Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   8 / 12

21K to 24K   out of 33.5K words

gaggawa ne shiyasa ya tafi ba shiri".

Abban Nabila yace "to Allah yasa mudace, nagode sosai", sannan ya dubi Nabila yace "Auta ina dai ana karatun ko"?

"Sosai sosai ma kuwa Abba", cewar Nabila.

Anan suka shiga mota suka wuce, Jabir yacigaba da rarrashin Nabila har suka isa ?ofar gidansu Nabila sannan Jabir yace "my dear ki kwantar da hankalinki akan wannan al'amarin yanzu zan ?arisa gida, idan naje duk yadda mukayi da Mummy nah zan kiraki a waya insha Allah".

Nabila ta ce, "to! Allah yasa muji alkhairi". Anan ta sau?a suka rabu.

Jabir ya nufi gida, a yayin da ya isa ya iske Mummyn sa na kwance a Wakinta, sallama yayi sannan ya nemi wuri ya zauna akan side drowern gadonta, cikin mamaki Mummyn Jabir dake kwance ta ce, "yau lafiya kuwa Jabir naganka haka"?

Jabir yace "ba lafiya Mummy".

Atake ta mi?e ta zauna ta ce, "subuhanallah, mikuma ya faru"?

Jabir yace "Mummy inaso ne ki kira Daddy yanzu ki sanar dashi ya kira Abban Nabila a waya ya nemamin aurenta".

Mummyn Jabir ta Wanyi ajiyar zuciya ta ce, "yoo Jabir banda abunka ai lamarin aure yawuce wasa, ba abu bane da kawai zai Waga waya ya kirashi suyi maganan aurenku ba, domin idan ya kirashi a waya ai bai mutunta lamarin ba, don haka ha?uri kawai dole zakayi sai ya dawo sannan ya shirya musamman yaje suyi magana gaba da gaba".

Jabir ya Wanyi chan yace "to Mummy ni kawai zan wakilta wani yaje min".

BuWan bakin Mummyn Jabir ta ce, "kabar wannan maganan domin bamai yiwuwa bane, muddun Daddyn ka yana raye to ba maganan kaje ka wakilta wani akan maganan aurenka, banyarda ba kuma ban amince ba, abinda nakeso dakai ka nutusu kasa aranka in har Nabila matarka ce, to tabbas sai ka aureta, domin wani baya auren matar wani, don haka kawai mu mi?a al'amarin wa Allah".

Bayan shiru da Jabir yayi harna tsawon wasu da?i?u batare da yace ko uffan ba, ya mi?e ya nufi Wakinsa ya bar Mummyn sa a wurin, shigarsa keda wuya ya ciro wayarsa dake alhujinsa ya lalimo lambar Nabila ya danna kira, yayi dace kuwa ta shiga ringing Winta Waya ta Waga takara a kunnenta sannan tayi sallama, ta ?ara da cewa "habibi ina sauraronka"?

Cikin tattausan murya Jabir yace "my dear, ansamu matsala, sakamakon Mummy nah ta nuna min bazaiyiwu Daddy na da Abbanki suyi maganan auren mu ta waya ba, domin idan hakan ta kasance to ya zama ba darajantawa kenan".

Nabila ta ce, "to yanzu miye abunyi kenan"?

Jabir yace "abunyi Waya ne kawai, zan kwanta rashin lafiyan ?arya, idan Mummy nah taga bayadda nake da zarar ta sanar ma Daddy na halinda nake ciki nasan zai dawo ba shiri, daga nan kuma kinga kafin ya ?ara komawa sai yaje ya samu Abbanki su zaunar da magana".

Nabila ta ce, "amma gaskiya wannan lissafine mai kyau, najidaWin jin wannan maganar don haka Allah yasa mudace kawai zamuce". Anan sukayi sallama suka katsar da wayar.

Washegari.

Jabir lafiyarka kuwa tun jiya kana kwance ko abince ba kafito kaci ba"? Cewar Mummyn Jabir. Shiru tamkar babu mutum acikin Wakin, ta?ara da ambaton "Jabir", har sau uku duk dai bai amsa ba, cikin firgici ta?arisa jikin gadon da Jabir ke kwance tasa hannu ta Wan jijjigashi, Jabir ba magana sai ido kawai, atake Mummyn Jabir tayi salati ta sanarwa ubangiji sannan ta Waga waya takira lammar Daddyn Jabir, Wagawarsa keda wuya suka gaisa sama sama ta sanar dashi halin da Jabir yake ciki, buWar bakin Daddyn Jabir yace "subuhanallah, to yanzu abunda za'ayi bari zanyi waya da Doctor yanzu sai yazo ya dubashi emergency, in yaso zuwa gobe sai kubiyo jirgi kuzo nan Japan inda nake, nafahimci yanayin wayan Wawainiyar da yake cikin makarantarsu ne yake sa Jabir yin laulayi, don haka gobe kawai sai ku taho nan, asamu ?wararrun likitoci su dubashi, idan ya samu sau?i kuma sai kawai ya cigaba da karatunsa ana Tokyo, tunda tunda akwai banbanci sosai da nan Japan da ?asar Nigeria, ni ina ganin wannan kawai shine mafita".

Jin hakan yasa Mummyn Jabir ta ce, "duk yadda kace ayi ai haka za'ayi Alhaji fatan mudai shine Allah yasa mudace, yasa kuma goben muna cikin rayayyu".

Bayan Mummyn Jabir ta katsar da wayar, jim kaWan Doctor ya samu isowa ya tarar da ita tanata kai kawo a cikin Wakin Jabir, ta kasa zaune ta kasa tsaye duk tabi ta Wimauce, ganin Doctor yasa ta Wan risina tana mai cewa "yauwa Doctor sannu da zuwa".

Doctor ya amsa da cewa "yauwa sannu, ina Jabir Win"?

"Gashi nan shine acikin bargon nan", cewar Mummyn Jabir, tana mai nuna shi da ?ar tsarta.

Doctor atake ya ?arisa kan Jabir ya fara gudanar da gwaje gwaje akansa, wanda ya shafe tsawon lokaci yanayi, kafin daga bisani ya dubi Mummyn Jabir yace "Hajiya a gaskiya duk wani gwaji da yakamata nayi na riga nayi shi yanzu, amma banga komai ba atattare da Jabir, sai dai kawai yanzu zan Waura masa ruwa sakamakon kince baya cin abinci, kafin zuwa goben in kunje chan Japan tayiwu sugano abinda yake damunsa domin suna da ingantattun kayan aiki".

Cikin gaggawa Mummyn Jabir ta ce, "to Doctor dan Allah kayi sauri maza ka Waura masa ruwan".

Da "to!" Doctor ya amsa, sannan ya ?ara da cewa "Hajiya ki kwantar da hankalinki pls, wannan bawani abun damuwa bane, zai samu sau?i insha Allah". Daga ya Waurawa Jabir ruwan atake ya fara tafiya ajin sa.

Washegari.

Da sanyi safiya Mummyn Jabir ta fara fitowa harabar cikin gidan Wauke da wasu manya manyan jakakkuna kirar trolly, tayi umurni wa driver da ya shirya jakakkunan acikin wata mota hilux dake fake car park, daga bisani kuma tasa wasu daga cikin ma'aikatan gidan suka Wauko Jabir suka sashi a mota, itama ta shiga driver ya Waukesu ya kaisu air port, saura minti goma kachal jirginsu Jabir ya tashi, ya lalilmo wayarsa yayi typing text message a fakaice "Aslm, my dear kiyi ha?uri da abinda zan faWamiki, yanzu haka jirgin mu zai tashi zuwa Japan. Amma kisani kina rai na". Anan Jabir ya kawo ?arshen sa?onsa ya turawa Nabila.

Bayan Kwana Biyu.

"Nabila har yau bakice min komai ba akan ba?on da yazo wurinki kwanan baya, to a ina muka kwana ne akan lamarin"? Cewar Ammin Nabila.

Nabila ta buWi baki ta ce, "Hajiya yanzu kam a Wan dakata da wannan maganar tukun, tunda kinga goben nan zamu fara exam in Allah ya kaimu".

Ammin Nabila ta ce, "to bakomai Allah yasa kugama lafiya, amma ya kamata nasan me ake ciki domin nasan ako da yaushe Abbanki zai iya tambayata wata matsaya kuka tsayar akan lamarin"?

Nabila ta ce, "insha Allah da zarar mun kammala exam zaku san duk abinda ake ciki". Sannan Ammin Nabila tawuce ta bar Nabila ta cigaba da karatun exam da takeyi.

Washegari.

Anwayi gari antashi da exam duk kannin Waliban kowa ya hallara domin rubuta jarabawar secend semester.

Falila.

"Nikam dai har yanzu banga banga Yaya Jabir ba, gashi kuma har ana shirin shiga exam hall". Cewar Falila.

Nabila ta Wanyi ajiyar zuciya sannan ta ce, "kibari kawai shi kam ai ya bar ?asar nan".

Cikin mamaki Falila ta ce, "kamarya yabar ?asar nan, ban fahimceki ba"?

Nabila ta ce, "kwanan bayan nan Daddyn sa yayi musu visa da Mummyn sa suka tafi wurinsa a chan Japan, hatta karatunsa da komai yanzu sun koma chan gabaWaya".

Suna cikin tsaka da zancen sukaga anfara shiga exam hall, wannan yasa suka mi?e suka nufi hall Win ba shiri. Haka suka kasance kusan kullum suna gudanar da exam har tsawon sati biyu, kafin suka samu nasarar kammalawa.

A ranar da aka kammala exam Nabila da Falila sunyi bankwana akan Nabila zata tafi hutu garin su Abbanta tana mai Wauki suka rabu.

Hajiya Laila.

"Ammi yau kam Allah yayi mun kammala exam Win mu, saura ki cika min alkawarin da kika Wauka min na cewa zamuje Jakusko", cewar Nabila.

Ammin Nabila ta ce, "masha Allah, to Allah yasa kun rubuta exam Win duka a sa'a,", sannan ta?ara da cewa "to batun zuwan mu Jakusko kuma bari Abbanki ya shigo zanyi masa maganar tafiyan insha Allah".

Da "to!" Nabila ta amsa tana mai farin ciki tawuce falo, shigarta ke da wuya ta iske Abbanta tare da Hajiya Jummai suna zaune suna hutawa, atake Nabila ta juya takoma ta sanar da Amminta domin tazo ta gabatarwa Abbanta ?undirin tafiyarsu. Hajiya Laila ta mi?e suka taho tare da Nabila gaba da baya har cikin falon Alhaji, anan Hajiya Laila ta gabatarwa Alhaji batun tafiyan su Jakusko.

Jin hakan yasa Alhaji yace "to wannan aiba abun damuwa bane, zuwa gobe sai kushirya har dake ma Hajiya Jummai sai mutafi muje mu kwana biyu muyi ziyara mudawo ko"?

Suna masu shau?i duk kansu suka haWa baki sukace "eh tabbas hakan yayi, Allah ya kaimu goben".

Washegari.

Suka kintsa tsab suka tafi Jakusko isarsu suka sau?a a family house Winsu Alhaji, wanda yake Wauke da wasu tsirarun ?an uwan Alhaji da suke zaune a cikinsa, sakamakon gida ne mai Wauke da ?ofa ?ofa daban daban, ganinsu Alhaji yasa ?an uwa da abokan arzi?i kowa yayi murna da ganinsu, kwanansu biyu a garin Alhaji ya fita cikin gari kamar yadda ya saba ya dawo musu da labarin "yau fa ina tafiya a mota kawai sai na haWu da Sabuwa tana tafiya a gefen hanya amma dakyar na ganeta, sakamakon naga gabaWaya ta tsufa min".

Jin hakan yasa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Hajiya Laila tunawa da maganar da Alhaji ya taSa faWa mata akan Sabuwa atake ta ce, "amma Alhaji nikam da zanso ka kaini inda Sabuwa take na ganta".

Alhaji yace "to badamuwa wannan kam, domin aita faWamin tana gidansu yanzu sakamakon aurenta ya jima da mutuwa, don haka ko yaushe ma zaku iya shiryawa sai muje gabaWayan mu ko"?

Duk kansu suka haWa baki sukace "mukam aiko yanzu ma inka yarda mutafi kawai".

Alhaji yace "to maza ku tashi muje", batare da Sata lokaci ba duk kansu suka Wauki mayafai suka sanya suka fita, basu tsaya ako ina ba sai a ?ofar gidan da Sabuwa take, Alhaji yayi birki suka fito a mota sannan suka shiga cikin gidan suka iske Sabuwa tana tankaWen garin masara, da sukayi sallama Sabuwa ta mi?e tana mai cewa "sannunku da zuwa marabanku", tawuce Waki ta Wauko taburma ta shimfiWa musu, suka zazzauna sannan suka gaisa sosai.

Bayan sun gaisa ganin Sabuwa duk kansu suka shigayi a tsakaninsu, mamaki duk ya ishesu duba da irin kammannin da Hajiya Laila takeyi da Sabuwa, wannan yasa Hajiya Laila takasa ha?uri ta ce, "baiwar Allah na tambayeki mana"?

Sabuwa ta ce, "to Allah yasa nasani".

Hajiya Laila ta ce, "dan Allah ke mutumiyar ina ne, sannan kuma inaso na Wanji kaWan daga tarihin rayuwarki idan bazaki damu ba"?

Sabuwa ta buWi baki ta ce, "ni haifaffiyar garin Jakusko ce, nan shine asalin gidan iyayena inda aka haifeni, a wanchan lokacin ya kasance ginin taSo ne saSanin yanzu kuma da yazamto ginin zamani, mahaifiyata sunanta Talatu yanzu shekara uku kenan da rasuwarta itama ?ar asalin garin nan ce, haka zalika mahaifina Malam Lawan shima Wan asalin garin nan ne, shima Allah ya masa rasuwa, sannan kuma abaya na taSayin aure a garin Damaturu sunan mijina Alhaji Falalu mun kwashe tsawon shekaru dashi muna tare amma Allah bai bamu haihuwa ba har muka rabu. To kinji wannan shine Wan ta?aitaccen tarihina kenan".

Jin hakan yasa Hajiya Laila ta?ara ?ura mata ido ta ce, "amma ko kin lura da muna kama sosai kuwa"?

"Eh sosai ma nima na lura da haka", cewar Sabuwa.

Cikin kwarin gwiwa Hajiya Laila ta ce, "ni suna Laila, ni iyalin Alhaji Alhasan ce, wannan kuma ?ata ce Nabila, sai kuma abokiyar zamana Hajiya Jummai, to a gaskiya sabida wasu kwararan dalilai idan bazaki damuba zanso kibani dama muje muyi gwajin kwayoyin halitta dani dake, sakamakon irin tsantsar kammani da ya bayyana a tsakanina dake".

Sabuwa ta Wanyi shiru chan ta ce, "to badamuwa idan Allah ya kaimu gobe sai kuzo muje muje babban asibiti sakamakon yanzu dare yayi tunda kinga yanzu tuwon dare na Waura akan wuta".

Hajiya Laila ta buWi baki ta ce, "to bakomai Allah ya kaimu goben, muna godiya sosai da sosai".

Anan sukayi sallama suna masu shau?i suka rabu da yarjejeniyar washegari zasu dawo domin zuwa asibiti.

Washegari.

Tun misalin ?arfe 8:00am, Hajiya Laila ta shirya tsaf ta fito take tsumayin fitowar abokanen tafiyar ta, ta kwashe sama da daki?a ashirin tana dakonsu a tsakar gidan kafin daga bisani suka fito suka shiga mota Alhaji ya tu?asu zuwa gidan Sabuwa, isarsu sukayi dace itama Sabuwa ta kintsa tsab jiran isowarsu kawai takeyi kamar yadda sukayi alkawari, wannan yasa batare da Sata lokaci ba, suka Wunguma gabaWaya suka shiga mota suka nufi babban asibiti da isarsu suka nufi lab kai tsaye, sun shiga sun tarar da mutane sosai a cikin wurin, amma Alhaji ya samu zantawa da Waya daga cikin ma'aikatan wurin wanda shine incharge, duba da irin gwajin da sukazo ya banbanta dana sauran mutane incharge yayi umurni a wani daga cikin ma'aikatan ya kira Hajiya Laila da Sabuwa suka shiga wani Waki na musamman. Bayan sun kwashe tsawon lokaci suna ciki daga bisani suka fito inda su Hajiya Jummai suke zaune, suna cikin hirarsu shi wanda ya gwadansu ya fito da takardun sakamakon gwajin a hannunsa ya mi?awa ko wacce nata a hannunta.

Hajiya Laila ta ce, "likita muna bu?atar kayi mana ?arin bayani dangane da sakamakon gwajin"?

Likitan yace "abinda sakamakon gwajin ya nuna shine, ke da ita jini Waya ne, wannan mahaifiyarki ce".

"Ya salam", cewar Alhaji, ya ?ara da cewa "Sabuwa kina nufin kenan Laila ?ar Alhaji Falalu ne"?

Sabuwa ta buWi baki ta ce, "a'a ba ?arsa bace".

Hajiya Laila ta rungume Sabuwa ta ce, "dan kiyi mana cikakken bayani mana, muna bu?atar kiyi mana bayani, minene gaskiyar al'amarin nan"?

Sabuwa tayi shiru, akayi akayi sam ta?i cewa komai, wannan yasa duk kansu suka shiga mota suka tafi fada gaban sarki suka ?irge masa duk abinda ake ciki, sarki ya dubi Sabuwa yace "baiwar Allah minene gaskiyan al'amarin nan kifaWa mana muna sauraronki"?

Sabuwa anan ta?ara yin shiru, babban zagi ya dubeta da babbar murya yace "ke! Ki kula nan a fada kike, sarki yana tambayanki kiyi bayani"?

Sabuwa cikin tattausar murya ta ce, "gaskiyar kenan ba ?ar Alhaji Falalu bace, ni Allah ya sani bantaSa haihuwa dashi ba har muka rabu, kuma a rayuwata shina fara aura kuma bayan shi ban?ara auren wani ba".

Jin hakan yasa sarki yace "to kenan kin samu wannan yarinyar ta hanyar zina ne"?

Sabuwa ta ce, "ni tunda Allah ya halicce ni bantaSa aikata zina ba a rayuwata".

Sarki ya Wan numfasa yace "ke wai mi kikeso ki mai damune, to amma kin yarda da wannan gwajin da akayi"?

Sabuwa ta ce, "eh na yarda na amince".

Jin hakan yasa sarkin malamai dake zaune a gefe ya shiga yin nasiha a Sabuwa yana mai cewa "baiwar Allah ya kamata kiji tsoron Allah da ya halicceki kifaWi gaskiya, koma miye tunda har bakiji tsoron Allah ba kika aikata to baikamata kiji tsoron Wan Adam ko kunya ba, dan Allah ina ro?onki da kidaure kifaWama gaskiyan abinda ya faru domin itama wannan baiwar Allah da kika amsa kece mahaifiyarta ta samu sau?i a cikin ranta, kiyi ha?uri kifaWa mana miya faru"?

Sabuwa ta ce, "abinda ya faru shine, watarana lokacin ina budurwa munje rakiyar biki Damaturu na wata ?awarmu, ni da ?awata Laure daf da magriba muka fita siyan awara akan layin unguwan anan muka iske Alhaji Falalu na zaune akan kujera a ?ofar gidansa ya fito la'asariya, ganin mu zamu wuce yace dani ke ?an mata zo mana, banyi masa taurin kai ba, na juya naje gareshi ya tambayeni ya sunanki? Nace da shi Sabuwa, ya ?ara tambayata ke ?ar gidan waye? Nace masa niba ?ar garin nan bace daga Jakusko mukazo biki, yace min a wani unguwa kike a Jakusko? Nace masa ina unguwar kan tudu, sunan babana Malam Shehu, ya Wanyi shiru yace toshikenan kuje kawai, mukawuce muka tafi washegari biki ya?are muka koma gida. Kamar wasa bayan kwana biyu da komawar mu gida, Alhaji Falalu ya taso yazo gidan mu yayi sallama da mahaifina yayi dace kuwa ya dawo daga gona ya iske shi a gida, mahaifina ya fito ya dan?areriyar mota a fake a ?ofar gidan mu, Alhaji Falalu ne ke tsaye a jikin motar, suka gaisai sosai, sannan yace masa nazo ne akan lamarin ?arka Sabuwa, idan ka amince inaso zan aureta, kuma banaso gabaWaya auren yawuce wata Waya kachal domin bana bu?atar komai daga gareku, a cikin wata Wayan ne kuma zan saka a rushe wannan gidan naka a gina maka sabo domin ayi hidima acikin sabon gida, daga bisani kuma sai na baka jari ka huta da zuwa gona da kake fama dashi. Jin hakan yasa batare da mahaifina yayi shawara da kowa ba yace ya amince masa, Alhaji Falalu ya tafi, shi kuwa mahaifina ya shiga gida suna kan maganar da mahaifiyata ni kuma na shigo na dawo daga tallen kunu a wanchan lokacin, suka ?irgemin duk halin da ake ciki atake na nuna ?in amincewata da lamarin, wanda hakan ya fusata iyayena har ya kaiga suka bani zaSi akan nazaSa ko saurayina Alhasan da nake tare dashi a wanchan lokacin ko su? Nace na zaSesu, buWan bakin mahaifina yace to kin zaSi Alhaji Falalu kenan, domin muddun kinaso ki zauna damu a matsayin iyaye to lallai sai kinbi zaSin mu, kuma sai kinyi biyayya a Alhaji Falalu. Inaji ina gani haka nayita kuka babu yadda zanyi akazo aka rushe gidan mu akayi ginin zamani daga bisani aka Waura aurena da Alhaji Falalu natare gidansa a Damaturu. Bayan natare daga cikin matsalolin Alhaji Falalu dana fara fiskanta shine, shi mutum ne mai auri saki, kuma ya kasance yana da matsala ta rashin haihuwa likitoci suntabbatar masa da bazai taSa haihuwa ba, wannan dalilin yasa yake amfani da tarin dukiyar da Allah ya hore masa wajen gudanar da auri saki. Bayan mun kwashe tsawon lokaci muna tare da shi, watarana bana mantawa yazo yace min Sabuwa wato a gaskiya na auri mata bila adadin arayuwata amma sai dai bantaSa auren macen da nakesonta bil?i ba irinki, don haka inaso nasa Wa wanda zai zamto tsatsonki ne, cikin mamaki nace masa Alhaji kaida ga matsalar da kake da ita kuma taya zamu samu Wa? BuWan bakin Alhaji yace kedai karki damu kishirya kawai acikin satin nan zamuje ?asar Egypt asibiti

8 / 12