taji anfara kiran sallan magriba sannan ta umurce ta da ta tashi domin yin sallah.

Tsawon kwana biyu Nabila ta kwashe tana cikin matsanancin hali, damuwa ta bayyana a fili a tattare da ita farinciki ya ?aurace mata, hatta abinci sai dai taci sama sama badan tanajin daWinsa ba ganin irin yanayin matsanancin halin da Nabila ta tsinci kanta aciki yasa hankalin kowa ya tashi a gidan ba yama Alhaji da yake ganin shi yayi silar faruwar hakan.

Akwana atashi watarana Alhaji ya fita kasuwa sai gashi ya dawo gida ba a lokacin da ya saba dawowa ba fiskarsa cike da annuri ganin dawowar Alhaji da kuma irin yanayin da ya shigo cikin gidan ya tarar da Hajiya Jummai da Laila a falo ya basu mamaki sosai.

BuWar bakin Alhaji yace "ina Auta"?

Ammin Nabila ta ce, "tana chan side Winta tana kwance".

Alhaji yace "maza Wanje ki kirawo min ita". Da "to!" Ammin Nabila ta amsa, sannan tawuce side Win Nabila, batare da Sata lokaci ba suka dawo tare Nabila ta ?arisa ta dur?usa a gaban Abbanta ta ce, "gani Abba".

Alhaji ya fiddo da hannunsa dake cikin babbar tigarsa Wauke da wani file ya mi?ashi a Nabila yace "gashi ri?e wannan Auta takardan admission Winki ne aciki tare reciept Win school fees Winki gabaWaya, don haka inaso dake gobe ki ?o?arta kifara zuwa makaranta, sakamakon yanzu haka ma lectures ya fara nisa, lamarin ?arfin jikin naki kuma idan kina zirga zirga shi zai baki daman ki warware gabaWaya insha Allah, sabida haka ina miki fatan alkhairi, kidage sosai da karatu, banda abokanen banza, banda kula samari kuma banda yawan ?awaye kitsare mutuncin kanki Nabila, abinda duk kike da bu?ata kisanar dani".

Nabila ta ce, "to Abba naji kuma insha Allah zan kiyaye bazan baka kunya ba, nagode sosai".

Juyawa Alhaji yayi takunsa biyu ya ?ara juyowa yace "Auta goben kiyi ?o?ari kigama shiryawa da wuri, domin nayi magana Yayanki Mubaraq zaizo ya kai ki makarantar". "To Abba insha Allah zanyi ?o?arin hakan", cewar Nabila.

Alhaji ya wuce tirakarsa ita kuwa Nabila ta mi?e ta ?arisa jikin kujerar da Hajiya Jummai da Amminta suke zaune ta mi?a musu file Win ta ce, "gashi kusa albarka", sukayi mata fatan alkhairi sosai.

Washegari tun sassafe Nabila ta kintsa tsaf tsantsar mararin fara zuwa makarantar jami'a da takeyi, gashi wannan rana ta kasance itace rana ta farko da zata fara halartar Uni Gash zata cika dogon burinta da ta jima tana addu'a akansa, wannan dalilin yasa wanzuwar farin ciki sosai a fiskar Nabila, hatta abinci ta kasa ci sabida Wauki ta kasance bata da aiki sai duba agogo tun wayewar gari da misalin ?arfe 8:15 am, Yaya Mubaraq ya samu isowa.

Shigowan Yaya Mubaraq ya tarar Nabila ce kaWai ke zaune a falo tana tsumayinsa, Abbansu da Umminsa da Ammin Nabila kuwa basu fito ba kunna, duk kanasu suna kwakkwance a cikin Wakunansu, wannan yasa yace da Nabila "uhm! Sarkin zumuWi kenan, ke kaWaice ma kika tashi a gidan tsabar Waukin fara zuwa jami'a".

Nabila ta ce, "Yaya Mubaraq ba haka bane, ni ai najima da daina komawa bacci bayan sallan asuba tunda naji irin tarin falalar da yake cikin wannan lokacin, na zamto kodai na zauna nayi tilawa ko kuma nayi zikiri har zuwa lokacin da rana zata fito".

Yaya Mubaraq ya Wan saki murmushi yace "tashi muje nikam na kaiki ki, kinji ko"?

Nabila ta wuce tabi Yaya Mubaraq suka fita tare har zuwa inda yayi parking Win motarsa a harabar cikin gidan, sannan suka shiga mota suka tafi makaranta kai tsaye batare da sun tsaya ako ina ba sai a cikin farfajiyar makarantar Yaya Mubaraq ya taka birki a gaban wasu ?an mata dake zaune a cool down a daura da hanya yace "?an mata barkanku dai, dan Allah muna tambaya muna tambaya ne"?

"Yauwa, Allah yasa mun sani", cewar ?an matan dake zaune a cool down.

Yaya Mubaraq yace "daga nan ita ina zamubi mu samu biochemistry department"?

?aya daga cikinsu ce ta mi?e tana mai nuna da yatsarta ta ce, "idan kabi wannan hanyar da tayi kwanan hagun a ?arshenta zakaga ta rabe biyu to ta Sangaren daman idan kabi har biochemistry department".

Yaya Mubaraq yace "to nagode sosai", sannan ya tada motar ya nufi hanyar kamar yadda tayi masa misali har bakin department Win, yayi parking Nabila ta buWe ta sau?a, anan sukayi sallama ya tafi, ita kuwa Nabila ta shige cikin department.

Nabila da bincika ta samu basu da lecture sai 11-1, wannan yasa ta samu wuri ta zauna kafin lokacin yayi, chan da misalin ?arfe 10:40, taji muryar Falila ta ce, "wa nake gani kamar a mafarki"?

Murmushi Nabila tayi ta ce, "aljana ce".

Falila ta ?ariso da sauri ta rungumeta, sannan ta ce, "besty ya akayi na ganki anan haka"?

Nabila ta ce, "ai yau tun ?arfe 9:00 am, nake nan, bayan na tambayi wata ce take faWamin ?an level 1 lecturen su sai ?arfe 11:00am, shine dalilin da yasa kawai na zauna anan".

Falila ta ce, "uhm! To amma kinsan zaki fara zuwa school miyasa baki kirani a waya ba"?

"Wallahi kawai naso nayi surprising Winki ne shiyasa", cewa Nabila.

Falila ta ce, "to gashi kuma ai kinzo kinsha jira abanza, don haka yanzu abunda ya kamata kifarayi shine ki copy time table, ya zamto a duk lokacin da muke da lecture zakina gani a rubuce, lokacin da babu kinga ba sai kinzo kinSata lokacinki ba ko"?

Nabila ta c??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e, "eh hakan za'ayi maganarki gaskiya ne".

Falila tasa hannu ta sau?e jakar goyo dake rataye a bayanta ta ciro time table ta mi?awa Nabila ta karSa tayi copy, sannan Falila ta ?ara da cewa "abu na biyu kuma yanzu saura maganan photo copyn hand out akwai bu?atar zuwa gobe kitaho da shirin mallakar duk wani hand out domin ki dukufa akan karatu, sakamakon muna daf da fara text, don haka ma kamata yayi yanzu muje na rakaki ofishin H.O.D ki karSi I.D card na department domin ba ashiga text sai dashi".

Nabila ta ce, "to muje ki rakani ?awar arziki".

Suna tafiya suna hirarsu har bakin ofishin H.O.D anan ne Falila ta tsaya ta ce, "yanzu sai ki buWe ?ofar kishiga domin shi doka ne mutum biyu basa shiga ofishinsa tare sai dai Waya bayan Waya".

Da "to!" Nabila ta amsa ta tura ?ofar ta shiga "assalamu'alaikum!"

H.O.D ya amsa mata sallamar ya umurce ta da ta rufe ?ofar sai ta shigo, ta shiga ta Wan tsaya daga gefensa kaWan ta gaishe shi, bayan ya amsa ya ?are mata kallo sama da ?asa sannan yace "bismillah, maza ki zauna ga kujera".

Nabila ta zauna tayi masa bayanin abunda ya kawo ta, atake ya binciko I.D card Winta ya mi?a mata, har ta juya zata fita yace "kitsaya mana, gaggawan me kikeyi ne"? "Sir muna da lecture ne yanzu haka", cewar Nabila.

H.O.D ya tsaki yace "kinga ki kwantar da hankalinki karSi wayar nan ki samin lambar wayar ki anan".

Nabila tasa hannu ta karSa ta samasa lambar ta, ya kira atake yaji ta shiga, ya Wan saki murmushi yace "shikenan kije kawai".

Nabila ta juya ta fito ta tarar da Falila na tsaye tana dakonta jikin Nabila da sanyi ta ce, "dan Allah kiyi ha?uri nasa mun makara".

Falila ta ce, "bakomai ai da alamun malamin ma baizo ba, sakamakon yanzun nan naga class rep Win namu ma ya wulga ta chan, aike kam mutuminki nema".

Cikin gaggawa Nabila ta ce, "wani mutumina kuma"?

Falila ta ce, "ni sunansa nake mantawa, wani class mate Win mu lokacin muna ss 2 inbaki manta ba, watarana malamar hausa tana tambayan kowa burinsa da yakeso ya cika agaba da akazo kansa yace shi anan gaba bashi da burin da yawuce ya auri Nabila Alhasan, lokacin aji akayita ihu mazan aji sukaita cewa Allah ya cika masa burinsa. Shin ko kin tuna"?

Nabila ta Wanyi ajiyar zuciya ta ce, "tir?ashi ina zan manta kuma, Jabir sunansa ai, kince akwai gwarama kenan a makarantar nan".

"Wata irin gwarama kenan Nabila"? Cewar Falila.

Nabila ta ce, "abinda ya faru kawai watarana Mamansa taje har gidan mu ta samu Ammina tace mata ita daga gidan Alhaji Salihu ne, akwai Wanta Jabir abokin karatun Nabila ne, sunyi secondry tare a Darul Alkam. Dalilin zuwan ta shine, tunda muka kammala makaranta muka rabu a gida Jabir kullum bashi da wani aiki sai hiran Nabila, lamarin ya kaiga yana kwance a cikin Waki zakiji yana rera wa?a, Nabila kizo inba kizo ni zanzo, Allah nake ro?o kabiya mini bu?atata, uhm! uhm!! uhm!!! To wannan dalilin yasa na taso nazo domin naji idan har Allah yasa ba ayi maganan auren Nabila da wani ba, to ina nemawa Wa na Jabir arzikin auren Nabila, idan har kun amince kuma yara sun fahimci junansu

2 / 12