Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   9 / 12

24K to 27K   out of 33.5K words

akwai abinda za'ayi miki insha Allah zaki haihu. Nayi shiru domin abun bai kama halina ba amma dana tuna da maganar iyayena da sukace min indai na bijirewa umarnin Alhaji Falalu to basu ya femin ba Allah ya isa tsakanina dasu sukace min, kawai sai nace masa to Allah ya kaimu. Bayan sati Waya dayin haka mukaje muka hau jirgi muka tafi ?asar Egypt wani babban asibiti, akayi mana gwaje gwajen duniya akan Alhaji Falalu ya naso amin tiyata asamin maniyyinsa a mahaifa ta, amma ina hakan bayyiwu ba, likitoci suka tabbatar masa da maniyyinsa bazaiyi ba, hakan yasa Alhaji Falalu bayyi ?asa a gwiwa ba, ya sayi wani a wurin aka sakamin wanda nima ban san ko nawaye ba, akayi dace aka gama aikin lafiya, sannan muka dawo gida Nigeria watan mu Waya da dawowa kuwa ciki ya bayyana ajikina, yau ne gobe ne na raini cikin nan har tsawon wata tara, kafin Allah yasa na haifi ?a mace, na haifeta a gida batare da naje asibiti ba, inata murna ganin na sau?a lafiya, Alhaji Falalu yazo yatarar da ?ar dana haifa, gata santaleliya fara tas, lafiyayyiyar yarinya sannan kuma gashi kamar mu Waya da ita, amma buWan bakin Alhaji Falalu sai yace min ai shi ba ?a mace ya keso ba don haka sai dai murabu da ?ar tun kafin ma mutane su san me ake ciki, cikin firgici nace masa haba Alhaji kamarya mu rabu da ?ar nan kuma yarinyar da aka haifeta yau Win nan? Yace min eh shi yasan yadda za'ayi na bashi zuwa gobe tunda yanzu dare yayi. Washegari da hantsi Alhaji ya kira mutum uku daga cikin ma'aikatan gidansa yace musu ya naso zasu Wauki wannan jaririyar sukaita gidan marayu, idan sunje mutum biyu daga cikinsu sutsaya a matsayin su hukuma ne, mutum Waya kuma ya tsaya a matsayin shi likita ne, sai suyi bayani akan cewa wata mata ce tazo haihuwa asibiti daga ?auye ta haifi wannan jaririyar bayan ta haifeta kuma jini ya Salle mata ba'asamu na sarar tsada jinin ba shi ya zama ajalinta, kuma kawo yanzu dai tunda aka gudanar da jana'izarta babu wani wanda ya Sullo a matsayin Wan uwanta, wannan dalilin yasa muka saka hukuma aciki domin mukawo jiririyar nan domin ta samu kuwalarku, kafin zuwa wani lokaci ko Allah zaisa asamu wani Wan uwan mahaifiyarta ya Sullo. Hakan kuwa akayi Alhaji Falalu ya Wauki jaririyar ta mi?a musu ita, suka tafi da ita nayita kuka harna rasa inda zansa kaina, wannan shi ya zama sanadiyar na kamu da sau?ar jini gabaWaya duk na lalace na fita a kammanni na, ana cikin haka mahaifina ya rasu. Bayan wasu shekaru muna tare da Alhaji Falalu yazo yace min shi bazai iya zama dani ba a yanayin dana tsinci kai, don haka ya sake ni na tattara na tafi shi aure zai ?arayi, haka na tattara nadawo Jakusko wurin Baaba ta na sanar da ita cewa ya sake ni, abun bai mata daWi amma babu yadda zatayi, haka muka cigaba da zama tare a gidan, har itama Allah yayi mata rasuwa, na dawo saura ni kaWai a gidan, ana nan watarana na samu labarin shima Alhaji Falalu Allah yayi masa rasuwa. To wannan shine abunda ya kasance dani wanda yasa tun bayan rabuwata da Alhaji Falalu ban ?arayin aure ba har yau, kullum naketa gwagwarmayar yadda zanyi naci na sha kawai a rayuwata har zuwa yanzu".

Jin hakan yasa duk kanninsu suka kaure da salati, sannan sarkin malamai yace "amma wannan labari naki cike yake da darrusa da kuma ban tausayi".

Sabuwa ta buWi baki ta ce, "wannan al'amari duk ya faru ne sanadiyar son zuciya da iyaye na suka nuna muraran akaina, sun bada aurena batare da sun gudanar da bincike akan wanda suka aura min ba, bin umurninsu ya kaini ga shiga cikin halin da na shiga a rayuwata domin Allah ya sani kafin nayi bantaSa amincewa wani Wa namiji ya rike ko da hannuna ba da sunan biye ma zuciya, amma sai gashi inaji ina gani aka buWe maihaifata aka sanya min maniyyin wani ?aton banza wanda ban sanshi ba, kuma da amincewar mijina. To wannan ba?in cikin kaWai ya isheni nasan bazan taSa daina takaicin zama da mutum irin Alhaji Falalu ba har iya ?arshen rayuwa ta. Daga ?arshe ina fata Allah ya raba duk wani muslimi da mummunar ?addara maka manciyar irin wannan".

A dai dai nan wani matsanancin kuka ya kwacewa Sabuwa, wanda yasa Hajiya Laila ta?ara kusantanta ta rungumeta tana mai cewa "kiyi ha?uri Umma, ba kuka zakiyi ba godiya ya kamata kiyiwa Allah da yasa kika ganni a rayuwarki, domin ni kaina bantaSa tunanin akwai watarana mai kamar ta yau zatazo na saki a idona ba, sakamakon kamar yadda kika zayyana mana abinda ya faru haka aka rubuta ajikin file Wina a gidan marayu wanda aka bani lokacin da aka Waura aurena da Alhaji Alhasan, shiyasa nasa a raina iyayena sun jima da rasuwa kullum kawai sai dai addu'a da nake musu, amma yau gashi Allah ya nuna min ke a matsayin mahaifiyata don haka babu abinda zance face alhamdulillah".

Bayan Sabuwa da Hajiya Laila sunyi kukansu sun ?oshi, Hajiya Laila ta dubi Alhaji Alhasan ta ce, "ni yanzu alfarma Waya nake nema a wurinka Alhaji, dan Allah ka taimaka ka amince mutafi da Umma nah gida tare domin inaso ta kasance a kusa dani sabida na samu damar bata cikakkiyar kulawa irin wanda duk wata ?a take burin ganin tabawa mahaifiyarta".

Alhaji ya buWi baki yace "wannan aiba wani abu bane da har sai kin nemi alfarma a wurina, babu komai na amince insha Allah zamu tafi tare da ita".

Sarki ya umurci sarkin malamai yayi musu addu'a kafin sutafi, suka kwashe tsawon lokaci sunata addu'oi, kafin daga bisani suka mi?e zasu tafi, wani abun mamaki kuma da Nabila da Hajiya har zuwa lokacin da suka mi?e al'ajabin abinda ya faru yasa basu iya cewa komai ba tamkar wanda basa wurin, haka suka sukayi sallama da mutanen fada suna masu godiya suka shiga suka tafi gida.

Bayan Komawarsu Gida.

Alhaji Alhasan ya bu?aci keSewa tare da Hajiya Jummai kaWai domin yin wata magana ta sirri. Alhaji ya fara da cewa "Hajiya Jummai na kiraki nan ne domin zantawa dake akan wata magana da bantaSayin ta da kowa ba tunda nake a rayuwata sai yau zan sanar dake dalilin ganin abinda ya kasance da Sabuwa yasa bazan iya cigaba da Soye maganar ba".

Alhaji Alhasan ya Wan numfasa sannan yace "bana mantawa na taso na tarar da iyayen da suka haifeni talakawa ne futuk a wanchan lokacin a garin Jakusko, mahaifina ya kasance yana aikin dakon kanwa ne itace sana'arsa a wanchan lokacin, ita kuwa mahaifiyata ta kasance tana yin aikatau, wannan dalilin yasa dana Wan tasa kaWan nima nafara yin aikin da mahaifina ya keyi na dakon kanwa. A wanchan lokacin akwai wasu matasa guda biyu wanda duk kanninsu kusan kan mu Waya ne dasu, da Bala da Tajo mutanen ?asar Niger ne ?an jihar Zandar ne daga chan suka shigo Nigeria neman kuWi har Allah ya haWamu tare cikin ikon Allah muka samu sha?uwa sosai da junan mu. Bayan mun kwashe tsawon shekaru munatare dasu kwatsam kawai watarana sai nagansu da motar shiga ?irar sterlet, cikin mamakin na tambayesu motar waye suka samu, buWan bakin Bala ya cemin ai tasu ce kai tsaye ya rantse min akan haka, Tajo ya Wauko min takardun motar yanu namin na tabbatar da tasuce, sai nashiga tuntuSarsu amma taya akayi kuka mallaki mota bayan kuma kullum tare muke wuni daku a wurin dako, sai sukayi dariya sukace ai kaWan ma kagani mu yanzu munfi ?arfin yin dako nan ba daWewa ba zamu koma Niger muje musan me ya kamata muyi domin mu gina rayuwarmu muma. Jin hakan yasa na ?ara za?ewa lallai inaso su faWamin ta yadda akayi suka mallaki irin kuWaWen nan, shine Tajo yace tsakanin mu ai munyi zaman amana don haka bazasu Soyemin komai ba, abinda ya faru akwai wani clinic a Damaturu anan ne wani ya kaisu suka sayar da maniyyinsu naira miliyan biyar biyar. Cikin mamaki na ?ara tambayarsu to amma su mutanen mi sukeyi da miniyyin mutum da har suke sayansa da tsada haka? Tajo yace oho wannan kam ai chan ta matse musu mukam ai munkama ?an kuWaWen mu. Na Wanyi shiru nayi tunanin irin yadda muka sha?u da Tajo da Bala kullum tare muke gwaggwarmayar rayuwa, na ?ara tuna yadda zan kasance idan suka tafi Niger suka barni, kawai sai na bu?aci taya za'ayi nima sumin hanya a sayi maniyyina? Bala yace min wannan kam aiba wani abu bane kawai zakaje kayi istimina'i ne sai ka kawo maniyyin naka muje a gwada idan zaiyi musu amfani shikenan atake zasu baka kuWaWen ka, a lokacin bnsan ma yadda akeyin istimina'i ba Bala ya kwatantamin naje nayi kuwa nazo mukaje kamar da wasa ma'aikatan suka karSa suka Wanyi wasu gwaje gwajensu sukace zaiyi, batare da Sata lokaci ba suka Wauki naira miliyan biyar suka bani, sannan saka jamin kunne sosai akan na kama bakina karna kuskura na bayayyana wannan lamarin. Na amince mukafita mukatafi, daga baya Tajo da Bala suka tafi ?asarsu ni kuma na fara harkar kasuwanci na kanwa da kuWin kamar wasa Allah ya samin albarka acikin kasuwancin abubuwa sukaita ?ara hayayyafa, har Allah yayi haWuwata dake Jummai mukayi aure. Bayan munyi aure watarana naji wani malami yana wa'azi akan aikata istimina'i yace ma'anar kalmar istimina'i itace zinar hannu, anan ana nufin mutum ya biyawa kansa bu?ata da hannunsa ta hanyar namiji yayi wasa da al'auransa ko mace tayi wasa da farjinta har ya kaiga fitar maniyyi, to wannan shi ake kira da zanar hannu, kamar yadda zina ta kasu kashi uku, akwai zinar ido, akwai zinar hannu, akwai zina ta hanyar mu'amala tsakanin mace da namiji. To tun a wanchan lokacin da naji wa'azin duk sai jikina ya mutu domin bayanan malamin akan istimina'i yazo daidai da irin abinda na aikata mukaje na sayar da maniyyina aka bani kuWi wanda kuma sune suka zama silar arzikina, hankalina ya tashi sosai a wanchan lokacin na kasa samun natsuwa naje nasamu wani malami nayi tambaya akan lamarin, Allah yasa yace min Allah (swa) bayya kama mutum akan laifin da ya aikata cikin rashin sani, amma kuma zama acikin jahilici ba jujja bane, ya zama wajibi mutum ya tashi ya nemi ilimi domin mutum ya san Allah ya san ta yadda zai bauta masa, abinda ya riga ya faru abaya sai ka yawaita yin istigfari ka kyamaci abun acikin ranka, domin Allah shi gafurul rahim ne. Wannan yasa tunda mukayi haka da malamin na haWiye abun acikin raina naketa tuba a kullum. To yau kuma bayanin Sabuwa ya ?ara rikirkitani gabaWaya domin tace maniyyin wani aka saya a ?asar Egypt aka sanya mata a mahaifa, sannan kuma kinga nima siyan maniyyina aka taSayi ban san kuma mi sukayi da shi ba a wanchan lokacin. To duba da irin wannan lamarin zanso kibini muje asibiti domin nima ayimin irin wannan gwajin na ?wayoyin halitta".

Hajiya Jummai ta buWi baki ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Harna rasa abinda zance akan wannan lamari, amma dai kawai yanzu abinyi shine mutafi asibiti kawai batare da kowa yaji ba".

Da "to!" Alhaji ya amsa, sannan ya wuce gaba Hajiya Jummai ta bishi a baya suka fita waje suka shiga mota suka wuce asibiti kai tsaye, suka isa a yayin da sukayi parking Alhaji ya baWe drowrn motar ya Wauki takardun gwajin Hajiya Laila da Sabuwa sannan suka ?arisa lab, sukayi dace kuwa likitan da yayi gwajin su Hajiya Laila shi suka ?ara samu, wannan yasa batare da Sata lokaci ba ya karSi takardun ya Wauki sirinji yaja jinin Alhaji, sannan ya shiga wani Sangare a cikkn wurin.

Bayan kwashe tsawon lokaci da yayi ya fito hannunsa Wauke da takardu guda uku ya ?ariso yadda Alhaji da Hajiya Jummai suna tsaye cirko cirko, ya bu?aci su Wan risina kaWan kafin daga bisani ya sanar dasu cewa "sakamakon muka samu a gwajin da mukayi ya tabbatar mana da cewa Hajiya Laila ?ar Alhaji Alhasan ce".

BuWan bakin Hajiya Jummai ta ce, "kai! Likita ?arya kakeyi, wannan sakamakon gwajin naka ba dai dai bane, tayaya zaka Hajiya Laila ?a Alhaji ce"?

Likitan ya Wan jijjiga kai sannan yace "Hajiya wannan sakamakon gwajin da kika gani duk inda kukaje a faWin duniyar nan shine irin sakamakon da zai ?ara fita, domin mashunan da muke aiki dasu kwanan nan mai girma gwamna yayi order aka kawosu daga ?asar China, dan haka a wannan zamanin babu sama da irin wa?an nan injunan".

Jin hakan yasa Alhaji Alhasan yace "na yarda da wannan gwajin domin komai zai iya faruwa, sakamakon bana mantawa kafin muje wurin da suka sayi maniyyin bayan su Bala sun bani labarin yadda tsarin yake, nayi musu tambaya akan idan sun siya misukeyi dashi? Bala yace min ai har daga ?asashen waje ana zuwa siya domin suma suna amfani dashi, to lokacin nikuma banyi tunanin ana sarrafa shi ta irin wannan hanyar ba, danaji batun kuWi kuma nayi duba da irin matsananincin talauci da nakeci kawai mukatafi wurin, batare dana nemi ilimi akan lamarin ba gashi yanzu abun ya haifarmin da Wan danasani bani kaWai ba hatta zuri'a ta wannan abun bazai daina binsu ba har iya ?arshen rayuwa".

A dai dai nan Alhaji ya fashe kuka ya ?ara da cewa "tabbas nayi nadaman wannan al'amari na ?wammace dana dawwama acikin taulaci da yafi min irin wannan jalala dana tsinci kaina a yanzu, domin ban san me zanje nace ma Allah ba akan irin hanyar da nabi na mallaki wannan dukiyar".

Anan kawai tari ya tirni?e Alhaji atake ya faWi ?asa, kafin aje a Wauko keke da a Wauke a shiga dashi emergency ina rai yayi halinsa, Alhaji Alhasan ya cika, ganin hakan yasa Hajiya Jummai dake tsaye akan Alhaji itama ta yanki jiki ta faWi sumammiya.

Atake aka Wauki Hajiya Jummai aka shige da ita Wakin bada agajin gaggawa, shikuwa Alhaji Alhasan aka wuce da shi mutuware, sannan likitan ya Wauki wayar Alhaji ya buWe yayi dace kuwa babu code akan wayar, ya shiga dialing call anan yaga lambar Hajiya Laila ya danna kira, ta shiga akayi dace kuwa ta Waga ta ce, "hello Alhaji ina kashiga ne tunda mukadawo da kuka fita har yanzu shiru, shin ko lafiya kuwa"?

Likita yace "am, ba Alhaji bane likita ne sun Wazo asibiti ne tun Wazu muna tare dasu anan sakamakon mai keke napep da ya fito musu agabansu suna tafiya da mota, to shine dama yanzu muke bu?atar wani yazo daga gida suna nan babban asibitin Jakusko".

BuWan bakin Hajiya Laila ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!"

Likitan da hanzari ya tari numfashinta yace "am, Hajiya ki kwantar da hankalinki, bawai wani babban hatsari bane ya faru dasu, kawai dai Wimuwa ne".

Hajiya Laila ta ce, "haba likita tayaya zakace ba wani babban abu bane, bayan lamarin har ya kaiga bazasu iya kiran waya ba".

Kawai Hajiya Laila ta katsarda wayar sannan ta dubi Umman ta da Nabila da suke tare ta ce, "to fa zama baikamamu ba domin yanzu haka aka sanar dani Abban Nabila Hajiya Jummai sunyi hatsari suna asibiti don haka kuyi maza kutashi mutafi".

Bashir duk kansu suka tashi suka mi?a asibiti kai tsaye, isarsu ke da wuya suka tarar da Hajiya Jummai ta farfaWo tana zaune akan bakin gado, cikin firgici Hajiya Laila ta ce, "Hajiya ashe abunda ya faru daku kenan, ina Alhajin kuma"?

"Alhaji fa sai dai muyi ha?uri, domin Allah ya karSi abunsa", cewar Hajiya Jummai.

Hajiya Laila ta ce, "ban fahimce kiba fa, kimin gwagwari tayadda zan gane".

Hajiya Jummai ta ce, "to ina nufin Alhaji Allah yayi masa rasuwa Wazu, sakamakon dalilin abunda ya kasance dashi arayuwarsa". Ta ?irge musu tsab duk yadda akayi har ya zama silar da Alhaji ya haWiye ransa ya mutu.

Rufe bakin Hajiya Jummai ke da wuya duk kanninsu uku da sukazo tare suka yanki jiki suka faWi a wurin, bayan angama ?o?arin Webesu a wurin Garzali da Mubaraq suka samu isowa asibitin, anan suka gama tattaunawa akasa lokacin jana'izar Alhaji a garin Gashua wanda za a gabatar washegari da misalin ?arfe 2:00pm, a babban masallacin mai martaba sarki, Daddyn Falila zai jagoranci sallar jana'izar.

Bayan sun gama cika ka idojin asibitin an Wauki gawar anbasu, sunyi ?o?arin bada sanarwan jana'izar a kafafen yaWa labarai domin sanar tarin abokan hulWar kasuwancin wa?an da suke nesa.

Alhaji Sha'aban yana Waya daga cikin ma kusantan Alhaji Alhasan da ya samu isowa tare da iyalensa daga ?asar Japan domin halartan jana'iza.

Washegari.

Da misalin ?arfe 2:00pm, na rana kamar yadda aka sanar aka gudanar da jana'izar Alhaji Alhasan, ya samu tarin dubban mutane, da addu'oi na musamman, kafin daga bisani aka sanar cewa babu zaman makoki".

Bayan Sati ?aya.

An wayi gari da sadakan bakwai, bayan anyi an kammala iyalan Alhaji Alhaji sun bu?aci su zauna dasu maluma wa?an da a cikinsu harda Alaramma Sa'ad domin warware sar?a?iyar da suka tsinci kansu aciki, ta hanyar shari'ar muslimci.

Da farko duk kanninsu iyalan Alhaji Alhasan sun hallara a babban falon gidan, anan ne Garzali ya ?irge musu duk halin da ake ciki, sannan ya jefa tambaya a muluman da suke zaune a wurin kan cewa "to malam yanzu dangane da wannan lamarin ya matsayin Hajiya Laila yake a wurin marigayi a muslimci"?

?aya daga cikin maluman yace "a muslimci shari'a ta kore auren Hajiya Laila da Alhaji Alhasan tun daga lokacin da ya gano ?arsa ce ko da yana raye to babu aure a tsakaninsu, haka zalika yanzu da ya rasu ma to babu takaba a tsakaninsu, sannan kuma bata da gadonsa domin ita ba ?arsa ta sunna bace. To wannan shine a takaice Allah shine mafi sani".

Garzali ya Wan numfasa ya ?ara cewa "to Alashigafatta malam to yanzu ya matsayin Nabila kuma yake"?

Malamin yace "na'am to zance mafi inganci kamar yadda yazo mana a shari'a Nabila ?ar marigayi Alhaji Alhasan ce, kamar yadda abaya aka sameta ta hanyar aure, to lallai ita ?arsa ce kuma tana da gadonsa".

Garzali ya Wan numfasa yace "to masha Allah, Allah ya sakawa malam da alkhairi muna godiya sosai, Allah ya ji?an iyaye".

Duk kaninsu suka haWa baki sukace "amin thumma amin", sannan suka

9 / 12