Author : Hadiza D. Auta Category : Aysha Cool Novels
ta what'sapp din sannan ta katse ta duba.
A zabure ta tashi ta zauna ganin motocin gararin da ya turo mata da zasu lashe millions of naira wai ta zabi wacce take so.
Ta murtsuke idanuwanta sosai dan ta sake gasgata ita Bilki ake yiwa tayin ta zabi guda cikin wadannan motocin?
Ta tabbatar dai ba gizo ba ne .
Sai ta rubuta masa wadannan duk sun yi mini yawa. Waɗanda basu kai wannan ba ta isa.
Ya ce "Amma tunda ba rokona kika yi ba, bai kamata na ce ga yadda nake so, ke kuma ki ce yadda kike so za'a yi ba ko?"
"Hakane"
Ta fad'a a takaice domin ta ji tamkar ya ji haushi ne.
"Kawai ki zabi kalar da kike so".
Ya fad'a cikin sigar umarni.
Maimakon ta yi masa voice irin yadda yake yi sai ta sake rubuta masa "Farar".
"Yauwa Maigadona! Na gode miki sosai Allah ya saka da alheri".
Tana mamakin jin godiyar da yake yi tamkar ba shine ya kamata ta yi masa godiyar ba. Ta jijjiga kai tana fad'in komai ma kake nufi ba yiwuwa zai yi ba dan ba kunyar wadda zaisa na k'wari kaina.
"Wai Maigadona!
Ta furta a bayyane.
Ta juya tana gyarawa Farha kwanciya.
Ta saki tsaki tare da fad'in "Ko ta ina na zama tasa?"
K'ira ya sake fadowa wayarta. Ta rasa yadda zata yi haka ta dauka akan dole.
"Maigado kin yi barcine?"
"A a Farha na gyara ta kwanta kan hannunta ".
"Sannu da kokari to"
Ta share tamkar bata ji ba.
Ya nisa ya ce "Maigado barci kike ji ne?"
Murya ba amo ta ce "um"
"To bari na k'yale ki haka nan, zamu yi magana da safe. Stay blessed".
Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa ta bi wayar da kallo cikin sake mamakin sabbin hallayar da yaya Asad ya tsiro da shi zuwa gare ta, sai take jin wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara. Ita fa ba yarinya ba ce ta san manufarsa akanta kuma sai dai ya yi haƙuri ba zata taɓa sonsa ba, ba ruwanta da kuɗinsa balle muƙaminsa ya je wani waje ya nemo matar aure dan kuwa ita bai mata ba.
Tunda ga ranar yaya Asad kullum da daddare sai ya kirata yana kashe mata murya, tare da hilatarta. Ita dariya ma yake ba ta ɗauka yake yi ba ta gane manufarsa ba nan ko kallon shi kawai take yi tana dai biye mishi sama sama domin ta ga iya gudun ruwansa, har zuwa ranar da zai furta manufarsa ita kuma a lokacin za ta taka masa burki ta faɗa masa gaskiyan cewa ba ta son shi daga nan sai ya kama kan shi da ita.
Haka Bilki ta cigaba da gudanar da kyakyawan rayuwarta a gidan Baba Babba ba ta da matsalar komai, gata da wani irin tattali ake nuna mata kamar su lashe ta, ihum kawai za ta ce a taso mata ana tambayanta ko tana son wani abu, ta samu kwanciyar hankali ta fara mai da jikinta kamar ba Maigadon da Sahal ya sukurkutawa rayuwa ba. Ta dawo cikin natsuwarta sai da ta ɗan sauya, wasu sabbin daɓi'u ta fito da su na abu kaɗan ne yanzu yake ɓata mata rai nan da nan za ta ruɗe ta fara faɗa daga nan sai kuka saboda cutar da ta yi na depression shi ya sa yanzu kowa ke lallaɓa ta, har Abida duk tsiyataku ta ta daina yi mata, kaffa kaffa take da ita sosai, zama suke yi su yi hira na tsawon lokaci suna dariya har da shewa, sannan su kan raba dare a ɗakunan juna suna hira.
Ana cikin haka ne irin zuwa ɗakinta da Abida take yi suna hira, ranar ma sun daɗe suna ta hira har wajen sha biyun dare Yaya Asad yana ta k'iranta a waya ta ƙi ɗauka Allah ya taimake ta, ta sanya wayar a silent da Abida ta lura da ta yi mata ɗan biki.
Suna cikin hirar Abida ta zama serious.
Tace "Maigado zamu yi magana muhimiya! Amma amanatul amana".
Bilki ta fara dariya tana tuna yarintarsu da lokacin da Abida ta ke siyar da jarida, idan kuma ba na kuɗi ba ne sai ta ce Amana ne.
"To Abida idan kuma subutar baki yasa na faɗa ma wani fa. A ranar lahira ta ci ni gudan jini ya faɗo?"
Suka kwashe da dariya har suna tafawa suna tuna lokacin yarintarsu da abubuwan da suka faru.
"Kai ba abin da ya fi ƙuruciya daɗi Abida.";
Bilki ta faɗa tana ɗan share ƙwalla daga gefen idanuwanta.
"Kamar jiya ta dawo. Kowa ya fi more lokacinsa a lokacin yarinta."
Bilki ta ce "haka ne kam suna tuno yaya Munnira suna cikin tsananin kewarta.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ta fad'a da alamun rashin sukuni.
Nan da nan Abida ta bata rai ta ce "Wallahi tunda na shirya sai mun je, ke ba dama a yi miki abin arziki sai kin gwasale mutum?"
A sanyaye Bilki ta mik'e ta ce "To jiramu mu shirya". Don tasan tunda Abida ta rantse to idan har bata kubutar da ita daga yin kaffara ba sai sun yi rikici mai tsananin gaske. Ita kuma a yanzu da suka shirya bata son su sake b'atawa da Abida.
Farha ta fara shiryawa cikin wani leshi Mai kyau Wanda aka yi masa kawataccen dinkin da ya sake fito da ainihin kyaunsa. Kai gaskiya telan d take bawa dinkin Amrah ta k'ware wajen iya d'inkunan yara.()
Ta fesa mata turare, sannan ta ce ta je falo wajen junior ta jirata.
Tunda suka dawo Abuja fir Farha ta ki sakewa da Abida. Duk da ko ina ta yi sai junior ya bita shi kam yana sonta tamkar yadda take son Yaya Farouk.
Ita ma cikin Egyptian abaya din ta Maman asalan da asala ta shirya ()
Ta kalli fatarta a madubi yadda farinta ya sake bayyana ga shi fatarta ta yi taushi ainun. Tunda matar Yaya Asad ta rasa rayuwarta a dalilin canja surar halitta da canja launin fata Bilki ta yi matuk'ar tsorata. Ta tsaya a iya mayukanta na oriflame da Aisha Lame ta zaba mata tun shekaru biyu da suka shud'e. Ta kuma gasgata ingancin products din oriflame. Babban abin da yasa ta likewa Aisha Lame saboda yadda ta nakalci rabe raben fatar dan adam tamkar wata shararriyar likitar fata.
Ta shafa hoda ta gogo man lebe a bakinta. Sai ta feshe jikinta da turarenta mai dad'in gaske.
Ta same su a falo tare da Momi. Suka yi mata sallama sannan suka fice tare da y'ayansu.
A motar Abida suka fice. Bilki a gaba yaran a baya yayin da Abida take tuki.
Kaitsaye millenium Park suka je. Suka dan yi chilling da hotuna. Sannan Bilki ta yanka cake tare da taimakon Farha.
Wani hoton da Abida ta d'auki Bilki ya yi matuk'ar yin kyau
Ta saka shi a status ta yi caption da cewa" Happy Birthday Maigado."
"Haka Mai gadon ta fita?"
Yaya Asad ya yi tagging hoton yana tambayar Abida.
Sai ya ga kamar kyan da ta yi, kamar kowa a wajen ita yake kallo. Kishi ya ji ya turniƙe shi from no where.
Ganinta a status din Abida duk sai ta sukurkuta shi ya ji ba zai iya sake wani dogon jira ba, yana son ya mallaki maigado cikin gaggawa kafin soyayyarta ta yi masa illa.
Abida ko da ta ga maganarsa sai ta tura masa emojin dariya.
"Haka muka fita dai."
Sai ta tura masa wanda suka ɗauka tare da Balki itama abayan ne a jikinta amma na ta ɓaka ce.
"Lalle zan zo na samu Baba Babba. Ya sake muku da yawa."
Haka ya ce mata ta bi shi da dariya.
Abida tana mamakinsa to menene abun da bai kyautu ba a tare da su?
Ranar sai dare suka koma gida washe gari dalleliyar motar ƙirar Toyata da Yaya Asad ya siya mata ta iso gida tunda Abida ta ƙyalla ido ta ga motar nan ta buga tsalle ta ce itama ba ta yarda ba sai an siya mata irinta.
"Tab lalle ne ma Yaya Asad ɗin nan, tunda Bilki da dawo gidan nan ya manta da ni. Wallahi nima sai ya siya mini wacce tafi ta Bilki tsada."
Ta fad'a tana kumfar bakin ya yi son kai, tana shinshino wani abune a ransa game da Maigado.
Momi ta gaji da mitar Abida ta saka baki da cewa ita ba tana da mota ba, ya siya mata kwanaki baya.
"Ai itama Bilkin tana da mota. In adalci ne ya siya mana gabaɗaya mana."
Abida ta fad'a tamkar ta fashe da kuka.
Baba Babba ya dinga dariya yana fad'in" Abida rigima."
Duk da haka ba ta haƙura ba sai da ta bi Bilki har ɗaki ta tsare ta da tambayoyi.
"Bilki me yasa yaya Asad ya siya miki wannan motar?
"To ni ina zan sani, ki kira shi ki tambaye shi mana"
Bilki ta bata amsa tana cunno mata baki.
Abida ta yi jim kafin ta ce" Baku da gaskiya daga ke har shi. Kuma idan bai siyo mini tawa ba. Billahillazi abin da ya faru a 2022 zai sake maimaituwa a wannan shekarar da muke ciki."
"Ya dade bai faru ba Abida ".
Bilki ta bata amsa cikin murya marar amo.
"Haka kika ce ko Maigado?
Da ni kike zancen, Allah sai na fasa kwan ai tuni na harbo jirginsa."
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Bilki to be sincire magana nake so mu yi dake, amma heart to heart."
Abida ta faɗa tana mai kallon Bilki a tsanake itama ganin haka yasa ta gyara zama tana sauraranta da dukkan nutsuwarta.
"Bilki ki ji tausayina! Ki duba halin da na ke ciki don Allah ba na ba ki tausayi?"
Ta faɗa tana mai nuna kanta muryarta har ya fara karyewa tana shirin ta fara kuka.
Abida mai taurin taurin zuciya amma yanzu rayuwa ta sanya duk ta yi laushi.
"Abida ina tausayin ki mana. Amma me ya faru ne?"
Bilki ta faɗa itama cikin damuwa ganin sauyawar Abida lokaci ɗaya.
"Dube ni fa Balki. Magana ta gaskiya ki ji tausayina ki faɗa mini in da Ya Sulaiman yake in kin sani. Ki duba shekaru uku ba kwana uku bane, ba sati uku bane haka nan ba wata uku ba ne, don girman Allah ki faɗa mini in dai kin san inda yake Bilki.".
Abida ta faɗa cikin karyewar zuciya.
Bilki ta yi tsam tana kallonta cikin wani yanayi na tausayin Abida tare da madaukakin mamakin yadda take cikin alhini da kewar Yaya Sulaiman.
A sanyaye ta ce
"Wallahi Abida na rantse miki da Allah tun ranar da Yaya Sulaiman ya bar gida ban ƙara ji daga gare shi ba. "
Ta faɗa tana mai kallon Abida da ta yi tsuru kawai tana kallon Bilki.
"Ki yarda da ni. Wallahi da na sa ni da zan faɗa miki."
"Na yarda da ke Bilki. Shike nan mu bar maganar. Ba sai an ji ba"
Kawai sai ta fashe da kuka har da gunji, jikin Bilki ya yi sanyi k'alau itama bata san ta fara hawaye ba sai da ta ji danshi a saman kumatun ta.
Tare suka zauna suka sha kukansu, ita Abida tana kukan gararin rashin mijinta ita kuma Bilki tana yin na rashin Yayanta da tausayin Abida.
Tasan kuma danne abin take yi a ranta dan kada a fahimci fargar jajin da take ciki.
Ranar ma tare suka kwana bayan sun gama kukan su nan Abida ta bingire ta fara barci sai da asuba ta farka.
Haka rayuwa ta cigaba da garawa Bilki ta hak'ura da dukkan zuciyarta mussaman da fahimci ya'yanta basa cikin mawuyacin hali sai kewarta da suke yi. Kullum ne sai sun yi waya sau biyu sau uku.
Domin tana ganin yadda take shiga farinciki in ta ga Ya Faruku ko ta ji ana mganarsa har gobe Maigado ba ta daina son Ya Faruku ba, kamar yadda shima tana da tabbacin bai daina son ta ha amma dai a yanzu ne ta kasa gane yanayin shi tun da yadda yi ma Balki wani kulawa ta musamman.
Washegari ya kama Birthday ɗin Bilki ne sai ga wani kayataccen cake mai delevery ya kawo dauke da sunan Maigado at 36 ɓaro ɓaro a jiki. Mamaki ya kama Bilki domin kuwa ita gabad'aya ta manta da yaune ranar haihuwarta gabad'aya.
Ta dinga tunanin wa ya aiko da wannan tsadadden cake din?. Zuciyarta ta harba don kuwa take ta hasaso mata Yaya Asad. Don shine ya lank'aya mata Maigado har kowa ya kama, sannan shi ko kudi da yake raba musu a envelop lokaci zuwa lokaci Maigado yake rubutuwa a jikin tata. Koma wanenne ta ji dad'i don sai kana da muhimmanci a wajen mutum yake tuna alamuranka mussaman har a rike ranar haihuwarka, ita ta shaafa'a ma 1 ga watan Aprilu ce yau.
Abida na ta fad'in tasan Ya Faruƙu ne ya aiko da sh.
Itama Bilkin fata take yi ace daga Yaya Farouku din ne. Ta dinga jin farinciki na mamamyarta. Tabbas tana son Yaya Farouku zata jure komai indai zata same shi. Duk sababin Jamila wannan karon ba zata bar mata shi ba.
Duk da Balki jin ta kawai take yi amma ita jikinta ya ba ta ba kowa ya aiko da wannan cake ɗin ba sai Ya Asad.
Nan da nan Abida ta yi wanka ta shirya cikin tsaleliyar Egyptian abaya ta()
Ta shirya junior. Da yake asabar ne duka muna gidan. Ta leko ta ganni kwance a gado Farha ma a kwance amma ta yi filo da cikinsa. Tana tambayar sauara kwana nawa su yaya Farouk su zo wajensu
Kafin Bilki ta amsa mata. Abida ta bude kofar. Ganinsu a kwance ba alamun komai ya snaya ta bude baki ta ce "Bilki wai ba shirya kuke yi ba dama?"
A sanyaye ta ce "Ni kawai ki dauko mu yanka anan. Me ya mini dad'i ne da zan tafi wani waje da sunan ina birthday!
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Tun daga ranar Abida ta fara tsokanta da Amaryan yaya Asad, yayin Balki ta yi ta masifa tana kufuluwa, don bata son wannan maganar ta yi tasirin da Yaya Farouku zai sake janyewa daga kud'irinsa akanta.
Dan haka kullum take bawa Abida amsa da fadin
"Allah ya tsare ni ya je can ya nemi amaryansa."
Abida kuwa bata fasa ba, don sosai take dariya idan ta ga yadda take fusata, ji take yi da auren Maigado da Ya Asad zai tabbata da tafi kowa farinciki da murna, amma tana ganin Bilki zata yi gardama, tunda ta lura da Bilki tafi son fararen maza.
Ya Faruku ma da ya zo ya ga mota sai da ya furta.
"Lalle Babban yaya alama da zafin sa ya kutso. Mu yara sai mu mu yi baya "
Balki ta ji zafin maganarsa sosai ta ɓata rai tana kallon shi kafin ta ce" Ya Faruku abin da za ka yi mini ke nan?"
Kana nufin abin da nake ga ni a idanuwanka wannan karon ma iska zai bi?"
Ya kasa bata amsa sai kawai ya tafi babu sallama.
Zuciyarta ta yi kunci bata yi zaton zata sake son wani namiji kwana kusa ba. Amma tabbas son Yaya Farouk ya kutso da k'arfin gaske daga inda ta sakaye shi a zuciyarta.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ana cikin haka sai ga Yaya Asad ya zo gidan. Bilki na wajen aiki. Gidan ba kowa sai Baba Babba, Momi ta je asibit ganin likita a dalilin ciwon k'afa ya matsa mata. Dan haka suke ta hirarsu da Baba.Tsawon lokaci yana zaune so yake Baban ya ɗan taɓo masa maaganar aure sai ya kawo masa maganar Bilki amma shiru Baban Allah bai sa ya yi masa maganar ba.
Haka nan ya tashi jiki ba ƙwari . Ya yi masa sallama tare da ce wa gobe zai dawo ya duba momi.
Yana harabar gidan ya ga an bude kofar ya ga motar Abida ta danno. Ya tsaya har ta fito ta nufo shi suka keɓe daga shi sai ita.
Dama tana jiransa ne tana zuwa ta fara masa kukan me yasa ya siyawa Bilki mota ita bai siya mata ba. Kowa sai ya rika nuna ya fi son Bilki akan ta, haka ma Yaya Faruku yake yi mata tun suna yara yanzu ma sun girma ba a daina banbanta su ba.
Ya nisa ya ce "Ho Abida! Yanzu nutsu ki saurare ni da kyau. Zan siya miki mota irin ta Bilki. Wacce kala ki ke so?"
Ta shagwabe fuska ta ce "Golden".
"To zamu yi magana, idan kin ba ni gudunmawa akan lamarin to da wuri motarki zata iso".
Ta murmusa tana jin ba abin da ba zata yi masa ba.
Ya maze sosai sannan ya ce
"Abida yanzu ba za ki taimaka mini a halin da nake ciki ba,? Kin fa son har yau ina son Maigado ba sai na zo na faɗa ba ya kamata ki taimaka ki taya nemin soyayyarta ba sai na fad'a miki ba".
Abida ta kunshe dariyanta tana kallon yadda yayan nata ya yi wani laushi
Shegiya Bilki tasan gwara kan maza, mazan ma irin su Ya Asad.
"Abida ki yi wani abu in son na killace Maigado a gidana cikin lokaci ina matukar son haka in kika tabbatar da faruwan haka zan jiyar dake dukkan daɗin duniya ba mota ba har ko jirgi idan ina da hali zan siya miki Abidan Baba."
Abida ta ji wata dariya ta sake kawo mata wannan karon ta kasa dannewa sai da ta fito
"Abida na zama abin dariya ne?"
Ya tamba a kufule.
"Abida da gaske nake yi ba. Ina son Maigado.".
Ya faɗa yana bayyana mata yanayin da yake ciki tausayin shi ya kamata ta san cewa yana sonta tun suna yara idanuwan Bilki ne suka rufe a wancam lokacin saboda wannan yaron yanzu kuma bata son me yasa ta sake runtse idanuwanta akansa ba.
"Ya Asad kaima da taka matsalar fa gaskiya.'"
"Menene matsalan tawa faɗa mini zan gyara in dai Maigado za ta saurare ni."
"Matsalar mu mata bama son idan ana son mu a yi ta kewaye kewaye. Gwara kawai ka fito ka faɗa mata gaskiyan abin da yake zuciyarka. Ballatana yanzu Maigado ba yarinya ba ce ta san abin da take so ta san abin da ba ta so, gwara ka tunkare ta da full confidence ka faɗa mata abin da yake zuciyarka.
Ya yi shuru yana sauraranta kafin ya jinjina kai ya ce" Haka ne Abida na gode. Cake ɗin nan da na aiko Maigado ta so shi kuwa?"
Abida ta yi wata dariya kafin ta ce' Daman kai ka turo shi,? Munafuka shi ya sa ta ƙi