Author : Hadiza D. Auta Category : Aysha Cool Novels
ba dad'i ne da shi ba idan aka taɓa shi mussaman raini baya son a raina shi tun suna yara haka yake da son girma.
Sanin halinsa da Faruku ya yi sai ya yi maza ya sassauta nasa fishin ya ce "Ka yi hak'uri ai yarinyace Sulaiman ma nawa yake a gabanmu bare su Bilki. Maganar bata sonka ma ai bata taso ba, don sai da so ake kishi kuma idan ka lura da kyau a8 kishi ne ya sanya ta yin wannan katobarar. Da bata sonka fa ba zata bika Calabar alhalin tana zaune a gida da sunan yaji ba. Dan Allah ka fahimce ta da kyau. Duk mutanen da suka yi fama da desperation sai ana yi musu uzziri don tunaninsu gabad'aya sauyawa yake yi. Sannan kai ma ina jan hankalinka with dew respect ka canja tsarin tarbiyar yara ba dan maigado ba sai don rayuwarsu ta gaba."
"To na ji Faruku na kuma yarda Zan gyara duk inda nake da laifi na kuma gode maka da baka yi mini fad'a a gabanta ba. Amma lallai ka fad'a mata ta yi hankali da ni, ta shiga taitayinta, don Wallahi idan ta ce zata dinga yi mini taurin kai da raini idan na murd'e mata, sai ta kasa fahimtar komai".
Da hanzari Faruku ya ce "A a Mai girma C P ba hakan za'a yi ba, ai yarinya ce ka dai yi hak'uri ba zata sake ba".
"Hmm ba wani yarinya kawai dai samun gu da iyashege ai dama Abida ta sha fad'a Bilki ta fita tsiya kawai fahimta ne ba'a yi ba, amma ni yanzu ai ina fahimtar tsiyatakunta bi da bi".
Faruku ya yi murmushi ya ce "Oga Asad na Bilki uban Bilki".
Dole ya murmusa tare da fad'in "Faruku kana da son kai ka ki yarda ka ga girman laifin kanwarka ko?".
Faruku ya ce "Na ga fa laifinta kuma na yi mata fad'a yanzu ma da na ji wannan laifukan nata zan sab'ar mata, na kuma yi maka alk'awarin ba zata sake yin zagi a gabanka bare ta yi maka maganganun da suke nufin ta zage ka".
Ya rausayar da kai ya ce "Allah yasa don gabad'aya yarinyar nan ta sauya"
Asad ya fad'a babu kuzari a tare da shi.
Faruku ya ce "In sha Allah ba zata sake ba, fatana ka ƙara hak'uri sannan ka rufe kofofin da ka bude da suke sawa jin ta gaji da zaman gidanka."
Daidai lokacin Aysha ta sauko ta tsugunna a gefensu da girmamawa ta ce "ABBA Ina kwana?"
Faruku ya ce "lafiya lau Aysha ya gida ya kannenki?"
Ta amsa da lafiya lau a sanyaye don gabad'aya yanzu bata jin dad'in zaman tunda dadynsu yake share su ita da Hafcy.
Kanta a k'asa ta ce "Dan Allah ABBA ka bawa Dady ya daina yi mana fishi. Ba zamu sake yin masa ba daidai ba".
Ta fad'a kuka na k'wace mata sosai.
Don tunda ya yi tafiyar nan wayar Bilkisu kawai yake amsawa ko ya k'ira. Ita kuma sai ta had'a shi da su Amal. Yau kuma da ya dawo ita kadaice a gidan duk sun tafi makaranta, yadda amsa mata gaisuwarta ya sake tayar mata da hankali ainun.
Jikin Faruku ya yi sanyi don kuwa da ya kud'ire sai ya turo musu Usman ya ci musu tunda jibi ake saka ran zai dawo Nigeria. Yana k'asar Faransa, shekara guda kenan da gwamnatin tarayya ta tura sojojin sama don koyon dabarun tsare sararin samaniyar k'asarmu.
Ya numfasa ya ce "To magana ta wuce amma lallai ki shiga cikin hankalinki, Maigado ai kanwarmu ce idan kuka ci mutuncinta kun ci namu, aurenta da Babanku ya yi kuma ya sake k'ara mata daraja a wajenku, amma shine kika made k'afar wandon cin mutuncinta, kin manta Idan kika taba ta daidai yake da kin tabamu gabadaya tunda ba ita ya kawo Kanta ba, aure ne ya kawo ta gidanku, bayan an shawo kanta da ƙyar. Aure ya zama tilas ya yi shi, sannan zai auri wacce yake so ne, ba wai wacce ake so ya aura ba. Ki faɗawa mai zuwa wajen na ki ya turo da magabatansa, Khadijah kam tunda a can mai son nata yake aurensu za'a daura musu su tare kawai. Wallahi kada na sake na ji ko da kallon banza kin yi sake yiwa Maigado bare kuma a kai ga jallin kina jagorantar kannenki kina kitsa musu shegantaka. Ya ya ina yabon hankalinki da illiminki sai kuma ki bamu kunya? Kullum da ke nake bugawa kaninki Ammar misali ashe kin sauya halayyar k'warai kin aro ta marasa da'a masu yin fito na fito da kwanciyar hankalin iyayensu? Ki yi maza ki gyara tun ba ki fara girban shukan da kike yi ba." Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:48]
Da kuka sosai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba".
"Yauwa Aysha Allah ya yi miki albarka, Allah ya jiqan mahaifiyarku, daina kuka kin ji, ya huce komai ya wuce."
Ta yi masa godiya ta tashi ta koma d'akinta.Tana jin nutsuwar zuciya, tana da tabbacin tunda ABBA ya ce Dady ya huce to babu haufin ya huce din.
Faruku ya mike yana fad'in"Bari na wuce "Allah yasa ba zan sake zuwa gidan nan da sunan bacin rai ba Oga Asad".
Murmushi Asad din ya yi tare da ce wa "Idan ta ji faɗanku ta kwantar da hankalinta ta ajiye tsiyatakun da ta aro ba zaka sake zuwa ba mana Baba Faruku".
Suka fita waje tare. Har jikin motarsa ya raka shi suka yi musabaha.
Yana tsaye yana jallon Faruku har ya fita daga gate din aka rufe sannan ya yi ciki. A ransa yana ayyana Duk cikin family lmsu ba wanda ya more irin Faruk.
Shine bai taba aikin gwamnati ba a rayuwarsa, amma kuma attajirine na sosai.
Sannan yafi kowa yiwa iyayensu hidima da jikinsa don shine yake da lokacin kansa, kullum yana tare da Baba yana yi masa hidima. Haka duk jinyar da zai yi Faruku na gefensa yana kula da shi. Shi kad'ai ne ya yi wannan sa'ar, su kam sai dai su yi da aljihunsu.
Hak'uri da sadaukarwarsa ya sanya hatta Momi da Baba kunyarsa suke ji bare kuma su. Yadda suke yi masa kacakaca ko su share shi basa taba yiwa Faruku haka.
Ya nisa ya ce "Allah ka sake son Faruku."
Ya shiga cikin gidan har ya zauna a falon sai ya tuna ya tashi da hanzari zuwa saman.
A d'akinta ya tarar da ita tana zaune a k'asan kafet ta mikar da ƙafafuwanta da suke a kumbure.
Murya ba amo ta amsa sallamarsa.
Ya zauna a k'asan yana fuskantar ta.
"Maigado ya aka yi kuma kika dawo alhalin kin ce Sai kin haihu, Babanki ma ya jaddada mini hakan?"
Takaici ya shak'e ta. Ta yi masa shiru amma idanuwanta sun cika da k'wallar takaicinsa.
Ya yi murmushi kad'an ya ce "To ya aka yi ne? Fasawa kuka yi ne ko ya ya ne?"
Murya na rawa ta ce "Na gode da muzancin da ka janyo mini Baban Bilkisu ".
Ya cije ya ce "Wacce magana kike yi ne haka. Me na yi miki?"
Hawaye ya k'wace ta ce "Akan me zaka ce mini yini kawai za'a yi ko kwana d'aya alhalin ba hakan bane a ranka."
Ya tattaro dukkan alhini ya yaba a fuskarsa tare da ce wa "Hakan ne a raina mana. To yadda kika dinga mak'ale mini ne ya sanya na fahimci kina buk'atar mu k'ara kwanakin, da na ce zamu k'ara kuma ba ki yi inkari akan haka ba. To menene laifina dan Allah, dole na yi mike ko kuwa kin tayar mini da hankali akan sai mun dawo?"
Ta kasa ce masa uffan tunda bata da bakin magana.
Ta girgiza kai ta ce ka koya mini darasi zan kiyaye a gaba".
Ya dauke kai ya ce " Allah ya nuna mana gaban lafiya."
Ya gyara zama ya ce "Ki saurare ni da kyau ki fahimci jawabin da zan yi miki da kunnen basira."
Ta goge fuskarta da tissue sannan ta nutsu sosia alamun shi take saurare.
Ya ce "Na mayar da Laura gida kamar yadda kike so, na sallami Jummai haka Charity goba zata koma inda na samar mata wani aikin, abin da yasa ma bata tafi ba kenan tuntuni, ba zai yiwu na rabata da wajen aikinta na farko ba, sannan yanzu na sallame ta ba tare da na samo mata wani aikin ba."
Bilki dai ido ta cigaba da zuba masa.
Ya zarce da fad'in "Yanzu za'a samo sabbin masu aiki, kin ga wanda za suzo basu saba da yara ba, bare su dinga girmama umarninsu sama da na ki."
Ta dan ji dis amma ta maze ta ce "Tom amma da ba'a kawo wasun ba, tunda dai akwai ma'aikata da yawa. Ga masu shara da wankewanke da goge goge, ina ganin hidimar girki a bar mini tare da taimakon Alti zamu yi komai" .
Ya ce "Kina iya shiga kicin duk sadda kike so, amma gaskiya ina son na ga ina da chef a gidana."
Zuciyarta d'aya ta ce "Ka manta nima girke girken na karanta? Sannan Alti ta iya girke-girke kala kala na ban mamaki".
Ya daure fuska ya ce "Alti ai ba zata dawo mini ba, tunda ta biki kuka tafi bata hana ki yi mini yaji ba, to na dakatar da ita. Wani irin al'amari ya daki zuciyarta. Nan da nan idonta ya ciko da hawaye ta ce "Baban Bilkisu ya haka kuma? Alti fa bata da kowa a duniyar nan sai ni, tun haihuwar Faruku muke tare da ita, yanzu idan an sallame ta ina zata je dan Allah?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:51]
Ta je koma ina ne".
Ya fad'a a dake.
Bilki ta zuba masa ido tana ayyana abubuwa masu yawa, ba k'aramin artabu zata sha da wannan mutumin ba lallai.
Ta tausasa harshe ta ce "Amma tun kafin mu yi aure sai da na ce Baba ya fad'a maka da ita zam zo gudun irin haka fa".
Kaitsaye ya ce "Na amince a farko ne ba tare da na yi tunanin komai a kanki ba. A yanzu da na gane inda kika dosa a kaina ba zai yiwu kuma na bi yadda kike so ba. Wallahi ba dan Baba ba, da kinsan kin zage ni a gabana. Amma tunda dole wani ya ci albarkacin wani na hak'ura na k'yale ki, amma Alti da Farha su zauna a gidan Baba wajen Momi."
Wannan karon bayan bugawa zuciya har y'ay'an cikinta sai da suka motsa da k'arfin gaske. Ta fashe da kuka mai tsananin gaske.
Takaici har makoshi. Cikin fitar hayyaci ta ce "Na rantse da Allah ba zan yarda ba, kawai ka sallame ni, dama ba sona kake yi ba tun filazal, ka samu abin da kake so shiyasa kake fito mini da halayya iri iri. Ko tafiyar nan da ka yaudare ni muka dade da kana sona ai ba zaka mini sanadin da zan muzanta irin haka ba, ka cigaba da cin zalina yadda ka saba tuntuni ".
Ya yi murmushin da babu nishadi ya ce "Ai da muka je din ba dole na yi miki ba, yanzu ma kuma ai ban daure ki ba, sai dai ki sani idan kika yi kuskuren sake saka k'afarki kika bar gidan nan, sai kin yi kuka na gaskiya don kuwa za ki dawo ne ki tarar da wata a cikinsa".
Kuka ya tsaya mata cak, ta zuba masa ido a maimakon ta ji tsanarsa yadda take ji a da, sai bata ji ba, ta kasa gane me take ji a ranta game da shi tunda babu so, kuna babu kiyayyar.
Ta tuna yadda suka rabu da Baba Babba da yadda ya tabbatar mata tashin hankalinsa ace bata zaune lafiya da mijinta, farincikinsa da burinsa bai wuce ace ta bada gudunmawar da zai daidaita zumuntarsu ba, bugu da ƙari Baba ya ce" Ba zai huce da ita ba sai ya ga Asad tsugunne a gabansa yana yi masa godiyar auren Bilkisu da aka ba shi. Wanne irin nauyi Baba ya dora mata, wacce irin biyyaya yake son ta yi, wanne irin dabaibayi Baba ya yi mata?
Zata yi komai, zata jure komai amma ban da rabata da Farha. Haka nan ba zata rabu da Alti ba har sai Faruku ya girma ta damka masa amanarta, shi take rikewa ita, yadda ta ci wahalarsa da rainonsa da ikon Ubangiji zai rik'e ta akan tsufanta a lokcin da zata fi koka rashin y'aya' da dangi.
Hawaye face face a idonta ta ce "Ayyah Baban Bilkisu amma alk'awari bai ce hakan ba. Magana biyu ba taka ba ce. Ni fa zan iya rabuwa da komai da kowa amma rabuwa da Farha mutuwa ce kad'ai zata gitta a tsakaninmu".
Ya sake harzuk'a ya ce "Asad ya rabaku alhalin ba mutuwa kika yi ba. Ai tunda kika gwada mini wulakanci kala kala akanta to ba zan zauna da ita ba. D'iyar Sulaiman ta fi ta kowa saboda rashin kara da wulakancinki ya kai k'urewa."
Ta yi sakare tana jin wani irin abu na mamayarta ashe shi a haka ya fassarata?
Murya ba amo ta ce "A haka ka dauka kenan? Ni fa Wallahi mantawa nake yi ba ni na haife ta ba. Gaskiya ni ba haka a raina, ban yi zaton zaka mini irin wannan fassarar ba, haka zalika ba zan iya rayuwa babu ita ba, na tsallake na bar y'anuwanta a Katsina amma ita kam tabbas ba zan iya ba. "
Ya sake girgiza kai ya ce "To zan ga yadda za'a yi na zauna da waɗanda bana son zama da su a gidana kuwa".
*Na gode sosia da soyayyarku ga rubutuna*.
*Na gode da uzzirinku*
*Surayya Gwaram*
✍️
Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:20]
*Assalamu alaikum barkanmu da lokaci!*
*Na gode da hak'urinku Allah ya saka da alheri ya bar zumunci*.
*Na gode da waɗanda suka mini addu'ar samun lafiya. Allah ya bamu lafiya gabad'aya*
*Zamu d'ora daga yau in sha Allah*
*Allah ya taimakemu gabadaya*.
*Godiya ta mussaman ha dukkan waɗanda suka siya labarin nan, Surayya ta gode Allah ya saka albarka da dukiyarki da ya'yanku*.
*Fatan alheri ga dukkan yan comments section na labarin Dingishin kwado Allah ya saka muku da alheri Allah yasa mu dade muna yi har a aljanna*.
*Wannan littafin na kudine biya 1k 238487685*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*
*08032773332*.
Bak'in ciki ya yi mata k'awanya ta rasa yadda zata yi sai kawai ta dage ta dinga zabga ihu da iyakacin k'arfinta.
A farkon ya dauka wasa ne amma da ya ga tana neman shidewa ya sanya ya bude baki ya ce "Wanne irin abu kike ne haka? Sai ka ce jahila?"
Bata saurare shi ba, ta cigaba da kukanta bilhakki.
Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi ya matsa kusa da ita da niyyar rik'e ta, ta goce ta ce "Kada ka taba ni, da ikon Allah na barka Yaya Asad dama dan a kirga mini aure ne ya sanya ka matsa ka kafe sai da ka aure ni".
Cikinta ya cure ya dunkule ta rasa yadda zata yi kawai ta kwanta rigingine tana murdaddawa tare da kuka mai gunji.
Ya kalli yadda cikin ya yi k'asa tamkar zai fito duniya a lokacin.
Murya ba amo ya ce "Ba za ki kwantar da hankalinki ba? Sai kin janyo mana sanadin wahala?
Cikin kuka ta ce "Da ikon Allah mutuwa zan yi na bar maka duniyar nan, in sha Allah sai na mutu na barka da sabbin jariran da zaka rasa mai basu nono, da ka raba ni da Farha gara na mutu na huta, in sha Allah sai ka sake samun sabbin marayu a gidanka"
Ta sake kecewa da matsanancin kuka.
Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi mussaman yadda ya ga ta jik'e da zufa duk sanyin AC da na iskar da standing fan take bayarwa a d'akin.
A firgice ya dagota, ta fisge ta sake komawa tana cigaba da ihu da murkukusu. A sanyaye ya ce "Ta shi mu yi magana na janye batuna to".
Ta sassauta kukan amma ta k'i tashin.
"Tashi mana!
Ya fad'a da sigar umarni.
Still ta k'i ko da motsi.
Ransa ya b'aci ya ce "Kin ga taurin kan nan na ki ne bana so, ba yadda za'a yi na ce da Rukayya ga yadda zata yi mini, ta kalle ni ta watsar da batuna. Amma ke ban isa da ke ba kwata kwata."
Hawaye na zuba a idanuwanta ta ce "Allah sarki ai sai ka bita makabartar ka cigaba da bata umarnin da ba zata sab'a maka ba."
Ya yi shiru yama rasa mai zai ce mata. Kan dole ya ce "Ki cigaba da yin fito na fito da ni".
Babu fargaba ta ce "ka cigaba da kwatanta ni da mai murabus".
Duk yadda ransa ya b'aci Sai da dariya mai sauti ta subuce masa.
Sai ya gintse fuska sai dariyae ta sake k'wacewa. Da ƙyar ya yi jarumtar danne dariyar ya ce "Yanzu Bilkisu duk yadda baiwar Allan nan take haba haba da ke ba zai saka ki dinga raga mata ba? Ya za ki ce mata maimurabus don ta mutu, ai bata mutu a zuciyata ba, saboda Allah fa?"
Ta d'auke kai tare da zumbura baki, a yadda take jin takaicinsa cikin jikinta ne cikas din da ya hana ta nada masa duka da sunan jinnu ne suka tashi. Don idan ta shammace shi ta dinga kai masa bugu da cizo kafin ya ankara ya ji jiki. Sai dai ba zata iya ba, tunda ita kanta fama take yi da kanta. Amma matuk'ar suna tare ya cigaba da yi mata batun mai murabus tare da nuna mata tafi ta yi masa biyayya zata dauki mataki.
Murya ba amo ta ce "Ya za'a yi ta mutu a zuciyarka tunda nima victim ce na shaida ba'a daina son first luv duk tsawon lokacin da za'a dauka ba'a tare kuwa".
Zuciyarsa ta harba. Gatse ta yi masa ko kuwa. To waye first luv din da take so Faruku ko wanccan sahalallen?
Ya ce "Da na janye batun rashin dawowar y'arki da Alti. Amma yanzu na jaddada dokar tunda babu nadama a lafuzanki".
Kuka ya sake k'wace mata duk da hakan sai da ta ce "Ba zan yi nadama ba, baka biyo ta hanyar da zan risina maka ba. Kuma in sha Allah sai ka fini nadamar wannan hukuncin da ka d'auka. Na yiwa Baba alk'awarin ba zan sake fita da sunan yaji ba, Sai Idan kai ka sake ni. Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:22]
Amma Wallahi yadda ka kuntata mini ka shirya fuskantar naka kuntatar zuciyar, babu kai babu farinciki