Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   3 / 12

6K to 9K   out of 33.5K words

to insha Allah za a iya gudanar da hidiman auren acikin wata kachal, sakamakon Jabir shi kaWai Allah ya bamu a matsayin Wa agaremu. Ammina tace mata to badamuwa zatayi magana dani duk abinda ake ciki zataji labari. Sukayi sallama ta tashi ta tafi, daga baya Ammina take sanar dani abinda ake ciki game da lamarin Jabir, kawai na fashe mata da kuka, tayi yin duniya nayi shiru na?i, ta sameni da maganan ya kai karo uku bata samu amsa daga gareni ba. Bana mantawa wataranar jummu'a naje ziyara gidan Aunty Hannatu da yake suna unguwa Waya ne, ashe shi kuma Jabir yaga lokacin da na shiga gidan, chan muna zaune muna hira a falo wani yaro ya shigo wai Nabila tazo inji Jabir yana waje, to Allah yasa Aunty Hannatu tasan Wan ajin mune, na tashi na fita na sameshi yana tsaye nace masa Jabir Salihu dan Allah indai kai ba maye bane kafita a harkata, tsakaninka da Allah ina ni inakai, yaushen kama, kaga ni banason yarinta wallahi don haka kafita a harkata daga yau. Yace min Nabila yarinta ta itace kaWai illata agareki? Nayi shiru, ya ?ara da cewa to tabbas na godewa Allah tunda har bani da wani aibu da zaki iya faWa nawa, maganan shekaru kuma basa daga cikin cika cikan aure, acikin watan nan zan cika shakara 18 a muslimci ya halatta idan ina da sana'a abani aure domin na mallaki hankalin da zan iya zama da mata. Daga ?arshe ina mai tabbatar miki da cewa ke naso, kuma ke nake so, ke zan cigaba da so har zuwa ranar jummu'an da bata da asabar".

Jin hakan yasa Falila ta numfasa ta ce, "tir?ashi lallaikuwa akwai gwarama, domin ni na Wauka tunda muka bar makaranta ya ha?ura".

Nabila ta ce, "ina bawai ya ha?ura bane, kawai ta inda na samu sau?in lamarin baya samun ya ganni, to gashi kuma yanzu ma mun?ara haWuwa a class Waya".

Falila ta Wanyi shiru ta ce, "kawai tsare masa zakirin?ayi, don haka mu?arisa class Win mugani ko malamin ya samu zuwa".

Isarsu kenan shima malamin ya iso da motarsa kirar Toyota Anacornda, suka shiga gaba da baya, tsawon 2 hours suka kwashe yana koyar dasu akan course Win chemistry 101 kafin ya kammala lecture ya fita.

Bayan lecturer ya fita Nabila da Falila sun fito tare a hankali, Nabila ta buWe ?ar ?aramar fox Winta dake hannunta ta ciro wayar ta, dubawan da zatayi taga miss call har uku da number mai Wauke da sunan H.O.D duban Falila, Nabila tayi cikin firgici tana dafe ?irji ta ce, "na shiga uku".

Da gaggawa Falila ta ce, "besty lafiya me ke faruwa"?

Nabila ta ce, "H.O.D ne ya kirani har sau uku muna lectures sakanakon nasa wayar a babiretin tana cikin fox Wina yasa banji ba, Falila dan Allah ko zamuje ki rakani ofishin sa yanzu"?

BuWan bakin Falila ta ce, "yanzu kam ai H.O.D ya daWe da tafiya, sakamako ?arfe 2:00pm ta wuce, sai dai zuwa gobe amma karki damu nasan tayiwu akwai wata takarda ne da aka manta ba asa a file Winki ba".

Nabila ta ce, "to Allah yasa mudace, yanzu har ?arfe 2:00pm tawuce to ya batun sallah kuma"? "Eh kinsan sakamakon muna da lecture 2-4, a LT 5/6 to dole sai dai muyi sallah akan hanyar mu ta zuwa chan kasanwar yanzu ma mun makara", cewar Falila.

Suka kama hanya a yayin da sukaje daidai labrary suka yanke shawarar tsayuwa suyi sallah, batare da Sata lokaci ba sukayi sallah sukawuce LT 5/6 har sunje daf da wurin sukaga Walibai suna dawo cikin mamaki Falila ta tsaida wata daga cikin course mate Winsu ta tambayeta "sister wai miyake faruwa ne, naga mutane anata dawowa"? "Eh class rep ne yace malamin ya kira wayarsa ya sanar dashi bazai samu zuwa ba, shine kowa ya watse".

Falila ta ce, "to Nabila kinji abinda yake faruwa, don haka sai ki kira Yaya Mubaraq yazo ya Wauke ki".

Da "to!" Nabila ta amsa, sannan ta buWe fox Winta ta ciro wayarta ta lalimo lambar Yaya Mubaraq ta danna kira tayi dace kuwa ta shiga ringing Winta biyu Yaya Mubaraq ya Waga "hello Auta kaddai kuntashi a school kenan"?

"Eh Yaya", cewa Nabila.

Yaya Mubaraq yace "to badamuwa kijirani a department Winku ina zuwa yanzu insha Allah".

Nabila ta katsar da wayar ta ce, "besty mu juya mu koma department mujirashi a chan yana zuwa yanzu".

Suka juya suka koma department suka zauna sunata hira sai ga Yaya Mubaraq ya ?ariso suka gaisa da Falila yayin da Nabila ta mi?e zasuyi sallama Yaya Mubaraq yace "Falila kema ai da tashi kikayi muka tafi tare muka ajiyeki a gida muka wuce, inaga ai yafi mutafi mubarki ana ke kaWai ko"?

Falila ta ce, "ba komai wallahi Yaya Mubaraq kuje ku kawai, domin idan direba yazo Wauka na bai sameni ba bazaiji daWi ba".

Anan sukayi sakayi sallama suka rabu, Nabila da Yaya Mubaraq basu tsaya ako ina ba, sai a gida shigarsu gida keda wuya Nabila tawuce kitching ta lodo abinci tazo falo ta zauna ta kintsa kanta daga bisani ta tashi tayi sallah ta fara copyn note da akai tayi abaya kafin ta fara zuwa makaranta.

Washegari

Nabila ta wayi gari cikin sanyin jiki, haka dai tayi ?arfin hali batare da ta sanar da kowa damuwarta ba da Yaya Mubaraq yazo gaisuwar safiya cikin gida kamar yadda ya saba, ta bishi ya Wauketa ya kaita makaranta ya ajiyeta shikuwa ya juya ya tafi abunsa.

Nabila tana tsaye tsakaninta da Falila ba tazara sosai, amma ta kasa ?arisawa wurin da ?awayenta suke zaune suke jiran isowar malami, Falila ba tayi ?asa a gwiwa ba ta taso ta?ariso inda Nabila take, Falila tasa hannu ta dafa kafaWan Nabila ta ce, "Nabila damuwa ta bayyana a fiskarki, shin miyake damunki haka"?

Nabila ta ce, "kibari kawai Allah ne kaWai ya san irin tashin hankalin da nake ciki".

Jin hakan yasa cikin tattausan murya Falila ta ce, "?awata banaso kiSoye min komai a game da abunda yake damunki, sakamakon ta yiwu akwai irin gudumawar da zan iya baki akan abunda yake damunki".

Nabila ta ce, "wato daga iya kaWai naji natsani wannan makarantar, sakamakon jiya bayan na koma gida da daddare ina cikin copyn note, naga shigowar kiran wayar H.O.D na Waga muka gaisa dashi sosai, wato abunda zai baki mamaki Wan talikin nan ashe ?aton kwarto ne, ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, maganganu gunduma gunduma na batsa har da irin wa?an da kunne na bai taSa jin irinsu ba, yana ta suffanta surar jikina da irin yadda zai mu'amalance ni idan muka haWu. Wannan dalilin yasa gabaWaya daren jiya ban iya yin bacci ba, domin na tsorata makarantar nan gabaWaya ta fita min a raina yanzu".

BuWan bakin Falila ta ce, "wannan lamarin ai da ya kamata kisanar da Abbanki ne besty".

"A'a wanan ba ?aramin lamari bane fa, da zarar Abban nah ya samu wannan labarin to kisa aranki sanadiyar barina wannan makarantar kenan, domin kullum yanayi min nasiha kar ina kusantar inda ake aikata alfasha, sannan kuma kar ina mu'amala da mutanen banza. To kinga kuwa da zarar ya fahimci akwai irin wa?an nan mutanen acikin jagororin wannan makarantar to tabbas zai fidda ni acikinta", cewar Nabila.

Jin hakan yasa Falila ta Wanyi ajiyar zuciya sannan ta ce, "to yanzu dai shawara Wayace da zan baki ya zama dole ki dage sosai da sosai wajen karatu, yadda zai kasance a ?alla ko wani course a baki ciki ba shine kici B a course Win, akwai fa'ida babba idan kinyi hakan, wanda sai lokacin yayi zanyi miki ?arin bayani akan hakan".

Nabila ta ce, "to naji, Allah yasa mudace, domin ni yanzu gabaWaya ma juwa nakeji inaga ma kawai gida zan koma yanzu".

Falila ta ce, "Allah sarki besty ai dole kiji juwa irin wannan mummunan al'amarin, to kiWan zauna a wanchan cool down Win ki huta bari naje na siya mana hand out na dawo sai na rakaki chan bakin gate ki hau taxi ki koma gida ko"?

Da "to!" Nabila ta amsa, sannan ta juya ta?arisa ta zauna a cool down, jim kaWan zamanta ke da wuya taji anyi mata sallama, kamar bazata amsa ba dai ta daure ta amsa "wa'alaikumussalam!"


Jabir fiskarsa cike da annuri yace "da ace kin mi?amin ragamar mulkin zuciyarki to da ya tabbata yau Falila sai ta fiskanci hukunci mai tsanani, duba da irin yadda ta barki cikin matsanancin kaWaici", dubansa Nabila ta Waga kai tayi ta ce, "Jabir dan Allah na ro?e ka, karka cikani da yawan surutun iska".

Gyara tsayuwa Jabir ya Wan ?arayi yace "haba my dear, ya kike kirana suna Jabir kai tsaye gatse gatse haka".

Nabila ta Wan Waga kanta ta galla masa harara ta ce, "to da wani irin suna kakeso na kiraka inba Jabir ba"?

Ana cikin haka sai ga wani matashin Walibi ya ?ariso inda suke yace "class rep kazo muje ana kiranka yanzu yanzun nan".

Batare da Jabir ya amsa tambayar da Nabila tayi masa ba yabi Walibin suka tafi gaba abaya ofishin H.O.D, da suka shiga yayi umarni a Waya Walibin ya tafi, sannan ya dawo kan Jabir yace "idan kazaSi ka gama makarantar nan lafiya to karna ?ara ganinka da wata ?a mace, domin na fahimci kai asalin Wan iska ne, baka samu tarbiya a wurin iyayenka ba, shasha kawai lalataccen yaro da baka san ma me yakawo ka makarantar ba, baka da aiki sai li?ewa ?an mata duk inda aka ganka yaro kamar bunsuru, to kafita kabani wuri na faWamaka wannan yazama shine karo na ?arshe da zan ganka da wata ?a mace, indai har kanaso ka gama lafiya".

BuWan bakin Jabir yace "sir" .....! H.O.D ya tari numfashinsa yace "kai karka yarda kace min komai anan, get out in my office".

Jabir ya juya ya fito cikin sanyin jiki yana ta fiya yanata sake sake, chan yaci karo da Falila tana ta sauri zata tafi lecture anan ya tsayar da ita suka jera tare ya tambayeta "ya naganki ke kaWai ina ?awartaki kuma"?

Falila ta ce, "yanzu haka daga bakin gate nake na rakata ta koma gida sakamakon kanta yana mata ciwo sosai".

"Ayya Allah sarki", cewar Jabir. Ya?ara da cewa "ko nima yanzu haka ?o?ari kawai nakeyi, amma da zan biye da dole gida zan tafi".

Falila ta ce, "uhm, su Jabir manyan masoya daga cewa Nabila kanta yana ciwo shikenan kaima harka kamu".

Jabir ya sauke ajiyar zuciya yace "wallahi duk ba wannan bane, wannnan matsalace tsakanina da H.O.D domin Wazu yayi min alwashin indai ya ?ara kallona da wata mace a makarantar nan to da zallar carry over sai ya koreni nabar makarantan nan. Kinga kuwa wannan ai abune mai matu?ar wuya agareni a matsayina na class rep".

Jin hakan yasa Falila ta rasa tacewa face jijjiga kai da tayi, tana mai kallon Jabir alaman tausayi ya bayyana a fiskarta.

Jabir ya ?ara da cewa "amma ni yanzu kawai matakin da zan Wauka akan wannan lamarin shine, zan ajiye matsayin class rep ne, kawai a bayar a wani, tinda dama ta dalilin wannan matsayin ne mata suke kulani, amma nayi imani bazan daina kula Nabila ba, akanta na zaSi a koreni a wannan makarantar".

Jabir ya ?ara da cewa "don haka yanzu nima zan koma gida, ke ki ?arisa wurin lecturen idan Allah ya kaimu gobe, in har Nabila ba ta samu zuwa makaranta ba, sai kiyi magana da Aisha mu haWu muje gidansu Nabila mu duba ta".

Falila ta ce, "amma tunda mun iso har nan wurin, da kayi ha?uri ka daure mun?arisa lecturen nan".

Jabir ya?i amincewa sam, ya juya yaje ya Wauki motarsa ya tafi gida, da shigarsa ya iske Mummynsa a falo tana kallon labaru a tv, cikin mamakin ta dafe ?irji ta ce, Jabir yau lafiya, naga kadawo ba a lokacin da ya dace kadawo ba"?

Jabir yace "lafiya ?alau Mummy, kaina ne yake min ciwo shiyasa na dawo, sabida ina bu?atar na Wan samu hutu".

Cikin alhini Mummyn Jabir ta ce, "ayya sannu, Allah ya sauwa?e, stress ne ba wani abu ba, ya kamata katashi ka shiga ka kwanta kaWan samu hutu ne yanzu".

Da "to!" Jabir ya amsa, sannan ya mi?e ya nufi Wakinsa. har ya isa daf da ?ofar falon, Mummyn sa ta ce, "oh! Jabir Wazu nayi nayi waya da Daddynka yace a gaishe ka, ya kira wayarka bai sameka ba".

Jabir yace "ayya wai yaushe Daddy zai dawo ne Mummy"?

Mummy ta ce, "soon insha Allah, domin kasan yanzu ya bar Dubai yana Chaina".

Jabir yace "to ni dai dama ki tabbar yana dawowa gidan nan yaje ya samu iyayen Nabila akan maganan aurena da ita, domin tun farko na fahimci babbar matsalar da aka samu yasa ki kaga ba ayi auren muba sabida kece kikaje kika samu Ammin ta, amma na tabbatar da Daddy ne yaje ya samu Abbanta to da yanzu anyi angama".

Ajiyar zuciya Mummy tayi sannan ta ce, "Jabir kenan, shi aure lokaci ne, amma inba haka ba, ni nafika burin naga aurenka, amma karka damu muyi fatan Allah ya dawo da Daddyn ka lafiya kawai, insha Allah zaije ya nema maka auren Nabila, don haka kacigaba da fatan alkhairi kawai, kashiga ka kwanta".

Jabir atake yaji ya samu wani ?arfin jiki, sakamakon maganar Mummynsa, hatta ciwon kai da yakeji, yaji babu shi tamkar ya sha magani boska, yana mai hamdala acikin zuciyarsa ya wuce Wakinsa.

Washegari.

Jabir ya tashi cikin ?arfin jiki da annushuwa ya shiga banWaki yayi wanka ya fito kamar yadda ya saba, amma irin shigarsa ta sha banban da irin wanda ya saba, domin ya Sata lokaci sosai yana shafe shafen mayika da turare na alfarma, kafin daga bisani ya taje gemunsa ya Waura agogonsa ya juya yaga mirror wanka tabi jiki, ya Wauki key Win motarsa ya fito yaci karo da Mummyn sa, duba da irin nau'in daddaWan ?amshi da yake tashi ajikin Jabir, ta dubeshi sama da ?asa ta ce, "wow, Jabir irin wannan haWuwa haka, sai kace wanda yau zakuyi course akan yin kwalliya"?

Jabir yayi murmushi yace "kibari kawai Mummy yanzu dai na makara, idan na dawo zamuyi magana". Yawuce ya ?arisa car parck ya tarar an ?yale masa motarsa ta fita tass, she?i kawai takeyi, ya buWe ya shiga, bayan ya fita a gida bai tsaya ako ina ba, sai a cikin department Winsu anan ya tarar da Falila da Aisha suna zaune suna tsumayin zuwansa, cikin gaggawa Jabir ya buWe ?ofar motar ya sau?o da ya ?ariso inda suke yayi musu sallama suka gaisa sama sama, sannan yace "to maza ku hanzarta ku tashi musamu muje gidansu Nabila muduba ta mudawo kafin zuwan malamin English ko"?

Aisha ce, ta fara mi?ewa da bismillah kafin daga bisani Falila ma ta mi?e suka ?arisa suka shiga motar, Jabir yayi key suka tafi, isarsu ?ofar gidan su Nabila yayi horn da sauri mai gadi ya le?o, ganin Falila a cikin motar yasa ya buWe musu gate batare tambaya ba.

Bayan sunyi parking a harabar gidan Falila ta jagorance su har cikin babban falon gidan, inda a cikinsa ne Nabila take kwance akan wata kujera ?irar 3 sitter hannayen ta suna rungume da filo, batayi aune ba, kwatsam taga Falila tare da Aisha ga kuma Jabir a bayansu.

Cikin firgici Nabila ta ce, "nashiga uku", sannan ta fara ?o?arin janyo Wan kwalinta dake gefenta ta yafa akanta, tana mai cewa "sannunku da zuwa", da alamun kunya atattare da ida.

Falila ta ?ariso gefe da ita ta zauna ta Wan rungumeta ta ce, "my besty, faWamin miyake damunki yanzun, ina fata dai babu wani abun da ya?ara faruwa ko"?

Nabila ta ce, "uhmm!" Duba da basu kaWai bane a wuri.

Falila ta ce, "to yau ga Aisha nan nakawo miki ita, dan nasan ba lallai kin taSa ganinta a school ba, domin itama kullum tana department Winsu".

Nabila duban Aisha tayi ta ce, "idonki kenan, ke kam Allah ya shiryeki wallahi Aisha, na rasa yaushe zaki chanja halinki na ?in son shiga mutane".

Aisha ta Wan jijjiga kai ta ce, "bazaku gane bane".

Nabila ta mi?e ta ce, "uhm, ku Wanyi ha?uri bari naje na kawo muku ruwan sha", sannan ta juya ta dubi Jabir ta ce, "wato bazaka gaisheni ba kenan ko"? Ta wuce ta nufi inda fridge yake.

Le?owa Ammin Nabila tayi ta ce, "Nabila da wa nakeji kina magana a falo"?

Nabila ta ce, "Ammi su Falila ne sukazo".

Jin hakan yasa Ammin Nabila ta ?ariso cikin falon domin ta gane ma idonta, tayi musu sallama, bayan sun amsa Jabir ya Wan risina yace "antashi lafiya Ammin"?

Ammi ta amsa da cewa "lafiya ?alau alhamdulillah".

Sannan daga Waya gefen Aisha ta mi?o tata gaisuwar itama suka gaisa sosai, daga bisani Nabila ta dawo hannunta Wauke da tiren silver ta sha?e shi dam da drinks kala daban daban taje ta du?a a gaban Jabir dake zaune akan kujera 1 sitter ta ce, "abun gara a fara da babban ba?o, domin bazan Soye maka ba, har ga Allah najidaWin ganinka a gidan mu, don haka ka faWamin wani kalan drinks kakeson sha na sanya maka a cup"?

Jabir ya numfasa ya ?ara duban tiren sosai yace "ki samin exotic".

Nabila ta ce, "angama rankaidaWe", sannan ta Wauki exotic ta buWe ta tsiyaya masa acikin wani glass cup, ta ri?e hannu bibbiyu ta mi?a masa, daga bisani ta juyo wurinsu Aisha.

Nabila duban Amminta dake zaune a falon ta ce, "Ammi kingane wannan kuwa"? Tana mai nuni da Jabir.

Ammin Nabila shiru ta Wanyi ta ?ara ?ura masa ido ta ce, "bangane shi ba gaskiya".

Nabila ta Wan saki wata bazawarar dariya ta ce, "to wannan shine Jabir kenan, Wan ?awarki Aunty Zulaihat, sakamakon kin san Wan ajin mu ne shima, shine sukazo dubani suga ya jikin nawa"?

Ammin Nabila ta ce, "ikon Allah, sai da kikayi magana kuma naga kamanni sosai".

Cikin gaggawa Nabila ta ce, "to taya zaki iya ganeshi kina ganinsa harda gemu". Taran numfashin Nabila Amminta tayi ta ce, "ke ?aniyarki", ta ?ara dacewa "Jabir ya Mummyn naka, nikam mun kwana biyu ko waya bamuyi ba".

Jabir yace "ta nan lafiya ?alau".

Ammin Nabila ta ce, "to masha Allah", daga nan mi?e ta fita tabasu wuri, suka cigaba da hirarsu cikin raha har na tsawon wani lokaci, suna cikin tsaka da hira Jabir ya Waga hannu ya dubi agogon dake hannunsa yace "to bayin Allah ya kamata kutashi mukoma".

Nabila sam ta nuna batason tafiyarsu, wannan dalilin yasa ta biyosu

3 / 12