Author : Hadiza D. Auta Category : Aysha Cool Novels
sosai zai kwaso musu?
Jikin Sulaiman ya yi sanyi don kuwa kishi muraran ne ya bayyana a dukkan gangar jikinta da k'wayar idanuwanta.
A tausashe ya ce "Ashe duk wa"azin da jan kunnenku da ake ta yi akan ku sassauta kishi ji kawai kuke yi, yana wucewa ta bayan kunnuwanku! Irin wannan tashin hankalin da kika shiga to idan Yaya Asad ne zai k'ara auren ya ya kenan?"
Ga mamakinsa sai ji ya yi ta daddage ta zunduma ihu da iyakacin k'arfinta."
Daidai lokacin oga Asad ya shigo a sukwane.
Ya dawo d'aukar wani file, ganin juyawa zai yi sai ya saka aka yi parking a waje bai shigo da mota ba.
Jin ihun Bilki ya sanya ya shigo a sukwane a zatonsa ta hadu da wani ibtilain ne wala na gas ko zamowa daga k'afar bene.
Ganinta zaune ga Sulaiman ya sanya cikin kid'ima ya ce "Menene Maigado, wa ye ya rasu?"
Da kuka ta ce "Wai ashe aure zaka yi?"
Da hanzari ya ce "in ji uban wa?"
Ta kasa magana illah kallon Sulaiman.
Oga Asad ya kalli Sulaiman ya ce "oooh wooh wato zuwa ka yi ka haddasa mini rikici ka tayar mini da hankali ko?"
Sulaiman ya kasa magana a dalilin ya ga oga Asad ya shiga yanayin da yake dealing da su".
A sanyaye ya ce "Wallahi misali kawia na yi mata".
"To akan me zaka yi misali da ni? Ka yi mata misali da kanka ko da Usman mana, ni sa'anka ne?"
Sulaiman ya yi k'asa da kansa cikin tsananin tu'ajibin Bilki da oga Asad.
Yana mamakin Bilki ne yadda ta k'ulla masa karya yana zaune akan idonsa.
Yana kuma mamakin oga Asad na yadda ya birkice tare da k'ok'arin gamsar da Bilki bai san maganar ba, shi ba zai k'ara aure ba, to mai ma zai yi da wata macen?
Sulaiman cikin tsananin mamaki yake kallon yadda shi kuma ake yi masa muzurai, ita kuma ana rarrashinta cikin rawar jiki tamkar su Farha.
Ya tsinci kansa da tambayar shi da oga Asad wa ya fi wani gudun zuciyar matarsa ne?
Don kafin su bata da Abida haka take yi masa sangarta iri iri yana rarrashinta cikin rawar jiki".
Bilki da Abida ja'iran yara ne na k'arshe. Ashe ba shi kad'ai ba ne yake zullimin a yi masa fishi. Son girma irin na Yaya Asad amma an saka shi yin b'are b'are a gabansa.
Sai da ya ga walwalarta sannan ya koma office bayan ya jawa Sulaiman kunnen kada ya kuma saka ta kuka.
Yana tafiya Sulaiman ya kalleta ya ce "Bilkina yaushe kika zama kwalba ne irin hak?"
Da murmushi ta ce "So nake ka fahimci ita yarinyar da kake ta kwarzantata iya zahirinta ka sa ni, sanin badininta zai yi maka wuya don ga shi nima da ka rayu da ni na ankarar da kai baka gama gane ni ba, bare wata can. Ka bar batun karin aure ka fuskanci iyalinka. Abida ta yi kukan rashin ka, ta yi nadama mai yawa, dan Allah let gone be by gone."
Ya nisa ya ce "Ki taya ni addu'ar zabin alheri. Yarinyar ta shiga raina haka take doguwa yar shawalwala bak'a tamkar dai Abidanki".
Bilki ta cuna baki gaba bata ce komai ba.
Ya mike yana fad'in "Gobe in sha Allah zan tafi Kano".
Itama ta mike tana fad'in "Sai yaushe zaka dawo?"
Ya yi shiru yana nazari.
Can ya ce "Nan da sati uku ko wata daya don zan je Katsina. Ba kuma zan dawo na sai da su Hamida".
Farinciki ya bayyana a fuskarta don tasan Yaya Hamida dolenta ta biyo Yaya Sulaiman ko ya yi mata tozarci a gaban mijinta.
*Wannam shafin dandano ne*.
*Cikkakun Shafuka na telegram*
*Surayya Dee*
*Na gode*.
Save Restricted Content Bot, [Oct 31, 2025 at 11:55]
*Dingishin Kwado*
08032773332
*Available on telegram and arewa pen*
Bai tafi ba sai da aka kawo masa twins ya gansu.
Ba yadda Bilki bata yi akan ya tsaya yara su dawo amma ya k'i.
Ta murmusa tana jinjina kawaicinsa akan Farha.
Farha ga ni take yi Sahal ne Babanta. Don yadda take ji da leshin da ya aiko mata wanda tare da Amra ya dinka musu da sallah kamar me.
Idan har zata yi kwalliya duk tsadaddun kayanta sai ta ce leshin da dadinsu ya aiko mata zata saka.
Bilki dai bata taɓa ce mata komai ba. Ta sani sannu a hankali zata gane su waye ainihin mahaifinta da mahaifiyarta.
Ba Sulaiman kawai ba hatta Abida tana kashe Bilki da mamaki don yana wahalar gaske ta yi maganar Farha haka siddan.
Suka yi sallama direban da ya d'auko shi, ya tafi mayar da shi.
Yana isa k'ofar gidan motar Abida ta iso.
Aka bude mata gate ta shiga.
Da yake daga k'ofar gida ya sauka.
Ya shiga cikin gidan daidai ta kammala parking.
Ta fito gabad'aya a gajiye take. Kallonta kawai ya yi ya fahimci a tsaye ta yini tana kuma jin yunwa.
Ba walwala, ba sukuni ta ce 'Yaya Sulaiman an yini lafiya?"
Bata jira zai amsa ko ba zai amsa ba, ta rufe motar ta tafi rik'e da labcoat da jakar hannunta.
Ido ya bi bayanta da shi yana ganin yadda take tafiya a gajiye.
A ransa yake ayyana da a gidansu suke ta dawo gida a gajiye haka da sai ya yi mata tausa tilas. Yanzu kuma takaicin yadda ta shige cikin gida kaitsaye ne ya kwamushe shi.
Akan me ba zata zo d'akinsa ta dinga hayagagar ita ta gaji tausa take so ba. Duk da yasan a yanzu ba zai yi mata ba. Amma dai ta zo mana. Wato da gaske ta gaji da ba shi hak'uri kenan? Ya jijjiga kai.
A fili ya furta "Dole ki dawo da rarrashina Abida."
Washe gari ya gama shirinsa akan zai je Kano. Ya yi sallama da su Baba.
A ranar Abida evening zata yi.
Dan haka Baba ya ce ta kai Shi airport da kanta.
Har cikin zuciyarta a dole zata kai shi kawai gardama da Baba ne ba zata sake yi ba.
Ta shirya junior ta tarar da shi a tsaye yana jiransu.
Ta bashi mukullin ya karɓa don gabad'aya yanayinta irin wanda baya so ne. Sanyi k'alau ba kazar kazar ba takalar faɗa ko rintom tana binsa kud'i.
Yadda ta ɗauko junior ya sanya ya gane ba zata yi wata doguwar magana ba, bare ta yi zantuka masu nauyi.
Haka ya ja motar suka fice. Sun yi nisa sosai ba wamda ya ce uffan.
Gabad'aya ya ji komai ya gundure shi. Ya waiwaiya ya ga junior ya yi barci ne.
Ya numfasa ya ce "Amma ina ga na sha fad'a miki ban son wannan dan gyalen da bai fi daidai Noor da Farha ba".
Tana kishingiden ta ce "Bubu ce a jikina ai babu damuwa".
A tunzure ya ce "To ni a wajena da damuwa" .
Maimakon ya ji ta hakikance tana fahimtar da shi sai kawai ta ce "Idan muna tare za'a gyara". Daga haka ta kame bakinta ta yi shiru.
Ya rasa kuma mai zai ce don gabad'aya ba haka yake so ba.
Shi yafi son su yi ta daru.
Ya kasa hak'uri ya ce "Ke nan kina jiran na sallame ki ko?"
Maimakon ta amsa masa da Baki Sai kawai ta fara kuka, kuka kuwa mai nauyi.
Hankalinsa ya yi tashin gauron zabi. Ya zuba ido kawai yana kallonta cikin kaduwa da lamari.
Sosia ta yi kukan sai da ta gaji dan kanta sannan ta bude jakarta ta goge fuskarta.
Ya nisa ya ce "Wato dai so kike ki nuna na zalunce ki ko Abida? Akan me za ki dinga yi mini irin wannan kukan?"
Bata ce masa komai ba.
Ya rasa mai zai ce. Kan dole ya rage gudun da yake yi.
Murya ba amo ta ce "Idan baka ji a jikinka ka zalunce ni ba. To ai baka da kaico kada ka damu kanka".
"A hassale ya ce "To menene ya sanya ki kuka, menene damuwarki ne?"
Hawaye ya sake k'wace mata. Ta ki yin magana illah hawaye da yake ta tsere a fuskarta. Hankalinsa ya yi tashin gauron zabi.
Ya fara fad'a.
"Ki cigaba da yi mini kuka ba gaira ba sabar. Ban yi miki komai ba, haka kawai sai kin tayar mini da hankali alhalin ma kamata ya yi na sake fita a harkarki tunda jiya da yau duk gaisuwar raini kika yi mini. Abida cigaba daga inda kika tsaya na wulakanci ai ba zan mutu ba. Ba dai aikin da zan je yi ne za ki yi sanadin da zan kwakwalewa mutane idanuwa ba. To Allah ya baki sa'a ki yi sanadin da za'a rufe ni saboda zan yi aiki babu nutsuwa a tare da ni." Save Restricted Content Bot, [Oct 31, 2025 at 11:58]
Maimakon ta yi shiru. Ai kawai sai ta cigaba da zirar da hawaye tamkar ruwan famfo.
"Har suka airport bata yi magana ba illah kukan sharb'e.
A ransa fad'i yake yi "Wannan shine ga mari, ga tsinka jaka. Shi dai a yanzu ba zai wani rarrashe ta ba. Amma kukan da take yi ya yi matuƙar dungunzuma zuciyarsa.
"Kai mata da kinaya suke barin ma dai Bilki da Abida".
Kan dole ya ce "Dauki wayata ki yi dialling lambarki. Sai ki yi saving sabon layina.
Dad'i ya kamata amma ta matse. Shekaranjiya ba irin rokon da bata yi masa akan tana son lambarshi kafin ta ga chart d'insa da budurwa amma ya hanata. Bayan ta ga chart kuma ta rasa kuzarin da zata kwafi lambar layinsa ko ta k'ira layinsa.
Murya ba amo ta ce "Bar shi kawai Yaya Sulaiman ba sai na ajiye lambar ba, tunda ba da ni kawai zaka dinga yin waya ko chart ba, ni na hak'ura kawai".
Ya zuba mata ido yana karantar yanayinta.
Cikin sakwanni ya fahimci da dukkan gaskiyarta ta yi jawabin. Hakan kuma alamace idan har zai yi aure to zata bar shi gabad'aya ne.
Ya hassala ya ce "Abida, Abida, Abida!
Kanta na kasa ta ce "Na'am Yaya Sulaiman ".
"Wallahi ki bini a hankali wato har kina da kuzarin da za ki saka mini sharadi, saboda na yi shiru ban bayyana abin da kika yi mini ba?"
Ta fara kuka mai sauti ta ce "Ni ban yi komai ba, ba yadda za'a yi ace Abida mai hankali da ilimi ce zata soki MAMI. Sharrin jinnul Ashiq ne ba ni ba ce. Duk da haka na baka hak'uri kan hak'uri amma ka kasa yafe mini. Tsakanina da Allah na gaji. Kawai ka fito ka fad'i laifin nawa, sannan ka yanke mana decision, don na gaji da wannan takurarren yanayin da nake ciki.
Idan zaka iya yafe mini komai ya wuce to hakan nake so.
Idan kuma a zuciyarka kana ganin ba zaka iya yafe mini ba, to be sincere bata mini lokacin da kake yi ya isa haka".
Ya yi shiru.
Cikin sigar umarni ya ce"Abida d'auki wayata ki yi abin da na sanya ki".
A wannan karon bata k'i ba.
Ta dauki wayar ta kira layinta sannan ta ajiye masa.
Sun isa airport ya yi parking a inda aka tanada.
Ya ga bata motsa ba.
Ya ce "Zan tafi"
Kanta na k'asa ta ce "Allah ya k'addara had'uwarmu".
"Kina daga zaune ba zaki taso ki rike mini jakata zuwa bakin entrance ba?"
Murya ba amo ta ce "Ka yi hak'uri jikina babu kuzari, idan ka dawo zan zo har can din in sha Allah."
Ya girgiza kai ya fice ya bude boot ya dauki jakarsa.
Ya bude baya ya shafa kan junior sannan ya rufe motar.
Ya ga tana zaune a inda take zaune ba alamun zata fito ta shiga mazaunin direba.
Ya ce "Abida fito ki ja maotar nan".
Bata kalle shi ba ta ce "Zan tafi ne."
"Yanzu za ki tafi".
Ba musu ta fito ta shiga ta yiwa mota key sannan ta yi gaba ta bar shi ba hon ko daga hannu.
Ya saki ajiyar zuciyar ya ce "Allah ya shirye ku kawai".
Don a yanzu ita da Bilki wani irin ga ni yake musu na daban.
Kaitsaye gidan Bilki ta dira.
...
Alti ta dinga murnar zuwanta. A gidan ta karya. Junior kuwa yana wajen wasan yaran da aka yi musu na mussaman.
Bilki ta ce "Me ya samu idanuwanki ne haka Abida?"
Ta ce "Hmmm wanccan yayan naki mana da yake neman kashe ni a tsaye. Tisa shi a gaba na yi da kuka mai gigitarwa kuma na k'i magana. Na fad'a miki ya rikice ya hau sababi da buyagin zan saka ya kwakwalewa mutane idanuwa".
Bilki da Alti dariya sosai.
Alti ta ce "Kina wuta Abidan Baba."
Ta nisa ta ce "Allah Alti al'amarin ya fara fin k'arfina. To nasan baya son ya ga ina kuka, tunda shi juninsa taurin rai to idan zamu hadu sau goma,.zai ga ina kuka".
Ta waiwaiya ta ce "Maigado ya fad'a miki yana neman aure a Kano?"
Bilki ta girgiza kai cikin nutsuwa ta ce "A a ".
Abida ta samun nutsuwar zuciya tunda bai faɗawa Bilki ba to kuwa ba da gaske ba ne".
Ta nisa ta bata labarin chart d'insa da ta ga ni".
Bilki ta k'i ta nuna mata wata alamar ta sani. Ta ce "Wane shi ya fara wannan katobarar ai da mun bar shi for life".
Dad'i ya cika zuciyar Abida ta ce "Ai kuwa tunaninmu d'aya don Wallahi hak'ura zan yi da shi matuƙar ya ce bayan wannan dogon lokacin da na shafe ina dakonsa zai mini tukuicin kishiya to kawai na yafe shi. Zan ta dumama ruwan dumi da gishiri ina gasa wajen ba shikenan ba?". Save Restricted Content Bot, [Oct 31, 2025 at 12:06]
Gabad'aya suka fashe da dariyar batunta.
Sosai suka yi hira ta warware sai yamma ta koma gida.
*Kano*
Zuwa yamma ya kammala da asibitin Makka eye Hospital da yake Gadon Kaya.
Ya saka hannun kan aikin da zai yiwa mutane 100 cikin kwanaki goma.
Wand za'a fara kwanaki biyu masu zuwa.
Ganin yamma ta yi kaitsaye ya zarce Bristol hotel da yake farm centre ya kama d'aki.
Washegari wajen shad'aya abokinsa ya zo a mota ya d'auke shi zuwa gidan Hamida da yake court road.
A bakin gate din gidan ya ajiye Shi akan idan sun gama ya masa waya ya zo ya dauke shi.
Sulaiman ya yi mass godiya.
Maigadin ya shaida shi don haka ya bude masa k'ofa babu bin ba'asin daga ina yake ko wajen wa ya zo.
Ya shiga katafaren gidan Hamida.
Amma tashin hayaniyar da yake jiyowa daga cikin gidan ya saka shi fargaba.
Haka ya kutsa cikin gidan ya tarar tana zaune tana kuka yayin da mijinta ke tsaye cikin tsananin fishi ga y'arta ta farko da k'aninta a gefe suma cikin wani irin yanayi marar dad'i.
Hamida na jin muryarsa ta zabura ta nufe shi ta rungume shi.
Shima ya rungumeta. Kanta na kan kafaɗarsa ta kasa magana illah kuka mai tsananin gaske da take yi tamkar zuciyarta zata yi bindiga.
Hankalinsa ya yi tashin gauron zabi.
Ya rike hannunta ya Ta zuwa kan kujerar da tafi kusa da su.
Ya kalli mijinta ya ga fishinsa ya ragu ba kamar sadda ya shigo ba.
Da girmamawa Sulaiman ya Fara gaishe shi don kuwa na sa'ansu ba ne zai kai Yaya Asad.
Shima Mai sharia da mutuntata ya karbi gaisuwar Sulaiman.
Ya ce "Zo mu je ka sauka a wajena."
Sulaiman bai ki ba, ya bishi zuwa falonsa.
Da kansa ya gabatarwa Sulaiman ruwa da lemo sannan ya zauna suka sake sabuwar gaisuwar yaushe rabo.
Jikin Sulaiman a sanyaye yake amsawa don halin da ya tarar da kanwarsa ya yi awon gaba da dukkan kuzarin da ya shigo da shi.
Ya kasa jurewa ya ce "Ranka ya dade na ga gidan naku babu lafiya, gabad'aya na shiga rud'ani".
Mai shari'a ya muskuta ya ce "Ai rufin asirinta daya da Allah ya turo ka a daidai wannan lokacin. Ba dan haka ba yau tabbas sai sun bar mini gida da ita wadannan yaran guda biya.".
Sulaiman ya sake rikicewa.
Murya na rawa ya ce "Subhannallah abu bai yi dad'i ba ranka ya dade. Lamarin mata ai hak'uri ne kawai, duk girmansu idan suka yi wani Abu sai a tamkar yara kananu da basu san komai ba. Ka ƙara hak'uri ai ba zaka biye mata ba. Ko ni nawa nake a gabanka bare ita yarinya ce ai".
Mai shari'a ya ce "Dr ba wani yarinta ina ce Ga y'arta nan da ace tana kammala sakandire aka aka yi aurenta da tuni tana da jikoki ai kuwa ba maganar yarinta iyashege ne kawai da shakiyanci a wajen Hamida.
Kuma tabbas ta kai ni bango. Nauyin iyayenku nake ji amma tunda ita ta riga ta kwashe kayanta a gaban ma'aiki to zan gwada Mata karshen iyashege."
Sulaiman dai hak'uri yake b shi don ya lura ya yi fishi mai tsananin gaske alhalin Shi mutum.neai hak'uri sosia.marar hayaniya.
A nutse Sulaiman ya sake cewa "Ka yi hakuri zata gyara in sha Allah".
Ya numfasa ya ce "Tunda ta fad'a mini Anisa ta samu matsala da mijinta ta zo zata zauna a nan".
Ban boye Mata ba, na ce Mata a a tunda Baba Babba da ransa ga su Asad gunsu yafi cancantar ta tafi daga Nan ma Sai Su samu gangara Su dinga zuwa komai ya wuce. Ido da ido ta ce mini ba zai yiwu ba, gidana da dai ba zata zo ba tunda bana son a zo a co arziki. A gabana ta yi waya da Anisa ta ce ta zo Kano ta je gidan kawarta da yamma ta shiga jirgi ta tafi Maiduguri. Hakan Kuma aka yi.
Dama Kuma haushinta nake ji ta riga ta bata yaran nan, basa ganin mutunci y'anuwana, kullum fad'a musu take yi basa sonta. Ace yayata ta zo gidan nan ya'yana suka kasa zuwa su gaishe ta? Kuma tana kallonsu. To ni ba zata mini wnanan BAK'AR TA'ADA din ba, Babu dole. Kuma abin kaicon ma ita da kanta fa ta yi sanadin da y'ay'an basa ganin girmanta. Bata isa ta ce ku yi ko ku bari ba. Idan ka ji su lafiya to ita take bin ra'ayinsu. Matuƙar zata ce ba za su yi yadda suke so ba, to kuwa yanzu zaka ji suna cacar baki a tsakaninsu. To gaskiya na gaji, ta kwashesu su tafi inda zasu je tunda ita ta bata su, na gaji da wulakancin da rashin iya bada tarbiyarta. Save Restricted Content Bot, [Oct 31, 2025 at 12:11]
Ga k'ananun yaran ma sun fara d'aukar samfur."
Gabad'aya Sulaiman ya rasa abin cewa don kuwa al'amarin akwai tayar da hankali.
Kan dole ya shiga ba shi hak'uri tare da alak'awarin zai ja mata kunne, zata gyara.
Nauyin Sulaiman ne ya sanya shi hak'ura. Amma da babbar murya ya ce "Ka ja mata kunne, ka gargadeta ta kure hak'urina. Dole ne y'anuwana su zo gidana. Dole kuma ya'yana su mutuntasu, ta shiga hankalinta dan Wallahi a yadda suka kawo mini wuya zan iya bar mata su gabad'aya!
Save Restricted