Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 33.5K words

isarsa ya iske alkalin na zaune a cikin wani wuri da ake kira da chamber a kotu da alamun hutawa ya keyi, cikin ?arfin gwiwa Baffa Ado yayi sallama ya shiga kan alkalin, suka gaisa sannan ya ?irge masa duk halin da ake ciki.

Atake alkalin yayi kira ma registrar, cikin biyayya ya gurfana a gaban alkali yana mai cewa "rankaidaWe gani".

Alkalin yayi masa umurni da "inaso da kai akwai wani ana kiransa da Alaramma Sa'ad zaka sameshi a makarantar islamiyyan nan ta tsallake don haka ka gaggauta kayi masa sammaci kayi ?o?arin ganin takardar ta shiga hannunsa".

Registrar ya amsa "an gama rankaidaWe", sannan ya juya ya fita a chamber, yabar alkalin tare da Baffa Ado.

Alaramma Sa'ad.

Alaramma Sa'ad zaune yake a farfajiyar wata bishiya dake harabar islamiyya yana ta muraja'a yaga wani kakkauran mutum da azahiri ya Wan manyanta yazo yayi parking Win mashin Winsa, sannan ya sau?a ya ?ariso yayi sallama yace "dan Allah ina tambayane, ina neman Alaramma Sa'ad ne"?

BuWan bakin Alaramma Sa'ad dake zaune ya mi?e yace "nine".

Suka Wan ja gefe kaWan ya fara da gabatar masa da kansa "ni sunana Malam Sule, nine registrar na shari'a court, wannan takardace ta sammaci na kawo ma, kotu tana bu?atar ganinka sakamakon shigar da ?ara da wani bawan Allah yaje yayi akanka".

Alaramma Sa'ad yasa hannu ya karSa sannan yace "to badamuwa zanbuWe na karanta kuma insha Allah zan amsa umurnin kotu, nagode sosai Malam Sule".

Anan suka rabu Malam Sule ya tafi, cikin Wan ?an?anin lokaci magana duk tabi ta yaWa ko ina a gari, lamarin da yasa mutane da dama al'ajabi.

Alhaji Sha'aban.

Jabir da Mummyn sa zaune suke a falo suna hira Daddyn sa ya shigo ya iskesu, duba da irin son da Jabir yake yiwa Nabila yasa Daddynsa ya bu?atar Jabir ya san an Waura auren Nabila da Alaramma Sa'ad kamar yadda Alhaji Saminu ya sanar dashi, tunin irin halin da Jabir zai tsinci kansa aciki yayin da ya samu yayi yasa yace dasu "albaishirinku".

Da gaggawa Jabir da Mummynsa suka amsa da cewa "goro fari tas!"

Daddyn Jabir yace "to kutashi kushirya yanzu yanzun nan direba zai kaimu air port London zamu tafi akwai gidan da akayi min talle sakamakon najima inason gida a estate Win, to shiyasa nakeso yanzu ku shirya mutafi muje kuga gidan".

Cikin shau?i Jabir ya mi?e ya Wanyi tsalle yace "wow, Daddy kamar kasan abinda na jima ina mafarki kenan a rayuwata", ya ?ara da cewa "Mummy ki hanzarta dan Allah mu samu mutafi karkiSata lokaci".

BuWan bakin Daddyn Jabir yace "kabarta ta kintsa a natse mana, domin ta chan ai zamu wuce Japan kaima ka koma makaranta, dama ina jiran ayi sadakan arba'in Win marigayi Alhaji Alhasan tunda Allah yasa anyi kuma to yanzu sai tafiya".

Jin hakan yasa Jabir yace "to Daddy indai daga London zamu wuce Japan to gaskiya akwai bu?atar kuyi min uzuri naje muyi sallama da Nabila".

BuWan bakin Daddyn Jabir yace "a'a Jabir a gaskiya bazaka samu wannan damar zuwa sallama da Nabila domin kuwa alfarmar ticket guda uku akayi min na tafiya London a Azaman office a air port wanda idan har kajawo mukayi losing flied Winnan yanzu to gabaWaya munyi failing mission Win mu kenan. To kawai don haka kayi ha?uri kashiga ka kintsa yanzu musamu tafi kaji"?

Da "to!" Jabir ya amsa sannan ya juya shige Wakinsa dake cikin katafaren falon wanda yake an tsarashi tsarin muhaWu a falo.

Jim kaWan batare da Sata lokaci ba Jabir ya kintsa ya fito falo, ya tarar da jakakkunan Mummynsa guda biyu a ajiye falon ita kuwa da Daddyn sa duk suna cikin Waki, wannan yasa Jabir ya zartar da ya fita harabar cikin gidan ya jira fitowarsu.

A yayin da Jabir ya fito harabar gidan ya iske drivern Daddyn sa da mai gadin gidan suna zantawa tare akan benci, bayan sungaisa da Jabir suka cigaba da hirarsu anan ne da Jabir ya Wan kasa kunnensa kaWan yaji acikin hirar tasu drivern yana faWin "ni tunda nake bantaSa jin irin Waurin auren da akayiwa ?ar marigayi Alhaji Alhasan ba, kawai shi wai ustaz an wakiltashi ya karSi auren yarinyar a wani Wan baffan ta sai ya karSawa kansa, yanzu haka anata rikici akan ya saketa yace shi wallahi babu abinda zaisa ya saketa, gashi yanzu har abun ya kaisu ga shiga kotu ba asan yadda lamarin zai kasance ba a kotu".

Mai gadin ya Wanyi dariya sannan yace "kai kuma da zarar kasha angur Winka sai kawai kazo kayita yiwa mutum tatsuniya kana cewa wai abun ya faru, yanzu dan Allah tayaya irin wannan abun zai faru"?

Drivern ya buWi baki yace "wallahi da gaske nake maka wannan abun ya faru kuma acikin wannan garin namu, domin katabbatar kuma insha Allah duk ranar da za'ayi shari'ar zan Wauke ka muje kotun tare domin kaji da kunnen ka".

Jin hakan yasa Jabir dake gefe da ya kasa kunnensa ya saurari duk kan bayanan da drivern yayi batare da Jabir yace uffan ba ya Wan numfasa kawai ya buWe motarsa yayi key yaja ya fita da mota, fitar Jabir kai tsaye ya nufi garin Jakusko babu ?a??autawa lara kawai yakeyi a hanya har ya shiga garin, batare da ya tsaya ako ina ba yawuce asibiti.

Ummin Falila.

Zaune take akan baranda batayi aune ba Waga kanta da zatayi taga Jabir a fijajan sai huci kawai yake furzarwa, cikin firgici Ummin Falila ta ce, "Jabir yau lafiya naganka haka, miyake ne"?

BuWan bakin Jabir yace "Ummi minene gaskiyan lamarin abunda naji akan auren Nabila, banaso kiSoyemin komai ina bu?atar kiyimin cikakken bayani dalla dalla"?

Ummin Falila da sauri ta dafe ?irjinta ta ce, "auren Nabila kuma, to wani irin aure kenan bayan wata da watanni gata a gadon asibiti bata da lafiya ma, balle kuma ayi wani maganar aurenta, to dai gaskiya bazan Soye maka ba Jabir nidai ina tare da Nabila anan amma wallahi bani da wani labari da ya shafi auren ta".

Jabir a fusace ya ?ara da cewa "kai! Ummi to inba ido miya kawo gurbin ido, gaskiya akwai dai wani abu sabida haka kawai ba yadda za'ayi naji ana labarin a Gashua".

Ummin Falila ta Wanyi shiru ta ce, "to yanzu dai sai dai muyi abu Waya kaga Nabila a kwance take yanzu bata bu?atar hayaniya, amma zan iya kaika gidan da Hajiya Laila take acikin garin nan domin muje muji gaskiyar lamarin tunda ba zaiyiwu a Waura auren Nabila bata da labari ba".

Hakan kuwa akayi Jabir yace "to muje Ummi". Juyawa tayi taja ?ofar Wakin da Nabila take kwance sannan suka tafi.

Sabuwa.

Da Sabuwa suka fara cin karo tun daga mashigar gidan, a karon farko da suka gaisa babu wanda yawayi wani acikinsu, har sai daga bisani suka gabatar da kansu a wurin Sabuwa sannan Ummin Falila ta ce, "Ummah munzo wurin Hajiya Laila ne".

Da "to!" Sabuwa ta amsa, sannan tayi musu jagora zuwa cikin gidan, anan ne suka iske Hajiya Laila na kwance akan wata garduma, gefe da ita kaWan kuwa flask Win shayi ne da wasu magunguna acikin leda.

Ganinsu UmminFalila yasa Hajiya Laila tayi ?arfin hali ta tashi ta zauna, tana mai cewa "yau manyan ba?i muka samu a gidan namu"?

Ummin Falila ta ce, "yau nida Jabir ne muke tafe wallahi".

Hajiya Laila ta ce, "Allah sarki to sannunku da zuwa ku ?araso tanan ga wurin zama".

Suka ?arasa suka zazzauna sannan suka gaisa sosai, daga bisani Hajiya Laila dubi Ummin Falila ta ce, "ke kam an barki da fama da Wawainiyar Nabila, kina ta shan Wawainiya sai da Allah ya saka zamuce kawai, sakamakon niWin ma har yanzu idan jikin ya tashi ba ?aramin wahala nake sha ba".

Ummin Falila ta ce, "lahh, bakomai ai, duk yiwa kaine wallahi, fatan mudai shine Allah ya yaye bakWaya".

Duk kansu suka haWa baki sukace "amin thumma amin".

Ummin Falila ta buWi baki ta ?irgewa Hajiya Laila duk kan labarin da sukaji a game da lamarin auren Nabila wanda shine yayi ma?asudin zuwansu domin su tabbatar da asalin gaskiyar abinda yake faruwa.

Hajiya Laila ta ce, "aure kuma, to wani irin aure kuma, tayaya za a Waura auren Nabila kuma bani da labari gaskiya wannan maganar ba gaskiya bace domin bata da asali kuma bata da tushe".

Jin hakan yasa Ummin Falila ta dubi Jabir ta ce, "to kadaiji ko, daga majiya mai ?arfi, don haka kasaki ranka domin ba a Waura auren Nabila ba".

Jabir ya Wan saki murmushi yace "uhm! Naji to Allah yasa mudace".

"Amin ya Allah", cewar Ummin Nabila sannan suka mi?e suna shirin tafiya, Hajiya Laila tace da Jabir "nagode sosai idan kakoma gida kagaishemin da Mummyn ka", sannan tacigaba da godiya tare da fatan alkhairi a Ummin Falila har suka fita suka iske Sabuwa ta tsumayin mai ruwa tana tsaye a bakin ?ofa sakamakon sukola da ta tara takeso tayi.

"Har kun fito"? Cewar Sabuwa tana Wan ?ara zakuWawa daga bakin mashigar gidan.

HaWe baki sukayi sukace "eh wallahi, mun fito zamu koma".

Anan itama Sabuwa tayita yi musu godiya ta taka musu har bakin mota sannan tajuyo sukuwa suka shiga suka tafi.

Alhaji Sha'aban.

Hannayen Alhaji Sha'aban duka biyu ya fito Wauke da jakakkuna, daga chan bakin gate mai gadi da driver da suke zaune suka tashi sukayi rige rigen zuwa karSan kayan dake hannun Daddyn Jabir.

Cikin biyayya suka haWe baki suna masu cewa "Alhaji barka da fitowa".

"Yauwa barkan ku dai", cewar Alhaji. Sannan ya ?ara da cewa "ina Jabir kuma"?

Driver yace "Jabir ai ya Wan jima da fita a gidan nan gaskiya domin muna zaune muna hira lokacin da fito ya Wan daWe a tsaye a gefen mu kafin ya Wauki motarsa ya fita yabi kudu".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Cewar Alhaji.

Cikin firgiji driver yace "Alhaji lafiya kuwa"?

Alhaji yace "gaskiya ba lafiya ba domin abinda nake gudun ya faru ne ya riga ya faru".

JINI NA=???



_____________________

Na sadaukar da wannan littafin zuwa ga

_Bilkisu Hamisu Kurfi.
(Big Aunty).



A gaskiya ina matukar jinjina a gareki sosai akan ?o?arin ki. Allah ubanguiji ya Waukaka rayuwar ki, Allah ya sadaki da dukkan wasu alkairan duniya da lahira, Allah ya inganta rayuwar ki. Ya kuma kareki daga dukkanin wani abun ?i da dukkanin shairin bayyananar halita da kuma Soyyayar halita. Ina yimiki fatan alkhairi, Allah yasa ki gama da duniya lafiya.=?O?



P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+P+

Fasaha Fans Group:https://chat.whatsapp.com/F0pA2JPFUp06Lr6EIGSnlD?mode=wwt

My Group:https://chat.whatsapp.com/Kas2I7DoSLCLAYTLSHBd7o?mode=ems_copy_t





NA


SAGIR ALIYU MAIGARI
(Sagiryellow
'?)






BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM









.Ana cikin haka Mummyn Jabir ta fito ta tarar da Daddyn Jabir da driver da mai gadi suna tsaye chirko chirko sai tatala sukeyi, ganin hakan yasa ta ce, "Alhaji yana ganku haka kamar an aiko muku da labarin mutuwa".

Alhaji ya Wanyi ajiyar zuciya sannan yace "kibari kawai na fito na samu Jabir wai ya Wauki mota ya fita, ina da tabbacin kuma wurin yarinyar nan Nabila ya tafi chan Jakusko, babban abunda nake gudu kuma shine zai iya samun matsala yayinda yaji abinda ya faru, don haka kawai yanzu mu koma mu zauna maganar ta fasaya".

Mummyn Jabir ta ce, "ban fahimce ka ba Alhaji, ya kana maganan Jabir zai iya samun matsala kuma amma kana maganar mu koma cikin gida mu zauna"?

Alhaji yace "eh na faWi haka ne domin yanzu haka ko da mun fita mu bamu san ina Waya zamuje mu sameshi ba, don haka mu koma mu zauna duk abinda yake ciki zamu samu labari ai".

Jin hakan yasa Mummyn Jabir ta Wanyi shiru chan kawai ta fashe da kuka ta juya ta koma falo.

Damaturu.

Alaramma Sa'ad.

"To Baba nikam yau insha Allah zan koma Gashua sakamakon gobe ne shari'ar mu a kotu, domin dama nazo na sanar daku abinda yake faruwa ne, don haka sai sai ku cigaba da addu'a Allah yasa muga alkhairi". Cewar Alaramma Sa'ad.

BuWan bakin Baba yace "babu komai wannan kam addu'a kullum acikin yi muku ita muke don haka katabbatar kayi sallama da sauran ?an uwanka kafin katafi daman".

Alaramma Sa'ad yace "to Baba insha Allah duk zanyi yadda kace, idan Baaba ta dawo kuma itama ka faWa mata halin da ake ciki domin ta ringa tayani da addu'a, ni yanzu zan wuce kawai nagode sosai Baba".

Gashua.

Washegari.

Da misalin ?arfe 8:00am, Baffa Ado da Alaramma Sa'ad suka gurfana a gaban Alkali a shari'a court, duk kannin ma'aikatan Sangaren shari'a suma duk kowa ya halarta, wannan yasa Baffa Ado a matsayinsa na mai gabatar da ?ara ya tashi ya ?ara gabatar da ?orafin da ya shigar da ?ara akansa.

Bayan Alkali ya saurari ?arar ya tambayi Alaramma Sa'ad cewa "to wanda ake ina fatan kaji abunda ake ?ararka akayi, shin kana da ja akan wannan bayan nasa ko baka dashi"?

Alaramma Sa'ad ya buWi baki yace "rankaidaWe duk kannin bayansa da yayi haka akayi, amma sai dai ina da hujja akan abunda na aikaita".

Jin hakan yasa Alkalin yace "to yanzu na Waga wannan shari'a zuwa jibi inaso azo min da ita yarinyar da aka Waurawa auren, sannan a taho da mahaifiyatta da shi kansa Waya yaron Sharif kafin daga bisani sai mugabatar da shari'a akan case Win".

Jabir.

Mummyn Jabir Jabir na zaune a falo ta zabga tagumi hannu bibbiyu tare da Daddynsa da kagansu tamkar masu zaman makoki, basuyi aune ba kawai sukaga shigowar Jabir cikin falon da hanzari Daddynsa ya mi?e yace "Jabir kai daga ina haka, ina kaje kasan munshirya ta fiya zamuyi aka rasa ka"?

Jabir ya Wanyi ajiyar zuciya yace "am sorry Daddy calm down, wallahi wani mummunan labari na samu wai an Waura auren Nabila shine yasa bansan lokacin da nayi key a mota na tafi Jakusko domin na tabbatar ba".

Daddyn Jabir yace "to yanzun miye gaskiyan al'amarin da kaje kaji"?

Jabir yace "duk ?aryace kawai irinta mutane, domin har Amminta sai da mukaje muka tambaya ni da Ummin Falila, daga ?arshe muka tabbatar da maganar bata da tushe".

Jin hakan yasa Mummyn Jabir dake zaune a gefe ta ce, "alhamdulillah, abu yayi kyau Allah ya ?arayi mana muwafa?a".

Duk kanninsu suka haWa baki sukace "amin thumma amin".

Bayan Kwana Biyu.

Kotu ta cika tam ba batse abisa umurnin Alkali daya bayar na halartar su Nbila a gaban kotu, cikin ikon Allah kuwa hatta Nabila da take gadon asibiti an Wauko ta zuwa kotu da motar ?an sanda, batare da tasan komai ake ciki ba, daga ita har Amminta.

Da farko Alkalin ya fara bayi akan aure a muslimci kamar haka "shi dai aure sunnace ta manzon Allah (saw), sannan kuma aure yana daga cikin ibada a muslimci, yana da kuma sharuWansa dole ne mutum ya kasance lafiyayye ta Sangaren kwakwalwa da gangan jiki, dole ne mutum ya kasance yana da hanyar da zai iya ciyar da iyali, abu na ?arshe kuma ana bu?atar a gina auren akan soyayya data shafi duk kanin Sangaren mace da namijin. Don haka duba da wa?an nan dalilan abun tambaya anan Alaramma Sa'ad miye dalilin da yasa ka aikata haka akan Nabila"?

Alaramma Sa'ad yace "rankaidaWe nayi hakane domin na shafe tsawon lokaci ina Wauke da soyayyar Nabila acikin zuciyata wanda har nasamu daman bin hanyar da ta dace nakaiga neman izinin fara zance da ita a wurin Abbanta, kuma cikin ikon Allah ya amince min ya bani dama, wanda hakan shiyake nuna ya yarda dani, muna kan gaisawa da ita kafin akaiga a tsaida maganar aure a tsakanin mu Allah ya Wauki rayuwar Abbanta, daga bisani kuma Baffanta yazo zai Waura mata aure da Wansa Sharif wanda kwata kwata Nabila ba tsararsa bace kuma batare da an shawarce taba, shiyasa nayi amfani da damar alwalanci da akabani na Waurawa kaina aurenta".

Alikalin ya Wanyi shiru na Wan da?i?a sannan yace "to Malam kai yanzu kotu ta saurari dalilanka, saura daga Waya Sangaren Baffan yarinya kaima zamuso muji menene dalilin da yasa kaso ka Waurawa Nabila aure tare da Wanka"?

Baffa Ado ya mi?e tsaye daga kan bencin da yake zaune, sannan yace "ya mai shari'a, dalilina shine ni yanzu nine matsayin mahaifin Nabila, shiyasa nayi duba da matakin shekarunta batare da aure ba, yasa naga yafi da cewa amatsayinsu na ?a?ana da ita da Sharif na Waura musu aure mutafi Gaidan da ita domin nasan zanyi iya ?o?arina naga cewa sun zauna lafiya a junansu".

Alakalin yace "to alhamdulillah, yanzu dai kotu ta saurari ?ara daga duka Sangarori biyun saura daga ?arshe muji daga bakin wacce aka Waurawa auren, Nabila shin menene ra'ayinki akan Alaramma Sa'ad da aka Waura miki aure tare da shi domin shari'a bazata bari aciki zarafinki ba in har bakyaso"?

Cikin tattausar murya Nabila ta buWi baki ta ce, "rankaidaWe na amince dashi a matsayin mijina, na karSi aurensa a matsayin zaSin Allah a gareni".

Atake Alkalin ya Waga wani katako mai launin guduma ya buga akan teburin dake gabansa, sannan ya buWi baki yace "masha Allah, wannan shari'a ta ?are anan domin aure tsakanin Alaramma Sa'ad da Nabila ya ?ullu da yardarsu, don haka muna muku fatan alkhairi".

Anan zaman kotu ta?are jama'an dake zaune suna sauraron ?ara suka fara watsewa.

Falila.

Duban Nabila Falila dake zaune a gafenta tayi ta ce, "haba Nabila miyasa zaki yanke irin wannan hukuncin anan, kinfi kowa sanin Jabir yana matu?ar ?aunarki da gaskiya amma kika saka masa da irin wannan Wanyen hukuncin".

BuWan bakin Nabila ta ce, "haba Falila hukuncin dana yanke anan shine daidai, domin inaso kisani shifa Jabir duk abinda muke ciki bai kaiga manya sun shiga cikin lamarin ba, har Allah yasa wannan abun ya faru dani, wanda a cikin irin wannan halin ba lallai Daddynsa ya amince masa ya aureni ba, duba da bana mantawa a kullum Jabir yana jaddadamin yana sona sabida asalina, to yanzu kuma da aka wayi gari asalina ya wargaje yakike ganin abun zai kasance, dole fa lamarin aurena da Jabir wani sabon ?alubale ne zai sake tashi wanda bazanso hakan ba. Dama ni kullum zaSin mafi alkhairi nake nema a wurin Allah kuma tunda kikaga haka takasance wannan kawai shine, muyi fatan Allah yasa mudace".

Falila tayi shiru harta rasa ta cewa, sannan Nabila ta ?ara da cewa "Falila kisaki ranki dan Allah, domin ni da kike gani farin ciki ya daWe da ?aurace min, wanda kuma bana tunanin zai ?ara dawomin don

11 / 12