Author : Hadiza D. Auta Category : Aysha Cool Novels
Farha ta matsa kusa da ita ta ce Mahmah ki ba ni kayana Dady ya ce "mu shirya za'a je shopping ".
Zuciyarta ta tsinke wato fishin nasa har ya yi tsananin da ba zai mata magana ba?"
Ta jijjiga kai tana fad'in tabdi jam a k'asan ranta. Ta yi tamkar ta ce Farha ba zata je ba, sai kuma ta tuna hakan ma laifine. Ta yunk'ura da ƙyar ta hau samanta Farha na biye da ita. Ta dauko mata doguwar rigarta mai kyau ta fesawa rigar turare. Ta watsa mata ruwa sannan ta shirya ta. Ta yi kyau sosai. Ta ce "Mahmah mai zan siyo miki?"
Ta murmusa ta ce "Duk abin da kika zabo mini ina so"
Ta fita da sauri tana fad'in "Sai mun dawo".
Tana zaune a bakin gadonta da yake Farha bata rufo mata kofar d'akin ba. Ta ga wucewarsa zuwa samansa. Ba jimawa ta ga ya sauko ya nufi k'asan da yaran suke. Ta yunk'ura ta bi bayansa. Yana shiga falon itama tana shiga. Ta ga duk yaran sun shirya wani irin k'amshi ya cika falon tunda sun yi amfani da turaruka daban daban. Sosai suka yi kyau. Hafcy ba za'a ce hannunta da ciwo ba ta shirya ta yi fes da ita. Ta ji sha'awar haihuwar y'anmata ya kamata haka nan sai ta ji tausayin anty Rukayya ya dirar mata ta mutu bata ga auren zaratan y'anmatanta ba. Haka Allah ya so. Itama ta ji tausayin al'amarin ina ga ubansu?
Da kanta ta fahimci dole ta canja taku akan yaran matuk'ar tana son ta samu kan Babansu. Ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa ya fito da ATM din asusun Zenith. Ya damkawa Hafcy tare da fad'in ki siya komai kike so don ke zasu raka. Ya juya ga Aysha ya bata wani ATM din ya ce "Dukkanku kowacce ta siyo abaya biyu da takalma biyu, sai turare da inner wears. Kada ku wuce hakan".
Ta shagwabe fuska don kuwa wanda ya bata takaitattun kudade yake zubawa sabanin na hannun Hafcy na babban asusunsa ne da komai za'a siya ba zai girgiza ba.
"Dady amma nima ya kamata ka jingina ni a wanccan ATM din gaskiya".
Aysha ta fad'a cikin shagwaba.
Ya rausayar da kai ya ce "Yau kam a hannun Hafcy yake ita kad'ai zata rik'e shi ta yi yadda take so. Ban da ita kuwa kowa ya yi hak'uri".
Bilki na tsaye tana kallonsu, take ta fahimci ya yiwa Hafcy haka ne don ta huce daga dukan da ta sha.
Suka rankaya suka tafi sai lokacin Laura ta fito itama sanye cikin tata Egyptian abaya ta maman asalan da asala.
Da wani irin salo ta ce "Sai mun dawo Dady".
Wani irin abu mai kama da kishi ya caki Bilki.
Yayin da shi kuma ya ce "Ki kula da yaran fa Laura" .
Bai zauna ba sai da ya ji an rufe gate tabbacin sun tafi.
Ya zauna yana danna remote ya kamo TRT.
Fitacciyar yar jarida Halima Umar Saleh tana bayanin k'alubalen tattalin arziki da nahiyar Africa take fuskanta.
Sosai ya nutsu yake saurarra. Ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya.
A hankali Bilki ta ja ƙafafuwanta ta isa kujerar da yake zaune mai cin mutum biyu ta zauna daf da shi.
Ta saka hannunta ta rik'e nasa a hankali ta ce "Baban Bilkisu how far?"
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Fine".
Ta sake jin wani iri da gaske dai fishi yake yi ta dukar masa y'ay'ansa.
Ta sake daurewa ta ce "Ka tura yara su siyo abayas din zuwa sallar idi babu ni. To ni da wacce zan je?"
*WANNAN LABARIN NA KUDI NE DUK WACCE TA KARAN BATA BIYA NI HAK'KIN WAHALAR DA NA SHA BA*
*ALLAH NE ALKALINA*
*WACCE TA SIYA KUMA TA FITAR ALLAH NA GANINTA NA BARTA DA SHI*
2384876855
*SURAYYA IBRAHIM*
*ZENITH BANK*
*GA MASU SON SAUKE HAK'KI*
Tana rufe baki ya ce "Ki shirya gobe James ya kai ki, Ki siyo".
A sanyaye ta ce "James kuma? Ni kai zaka kai ni ".
Ta fad'a tana turo baki irin na shagwaba.
Ya girgiza kai ya ce "A a ina da ayyukan da zan yi kada ma ki saka rai".
Ya fad'a idanuwansa na kan tafkekekiyar allon talabijin din da take girke ƙirar zamani.
Ta ce "Tom shikenan Allah ya kaimu goben ".
Bai amsa ba. Ta yunk'ura ta ce "Sai ka hawo".
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Tom".
Ta hau samanta, kaitsaye wanka ta shiga ta fito ta tsane jikinta da tawul ta shafa tuararukanta kalakala masu dad'in gaske.
Ta sanya wata irin rigar barci mai bayyana komai mai kyaun gaske. Ummu asalan da asala k'arshe ce wajen kawo mana abayoyi da rigunan barci masu tafiya da imanin mazaje.
A ranta kuwa ayyanawa take yi duk tsiyarsa yau sai ya huce da fishin da yake yi da ita tun daren jiya.
Ta zunduma hijabinta na gunis hijab...
Ta shiga kicin dinta na saman nata ta hado masa shayinsa ta shigo masa da shi. Daga nan ta yi sallar isha. Ta Dade tana lazimi akan sallayarta. Sai wajen shadaya saura ta ji motsin dawowarsu. Don haka ta mik'e da hanzari ta sauka ta tarar da shi a inda ta bar shi. Ya dago ya kalle ta don k'amshinta ya cika masa kofofin hancinsa.
K'ananun ne suka fara shigowa kowa da ledarsa a hannunsa Amal da Noor da kuma Farha suka nufe ta suna nuna mata abin da suka siyo.
Da murmushi ta duba na kowa a cikinsu tare da yaba musu sun iya zabe.
Bilkisu ma ta nuna mata. Sababin Aysha da Hafcy da suka nunawa Babansu kawai. Hafcy siyayyar da ta yi tamkar da gayya don kuwa har da zoben gold ta siyo da hadaddun turaruka designers. Ban da dogayen riguna da takalman da ya ce. Ya kalli Laura da ta gefe ya ce "Ke ina na ki kayan?".
Ta matsa kusa da shi ta bude ledar ta fito da su ya ga ni.
Daga haka ya karbi ATM d'insa ya ce "Oya ku je ku kwanta don ku tashi qiyamul lail".
Kowa ta debi kayanta cikin murna suka haye samansu.
Suna fad'in "Mun gode Dady".
Tuni an kammala labaran TRT. Don haka ya latsa remote ya kashe talabijin din a sanyaye ta ce "Mu ma muje mu kwanta kada mu makara".
Bai ce komai ba, ya mike ya rigata tafiya, ta tsaya ya kashe komai sannan ta bishi.
Ta tarar ya zauna ya fara shan shayin da ta ajiye masa. Yayin da ta shiga bayi ta yi fitsari ta fito kaitsaye ta haye gado. Sannu a hankali ya gama shan shayinsa ya shiga wanka, ya fito ya shirya, sannan ya kwanta. Mintina goma bata ji ya kai hannunsa ba, ta ji wani irin takaicinsa na kamata. Tsawon lokaci suna kwance kowa na tunanin zuci. Cikinta ya cure ya dunkule waje d'aya sannan sai harbin inda ya dunkule din yake yi sosai. Da azama ta kamo hannunsa na dama ta d'ora akan cikin daidai inda ya dunkule din yake bouncing da k'arfin gaske.
Jin yadda cikinta yake yin lugude tamkar ana kokawa a ciki ya sanya jin tausayinta har cikin zuciyarsa ya ratsa shi. Da sauri ya matso gabadaya ya rungumeta ta baya yana fad'in sannu "Maigado, sannu kina jin zafin naushin nan ko?"
A tausashe ta ce "Tun jiya fa har yanzu ban huta ba."
Murya na rawa ya ce "To ko asibiti zan kai ki a duba a ga ni, kada ya taba miki kidney ko liver!
Ya fad'a da firgici. A shagwabe ta ce "A a da zarar ya samu an zuba masa abin da yake so zai k'yale ni na huta".
Murya na rawa ya ce "me yake so to?"
Da wata irin murya ta ce "Baku gaisa shekaranjiya, da jiya ba, yau ma ya jika shiru" .
Jikinsa na rawa ya hau kai mata kisses masu zafi daga nan kuma suka lula sama jannati.
Tsawon lokaci suna dirzar juna kafin su samu nutsuwar da ta dace da su. Da kansa yake mamakin yadda ita bata gajiya da harkar, takaici ya kama shi na yada waninsa ne ya horar da ita da son wannan al'amarin. Matarsa ba mai yawan sha'awa ba ce, bata kuma da juriya a fannin amma Maigado kam ya lura sun yi matching da juna, mai juriya ce duk yadda zai gurje ta bata nuna ta gaji ko ya gundure ta kawai ruwa take feso masa da yake k'ara masa kuzari da gamsuwa. Cikin jikinta bai rage musu komai ba illah k'ara mata zalamarsa da ya yi. Ya dinga jin kishin yadda Sahal ya kwashe shekaru masu yawa yana kwasar ganima da babbar mace irin Bilki alhalin ita din matar manyan maza jarumai ne ba irinsa da yake a lankwashe ba.
Tare suka yi wanka suka kwanta Yana shafa cikin da ya yi luf da alamu suka nuna ya yi barci.
Murya ba amo ya ce "Maigado na ji ya baje daga nan".
Ta taya shi d'ora nata hannun ta ce "Ya ji ruwan dumi, ya ji lafiyar babansa, ya yi barci".
Dariya ta subuce masa ya ce "Maigado bana son sharri fa ke dai ki fad'i gaskiya kina son a jijjiga ki kawai, ba sai kin jinginawa unborn ba"
Da murmushi sosai ta ce "Allah Dady shine ga zahiri ka ga ni, yanzu ba ya daina hautsinawa ba?"
Ya yi saki gauron numfashi ya ce "Na yarda."
Ta karya harshe sosai ta ce "Baban Bilkisu gobe idan an sha ruwa tare zamu fita ka yi askin sallah, nima a wanke mini kaina. Jiya na yi Oder din abayas a wajen Maman asalan da asala mazauniyar Eggypt din nan".
Da hanzari ya ce "Tom Allah ya kaimu, zamu je. Amma ban da kin fad'a mini ai har da yaran Sai a siyo musu daga can din".
Dad'i ya ratsata waton dama ba wani abin da zai yi?
A tausashe ta ce "Yanzu ma tunda bata turo mini ba, sai ta hado da nasun, gobe zan yi magana da ita sai Slsu zabi design din da suke so. Na gode ka ƙara hakuri da ni Allah ya tsare ka daga dukkan sharrin zamani".
Dad'i ya ratsa shi ya amsa da fad'in "Ameen Maigadona Allah ya sauke ki lafiya na k'osa na yi tozali da abin da ke cikinki k'warai da gaske. Tun ban gan shi ba ya samu matsayi mai yawa a zuciyata. Ina sonki ina son duk abin da ya shafe ki sarauniyar shaiba!
Daga haka ya latsa makunnar wutar. Ya karanta falaki da nasi tare da ayayul kutsiyu ya tofa a hannayensa ya shafe mata jikinta.Wani irin faricinciki ke tunda ga k'asan zuciyarta tare da wani irin shaukin da bata taɓa jinsa akan kowa ba sai akan Baban Bilkisu.
Ta kasa magana amma tabbas yanzu tasan ta yi aure, yanzu ne ake jiyar da ita dad'i tare da gusar mata dukkan sha'awarta. Tana jin ya sake karanto wasu surorin tsarin ya shafe nasa jikin sannan ya kwanta ya rungume ta a haka barci ya sure su.
Daga haka ya warware bai sake yi mata fushi ba. Da daddare kuwa ya dauke ta suka fice basu dawo gidan ba sai wajen shabiyun dare.
Aysha da Hafcy sun shiga hayyacinsu da ita, sun daina yi mata habaici haka nan sun fita a harkar Farha basa dukanta. Sai dai kuma basa yiwa Bilki magana.
Sun tafi a fahimtar ba haka kawai ta bar ubansu ba.
Abubuwan da yake yi a kanta ba iya soyayyar Allah da Annabinsa ba ce.
Dan haka ta samu sauk'in matsaloli amma bata jin dad'in yadda yaran suke gaba da ita. Da kanta ta fahimci duniya haka take babu wani cikakken dad'i. Wannan auren tabbas shine abu mafi dad'i gareta a yanzu. Don auren Asad ne ya fahimtar da ita akwai wani abu farinciki a duniya. A duk sadda cikin jikinta ya motsa sai Yaya Asad ya faɗo mata sannan kuma sai ta ji zuciyarta ta motsa a kansa. Zuwa yanzu babu k'insa da take ylji babu dalili a zuciyarta. Sannan ta gamsu ta fara sonsa, irin son nan mai shiga da sanɗa kafin an ankara ya yi tasirin gaske .
Tun ba'a je ko ina ba ta fara jin takaicin dogon zaman da ta yi da Sahal kuruciyarta na tsiyayewa a banza. Da tasan haka al'amarin yake da Yaya Asad zata aure tun farko Allah bar shi su fafata da matarsa. Don ko yanzu da Rukayya take kwance a k'asa duk yadda suka yi mu'amala mai dadi kishinta take ji, saboda hotunanta da suke samansa da dakin barcinsa ya sanya ta haramtawa kanta kwana a d'akinsa. Kuma tabbas nan gaba kad'an zai san yadda zai yi da su dan kuwa yadda ya girke su da hannuwansa to kuwa da hannayen zai kwashe su ya sakaye a wani lokon.
Ranar sallah Asad da kansa ya tuka iyalinsa a mota zuwa masallacin kasa na birnin tarayya(National mosque) don yin sallar idi.
Sai dai motor y'ansanda tana binsu a baya don kare lafiyar maigidansu da iyalinsa.
Daga masallaci gidan Baba suka zarce.
A gaban ya'yansa da yaransa ya fito ya budewa Bilki k'ofa ta fito ya sara mata bayan ya karbi jakar hannunta. Ganin hakan ya sanya ayarin y'ansanda ma suka yi abin da ogansu ya yi tare da fad'in "Madam barka da sallah!.
Aysha da Hafcy suka ido suna kallon ikon Allah ya yin da Bilkisu junior take vedio da tsaleliyar wayarta. Don abin burge ya ya yi tare da fatan itama ta auri jami'in tsaro ya dinga saluting dibta8cike da soyayya da girmamawa a gaban kowa.
Aysha da take lauya cemm tuni ta gama lissafinta ta gano dalilin da ya sanya mominsu yin surgery wato Dady na son mata masu mazaunai da cikar kirji ita kuma bata da su. Idonta ya cika da hawaye a dalilin ta yi amannar ko momi na da rai zai nade k'afar wando ne ya auro mata Anti Maigado ya kuma sha shagalinsa da ita, a yanzu kuma da babu ranta yana holewarsa da ita a gaban kowa yake nunawa ita din ta mussaman ce babu alhini ko tunanin tsohuwar matarsa. Ta saki gauron numfashi a dalilin Su din bai gaza musu da koami ba, komai suke so haka zai yi musu, Duk kuma soyayyar da yake yiwa Bilki da suke adawa da hakan bai hana ya basu lokaci musu tattauna ko ci abinci tare ba.
Haka ma Anty Maigado bata yi musu komai ba, illah auren Babansu alhalin ya k'i anty Laura. Sannan dangin uwarsu kaf fad'a musu suke yi rabon auren Bilki ne ya kashe uwarsu.
Tunda shi ba mai ra'ayin aure aure ba ne. Amma yanzu Aysha ta fara kokwanton dan Babu Momi ne ya sanya ya aure ta. Tabbas ko ta na nan sai ya auro ta. Kuma ta yi imani takwarar da ya yi mata tun tana budurwa ba dan zumunci ba ne, dan yana sonta ne yana kuma rarrashin zuciyarta ta amince masa.
Duk zumuntarsu da anty Abida bai sanya sunanta ba. Kuma dukkansu sun san anty Abida ce favourite sister d'insa. Shiyasa take yiwa mominsu wulak6da isgili ba tare da iya yi mata hukunci ba, a karshe ma Sai Dai ya ce momin ce bata son y'anuwansa, shi kuwa duk mai sonsa to ya so Abida.
Haka ta ja jiki ta bisu a baya zuwa cikin gidan gabad'aya jikinta a sanyaye tana ta tunanin da shine ya rasu to da Momi zai yi wahalar gaske ta yi aure. Idan har kuwa zata yi to ba zata yi a kusa irin haka ba, idan kuwa ta yi shekararsa d'aya kacal a k'asa society Sai sun fitine ta da fad'in bata damu da mutuwarsa ba tunda ya bar kudi daga mutuwarsa har ta yi aure saboda tsananin fitina.
A babban falon ta tarar da dadynsu da dukkan tawagarsa sun gurfana gaban Baba da Momi da suke zaune a kan kujera.
Itama ta durkusa gefen Bilki tana mik'a tata gaisuwar.
Baba ya dinga addu'a da fatan Allah ya karbi ibada. Yayin da jikin Bilki ya yi sanyi tana hasaso ita nata mahaifan babu ko d'aya.
A hankali y'ansanda suka fice suka bar iya ahalin gidan. Tuni kuma an cika musu gabansu da cimaka iri iri. Abida ta fito sanye da gown ta Malaysianfabrics...... Ta yi kyau sosai duk ba kwalliya ta yi ba junior na biye da ita cikin shudiyar tsadaddiyar shadda.
Aysha da su Laura suka dinga gaishe ta cike da girmamawa. Dama haka suke kaffa kaffa da ita tunda ba ta yi musu.
Ta isa gaban Yaya Asad ta yi saluting d'insa ta ce "Barka da sallah Baban Bilkisu I.G.P din gobe da yardar Allah ".
Dad'i ya kama shi ya mike ya cire hularsa ya yi saluting dinta ya ce "Barka dai Abidan Baba k'anwar Bilkisu ".
Bilki ta kalle su cikin shauki da tuna baya, ta sani Yaya Asad da Abida wata irin kaunar juna suke yi ba kad'an ba, tamkar dai yadda suke ita ta da Yaya Sulaiman.
Karon farko Abida ta sunkuya ta cicciba Bilki ta yi saluting dinta ta ce "Yaya Maigado barkanmu da ibada".
Dad'i ya ratsa Baba Babba yana jin had'uwar kan mutanen ukun nan za'a ji ci lagon gabar da ta yi k'arfi a tsakanin ya'yansa da na Baba k'arami.
Shiyasa tunda al'amarin ya faru Bai sake barci cikakke ba Sai bayan auren Bilkinsa Asad. Wannan auren shine tsanin yin sulhu da afuwa a tsakanin ya'yansa da na k'aninsa. Don kuwa gidan Asad zai zama kowa na da alaka da gidan kaitsaye. Shiyasa kullum sai ya yi musu addu'ar Allah yasa albarka a cikin aurensu ya kuma dauwamar da shi.
Da dabara Abida ta janye Bilki suka yi d'aki.
Ta ce Maigado cire mini wannan bubu abayar na ganki sosai. Wato watannin aurenki watannin cikinki, ke Maigado ki rage had'ama".
Dariya ta k'wacewa Bilki ta ce "Ni da kika raina kya fad'a mini haka mana, alhalin shi ya kamata ki tambaya ki kuma jingina masa had'amar."
Abida ta ce "Ke da shi dai sak kun dace halittarku d'aya. Na taɓa jin matarsa na faɗawa wata aminiyarta cewar shi mabukaci ne na sosai ita kuma tsaka tskai ce. Kin ga kema tuni na san mabukaciyar ce kin ga ai abu ya yi kyau dole na jiki shiru babu wani borin ba Kya sonsa."
Kunya ta lullube Bilki don ta san gaskiya Abida take fad'a.
Can ta nisa ta ce "Bilki na fa k'osa wanccan birkitattancen yayan naki ya dawo, na k'osa k'warai da gaske ki faɗawa mijinki nima irin halittarmu d'aya da ku, an fara bincikem inda yake kamar yadda ya