DINGISHIN KWADO 3 & 4 COMPLETE BY HADIZA DA AUTA.txt

Author :  Hadiza D. Auta Category :  Aysha Cool Novels

Chapter   34 / 50

99K to 102K   out of 149K words

Sule ko ban ci arzikin komai ba na ci na junior mana." Ta fad'a murya ba amo.
Ya muskuta ya ce "Wai kina nufin jikan mami ne?"
Ta d'ago a kidime ta ce "Haba Dr wacce irin magana ce haka?"
Ba walwala ya ce "Ta gaskiya da gaskiya mana".
"Amma dai Yaya Sule ko makaho yasan d'anka ne ai".
Ya numfasa ya ce "Hakane amma bani biro da takarda na yi lissafi. Duk da ta kad'u sai da ta bude jakarta ta dauko biro da jotter ta ba shi.
Ta kunna mass fitilar motar. Ya ce ni dai nasan a Germany kin samu ciki a had'uwar da kika k'irata k'addara. Ya rubuta ranar.
Ta Kalla tabbas bai manta date din ranar ba.
Bata yi mamaki ba don kuwa shima guru ne tamkar ita.
Ya sake rubuta date din da ta yi masa cin mutuncin tare da yunkurin cire ciki da jini ya b'alle mata.
Ya kalleta ya ce "Kin zubar da cikin da ya kai wata uku. Tunda ga lokacin bamu sake haduwa ba ko?"
Murya ba amo ta ce "Eh. "
"To ta ya ya kike ganin zan gamsu junior jikan mami ne?"
Ta kasa cewa komai. Saboda yadda zuciyarta ta yi nauyi. A hakan ya daure ya rubuta mass ranar haihuwar junior, ya yi masa llissafin kwanaki wanda lissafin ya dire zuwa ranar da aka sami cikin. Ya tabbatar daii shine bai zube ba wani ne daban ba.
Tsawon lokaci sun yi shiru zuciyarta na bugawa da k'arfin gaske.
Wanne irin dan bala'i ne haka Sulaiman? Ta sake gasgata Baba da ya ce duk abinta Sulaiman ya dama ta ya shanye yafi k'arfinta. Dama ta gasgata Baba. Amma a yau ta sake yarda dole ta bishi a hankali idan ba haka ba ya rugurguzata bak'in cikin da ta zata kasa fahimtar komai.
Tsawon lokaci yana rubutu a rubuce wanda duka lissafine. Ya gama buge buge lissafinsa hawa hawa.
Ya dago ya ce "Na yarda d'ana ne bana inkari akan hakan, tunda na gan shi na gamsu jinina ne, jikan mami ne tabbas. Amma ki rike abinki na bar miki shi ban da buk'atarsa tunda ya zo ne bisa tsautsayi da k'addara ba dan kina so ba. Da kin yi aiki da lura ma da sai ki k'i fad'a masa nine ubansa ya dinga amsa Sulaiman Abida ba Sulaiman Sulaiman ba."
Ta fashe da kuka mai sauti tana fad'in amma "Yaya Sule duk rawar jiki da hak'urim da nake baka ala dole sai ka saka mun yi tashin hankali? Na baka hak'uri fa. Na sa ni ban kyauta ba shiyasa na kwantar da kaina nake ta binka ashe kai kallona kake yi kana mini tanadi iri iri?" Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:14]
Ya girgiza kai ya ce "Abida kada ki kwantar mini da kai dan Allah. Fito min a Abidan Baba kin ji. "
Ta yi maza ta saka hannu a bakinta ta danne alamun ta so yab'o masa bakar magana ne ta yi maza ta fasa.
Ya ja k'aramin tsaki ya kishiginda. Alamun ya gama magana. Ta zuba masa ido tana jin jarabawa ne kawia ya sanya aka saka mata sonsa da yawa. Ban da haka da bai isa ya tisa ta a gaba yana mata gadara da nuna mata iyakarta ba.
Ta ci kuka ta k'oshi don ta riga ta gama ganewa duk dabararta Sulaiman ba yarda zai yi su shirya salin alin ba. Dole sai ya gurfanar da ita a gaban Babansu wataƙila ma da duka yayyensu. Ita babban tashin hankalinta ace y'anuwansa su ji ta zagi MAMI. Ta sani wasarta zasu yi, duk da ba komai zata NEMA a gunsu ba amma zata so ace akwai fahimtar juna da soyayya a tsakaninsu mussaman ma da ya kasance su yan uwan juna ne. Ai ko Bilki ta ji maganganun da ta yi akan uwarsu sai ta k'ullace ta, bare kuma su Yaya Hamida da Ansari da y'ay'an da ta haifa ma sai sun washe su matuƙar akan mami ne.
Cikin rishin kuka ta ce "Ka yiwa Allah ka yiwa alfarmar zumunci kada ka fad'awa y'anuwan haihuwarka marab'aina sun kushe MAMI. Ni Wallahi ban soke ta ba. Wallahi summa Tallahi aljanun da suka hana ni aure tuntuni ne suka motsa a lokacin saboda sun kasa raba ni da kai".
Hatta jinin da ya balle mini na cikin sharrinsu. Addu'ar da na dage da yi ne na fatattake su, ai har junior suka so shafa. Allah ne ya takaita."
Ta fad'a tana kuka sosia.
Ya zuba mata ido yana ganin yadda take kuka ainun.
Ta kuma hakikance jinnu ne suka shige ta. Yanzu da jinnu zai yi rikici kenan ko me take nufi.
A ransa ya ce "Kinayar mata babba ce. Yanzun nan zasu rufta mutum. Kuma yanzu tunda ta ce jinnu ne to kuwa akan haka zata tafi duk runtsi ba zata yarda ita ce ba.
Ya rasa mai zai ce illah zuba mata ido tana ta rera kukanta tamkar sarewa.
"Abida ja motar nan mu tafi na gaji". Ya fad'a a kausashe
"Yaya Sule ba zan iya tuki ba Wallahi. Kana mini fishi irin haka ina zan iya to ta ya ya ma?"
Ta fad'a cikin gunjin kuka.
Ya bude k'ofar ya fita ya zagaya ya ce "Fito ki ba ni waje."
Tana fitowa ba zato kawai ya jita a k'irjinsa ta rungume shi sosai.
Gabad'aya ya ji shocked ya zama mutum mutumi.
Ita kuma ta shimfide fuskarta tana tsiyayar masa da hawayenta a k'irjinsa.
Da wata irin murya hade da gunjin kuka ta ce "Yaya Sule Kada ka hukunta ni da laifin shaidanun halittun da suke son rabamu Wallahi jinnul Ashiq ne suke shafata from time to time. Ka yi hak'uri ka yafe mini, ina sonka dan Allah ".
Daga haka ta sake shi ta wuce ta zagaya ta shiga gaban motar.
Mutuwar tsaye kawai ya yi. Komai na jikinsa ya amsa. Hawayenta ya raunana shi matuƙa gaya.
Shi da kansa da ya karbi motar a kasalance yake janta.
Har suka isa gida basu sake magana ba.
Tuni an yi sallar isha. Basu tarar da Baba a falo ba, dan haka Sulaiman ya juya zuwa d'akinsa Abida ta shiga ciki.
....
Yau ma ba za ki je d'akin mijinki ba Mahmah?"
Alti ta tambayi Bilki da ta ga ta yi shirin barci ta haye gadonta ta kwanta.
Uffan bata ce mata.
Ta sake maimatawa a karo na biyu.
Nan ma ko motsi bata yi ba. A kufule ta ce "Da wannan bak'in cikin da kike cusa mini gwara na tattara na baki waje. Kuma dan ban isa ba ne, da ace ina da kima a wajenki da ba ki mayar da ba a bakin komai ba. Dole Alhaji ya dinga ganina shekeke ya dauka na isa da ke, bana fad'aiki gaskiya nan kuwa isa ne ban yi ba. Da kina da hankali labarin da Abida ta bamu dazu da yasa kin je makantar ta nutsu amma tamkar ana zuga ki. Sam nabu nadama a lamuranki!
Bilki da ta gaji da suratan Alti ba kakkautawa kawai sai ta mike ta isa gaban madubi ta sake fesa turarenta na weekend. Sannan ta bude kwalbar turaren mkbees perfumery.... Ta shafa.
Ta d'auki hijab ta ce "Sai da safe."
Alti aka ce "Yauwa Allah ya yi miki albarka aje lafiya a dawo lafiya ko ke fa?" Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:18]
Bilki ta fice ta ja k'ofar.
Alti ta gyara yara ta kwantar da su ta kashe fitila ta kwanta bayan ta yi addu'a.
Bilki kuwa daya d'akinta ta bude a hankali ya shige ta yi kwanciyarta.
Bata jima da kwanciyar ba wayarta ta dinga haske. Ta duba ya ga Baban Bilkisu ne.
Da kamar ba zata d'auka ba sai kuma ta kasa sharewa. Ta dauka ta saka a kunnenta amma ta yi shiru.
Murya ba amo ya ce "Yanzu Bilki ba kya jin tsoron hak'kina. Wai menene yake faruwa ne haka?"
Ta yi shiru.
Ya numfasa ya ce "Ki zo yanzun nan".
A hankali ta ce "Ni na riga na yi addu'ar barci".
"Ba za ki zo ba kenan?"
"Ni gaskiya samanka gabad'aya bana sonta, tana saukar mini da takurarren yanayi gaskiya ".
Ya sassauta ya ce "Dan Allah ki zo, just an hour's sai ki dawo ba sai kin kwana gabad'aya ba."
Ta yi shiru tabbacin bata gamsu ba.
Ransa ya fara b'aci ya ce "Yau ma wulakancin za ki sake yi mini?"
Ta yi shiru.
Ya katse wayarsa. Amma a yau hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi. Tabbas akwai abin da yake ranta, kuma sai ta fad'a da ya samu nutsuwa ya gaji da wannan bala'in da kisan mummuken da yarinyar take yi masa. Shi irin wannan nunkufircin ne baya so a halayyarta tuntuni. Baya son shiru shiru ya yi yawa. Ga shi yanzu da girmansa da mutuncinsa sai faman gana masa azaba take yi. Ta tashi hankalinta ta tashi nasa.
Ranar bai yi wani barcin kirki ba don zuciyarsa ta rinjayar masa so take ta bar shi, ta koma gidanta wajen y'ay'anta. Duk juyin da zai yi tunanin twins da tausayinsu ke neman kassara shi.

*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Sanyi flusher kuwa best seller ne*
*Just DM for your order @08033773332*.


Wani shashi na zuciyarsa ya kore tunanin hakan ya kutso masa da tunanin y'anuwanta ke zugata ta bijire masa.
Wadannan hasashen da suke bijiro masa sun sake dungunzuma masa lissafi ainun.
Amma a gobe za'a yi komai a kare ya riga ya gaji k'warai da gaske.

..
A daddafe ya kai asuba
Yana dawowa daga masallaci ya dauki waya ya lalubo Faruku.
Bugu d'aya ya d'auka tare da fad'in "Ran oga ya dade! Sassafe haka. Allah yasa lafiya?"
A kidime ya ce "Faruk babu lafiya wannan k'anwar taka ta k'i dad'in kasafi. Ka zo goma ina jiranka. Zan fita 12 ka zo da wuri na riga, na gaji gaskiya."
Faruku ya ce "Sai hak'uri oga yarinya ce kuma bata fahimce ka ba. Ka yi hakuri komai zai daidaita ".
Oga Asad ya ce "Gaskiya fa Faruku ba zai yiwu ina lallabata tana mini wulakanci ba. Haka siddan ta d'ank'ware ranta sai rama take yi a tsaye. Dazu da Sulaiman ya zo ya ganta ta yi wani zuru zuru da ita tamkar na nutse tsabar takaici. Haba yarinyar nan tana cutata gaskiya. Gaba fa take yi da ni ba gaira ba sabar. Gaishe ni ma da ƙyar take yi wanne irin al'amarine haka. Yau kam komai zai iya faruwa a tsakaninmu. Matuƙar ba ta bude baki ta fadi me nake yi mata ba."
Faruku ya ce "Zan zo in sha Allah. Ka yi hak'uri."

K'arfe goma a gidan oga Asad ta yiwa Faruku.
A falon da ya sauki Sulaiman jiya anan ya sauki Faruku.
Suka gaisa Faruku na dariya ya ce "Yanzu saboda Allah oga ace ba zaka iya shawo kanta ba sai ana muku shari'a?"
A kufule ya ce "To ai ba sona take ba shiyasa. Ba zaka gane gashin k'umar da take yi mini ba ne. "
Faruku ya k'ira layinta ta dauka cikin nutsuwa take gaishe shi.
Daidai lokacin tana shan shayin da ya zama k'aida sai Alti ta had'a mata ta sha da zarar ta fito daga wanka.
Faruk da ya ji muryarta ba sukuni ya ce "Ko ba ki tashi bane?"
"Na tashi Yaya Faruku".
"To zo mu gaisa ga ni a gidanki".
Tana jin muryar oga Asad yana fad'in "Na bata gidan ne da zaka ce mata gidanta?" Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:23]
Jikinta ya bata k'ara ya kaita
Da yake ta yi wanka ya shirya. Sai kawai ya d'ora tsadaddiyar Egyptians abaya ta umm asalan...
Alti zan je k'asa Yaya Faruku ne ya zo".
"To ki gaishe shi da kyau ".
Ta fadi hakan da walwala.
Tare ta tarar da su. Suna zaune a kujera. Fuskar oga Asad a daure ainun.
Ya zauna a k'asa ta gaishe su . Faruku ya amsa yayin da oga bai amsa ba.
Kanta na k'asa.
Faruku ya ce "Maigado me yake faruwa ne, menene matsalarki?"
Ta yi shiru.
Ya sake maimaitawa.
Ta ce "ba komai Yaya".
"Ba komai amma kike bijirewa mijinki? Kinsan hukuncinatar da ta kangarewa mijinta, sanin kanki ne tana cikin fishin Ubangiji amma kika bi wannan turbar?"
Murya ba amo ta ce "Ban kangare masa ba ni".
A tunzure oga Asad ya ce "Kangarewa ta nawa kuma? Ai na riga na gaji da wulakancinki, na gane inda kika dosa. Ba kya son zama da ni saboda kina son komawa wajen y'a'yanki. To nima na shirya idan kin k'i zama da ni ai ba mutuwa zan yi ba. Mata suna nan birjik kowacce iri nake so zan auro na samu farin cikin da nake buk'ata."
Ta yi k'asa da kanta hawaye ya fara yi mata tsere.
Faruku ya ce "A a oga bi a sannu mana, take heart pls."
A fusace ya ce "Ka san Allah ba zan bita a sannu ba yau. Shaida zaka zame mini a wajen Baba don na gaji gabad'aya. Sai ta bude baki ta fadi laifin me na yi mata ko kuma, a yita ta k'are!

"Bilkisu".

Faruku ya k'ira a tausashe.
"Na'am". Ta furta cikin muryar kuka.

"Menene damuwarki fad'a mini kin ji".
Da kuka sosia ta ce "Na gaji ne, na gaji fiye da yadda yake ƙirarin ya gaji".
"Ka ji ko Faruku na fad'a maka hankalinta ba anan yake ba. Ba dai na halasta musu zaman ba, ai dole ta butulce mini!
Ya fad'a hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi.
Jikin Faruku ya yi sanyi ganin yadda d'anuwansa ya daburce.
"Bilki fad'a mini me yake faruwa kada na gasgata zatonsa. Da kuka sosai ta ce "Ka yarda da batunsa kawai Yaya Faruku. Bana son zama da shi, can nake son komawa ba shike nan ba!
Save Restricted Content Bot, [Oct 24, 2025 at 13:48]
Hatta Faruk ya shiga rudu. Ya ce "A a Maigado ba hakan ba ne."
"Hakane Yaya Faruku".
Nan da nan oga Asad ya bar kujerar da yake zaune ya isa inda take zaune ya durkushe ya kama hannunta ya ce "Ki ji tausayina dan Allah, ki duba jariran yaran nan sun fi waɗanccan buk'atarki. Ki dube ni da nake son zama da ke. Wanda yake son sonka, yake son zama da kai ai adalci kake yi masa. Ko ba kya sona ki yiwa Allah ki ji tausayin ya'yana, ni kuma ki yi mini adalci Maigado ya ya kike son na yi ne?"
Faruku ya yi tsam yana kallonsu. Bai taɓa ganin abin da ya raunana oga Asad ba. Amma a yanzu dukkan rauninsa ya gama bayyana. Firgici sosai a tare da shi.
A da gani yake yi ya fishi son Maigado. Amma yau ya tabbatar nan duniya ba mai sonta fiye da oga Asad.
Ga mamakinsa sai ya ji zuciyarsa ta yi masa nauyi. Ba ko tantama kishine yake neman murd'e shi don kuwa ya hango soyayyar oga Asad baro baro a idanuwanta. Ya yi maza ya dinga a'uziya a zuciyarsa don kore shaiɗanin da yake neman kawata masa ita.
Ya numfasa ya kaurara murya ya ce "Maigado ba zan sake tambayar ki ba. Tunda har na tako don na ji ba'asin halin da kuke ciki ai kinsan dan ya san na isa da ke ne, shiyasa ya k'ira ni. Idan kuma ban isa ki fad'a mini matsalarki ba sai na tashi na tafi harkkokina".
Cikin kuka sosai ta ce "Tunda na zo gidan fa gabad'aya hak'uri nake yi. Baya binciken komai. Haka na sha wahalarsa akan yara bai taɓa ba ni dama mun tattauna ba. Sai dai ya yi ta yi mini fishi. Lokacin da yake ganin Farha kullum tare da ni bai taɓa tambayar dalilin da ya sanya bata zuwa cikinsu ba. Sai dai ya balbale ni da fad'an ina ware ta alhalin cin zalinta suke yi.
Aka gama wannan danbarwar.
Akan idonsa ya ga chart dinsu suna zagina suna zagin uwata bai d'auki mataki ba. Amma ni nan dan na zagi maimurabus da uwarta ba bala'in da bai yi ba.
Wato uwata bata da kima a wajensa sai maimurabus da uwarta? Kuma tunda na ce ba zan zauna da Laura ba shine ya kori Farha tare da dakatar da Alti. Duk fa na yi hak'uri saboda Baba.
A hakan kuma d'an kuskure kad'an zan yi masa ya hau sarhutun maimurabus ta fini biyayya, ta fini kaza, ta fini iya kaza, Maimurabus tana da alfarmomi a wajensa. Komai na yi masa haka zai kalle ni ya ce shi ba haka ake yi masa ba, shi matarsa ba irina ba ce, bata yi masa fishi. Ni ba ni da alheri. To na bar mata kayanta ya bita kushewar su had'ehta cigaba da sonsa da yi masa biyayya ina ce shikenan?"
Faruku ya kasa bude baki ya yi magana don kuwa dariya ce fal a bakinsa.
Wai Rukayya ce maimurabus. Wanne irin sababi ne haka take ga ni? Wato mata akan kishi babu kyua. Sannan ya Ƙara gasgata Bilki mai tsiya ce ta gaske.
Kan dole ya mike ya ce "Ina zuwa".
Kafin su amsa masa ya fice da azama. Gefe daya ya samu ya yi dariyarsa. Ba abin da yake ba shi dariya irin yadda take fad'in maimurabus ga kuma oga Asad da kansa gurfane a gefenta tamkar ba shi ya gama cika bakin yau komai zai k'are don ya riga ya gaji ba.
Kai mata mata Allah ya shirye su kawai.
Sai da ya nutsu ya shanye dariyar sannan ya koma fuska a daure.
Ya bude murya ya ce "Yanzu ki yi hak'uri Maigado komai ya wuce. Kema ki dinga yi masa bayani idan ya bata miki, ki daina rikewa a zuciyarki indai ba so kike ki kwanta jinya ba".
A hankali ta ce "To ai ni da na ga baya bincike na d'auka yana ganin komai ta cctv camera don kuwa gida irin wannan, kuma gidan jami'in tsaro ba'a yi tsamammanin babu ita ba".
Oga Asad ya ce "Hadawa ne ba'a yi ba. Amma za'a had'a. Yanzu tunda na ji matsalar to komai ya wuce ba zan sake kwatanta ki da Rukayya ba."
Ta yi shiru. Ya nisa ya ce tunda kin fad'i matsalolin na kuma yarda zan gyara to ki ware zuciyarki ki dinga walwala ".
Nan ma bata amsa ba.
Faruku ya ce "Shikenan matsalolin ko da saura Bilki?"
Sai ta yunk'ura zata yi batun hoto sai ta kasa.
Faruku ya ce "To me yasa

34 / 50