Author : Hadiza D. Auta Category : Aysha Cool Novels
sunkuya ta ciccibi Hafcy ta mike tana rusar matsanancin kuka rik'e kuma da hannun da ta fadi a kansa.
Awa d'aya a tsakani Haj Surayya ta iso wacce kanwa ce ga marigayiya Rukayya, yayar Laura. Ta girmi Bilki sosia don kuwa sa'arsu Yaya Salaha ce.
Hamshakiyar mace fara sol mai jiki, ma'aikaciya a hukumar sufuri reshen Abuja. Tana zaune da mijinta da wajen aikinsu d'aya da yaranta. Bilki Sai labarin Alti ta bata na cewa ta tafi da yaran duka gidanta.
Hankalin Alti ya tashi matuƙa don kuwa ta fahimci hannun Hafcy ya samu matsala da gaske sannan tafiyar da aka yi da su, abin da zai biyo baya ba mai sauki ba ne.
Yayin da Bilki ko a jikinta ta riga da ta saba da ganin tashin hankali iri iri, tana jiran ya dawo su fad'a masa ya sauwake mata. Don kuwa ba zata bari su manna mata ciwon zuciya ba.
Yayin da Alti ta yi jarumtar rufe ta da fad'a tamkar ba uwargijiyarta ba. Fad'i take yi "akan me za ki biyesu. Ai kin ringa kin tsere musu ko suna so ko basa so sun kin yi musu nisa tunda kina ganin babansu a tube, da uwarsu ta nan itace abokiyar burminki, idan sun mutunta ki, ki mutuntunta uwarsu, idan sun fitine ki, ki fitini iyayensu. Amma yanzu tunda babu ita ai dole ki yi hak'uri mai yawa mussaman ma da aka yi sa'a y'ay'a mata ne nan ba da jimawa ba, ko wacce tana d'akinta itama tana fama da matsalar gidan aurenta. Amma dan rashin hak'urin da yanzu kika koyo shi, ki kama masa yarinya, ki yi mata mummunan duka irin haka ai bai yi ba. Ai ubansu za ki duba, idan karaya ta samu a hannun ya ya zamu yi ne?"
A sanyaye Bilki ta ce "Sai ya sallame ni mana. "
Alti ta jijjiga kai tana mamakin yadda Bilki ta zama mai taurin zuciya.
Da yammaci sosai ya iso gidan. Ba wata alama na ya san gidan a rikice yake. Ya fito a wanka yana tsane jikinsa da tawul.
Ya ce "Farha kawai na ga ni, ina sauran yaran?".
Murya ba amo ta ce "Basa nan k'anwar mominsu ta zo sun bita"
Ya rik'e rigar ya fasa sawa ya ce "Don me ba ki saka sun fad'a mini ba, ko kuma ke mai ya hana ki fad'a mini a waya kafin su tafi?"
Ta yi shiru don bata san me zata ce ba.
Ya numfasa ya ce "To me yasa basu tafi da Farha ba, ban hana ki dinga cire ta a cikinsu ba?"
Idonta ya ciko ta yi k'asa da kanta, ta kasa cewa komai.
Ya zura rigarsa ya fesa turare ya nufi hanyar barin d'akin. Har ya bude k'ofar sai ya rufe ya dawo. Da tarin bacin rai ya ce "Ba kya yi mini abinda ya kamata fa Bilkisu! Gabad'aya kin nade hannunki kin bar mini yara, kin k'i sakin jikinki da su, tunda ba sona kike yi ba".
Kanta na k'asa hawaye ya k'wace mata. Yayin da shi kuma ya fice ya barta.
Ranar dai haka suka sha ruwa daga shi, sai ita da Farha wanda ko kad'an babu armashi don ba wanda ya ci abincin kirki a tsakaninsu.
Sun idar da sallar isha kenan wayar Haj Surayya ta shigo wayarsa. Ya amsa ta shaida masa zasu zo yanzu da yara amma tana son ganinsa akwai babbar matsalar da zasu tattauna.
Ya amsa mata da fad'in babu damuwa yana gidan zai jirasu.
Tara daidai suka iso gidan, ita da yaran. Hannun Hafcy an nad'e shi da bandage mai yawa.
Ga zazzabi ya rufe ta, haka nan ana iya ganin wasu daga shatin kebran da ta sha.
Aysha kuwa kuka take yi sosai idanuwanta sun yi luhu luhu.
Ganinsu a haka ya yi matuk'ar tayar masa da hankali yayin da zuciyar Bilki take yin lugude sosai. Ba tsoron ya sake ta take yi ba, kawai kada ta wulakanta ta a gabansu ne zulliminta.
Ya amsa gaisuwar Haj surayya hankalinsa na kan Hafcy. Ya kasa hakuri ya tashi ya isa inda take ya ji jikinta zafi ainun sannan uban bandejin da yake nade a hannunta ya dungunzuma masa lissafi.
A rikice ya ce "Menene, me ya same ki?"
Ta kasa magana illah hawaye da yake sintiri a idanuwanta.
Ya juya ga Aysha da take kukan sharb'e yana tambayar me ya same su.
Duk sun kasa magana.
Yayin da Bilkisu junior da su Amal suka yi tsamo tsamo.
Ya kalli Haj Surayya ya ce ". Wai menene, fad'uwa suka yi ko kuwa?"
Rai a b'ace a kuma takaice ta ce "Dukan rashin imani aka yi musu babu gaira babu sabar".
A zabure ya ce "Duka! Wa ya dake su irin haka?"
Da kaudi Laura ta ce ", Anty Maigado ce".
Mamaki ya yi matuk'ar kama shi. Ya kalli inda Bilki take zaune ya zuba mata ido tare da son gane da gaske ita ce ta yi hakan ko kuwa sharri za'a k'ulla mata. Take ya gano ita din ce don babu alamun razani ko mamakin da ta shiga akan jawabin Laura.
Falon ya yi tsit don kuwa ya rasa ta yadda zai bude baki ya yi magana. Amma ransa ya rub'anya baci.
Jin ya yi shiru ya sanya Haj Surayya gyara zama ta ce "Abin da ya sanya na zo takanas shine na ji ba'asin da zata kama manyan y'anmata ta jibga son ranta, ko ita ta haifesu ai ba zata yi musu hakan bare ba d'aya.
Akan me ba za'a k'yalesu su ji da azabar rashin mahaifiyarsu ba? Ban da rabon haihuwa mai kauda wani! Ya za'a yi ace wata mace ce a cikin wannan gidan ba wacce aka yi gwagwarmayar rayuwa da ita ba? Sannan dan rashin adalci sai a mayar da yara marasa galihu a gidan ubansu. To Wallahi ba zamu lamunci duka ba, ko wannan din ma ba zai tafi a banza ba."
Baban Bilkisu ya kaurara murya ya ce "Surayya ina ganin ki bar maganar nan a hannuna tunda ina nan nine yafi cancantar na yi hukunci a gidana. Ita matatace su kuma ya'yana ne, dukkansu suna k'arkashin ikona ne dan haka ki bar maganar hannuna zan dauki matakin da ya dace ".
Ta hassala don kuwa sai ta ga fishinsa ya ragu sosai.
A hassale ta ce "Ni ce nake zaman uwarsu dan haka sai ta fad'a mini dalilin da zata yi musu wannan cin zarafin, ai tasan zafin haihuwa, idan aka kama nata ya'yan aka yi musu irin wannan izayar ai ba yarda zata yi ba".
Cikin nutsuwa Bilki ta zuba mata idanuwanta duka biyun ta ce "Dalilin da ya sanya kika zo don ki bi musu kadin zaluncin da na yi musu a matsayinki na k'anwar uwarsu, shine dalilin da ya sanya na gyara musu tarbiyar da ta yi musu k'aranci a matsayina na k'anwar ubansu, idan ban isa dukkansu a matsayin matar tsohonsu ba, to na dakesu ne a matsayina na goggonsu, kuma ina kan bakana ko yanzu suka biyo ni d'akina da nufin su ci mutuncina sai na yi musu dukan da zasu gigice don kuwa gidanmu gidan tarbiya ne dan haka ba zan bari su fita zakka a zuri'armu ba".
Bak'inciki ya kama Surayya tamkar ta tashi ta rufe yar iskar yarinyar nan da duka. Yaushe Bilki ta yi bakine? Tana tuna ta da wata sumu sumu da ita. Ta kalli yadda ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi, uffan ya kasa ce mata duk da yadda ya dinga rawar jikin b'acin rai kafin ya ji itace ta duke su
Ta ji tamkar ta ce mata a wanne zumuncin da kuka kai ubansa kotun ne za ki yi ƙafafar zumunta irin haka?
Sai dai ta sa ni idan ta fadi hakan shi da ita abin zai juye dan marigayiya Rukayya ta taba fad'a mata har aka yi abin aka gama bai taba buda bakinsa ya fad'a mata ba, bai kuma bata fuskar da suka yi maganar rikicin Ladi farm shi da ita ba, har ta bar duniya. Kan dole ta shanye ta mike ta ce "Dadyn Aysha zan tafi tunda ka ce hukunci na hannunka to dan Allah a kiyaye don ba dan girmanka da mutuncinka ba sai dai a jimu da yarinyar nan a media ko kotu don keta haddin ya isa. Dubi hannun Hafcy. Ace an doki mutum har k'ashinsa ya tsage ai ansan da mugunta a ciki"
Ya fesar da iskar b'acin rai ya ce "Allah ya sauwake. Ta yi masa sallama ta tafi Laura ta yi mata rakiya zuwa wajen motarta. Su Aysha suka yi sai da safe suna daga zaune.
Ya kalli Bilkisu junior ya ce "Bilkisu ku je ku kwanta".
Ta mike Amal da Noor suka bita.
Ya kalli Aysha ya ce "Me kuka yi mata ta doke ku?".
Aysha ta fashe da kukan bak'in ciki ta ya ya ma zai tambaye su, ita duk zatonta kawai zai yi fad'a na tashin hankali mussaman idan ya ga Hafcy da bandeji da shatin duka. Sai kawai ya tambayi me suka yi?
Tabdi jam!
Ya tsare gida sosia ya sake maimaita tambayarsa. Cikin nishin ciwo Hafcy ta ba shi labarin Farha ce ta yi mata rashin kunya shine ta bita d'akin Anty Maigado ta doke ta, shine itama ta rufe ta da duka" .
Ya juya ga Aysha ya ce "Ke kuma menene sanadin na ki dukan?"
Murya a dakushe ta ce"Hafcy na je ceto kada ta kashe ta, ban ankara ba kawai ta zabga minin bulalar da iya k'arfinta har wajen ya fashe ".
Ya ce "Idan na fahimta dukkanku a cikin d'akinta ta doke ku, hakane?"
Ya yi tambayar hankalinsa yana kan Aysha.
Ta kasa amsawa. Ya gyara zama ya ce "Yaune rana ta k'arshe da wata a cikinku zata bi yara d'akin Maigado ta dokesu. Haka nan na haramta muku dukan yaran nan ba Farha kawai ba, dukkan yaran ban yarda ba.
Ya zubawa Aysha ido ya ce "Maigado kanwata ce. Ko ban aurenta ba Antinku ce, aurenta da na yi kuma ya sake mayar da ita uwa ta sosai a wajenku. Ban ji dad'in dukan da ta yi muku ba mussaman na Hafcy amma tunda ta ce ta doke kune bisa hujjar ita din kanwata ce to magana ta wuce ba zan iya ce mata komai ba. Dole ku bita, ku girmamata don matata ce.
Duk wacce kuma ta ce zata yi fito na fito da ita to tabbas da ni ta shirya yin tashin hankali ".
Dukkansu kuka suke yi tare da hakkake ta doke su a bulus ba wani matakin da zai dauka. Gabad'aya sun gane tsoronta yake ji da gudun zuciyarta. Ba dan haka ba, ba yadda za'a yi a yi musu hakan ya kasa rikicewa ya dauki mummunan mataki.
Laura ta yi sakare tana kallonsa tare da jinjina yadda bai d'auki al'amarin da zafi ba. Ta tuna ko momi idan ta daki wani ya dinga yi mata fad'a, yana rarrashin wanda aka doka. Amma yau an yiwa manyan ya'yansa dukan kawo wuka ya kasa motsa k'wanji.
Ya kalli Bilki ya ce "A dafa mini shayi a hau mini sama da shi".
Ta mike ta yi kicin dan yin abin da ya ce din, ta sa ni kuma sallamarta ya yi. Ta samu k'warin jiki a dalilin bai tsinkata ba, illah girma da ya siya mata. Ta yi imanin zasu shiga taitayinsu.
Ta dafa shayin ta fito ta wuce su.
Bayan ta tafi ya dinga yi musu nasiha da rarrashi tare kuma da jaddada musu dole su mutuntunta matarsa, bayan haka kuma wannan ne karon k'arshe da za'a taba jikinsu da sunan duka ya yi musu wannan alk'awarin.
Sun dan ji dad'in rarrashin da ya yi musu sai dai sun so a gabanta ya yi musu wannan rarrashin tare da alak'awarin ta yi na farko ta yi na k'arshe bayan ya gama cin mutuncinta. Gabad'aya sun dauka zai sake ta tunda uwarsu ma baya kaunar ya ga ta daga musu hannu.
Ya raka Hafcy d'akinta ya ce Laura ta kwana da ita.
Sannan ya dawo falon ya kashe fitilu da AC ya hau saman Bilki tunda haka siddan ta k'i samansa.
Ya same ta daure tawul ta fito daga wanka. Cikin jikinta ya turo sosai. Duk yadda ya tunzura da ita ganin cikinsa a jikinta sai ya tafi da kaso sittin na zafinta da ya ji.
Band'aki ya zarce ya yi wanka, ya fito ya ga ta ajiye masa shayi a wajen da ya saba zama ya sha din.
Ya saka jallabiya ya fesa body spray ya zauna ya fara shan shayin, yayin da ita tuni ta shirya ta haye gado ta lullube rabin jikinta da duvet.
A nutse ya kammala ya kashe fitilar sannan ya tarar da ita. Ya kwanta a bayanta. Tsawon lokaci tana dakon ta ji hannunsa a jikinta amma shiru. Ta ji babu dad'i sai dai ta matse ta k'i yin ko da motsi.
Can ta ji ya ce "Maigado". Cikin murya marar amo.
"Na'am" ta furta a sanyaye.
Ya ce "Zamu yi magana a matsayin yayanki ba mijinki ba".
"To" ta fad'a a takaice.
"Idan yaran nan sun yi ba daidai ba ki yi kokarin yi musu hukuncin da ba zasu ji ciwo ba. 'Ya'yana ai ya'yanki ne. Sannan bai kamata akan diyarki ki dokesu ba, na sa ni tunda suka zo cikin dakinki sun yi babban laifi, amma tunda akan Farha ne bai kamata ki dau irin wannan hukuncin ba don kuwa zan ji a raina, kin banbanta tsakanin ya'yana da ya'yanki ko na Ansari!
Zuciyarta ta harba mussaman da ta ji b'acin ran da yake zuciyarsa
ya bayyana har cikin muryarsa.
Gabad'aya jikinta ya mutu.
Tsawon lokaci bai ji ta ce komai ba.
Ya numfasa ya ce "Yanzu kuma Zan yi magana a matsayin mijinki ba yayanki ba. Kada ki kuma dukansu duk abin da suka yi miki, ki fada mini, nine zan dauki mataki ba ke ba. Ina fatan yaune rana ta k'arshe da za ki d'agawa yaran nan hannu da sunan duka, bana so, bana so, kuma dokar nan har akan d'iyar gold din ta ki Farha!
Daga haka ya juya mata baya tare da jan bargo.
Ba'a jima ba ta ji saukar numfashinsa tabbacin ya yi barci, hakan da ta ga ni ya tabbatar mata fishi ya yi da ita. Don duk gajiyar da ya kwaso idan ya yi tafiya baya hana ya sauke mata gajiyar sannan ya rungume ta a k'irjinsa su yi barci. Amma yau ba d'aya.
Gabad'aya ta ji wani irin al'amari mai kama da nadama ya mamaye ta. Mussaman yadda ya juya mata baya ya yi barcinsa ba tare da ya rungeme ta ba. Wannan abu ya yi mata ciwo.
Ta yi tsam da ranta tana nazarin sauyin da ta samu cikin rayuwarta. Ta fara auna banbancin aurenta na farko da wanda take ciki yanzu.
A yanzu bata siyan kayan abinci, bata siyan komai ma da kudinta ko da kuwa abin ita kad'ai ya shafa. Bandir bandir din kudi yake ajiye mata masu yawa. Store din gidan duk wani nau'in abinci akwai shii tamkar banza. Kifi da naman rago da na kaji kuwa har yan aikin gidan bai zame musu abin kwadayi ba, haka k'wai. Mafi dad'i da kwanciyar hankali.
A yanzu gangar jikinta bata kewa, bata kwana da ciwon mara,
bata kwana tana kukan son a marabci gangar jikinta. A yanzu ana yabon kwalliyarta ana yabon girkinta. Sannan a zahiri yana nuna mata tana da muhimmanci.
Wadannan sune abubuwan da ta rasa a gidan aurenta na farko.
Ta numfasa tana ayyana a can kishiya ce da ita ba wai ya'yan mijine kishiyoyin ba. A can ba yaron da zai mata sharri ko ya zage ta, haka nan a can ya'yanta sun girma suna sanya ta farinciki babu kuma mai zalintar. Haka nan a can ba a yi mata yarfe ko ba'a. Da ace a can ne ake suburbudurta yadda ake yi mata a nan da ta ce gwara can don duk yadda take hidimar rik'e gidan da aljihunta gara can da masifar ya'yan miji sangartattu irin wadannan. Ta nisa ta sake yin istigifari tare da yiwa Annabi salati ta daga dukkan hannayenta sama ta ce "Ubangiji ka taimake ni akan sha'anin yaran nan, Allah ka kawo mini mafita ka shirye su ka fahimtar da su ba ni da niyyar zaluntarsu, Ubangiji a duba hak'urin da na yi a baya a sassauta mini wannan matsalar. Allah ka mini zabin alheri ka ƙara mini hakuri da juriya. Hawaye ya k'wacewa mata. Ta rufe addu'a da yiwa iyayenta addu'ar samun Rahma. Tana jin k'addarar cikin jikinta ya saka ta auren uban marayu.
Dan Allah waɗanda Baku mini likes a YouTube ba ku daure ku yi, ba saui kun ji ba, dannawa kad'ai za'a yi a fito.
Na gode Allah ya saka da alheri.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: [Sep 18, 2025 at 11:37]
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
*DAN ALLAH A MINI LIKES DIN LABARIN NAN A TASHAR LIMAMIN TSAKAR GIDA TA YOUTUBE EPISODE 1-10 KAD'AI ZA'A DANNA MINI DON LABARIN YA KAI GA MATAKIN NASARA*.
Da suka tashi sahur bata wani gane kansa ba. Haka dai ta gabatar tar masa da inibi da kankana hadi da ruwan roba. Ita kuma ta sha kunun gyada.
Sassafe ya fice daga d'akinta. Tana zaune har wajen takwas akan sallayarta.
Ga mamakinta sai jin tashin motarsa ta yi. Karon farko da ya yi mata hakan tunda ta zo gidansa. Ta jijjiga kai don kuwa a yadda yake son ya'yansa ta dauka ma hukuncin da zai dauka a kanta zai fi haka tsauri.
Ta yi shiru tana nazarin yadda jiya ya ƙi yarda Surayya ta taka ta, sannan ya ki yarda ya nuna ta yi laifi a gaban yaran. Hakan ya fahimtar da ita son da yake yi mata ne ya hana shi kuzarin ci mata mutunci bare ya bari a ci mata. Don haka duk abin da zai yi yanzu ba zata ji ciwo ba, tunda ya daura zani a kasuwa.
Bai dawo gidan ba sai daf da shan ruwa.
Suna idar da salla Isha ta ga sun yi dakunansu,