Author : Hadiza D. Auta Category : Aysha Cool Novels
tare da fadin yaya Sule kenan".
Saia suka yi salla suka huta. Sannan Abida ya gabatar musu da abinci.
Tare suka ci gabad'ayansu a falon. Kuzarin Baba ya k'aru. Zuciyarsa ta cika da annuri. Yana jin zuciyarsa na warkewa daga takurar da take ciki. Addu'a ya yiwa Sulaiman tafi cikin kwando.
Yana yi yana nasihar ayi ibada, a yi hak'uri da juna, a yi zumunci a kuma kuma kula da marayu don Annabi ya ce kafaɗa da kafaɗa zasu shiga aljanna da mai kulawa da maraya".
Abida ta ce Razina ta zauna a shashin Momi ta dinga yi mata aiki kafin nata yan aikin su iso gobe.
Sai yamma sannan ta yi musu sallama ta tafi wajenta.
Sulaiman kuma ya fita cikin gari da junior.
Oga Asad da Bilki sun fi kowa kewar Baba don sun kad'ai za'a bari a Abuja. Sai dai dukkansu sun gamsu tare da amannar komawarsa Funtua shine mafita mafi kyau. Don shi da kansa yafi son zamansa a Funtua.
A hankali Faruku ya kammala parking din komawa Funtua.
A wannan karon kuma a cikin gidansu zai zauna kamar yadda Sulaiman ya yi fata.
Gidansa kuma an gyara an bawa local government hayarsa tana saukar baki a cikinsa.
Sulaiman da Faruku sun fara shiga Ladi farms suna ganin durk'ushewar da ta yi ba kadan ba ne. Akwia dabbobi sai dai ko kusa ba irin na da ba ne. Madarar da ake yi a da yanzu ba a iya yinta.
Ba gyara irin na da.
Don haka su uku.
Oga Asad, Farukun, Sulaiman suka zuba makudan kuɗaden wahen ganin Ga gargadi.
Aka gyara duk inda yake da gyara.
Aka yi orders din shanun da suke bada madara masu yawa.
Sannan aka siyo k'ananun dabbobin da babu irinsu a yanzu a gidan gonar.
Anyi haka bisa sharadin idan gona ta fara bada riba za'a biya kowa kuɗinsa da ya zuba da ribarsa. Sai a dinga biyan ma'aikatan tunda ga kan Faruku har zuwa masu shara. Sauaran kudin kuma yana asususn baital man da za'a dinga yin hidimar wakafi da su.
Komai ya gama daidaita Ladi farm ta fara aiki k'arkashin Jagorancin Faruku Musa Funtua.
Ba jimawa Sulaiman ya fara shirin tafiya saudiyya tunda watanni biyu aka bashi.
Zai je ya ajiye aikin ne daga nan ya tattaro komai nasa ya dawo gida gabad'aya.
Abida tunda ta ga haka ta tsiri kukan da yake daga masa hankali. Kuma bata yi sai yana gida. Juyin duniya ta ba shi passport d'insa kuma ta ce bata dauka ba.
Wani dare tana zaune har shabiyun dare tana masa kuka tamkar Mai wake.
Hankalinsa ya kai koluluwar tashii.
Ya ce "Za ki dawo da halayyarki ko Abida? Bana son kuka amma kullum sai ki tisa ni a gaba kina tayar mini da hankali ko?
Na ce miki ba dadewa zan yi ba, zan dawo. Amma kin ki yarda da ni. Yanzu fad'a mini menene damuwarki akan tafiyar da zan yi?"
Cikin kuka ta ce "Zamu raka ka ni da junior."
"Abida junior ba shi da passport kafin ayi ya samu visa long process ne, kuma bana son mu tafi gabad'ayanmu mu bar shi, shi kadai kuka zai yi".
Ta mike ta fita zuwa d'akinta ba jimawa ta dawo da passport din junior da nata.
Ta mik'a masa ta ce yana da passport ga shi nan".
Ya ce "To d'auko mini nawa."
Ta yi shiru.
Ya ce "Kin ji".
"Ni fa dadyn junior ban gan shi ba, amma ka gama mana namu shirin zan duba maka a hankali cikikn kayanka ko za'a dace a gan shi ai baka da matsala don ticket kawai zaka siya."
Ya ce "Allah ka shiryi Abida ".
Haka ya shirya musu tafiya tare da ita da junior sannan hankalinta ya kwanta.
Sai da ta ga Komai ya tabbata kowa yasan tare zasu tafi. Ta lallaba ta ajiye masa cikin kayansa a inda zai ga ni.
Ranar da ya ga ni kuma ta hakikance dama tasan a gunsa zai fito don ita bata dauka ba.
Haka ya yi shiru yana kallonta.
Sun sauka a Jiddah lafiya lau. Kwanansu uku a Jeddah sannan suka wuce Makka suka sauke umra. A hotel suka kwana Sai da ya je ya bude gidansa aka share aka gyara sannan ya je ya dauko su ya kai Su can.
Shi kuma ya dinga zirga zirga a asibitin Saudi Germany har ya kammala da su.
Basu yarda sun sallame Shi gabad'aya ba.
Kasar jamus ta ce nan da shekara d'aya ya dawo ya cigaba da aiki da su don sosai suke jin dad'i aiki da Shi. Sannan rife shi da ta yi ba bisa k'aida ba sai suke ta girmama shi tare da rarrashi don sun san an shiga hak'kinsa.
Yayin da k'asar Saudiya kuma suka d'auke shi aiki amma a asibitinsu Na Makka da yake Kano.
Dan haka Idan shekara ta cika Yana son dawowa ya dawo ya cigaba da aikinsa.
Idan kuma zai cigaba da yi a Nigeria shikenan.
Kullum safiya zata tashi ta gyara gidan ta yi musu abinci, sannan tayiwa junior wanka.
Komai da wuri take yi ta kammala.
Rannan Sulaiman ya ce "Abida yanzu ba ni da duty ne a gidan tunda babu yar aiki?"
Ta rike baki ta ce "Dadyn junior aljanna nake nema tuburan. Na yafe maka da din ma da na dinga raba mana duty ba a hayyacina nake ba duk sharrin jinnul Ashiq ne".
Ya yi dariya sosai don ya tabbatar Abida ta ajiye duk wani zafin kanta da tunanin aure ba dole ba ne.
Satinsu uku sannan sukka dawo Nigeria ya fara aiki a babban asibitin Funtua. Da kuma Makka eye Hospital. Zancen budurwa ya bi ruwa.
Litinin da talata yake shiga asibitin Funtua.
Sai ya tafi Kano laraba da safe. Ya ga marasa lafiya laraba da yamma da alhamis da safe Har zuwa yammaci.
Sai ya dawo Funtua juma'a.
Asabar da lahadi kuma yana tare da Yaya Faruku a Ladi farm.
Abida ta cigaba da aikinta a general Hospital Funtua.
Amma Sulaiman ya tabbatar mata zasu koma Saudiya da zama next year sai ta zurfafa iliminta a can ba zasu dawo ba Sai sun tumbatsa da ilimin likitanci.
Ta ji dad'i sosia. An saka junior a makaranta mafi kyau a Funtua. Tare da yaran Yaya Faruku suke tafiya.
Hutun December Na k'arshe shekara gabad'aya yayan gidan da ya'yansu sukanhadi a Funtua dan yiwa Baba barka da dawowa. Har munira ta zo k'asar.
Oga Asad da iyalinsa kaf, Usman da nasa iyalin, haka Hamida da Ansari kowa kwansa da kwarkwata, Saddiqa da Anisa da Yaya Salaha. Gida ya cika damkam.
Oga Asad ya tura mota aka d'auko Faruku da Amra. Tunda Anisa ya koma Yola.
Su da kansu sun tabbatar Idan zasu yi biki ko basu gayyaci kowa ba to kuwa kowa yana isu isu zasu cika taron. Bare a hada da sauaran dangi.
Su Bilki suka hadu gabad'ayansu suka ke gidansu su MAMI da gidajena y'anuwanta suka gaishe tare da yi musu alheri.
Sati guda suna tare kafin a hankali kowa ya koma inda ya fito da iyalinsa.
Zuciyar kowa cike da farincikin dawowar gidansu tamkar shekarun baya.
Baba K'arami da MAMI suna shan addu'o'i don su kad'ai ne babu su.
*Watanni biyar a gaba.*
Oga Asad da iyalinsa cikin wani shararren shagon gwalagwalai a birinin abudhabi na k'asar Dubai.
Shirye shiryen bikin ya'yansu suke yi gida uku.
Aysha khadija da Hafcy.
Dan haka ya shirya musu tafiya don su yi siyayya.
Dukkansu ya ce kowacce ta d'auki sarka da bangles yaran kuma Bilki ta taya su zabe.
Dan haka suka dinga d'aukar design da ya kawata da su.
Yayin da Bilki take taya Amal, Noor da Farha zabe.
Suka kammala ya ce "ke ba ki d'auka ba".
Ta murmusa ta ce "Na ga ka siya mini sarka da bangles sannan ina da wasu ma. Sun isa.
Ya yi shiru yana mamakin yadda sam bata da zalamar abin duniya haka take tin filazal.
Ya hasaso kura Abida da ita ce da tuni ta d'auki makekiyar sarkar da zai yi wahalar gaske ta skaa ta a wuyanta.
Da wata ce ta ga ya siyawa ya'yansa mata shida abubuwan da suke cinye kudi mai yawa da sai ta ɗiba itama.
Ya numfasa idonsa ya sauka kan wani dunkulallen zobe da zai yi nauyi a ma'auni ya ce "Wannan zai yi kyau a yatsanki sarauniyar shaiba. D'auki ki mayar da gurbin wanda kika bawa Autar Momi da bata gajiya da tara dukiya."
Ta ce "Na gode."
Washegari ya fita shi da ita. Yayin da yaran ma suka yi tafiyarsu daban tare d Alti da tagwaye.
Kaitsaye shagon jiya suka koma.
Ta dinga mamakin hakan.
Na zato ya ce "Ki d'aukarwa Amrah sarka da bangles irin Wanda bilkis6ta d'auka".
Dad'i ya ratsa ta don kuwa ta kud'ire zata dawo ita kad'ai ta siya mata irin wacce zata iya siya.
Sai ga shi ya shayar da ita mamaki.
Sosia ta ji dad'i.
Bata gama mamakin hakan ba ya d'auko mata wata iron sarka mai balls tamkar dai carbi. Kallo daya zaka yi masa ka gane ya kerewa gold daraja.
Kudinsa ya zarta kudin duka sarkokin da suka siya.
Ya ce ina son murjani tunda ga wannan sai ki dinga mini kwalliya da shi sarauniyar shaiba.
A gun ta rungume shi tana fadin "Na gode Baban Bilkisu, Allah ya saka da alheri ya shirya zuri'a."
*Duk wacce ta siyi littafin nan bamu yi saving contact din juna ba.*
*To ta yi mini magana na yi saving contact ɗinta.*
*Don samun discount yayin siyan kayan garari na Bojuwa herb's*.
*Na gdoe Allah ya saka muku da alheri*
08032773332.
Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:31]
*DINGISHIN KWAD'O*
*SURAYYA GWARAM*
08032773332.
*Fatan alheri ga Dr Fadila Kabir*
*Na gode da kokarinki da shwarwarinki*.
*Allah ya albarkaci su Maheer*.
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
Khadija da ba za'a yi mata jere ba tunda a London zata zauna ya sanya Bilki ta saka aka kara mata sarka da manyan warwaraye tunda y'anuwanta siyayya ake yi musu ta alfarma.
Sun kammala siyayyar suturu da kayan kicin a Dubai.
Suka zarce Turkey don oga yafi son asalin katakon k'asar turkey masu k'ololuwar daraja fiye da na Dubai.
A can aka yaye twins da suka shekaru d'aya da haihuwa.
Hafcy da khadija masu son hidimar suka shirya musu birthday celebration a wani kayataccen waje a birinin Istanbul.
Sati biyu da dawowarsu Abuja Wanda ya yi daidai da bikin Laura wanda dama tazarar sati uku ne tsakanin bikinta da na su Aysha. Tuni kuma Bilki ta yiwa Amare order din sanyin flusher tare da bridal package daga Bojuwa herbs Kano. Kazar sababi ce kawai sai sati biki za'a turo musu wataƙila ma sai sun isa Funtua.
Yara suna ta shirin tafiya Kaduna.
Oga Asad ma a cikin hidimar take don da gaske shine uba.m ba abin da bai yi mata ba.
Saura hud'u a fara biki ya Bilki ta shirya jibi zasu tafi Kaduna tare da yara zasu yi kwanaki hud'u su dawo. Shi sai ranar d'aurin aure zai zo.
Ta kasa boye yadda bata son ta je.
Ta ce "Baban Bilkisu gaskiya yara su tafi ni kuma mu je tare ranar d'aurin aure mu dawo".
Ya zuba mata ido sosai har ta tsargu.
Ya nisa ya ce "Ku je tare Maigado. Yarinyar a hannuna ta girma k'anwar Rukayya ce da tana da rai ai anan za'a yi komai, da bata raye kuma sai iyalina suje gabad'aya ba a tura yara kawai ba."
Ta yi shiru tabbacin ita ba hakan take so ba.
Tasan Surayya na can haduwa zasu yi da Laura da sauran y'anuwansu su tisa ta a gaba da kallo da zunde iri iri cikin isgili. Amma shi ba zai gane hakan ba. Menene aibu dan ta je rana daya ta dawo?
Ya kalleta ya ce "Kin yi shiru sarauniyar shaiba.
Ta sake yin shiru.
Ya mike ya ce "Bilki jibi zaku tafi Kaduna tare da yara".
Ya saka kai ya fice.
Takaici ya shak'e mata wuya. Idanuwanta ya cika da k'walla. Akan me za'a ce sai ta je ta yi kwanaki a gidan da ba dolenta ba? Ita bata son cusa kai da shisshigi. Yara ne dole su je ba ita ba.
Ko da ya dawo fuska a daure haka suka kwana kowa zuciyarsa na tunzure. Ya riga kuma ya kud'ire sai ta je Kaduna a gobe ko kuma ranta ya yi mummunan b'aci.
Yadda ya fitittike ya dauki fishi ya sake hassala ta. Wato duk abin da ya shafi Rukayya bai d'auke shi da sauk'i ba. Da a ce ba sabgar da ta shafe ta ba ce ta tabbatar ba zai yi mata tilas irin haka bare har ya shareta ba.
Bak'inciki kamar ta rusa ihu.
Da yamma kan dole ta yarda Alti ta shirya mata kayanta a akwati. Tana hadawa tana fadin "Ni ban ga abin b'acin rai irin haka ba Mahmah. Ai da gaskiyarsa a hannunsa ta girma dole ki je a yi komai da ke.
Bilki ta yi shiru don ba zasu fahimci manufarta ba. Kan dole da yamma da ya dawo ta shirya ta hau samansa don tasan idan ya cigaba da fishin goben ma ficewa zai yi ba tare da ya tsaya sun yi sallama ba. Idan kuma ta bar yara suka tafi su kad'ai ba sharewa k'alau zata yi ba, tunda ya kafe sai ta je, to sai ta je din kuwa.
Ta shiga falonsa baya nan.
Ta doshi cikin d'akin.
Ta tarar da shi a kwance shame shame tabbacin a gajiye take matuƙa da gaske.
Ta mak'ale a gefe bata isa gare shi ba, ba kuma ta juya ba. Ya kalli yadda ta yi. Dariya ta kama shi. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:33]
Tunda ta zo ai yasan ta sauko ne. Dan haka ya had'iye fishinsa ya ce "Zo kusa da ni sarauniyar shaiba".
Ta cuna baki ta d'auke fuskarta zuwa gefe daya.
Haka ya yunk'ura ya tashi ya isa kusa da ita. Ya rik'o hannunta ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyoyinsa ya ce "Na huce da Maigadon zinare. Ya ake ciki ne, menene?"
Cikin shagwaba ta ce "Kai zan tambaya tunda kake yi mini fishi haka siddan".
Ya ce " A a ba haka siddan ba dai sarauniyar sheba.
Kin kasa gane ni me gabad'aya. Ni fa Na tsani gardama mussaman ace matar da nake aure ne zata dinga yin fito ma fito akan umarnin da zan bata. Na ce ki shirya ki raka yara biki menene abun damuwa ko bacin rai a ciki?"
Ta yi shiru don idan ta ja al'amarin rikicewa zai yi.
Daga nan ya zarce da rattabo mata alfarmomin Rukayya.
Ta nisa a dole ta ce "To zan je".
Ya rungume ta yana fadin yauwa Bilkisu yayar Abida".
Ta murmusa ta ce "Amma dai Alti da twins su zauna a gida bana jin dad'i kuma su rikicinsu yawa ne da su".
Ya ce "Anya Maigado kasalar nan ta ki da saurin hassala ba gamo kika yi ba?"
Ta yi masa shiru don kuwa tabbas cikin ne da ita.
Ya ce "Ku tafi tare da su. Alti ta dinga tafiya da su gidan saddiqa suna kwana. Amma ke da Farha da tare yaran nan kuna wajen Hajiya".
Ta yi shiru a zuciyarta kuma fadi take yi shi a dole a ce kaf iyalinsa sun halarci bikin k'anwar maimurabus.
A fili kuma ta ce "To".
Washegari suka shiga jirgin kasa da yamma zuwa Kaduna.
Suka tarar da motar y'ansanda suna jiransu.
Hajiya ta karɓe su ba laifi. Amma da ta shiga dakinta sai da ta yi kukan ganin ahalin Rukayya babu ita sai wata.
Surayya ma bata nuna mata komai ba sai dai kuma ba wata fuska. Anyi hidima lafiya an kammala lafiya. Oga Asad kuma ya yi musu mugun k'ok'ari ko Rukayya na da rai iyakacin abin da zai yi kenan. Hatta ruwan roba da lemo da aka dinga wadaka da du duka daga gare shine. Kayan d'akinta kuma masu kyau ya yi mata. Hakan ya rage musu zafin Bilki da tagwayen ya'yanta don sun gane bata gama da shi ba, kamar yadda suke hasashe.
Bilki kam a matuƙar takure ta yi wannan zaman don yini ake ana shiga ganinta a d'akin da aka sauke ta tamkar hoto. Tana ganin Laura da sanyi flusher da sauran kayan gyaran Amare ta gane Aysha ce ta yi mata Oder din kayan don da lambar a jikin dukkan kayansu. Shine ta dauki lambar a jikin nata kayan ta yi mata order itama.
Ya zo d'aurin aure ya ce su gobe zasu dawo tunda yau za'a kai amarya.
Ta roke shia akan idan akan kai amarya ta wuce gidan saddika ta kwana mana gobe sai ta zo ta d'auki yaran su yi sallama da Hajiya. Bai k'i ba ya amince don ya tabbatar ta yi iya kokarinta kuma zuwa gidan saddika ya kamata.
Washegari kuwa sai shida jirginsu(train) ya tashi zuwa Abuja.
Ya dinga yi mata sannu da tare da godiya har kunya ta kamata.
Kwanaki kad'an suka fara shirin tafiya Funtua don a can za'a yi biki da d'aurin auren su Aysha.
Kowa a zuri'arsu kokari yake ya yiwa oga Asad alheri don ya gane sun gode da hidimar da yake da su da dukiyarsa da bata tsole masa ido ba.
Mazansu da matansu kuwa. Ba yadda za'a yi a dumfare shi da sunan bsbu waji abu ko ana buk'atar abu kaza kowa yi yake yi kawia da dukkan k'ok'arinsa. Hakan ya dada sanyaya zuciyar Baba tare da gasgata Allah ya karbi rokonsa na a jefa soyayya da tausayin juna a tsakaninsu gabad'aya.
Bilki da Abida tare da amare Kano suka tafi takanas don yin lalle. Don yin Bilki a Kano ta tabbatar bata sake samun wacce ta iya kunshi irin Maman Farhan ba.
Tiryantiryan har Farawa. Yini guda su aka yiwa kunshin da ya amsa sunasa.
Oga Asad kuwa mita yake ace sai an tafi Kano yin kunshi don tsabar fitina da wuyar zama iron na Maigado. Sulaiman na gefe na taya shi da fadin ai Abida da Bilki fitina da munubarsu ta kai k'urewa. A hanasu zuwa su tisa mutum da matse matsen k'walla mai sake rauni a kirji".
Ya bawa oga Asad dariya k'warai da gaske. Ya ce "Haka kuwa suke yi Dr Sulaiman to ya za'a sai hak'uri yara ne ai ". Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:35]
Duk wata nasiha da ta dace ba wacce ba'a yiwa Amare ba. Haka ma Baba da Momi da dukkan iyayen Amare