Jinina Book Complete Hausa Novels By Sagiryellow.doc

Author :  Sagir Yellow Category :  Hausa Novels 001

Chapter   5 / 12

12K to 15K   out of 33.5K words

shawara ba, da zuciyata zanyi".

"To badamuwa Allah yasa mudace", cewar Jabir. Ya ?ara da cewa "gashi wa?an nan papers Win test Winki ne. Nabila tasa hannu ta karSa tana mai godiya ta wuce tabar Jabir a wurin.

Wucewar Nabila taje tasamu wuri ta zauna ta fara duban takardun test Winta, ganin yadda sakamakon test Win ya kasance ya zame mata abun farin ciki sosai, ?ara kallon takardun takeyi tana murmushi, batayi aune ba taji an rufe mata idaniyanta batare da tasan kowaye ba, buWan bakin Nabila ta ce, "besty".

Falila tasa dariya ta ce, "ya akayi kikagane ni"?

"Haba ke kuwa yau da gobe ai yawuce wasa", cewar Nabila.

Falila ta ce, "hakane kam, ?awata ya kikaga takardun test Winki, a gaskiya kin bada wuta sosai".

Ajiyar zuciya Nabila ta sauke ta ce, "ke yanzu dai duk ba wannan ba, mutuminki wai yana sona".

Cikin mamaki Falila ta ce, "wa kenan, Yaya Jabir"?

Nabila ta ce, "eh!"

Falila ta ce, "lallaima besty wai ma fa kike cewa Yaya Jabir yana sonki"?

"eh mana", cewar Nabila, ta?ara da cewa "na Wauki tsawon lokaci inajin jita jita cewa Jabir yana sona, amma ni sai yau na tabbatar da naji daga bakinsa, kuma inda bai furtamin da bakinsa ba, inza a shekara Wari nan gaba haka zan cingaba da Waukar lamarin ko oho, sakamakon ina son naga mutum yana da comfidence musamman akan abinda mutum yake so".

Jin hakan yasa Falila ta Wauke zancen ta ce, "to yanzu dai kitashi mu ?arisa wurin test Win nan".

Suka tashi suka kama tafiya suna hirarsu har suka ?arisa wurin, zuwansu yazo daidai da an hau layi an fara shiga, suma suka hau layi aka tantancesu suka shiga, chan bayan wani lokaci aka fara fita a yayin da fitar Jabir da Falila ta zamto gaba da baya, da hanzari Falila ta isko Jabir a lokacin da yake tunkarar inda ya faka motarsa.

Falila ta ce, "Yaya Jabir yau kamin daidai wallahi, domin yau koba komai ka kashe boss, najidaWi da ka furta kalmar so a Nabila, domin zakaga amfanin hakan, daga yau ka rubuta ka ajiye ko da bata sonka to kawuce ta sakeyi maka irin rainin da ta saba yimaka abaya, wannan Wabi'ace tamu ta mata duk haukar yarinya indai ka furta kana sonta to dole intaganka tasha jinin jikinta sabida kalmar so kalmace mai nauyin gaske a wurin duk wata ?a mace".

Jin hakan yasa Jabir ya Wanyi ajiyar zuciya yace "?anwata kenan, inaso zamuyi magana amma banaso Nabila ta ganni dake a matakin yanzu don haka ki koma nasan ta fito tana jiranki yanzu daga baya zamuyi magana".

H.O.D

"Akwai saura sati Waya da ya rage mufara exam anan gaba, sabida haka har yanzu kina da damar da zaki iya amfani da ita ki gyara feturen ki, sakamakon akwai yara mata da yawa irinki da sukayi amfani da damarsu suka kammala karatunsu da kyakkyawan result, irin wanda duk wata babbar ministry a ?asar nan suke da bu?ata, da dama daga cikinsu wasu suna NNPC, wasu suna PORT AUTHORITY dadai sauransu, don haka kema kina da damar da zaki iya kasancewa Waya daga cikin wa?an nan ma'aikatun", cewar H.O.D.

Nabila ta ce, "Sir kayi ha?uri da abinda zan faWa, domin a gaskiya bazan iya aikata alfasha ba, sabida ina tsoron azabar ubangiji, don haka na Waukawa kaina alkawarin sai nakai budurcina Wakin mijina, a gaskiya nazaSi ka zartar da duk wani hukunci saSanin abinda kakeso mu'aikata naje na tarar da azabar Allah".

Juyawar Nabila ke da wuya, H.O.D ya Waga hannu ya bigi teburin dake gabansa yace "yarinya ?arya kikeyi wallahi".

Nabila ba tayi ?asa a gwiwaba ta fice daga office Win, fitowarta Sacin rai yasa batayi tsumayin Yaya Mubaraq ba tawuce gida, a yayin da Nabila ta isa gida duk da irin jalalan da take ciki bashi ya hanata dukufa akan karatu ba, wanda takasance kullum ba dare ba rana har zuwa ranar da aka wayi gari sun fara exam.

Bayan Exam.

Hutun tsawon sati Waya kachal akayi wanda shine ya raba tsakanin first semester da second semester, sati Waya da dawo kuwa acikin na biyun aka fidda result Win jarabawar da aka gabatar na first semester, result yayi kyau sosai a mafi yawan Walibai, wasu daga ciki kuwa sai dai ace ba yabo ba fallasa, kamar irin Nabila da sauran wasu tsirarun Walibai kuwa, ya tabbata sunyi refeating tun a matakin jarabawar first semester sakamakon irin tarin carry over da yake kansu.

Falila.

"Wato yanzu Allah ya kawomu wani zamani ne wanda rayuwar ?a mace abune mai matu?ar hatsari, domin yana da wahala kiga ?a mace ta taka matakin nasara bata fiskaci ire iren wa?an nan ?alubalen ba na miyagun maza. Abinda zai baki mamaki irin wa?an nan al'amuran alfashan basu tsaya a iya makarantu ba, hatta a asibiti kwanan baya da naje ganin likita haka Wan talikin nan ya ringa ?o?arin kai hannunsa wasu Sangarori na jiki na wa?an da basu shafi lalurar da take damuna ba, ?arshe har sai da yaga raina ya Saci ina ?o?arin tara masa jama'a, sannan jikinsa yayi sanyi ya fara bani ha?uri, inaji ina gani haka na fito na koma gida na ha?ura da ganin likitan, to irin wannan abu shine ya zama ruwan dare, ?an mata zina, matan aure zina, kwata kwata wasu mutane basa tunanin makomarsu, da kuma yadda rayuwar ?a?ansu zata kasance a gaba. To da wannan nake fata Allah yasa mufi ?arfin zukatan mu, ya bamu ikon mu tsira da mutuncin mu".

Nabila ta buWi baki cikin shishshitan majina tana kuka ta ce, "to Allah dai yasa mu dace kawai, amma wallahi ni yanzu harna rasa ma me zanyi a rayuwata".

Cikin alhini Falila ta ce, "abunyi Waya ne kawai yanzu, wasi?a zamu rubuta mukayi senate na wannan makarantar a admin block, akan cewa lallai ke baki yarda kin faWi jarabawa ba, tunda akwai wannan tsarin dama a cikin dokar makaranta, idan kina da ya?inin kinci jarabawa kuma kikaga kin faWi to zaki iya shigar da ?ara, a doka za'asake yimiki jarabawa akan course Win, anemo wani lecturer daga wata jami'a yayi marking, idan har kinci to lallai dole hukumar makaranta zata kori malamin, idan kuma har bakici ba to kema dole za a kore ki. Don haka ina da ya?ini akan zakiyi nasara akan wannan azzalumin mutumin, sabida haka kiyi ha?uri maza kitashi muje".

Batare da Nabila tace uffan ba, ta tashi suka shiga cikin Waya daga cikin ajijjiwan da suke department Winsu, a lokacin Falila ta cire fallen paper ta tsara wasi?a yadda ya dace, sannan ta bu?aci Nabila ta tashi sukayi, Nabila ta mi?e suka nufi admin block, isarsu wurin Falila ta dam?a mata takardar a hannunta ta?arisa ciki ta mi?a musu ta fito, sannan Falila ta ce, "yanzu abinda ya kamata muyi shine, muje ta commercial mu sayi ruwa ki wanke fiskarki, domin duk wanda ya ganki yanzu ya san kinyi kuka".

Da "to!" Nabila ta amsa, sannan suka nufi commercial domin siyan ruwa, anan suka iske Jabir tare da abokansa a wani resturant suna cin soyayyen dankalin turawa.

Batare da Jabir ya san halin da ake ciki ba, ya taso yasha gabansu yace "Nabila wurinki nazo".

Jin hakan yasa Falila tawuce ta nufi wani shago da ake sayar da drinks a harabar wurin, shi kuwa Jabir ya Wan ?ara gyara tsayuwa yace "Nabila kwana biyu na jiki shiru, akan maganar da mukayi, ni yanzu kawai zanso naji ra'ayinki akaina"?

Nabila ta buWi baki ta ce, "badamuwa nima na'amince".

ZumuWi Jabir ya shigayi yana mai cewa "Nabila wai yanzu kina nufin kema kina sona kenan, kai amma ni yau zan iya cewa duk duniya ba wanda ya kaini sa'a, don haka tsantsar farin ciki dana tsinci kaina aciki yanzu yasa bakina bazai iya furta miki komai ba face "ina godiya sosai, ina fata kuma Allah yasa muci ribar soyayya, na barki lafiya".

Anan Jabir yawuce ya bar Nabila na tsaye a wurin tana jiran dawowar Falila, shiru ba labarin Falila har Nabila ta ?osa da tsayuwa ta bita shagon da ta shiga ta isketa a zaune akan wata kujera hannunta Wauke da goran peach da alamun kurSa takeyi a hankali, ganin hakan yasa cikin Sacin rai Nabila ta ce, "Falila wannan wani irin abune kuma, kin san kinbarni a tsaye zakizo ki kama wuri ki zauna"?

Cikin ba'a Falila ta ce, "Allah ya baki ha?uri besty, ni wai na baku wurine domin kuWan soye abunku".

Nabila ta ce, "a'a barin mu kikayi mu ?one ba soyewa, ?ar rainin wayo kawai".

Falila ta Wanyi murmushi ta mi?e ta karSi faro botle water, ta mi?awa Nabila ta ce, "to ki karSi ruwan nan ki wanke fiskarki sai mutafi ko"?

Da "to!" Nabila ta amsa, sannan tasa hannunta ta karSi goran ruwan suka fita a shagon, chan har sunyi nisa da tafiya Falila ta ce, "am, besty nikam ya kukayi da Yaya Jabir ne Wazun"?

Nabila ta ce, "ya ?ara tuntuSana ne akan amsar soyayyarsa, duba da abunda ya faru dani a school, ni yanzu idan na tafi bazan ?ara dawowa ba har sai idan ya tabbata naci jarabawar da za a ?aramin kwanan nan kafin na cigaba zuwa makaranta, to shiyasa nace masa ba matsala na amince, sakamakon nasan balallai mu?ara haWuwa dashi a kusannan ba, dan yanzu gadan gadan zabuWe wuta a hadda ne sosai, sabida tafiyan mu Abuja yayi kusa".

Jin hakan yasa cikin sanyin jiki Falila ta ce, "haba besty miyasa zakiyi saurin yanke hukuncin daina zuwa makaranta, bayan kinsan yanzu ne lokacin da ya kamata ki tsaya ki mayar da hankali akan wannan semestern, to gaskiya ni ban laminta da wannan shawaran da kika yanke ba".

Nabila ta ce, "abinda zaki duba anan shine, ba a tauna taura biyu a baki Waya ai, dama yanzu anzo matakin da ko da komai yana tafiya normal to dole na daina zuwa school na dukufa akan hadda ba dare ba rana domin abinda nake tunkara anan gaba".

"Eh to kema kince wani abu", cewar Falila. Ta ?ara da cewa "amma dai ki sani daga ni har Yaya Jabir ba ?aramin kewarki zamuyi ba". Anan sukayi sallama suka rabu.

Bayan Sati ?aya.

Hukumar makaranta ta samu sanarar kammala bincike akan ?oarafin da Nabila ta shigar game da jarabawar da ta faWi a semestern da ya gabata, wannan yasa aka gayyato wani leturer a sashen biochemistry dake jami'ar Kaduna State University (KASU), domin yazo yayi marking na jarabawar da za asake bada dama a Nabila ta rubuta, cikin ikon Allah da yardarsa an wayi gari Nabila ta kammala dukkanin exams Win da takai ?orafinta akansu cikin kwana biyar kachal aka gama komai yanzu dai kallo duk ya koma kan lecturer da aka gayyato daga Kaduna State University yazo Uni Gash domin tabbatar da gaskiya akan marking Win jarabawar Nabila.

Nabila.

Nabila tana zubda hawaye ta ce, "ni dai na riga da nami?a dukkannin al'amurana wa Allah, a kullum ina ro?onsa ya tsayamin akan al'amurana, tunda yau saura sati biyu kenan a fidda result Win jarabawa na, gashi kuma kinga gobe ne tafiyata musaba?a Abuja, don haka tayiwu yau shine ?arshen haWuwata dake acikin makarantar nan besty, idan ya kasance an kore ni, to shikenan inayi miki fatan alkhairi akan karatunki, sannan kuma nasiha ta agareki itace, kar kisake wani ?aton banza ya ruWeki ya rusa miki tarbiyarki da sunan wai zai taimakeki akan ko wani irin abune arayuwar nan domin akwai mutuwa, ya kamata kirin?a tunawa da wannan, kiji tsoron Allah a duk inda kike".

Anan Nabila ta kawo ?arshen maganarta kawai ta rungume Falila sukaita kuka har sai da suka ?oshi abunsu, sannan sukayi bankwana a wurin.

Washegari.

Da sassafe Nabila ta kintsa tsaf ta fito falo ta tarar da Alhaji tare da Hajiya Jummai da Amminta duk kansu sun hallara a falo domin yi mata addu'a tare da yin bankwana da ita.

Duba da yanayin lokacin da aka tsara na tashin jirginsu Nabila zuwa Abuja yasa a gurguje suka gabatar da addu'oi tare da fatan alkhairi, sannan suka fito harabar cikin gidan, anan suka iske Ubale driver yana goge Waya daga cikin motocin gidan, Alhaji ya juya ya dubeshi yace "Ubale zo maza ka hanzarta kaWauki Nabila a mota ka kaita islamiyyarsu yanzu yanzun nan".

Da "to!", ya amsa, sannan yayi hanzari ya Wauki jakar kayan Nabila ya sanya acikin boot Win wata mota ?irar camry blutooth, duban Nabila yayi yace "bismillah ki shiga mu tafi ko"?

Atake Nabila ta buWe ?ofar motan ta shiga, Ubale ya tayar da motar suna bye bye a junansu yaja suka tafi, kai tsaye basu tsaya ako ina ba, sai a farfajiyar islamiyyan Ubale yayi parking.

Fitowar Nabila a cikin motar anan ma ta tarar da malamai da dama sun hallara domin ganin tafiyar ta, a yayin da senior master ya kasance shine wanda hukumar makaranta ta wakilta a matsayin wanda zasu tafi da Nabila, wannan yasa batare da Sata lokaci ba Nabila ta gaggaisa dasu sama sama, sannan senior master ya shiga mota suka nufi garin Damaturu domin hawa jirgi a babban filin hawa da sau?an jirage dake garin (air port).

Kasancewar Ubale driver mutum ne wanda ya kwashe tsawon shekaru a harkar tuki, irinsu ne ake kira da tsofin direbobi, sakamakon ya samu ?warewa sosai a fannin tu?i, wannan yasa da suka hau kwalta Ubale yaja sit belt ya sanya, kafin kyafta ido da bismillah kawai sai gasu a cikin filin jirgi a garin Damaturu.

Isarsu ke da waya saura ?an mintuna ?alilan jirginsu ya tashi, sakamakon dama anyi musu booking fly, tun kafin ranar domin tafiya musaba?an. Jim kaWan suna tsattsaye kawai sukaga an fara shiga jirgi yana shirin tashi. Anan sukayi bankwana da Ubale suma suka wuce wurin shiga jirgi.

Abuja Nigeria.

Cikin ikon Allah da yardarsa jirgin su Nabila ya sau?a a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja lafiya ?alau, daga Damaturu zuwa Abuja tafiya ce wacce ta Waukesu tsawo minti 40 kachal acikin jirgi, sau?arsu ke da wuya saka hau taxi zuwa International Comference Center (ICC), inda anan ne aka shirya national musaba?an, suka shiga taxi ya kaisu har bakin gate Win wurin kamar yadda suka ba?aci hakan, anan suka sallameshi ya tafi, sannan sukayi amfani da takardun shaidar halartar musaba?an akabarsu suka shiga cikin wurin.

Tsawon kwana biyu aka kwashe tare da mahalartan musaba?an acikin ICC, anan tantance Walibai batare da an fara gudanar da gasar ba.

Wayewar garin ranar litinin aka tashi da fara gabatar da gasar kamar yadda aka tsara, za a Wauki tsawon kwana goma ana gudarwa kafin daga cikin Waliban a ware zakaru guda uku daga cikinsu.

Akwana atashi an wayi gari kwana goma ta cika cif cif, a yayin da aka kira chairman na musaba?a mai suna Alaramma Sa'ad da yazo ya sanar da sakamakon yadda musaba?an ta kasance, Alaramma Sa'ad ya fito ya fara da godiya ma Allah da ya bada ikon kammala wannan gasa lafiya, daga bisani ya ?ara da jawabai masu jan hankali, da kuma muhimmancin ri?o da alqur'ani mai girma, sannan daga ?arshe ya ayyana sunan "Nabila Alhasan itace Waliba da tayi nasarar zuwa mataki na farko a wannan gasa da aka gabatar, don haka Nabila Alhasan sai ki fito wannan fili domin ki karSi kyaututtukanki kamar yadda aka tanadar a duk wanda yayi na sarar lashe wannan gasa".

Nabila ta mi?e daga cikin sauran Walibai da suke zaune a babban Wakin taron, mi?ewar Nabila ke da wuya wurin ya ruWe da kabbara har ta ?arasa gaban Alaramma Sa'ad ta tsaya, daga cikin kyaututtukan da Nabila ta samu, tasamu kujerar hajji, na biyu kuma, an bata scholarship zuwa jami'atul Madina, domin samun daman ?ara inganta karatunta, tare da kyatar 5 million.

Nabila tayi matu?ar farin ciki sosai, daga ?arshe aka bata dama tayi jawabi akan irin yadda takeji amatsayin gwarzuwar musaba?a, ta fara da cewa "babu abunda zance sai dai ince alhamdulillah, domin nasani acikin wannan nasara babu wayo na haka kuma babu dabarata Allah ya zaSeni, don haka inayiwa kowa fatan alkhairi, ina kira ga ?an uwa musamman matasa da mutashi mu ringa neman ilimi, domin kuwa Allah (swa) ma da kansa yace kusanni kafin ku bauta min, da wannan nake ?ara jan hankalin mu, damu tashi mu nemi ilimi domin shine zai ?ara haskaka mana rayuwar mu. Ina godiya sosai". Anan aka kawo ?arshen taron mutane kowa ya fara tafiya.

Alaramma Sa'ad.

Nabila ta fito harabar wurin tana hangen ta ina zata hangi senior master, taji anyi mata sallama da kakkausar murya daga bayan ta, juyawarta suka haWa ido da Alaramma Sa'ad, ta amsa cikin girmamawa, sannan ta ce, "malam barka da rana".

"Yauwa, sannunki", cewar Alaramma Sa'ad. Sannan ya ?ara da cewa "Malama Nabila idan baki manta ba, na taSa isar miki da sa?ona da ya shafi zuciyata watarana muna kan hayar tafiya wa'azin ?asa zuwa garin Mai Gatari, Allah ya haWani dake a Gashua, kuma in zaki tuna, na tabbatar miki da cewa zanje na cigaba da addu'a akan lamarin, duba da ?in?i tsayuwa ki saurareni balle har ki faWamin sunanki ko wani abunda ya shafeki, to yau gashi cikin ikon Allah mun ?ara haWuwa kuma nasamu duk kannin wasu bayanai da nake bu?ata a tattare dake. Don haka Malama Nabila yanzu ke mizaki iya cewa akan lamarina dake"?

Nabila cikin tattausar murya ta ce, "Malam nagode sosai dajin furucinka, kuma najidaWi sosai da irin yadda ka nuna min kana sona, to amma matsalar Waya ce gaskiya akwai wanda nake tare dashi a yanzu, don haka Malam dan Allah kayi ha?uri bawai dan wala?anci bane ko dan wani abu ba, sai dan kawai wannan dalilin".

BuWan bakin Alaramma Sa'ad yace "ban gamsu da wannan dalilin naki ba gaskiya, bazan Soye miki ba Nabila kinzo daidai da irin macen da nake burin na aura, don haka sai inda ?arfina ya ?are akan lamarin aurenki, gara kisa aranki zan iya yin duk mai yiwuwa domin naga na aureki. Nabarki lafiya, amma ako da yaushe zan iya zuwa gidanku".

Juyawa yayi ya wuce ya bar Nabila a tsaye cikin zulumi, wanda yasa har senior master yazo ya tadda ta a wurin batare da tasan isowarsa ba, ganin yanin Nabila ya chanja sosai yasa senior master yace "Nabila lafiyarki kuwa, me yake damunki ne naganki haka"?

Da sauri Nabila ta ce, "bakomai fa, kawai rashin ganinka ne yasa duk hankalina ya tashi Malam, domin yanzu haka ina daf da fara yin kuka kenan sai gaka".

Senior master ya Wanyi dariya yace "shikenan ke yau gaki sarkin hawaye ko, to ina mai

5 / 12